طاهر جبريل دكو
_28 _December _2013هـ الموافق 28-12-2013م, 10:25 AM
إِذَا السَّمَاءُ انْشَقَّتْ (1)
Idan sama ta kece.
وَأَذِنَتْ لِرَبِّهَا وَحُقَّتْ (2)
Kuma ta surari umurnin Ubangijinta tayi biyayya, kuma ya dace tayi biyayyan.
وَإِذَا الْأَرْضُ مُدَّتْ (3)
Kuma idan aka mike kasa.
وَأَلْقَتْ مَا فِيهَا وَتَخَلَّتْ (4)
Kuma ta jefar da abinda ke cikinta ta wofanta daga komai.
وَأَذِنَتْ لِرَبِّهَا وَحُقَّتْ (5)

Sharhi: idan sama ta kekkece kuma ta barke da giragizai a ranar kiyama, kuma tabi umurnin Ubangijinta cikin abinda Ya umurceta dashi na tsagewa, kuma ya dace gareta ta sallama ga umurninSa. Kuma idan aka shimfida kasa kuma aka fadadata kuma aka dandaka duwatsunta, a wannan ranan kuma ta fidda abinda ke cikinta na matattu kuma ta wofanta daga garesu, kuma ta sallama ga umurnin Ubangijinta cikin abinda Ya umurceta dashi kuma ya dace ta sallamawa umurninSa.
يَا أَيُّهَا الْإِنْسَانُ إِنَّكَ كَادِحٌ إِلَى رَبِّكَ كَدْحًا فَمُلَاقِيهِ (6)
Ya kai mutum! Lallai kai mai aikin wahal da kai ne zuwa ga Ubangijinka wahala mai tsanani, to kai mai haduwa da Shine.
Sharhi: ya kai mutum, lallai kai mai tafiyane zuwa ga Allah kuma mai aikata alheri ko sharri, sa'annan ka sadu da Allah ranar kiyama saiYa sakanta maka gameda ayyukanka da falalarSa ko adalcinSa.
فَأَمَّا مَنْ أُوتِيَ كِتَابَهُ بِيَمِينِهِ (7)
To amma wanda aka bawa littafinsa da damansa.
فَسَوْفَ يُحَاسَبُ حِسَابًا يَسِيرًا (8)
To za'ayi masa hisabi hisabi mai sauki.
وَيَنْقَلِبُ إِلَى أَهْلِهِ مَسْرُورًا (9)
Kuma ya juya zuwaga iyalansa (a aljanna) yana mai raha.
Sharhi: amma wanda aka bashi littafinsa da hannunsa na dama, alhali yana imani da Ubangijinsa, to da sannu za'a yi masa hisabi hisabi mai sauki kuma ya koma ga iyalansa a cikin aljanna yana cikin farin ciki.
وَأَمَّا مَنْ أُوتِيَ كِتَابَهُ وَرَاءَ ظَهْرِهِ (10)
Kuma amma wanda aka baiwa littafinsa daga bayan bayansa.
فَسَوْفَ يَدْعُو ثُبُورًا (11)
To da sannu zai rikan kiran halaka.
وَيَصْلَى سَعِيرًا (12)
Kuma ya shiga (wutan) sa'ir
إِنَّهُ كَانَ فِي أَهْلِهِ مَسْرُورًا (13)
Lallaine shi ya kasance (a duniya) a cikin iyalansa yana mai raha.
إِنَّهُ ظَنَّ أَنْ لَنْ يَحُورَ (14)
Kuma lallaine yayi zaton bazai komo (ga Allah) ba.
بَلَى إِنَّ رَبَّهُ كَانَ بِهِ بَصِيرًا (15)
Na'am! Lallaine Ubangijinsa Ya kasance mai gani gareshi.
