ÇáãÓÇÚÏ ÇáÔÎÕí ÇáÑÞãí

ãÔÇåÏÉ ÇáäÓÎÉ ßÇãáÉ : Sharhin arba'una hadith daga malam ja'afar allah yayi masa rahama hadisi na biyar


ØÇåÑ ÌÈÑíá Ïßæ
_12 _April _2014åÜ ÇáãæÇÝÞ 12-04-2014ã, 01:23 AM
ARBA'UNA HADITH (5) HADISI NA BIYAR
An karbo daga uwar Mu’uminina Ummu Abdullahi
Aishatu (R.A) tace manzon Allah (SAW) “yace wanda
ya kirkiro wani abu cikin lamarinmu wannan abin da
baya cikinsa to a mayar masa da kayansa.” Bukhari
( 2695) Muslim (1718) Aruwayar Muslim Wanda duk
ya aikata wani aiki daba umarninmu a kai an mayar
masa da shi.
SHARHI
Aisha daya ce daga cikin matan Annabi (S.A.W) ta
samu falalar kasanecwar matar Annabi (S.A.W) duk
cikin matan Annabi (S.A.W) Annabi yafi kaunar ta
sama da kowa don an tambayi Annabi (S.A.W) waka
fi so ? yace, Aisha, Aka ce “ aciki maza fa ? yace
Babanta Abubakar (Bukhari ( 3662) Amma duk da
Annabi (S.A.W) ya fi son Aisha baya zaluntar sauran
matansa saboda ita a hannunta Annabi(S.A.W) ya
cika ya bar duniya tace, “ Allah ya karbi ran Annabi
(S.A.W) a lokacin ina tallafe da shi a tsakanin
cinyoyina da kirjina kuma aka binne shi a dakinta
( Duba Bukhari (1389) da Muslim ( 2443) domin
bayan rasuwarsa aka ce ina za akai shi wadansu
sukace a kai shi masallaci wadansu suka ce “a kai shi
baki’a wadansu sukace “ akaishi wuri kaza sai
sayyadina Abubakar yace “ Annabi (S.A.W) ya fada
cewa babu wani Annabi da ya taba mutuwa face sai
an binne shi a in da Allah ya karbi ransa
1. [ Duba Al’musnad na abu Ya’ala (22)] ba daukar sa
a akai shi wani wuri don haka sai aka binne shi a
dakin Aisha wannnan falala ce ! don da ma Imamu
Malik ya rawaito a cikin Muwadda cewa Aisha ta yi
mafarkin taurari guda uku sun fada a cikin dakinta, sai aka wayi gari
sai ta tambayi abubakar sai yayi shiru ya kyale ta bai
ce mata komai ba. Annabi (S.A.W) ya bar duniya aka
binne shi a dakinta sai tace to wannan daya daga
cikin taurarin kenan biyun suna tafe
(Duba`Muwadda-Babu Ma ja’a fi dafnil mayyit) sai
sayyadina Abubakar kuma ya bar duniya shi ma sai
aka binne shi a dakinta kusa da kabarin Annabi
(S.A.W) Aisha tace, so nake in mutu a binne ni a
wajen “ sai kawai Umar dan khaddab ya nemi
Alfarma wajen Aisha cewa in ya riga ta mutuwa yana
so a binne shi a kusa da Abubakar ta amince in ya
riga ta a sa shi sai Umar ya riga ta mutuwa “Wannan
mafarki ya tabbata.
Ana ce mata Ummu Abdullahi ba don ta taba
haihuwa ba, sai dai kawai ya yarta mai suna Asma’u
bintu Abubakar, tana da da Abdullahi dan gidan
Zubair bin Auwam, daya daga cikin Mutum goma da
aka yi musu Albishir da Aljanna to wannan Abdullahi
dan Zubair bin Auwam din, shi ne Annabi (S.A.W)
yake jingina wa Aisha yace mata ummu Abdullahi.
Kuma daga wannan ne Malamai suka ce ya halattar
mutum yayi alkunya ko da bashi da da.
