طاهر جبريل دكو
_18 _March _2019هـ الموافق 18-03-2019م, 07:22 PM
بسم الله الرحمن الرحيم
HARAMCIN ASKE GEMU
Dan'uwana Mai girma: ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATUL LAHI WA BARAKATUHU.
Ina gabatar maka da kyautar wadannan kalmomin, kuma ina fatan su samu gurbi a cikin zuciyarka.
Dan'uwana Masoyi: Ka san lallai Annabi SAW shine abin koyinmu, kuma wajibi ne akanmu mu bishi ta hanyar aiki da umurninsa da nisantar haninsa, kuma hakika annabi SAW ya ce: "Ku sabawa mushrikai ku cike gemu ku rage gashin baki", saboda haka; aske gemu haramun ne da ijma'in mazhabobi guda hudu, kuma ya saba wa shiriyar Manzanni, kuma yin kwaikwayo ne ga kafirai, kuma ya zo a cikin hadisi: "Wanda ya kwaikwayi wasu mutane to yana daga cikinsu", Kuma babu wani Musulmin da yake aikata hakan a zamanunnukan da suka gabata.
Sai ka yi da'a ga Annabinka, kuma ka rika kwaikwayonsa; domin a tayar da kai karkashin tutarsa, kuma ka sha daga dausayinsa.
Kuma ka rika saba wa son zuciyarka; domin ka rabauta da shiga Aljannonin ni'ima.