Sharhi: amma wanda aka bawa takardan aikinsa daga bayan bayansa alhali yana mai kafircewa Allah, to da sannu zai rika kiran halaka da tabewa, kuma ya shiga wuta yana mai dandanar zafinta. Lallai shi (kafirin) ya kasance a cikin iyalansa a duniya mai fara'a da ruduwa, baya tunani gameda karshen (al'amura) lallai shi yayi zaton cewa bazai koma ga Mahaliccinsa ba yana rayayye domin hisabi. Na'am! Da sannu Allah zai mayar dashi kamar yadda Ya fareshi kuma Ya sakanta masa akan ayyukansa, lallai Ubangijinsa Ya kasance mai gani kuma masani ga halinsa tun daga ranan halittarsa har zuwa ranar tashinsa (daga kabari).
فَلَا أُقْسِمُ بِالشَّفَقِ (16)
Ina rantsuwa da shafaki.
وَاللَّيْلِ وَمَا وَسَقَ (17)
Da dare da abinda ya kunsa.
وَالْقَمَرِ إِذَا اتَّسَقَ (18)
Da wata idan (haskenta) ya cika
لَتَرْكَبُنَّ طَبَقًا عَنْ طَبَقٍ (19)
Lallaine kuna hawan wani hali daga wani hali.
Sharhi: Allah (madaukaki) Yayi rantsuwa da launin ja (wato shafaki) wanda ke kasancewa a kusurwan (sama) yayin faduwar rana, haka kuma Ya (rantse) da dare da abin da ya tattara na dabbobi da kwari da halittu masu guba da sauransu, hakama Ya (rantse) da wata yayinda haskenta ya kammala. Lallaine zaka hau matakai masu yawa, halaye mabanbanta, daga digon maniyyi zuwa gudan jini zuwa gudan tsoka zuwa busan rai zuwa mutuwa zuwa tayarwa (bayan mutuwa). Kuma baya halatta ga abin halitta yayi rantsuwa da wanin Allah, da zai aikata hakan kuwa da yayi shirka.
فَمَا لَهُمْ لَا يُؤْمِنُونَ (20)
To me ya samesu ne basu yin imani?
وَإِذَا قُرِئَ عَلَيْهِمُ الْقُرْآنُ لَا يَسْجُدُونَ (21)
Kuma idan aka karanta Alkur'ani akansu basuyin tawalu'u ?
بَلِ الَّذِينَ كَفَرُوا يُكَذِّبُونَ (22)
Ba haka ba wadanda suka kafirta sai karyatawa sukeyi.
وَاللَّهُ أَعْلَمُ بِمَا يُوعُونَ (23)
Alhali, Allah Shine mafi sani game da abinda suke tarawa.
فَبَشِّرْهُمْ بِعَذَابٍ أَلِيمٍ (24)
Saboda haka kayi musu bushara da azaba mai radadi.
Sharhi: to menene zai hanasu imani da Allah da ranar karshe bayan an bayyana musu ayoyi? Kuma me ya samesune, idan aka karanta musu Alkur'ani basuyin sujjada ga Allah, kuma basu sallamawa abinda ke cikinsa (wato Alkur'ani), kawai dabi'ar wadanda suka kafirta shine karyatawa da sabawa gaskiya. Allah Shine mafi sani gameda abinda suke boyewa a cikin zukatansu na kangarewa, tareda saninsu gameda cewa abinda ya zo a cikin Alkur'ani gaskiyane. Saboda haka ya kai wannan manzon, kayi musu bushara da cewa Allah (mai girma da buwaya) Ya riga Ya tanada musu azaba mai cutarwa.
إِلَّا الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَهُمْ أَجْرٌ غَيْرُ مَمْنُونٍ (25)
Face ga wadanda sukayi imani kuma suka yi ayyukan kwarai, suna da wani sakamako wanda baya yankewa.
Sharhi: saidai wadanda suka yi imani da Allah da manzonSa kuma suka aikata abinda Allah Ya farlanta musu, suna da sakamako a lahira wanda baya yankewa kuma babu tawaya (a cikinsa).