Lafazin “lamarinmu” Da yazo a wannan hadisi yana
nufin Musulunci ma’ana wanda ya kirkiro wani abu a
cikin addininmu na musulunci abin da baya cikin
musulunci (Duba Jami’ul Ulum wal-hikam na Ibnu
Rajab 1/63)
Wannan hadisi shi ne kashin bayan rusa dukkan
bidi’a a akan kasa duk abin da yake bidi’a ne wannan
hadisi ya rusa shi abin da duk mutum ya gina a kan
bidi’a, Allah ba zai ba shi lada ba, don ma ba zai
karba ba. Akwai wasu wadanda za su zo wajen
maganar bidi’a sai su ce to ai idan kace bidi’a
kamar ka ce kar mu hau keke kar mu hau babur kar
muyi amfani da dukkan wani abu kirkirarre don
wadannan abubuwan bidi’a ne, don lokacin Annabi
(S.A.W) babu su. Sai ka ce da shi, wadannan
al’amura da ka zana. Ba addinin ba ne su. Wani abu
ne na bukatar rayuwa. Annabi (S.A.W) kuwa ya rasu
duk abin da an kirkire shi ne sunansa addini, yace
“Wanda ya kirkiro cikin wannan….” Lafazin wannan
kuwa daya zo a nan, nuni ne zuwa Musulunci. Babu
wanda zai ce idan na hau babur daga nan wurin na
tafi Damaturu, ladana bai kai na wanda ya hau mota
ba; wanda ya hau mota gingimari ta katako, ladansa
bai kai wanda ya hau bambalasta ba. Babu wanda zai
fadi haka, duk bidi’a da ta shafi lamarin duniya,
kirkira kenan. A duniyance ka kirkiro mota, ka kirkiro
kwamfuta da dukkan abin da zai taimaka wa rayuwa
ta ci gaba, wannan shari’a ba ta hana ka ba, amma
kirkira ta fuskar addinin, ka kara ko ka rage, ka kawo
wani zikiri, ko wata falala, ko wata sallah, ko wani
sallo na istigfari, to wannan shari’a ta rushe. Ya
tabbata a sahihi Muslim (#2363), Annabi (S.A.W) an
tambaye shi cewa, ga wasu mutane suna yin kilili.
Shi ne su dauki dabino idan ya yi huda, su tsaga su
dauko irin nan. Su sa a nan, don ya ba da mai kyau.
Sai Annabi (S.A.W) yace, “Wannan ba zai yi amfani
ba.” Sai sahabbai suka ce, “Ai mun sha yi, kuma yana
amfani.” Sai Annabi (S.A.W) ya ce “Ku kuka fi ni
sanin lamarin duniya, ku je ku yi kayanku.” Saboda
wannan ba hailala bane, ba istigfari bane, don haka
baya jiran sai Annabi (S.A.W) ya bayar da umarni
kafin su je su yi. Domin duk abin da yake gwaji ya
tabbatar, idan aka hada sinadari kaza da kaza zai
bayar da kaza, wannan a duniyarka ka je ka yi ta
kirkire-kirkirenka, ba a hana ka ba. Amma a cikin
lamarin addini dole, ka bi fadin Allah.
( ﻭﻣﺎ ﺀﺍﺗﻜﻢ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﻓﺨﺬﻭﻩ ﻭﻣﺎﻧﻬﻜﻢ ﻋﻪ ﻓﺎﻧﺘﻬﻢ ﻭﺍﺗﻘﻮﺍ ﺍﻟﻠﻪ ﺇﻥ
ﺍﻟﻠﻪ ﺷﺪﻳﺪ ﺍﻟﻌﻘﺎﺏ) (7) (ﺍﻟﺤﺸﺮ7 : ).
(Duk abin da Mazon Allah ya zo muku dashi ku karbe
shi, abin daya hana ku, ku hanu. Lallai Allah mai
tsananin ukuba be.) {Al-Hashr: 7}
Kuma babu wata bidi’a mai suna kyakykyawa,
dukkan bidi’a batace..........
Allah yayi mana jagora