طاهر جبريل دكو
_10 _May _2018هـ الموافق 10-05-2018م, 08:30 PM
ABABEN DA BASU KARYA AZUMI ما لا يفطر
ABABEN DA BASU KARYA AZUMI
(ما لا يُفطِّر)
Lamura dayawa ne Mai yin azumi ke bukatar amfani da su, Kuma zai iya zaton cewa, suna karya azumi, amma ba haka lamarin ya ke ba;
Misalinsu, shine
KURKURAN BAKI, DA SHAKA-RUWA A HANCI, ba tare da zurfafawa ba.
DA SANYA KWALLI. DA 'DAN'DANAR ABINCI, Idan akwai bukatar hakan.
Daga cikinsu, akwai TONAN HAKORA, DA CIRE HAKORA, DA TSAFTACE SU, da aswaki ne, ko brosh, tare da kiyaye isar makilin cikin makoshi. Tare da cewa, abinda yafi tsantseni dangane da lamarin makilin shine yin amfani da shi, da dare.
Kuma daga cikinsu, akwai ABIN WANKE KUNNE, DA ISKAR DA AKE FESAWA DOMIN MAGANIN ASMA KO MATSALAR NUMFASHI (INHELA), DA KWAYOYIN MAGANI, WADANDA AKE IJIYE SU KARKASHIN HARSHE, DOMIN SU BADA KARIYA KAN MATSALOLIN CIYON ZUCIYA. DA KUMA ISKAR DA AKE MAGANIN WASU MATSALOLI DA SUKE CIKIN BAKI. Saidai haramun ne mutum ya yi gangancin hadiye wani abu daga cikin abinda ya gabata, ko
isar da shi ga makoshi.
HAKA SUMA ABABEN DA AKE SANYA SU A CIKIN MAHAIFA DOMIN YIN MAGANI KO WANKI A GARE SHI, DA MAKAMANCIN HAKA (BASU KARYA AZUMI), HAKA SUMA ALLURAI DON MAGANI GA FATA KO JIJIYOYI, in banda alluran da suke dauke da abinci, wadannan su kam suna karya azumi.
Haka ababen da suke shiga cikin jiki, TA HANYAR FATAR JIKIN TA TSOTSE SU, Kamar nau'ukan mayi, da sauran ababen shafawa, da mannawa na magani, da shigar da NA'URAR GANIN MATSALAR DA TAKE CIKIN CIKI, TA HANYAR FATAR CIKI, KO TA CIKIN TUMBI, MATUKAR BA A HADA DIRIB NA RUWA KO WASU SINADARAN NA DABAN BA.
Hakika Allah ya saukake mana addininsa, sa'annan ya dauke duk wani abu mai sanya kunci, Kuma Annabinmu –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya yi gaskiya cikin fadinSa:
((بُعثتُ بالحنيفية السَّمْحة)).
Ma'ana: "An turo ni da mikakken addini, mai sauki"
ABABEN DA SUKE LALATA AZUMI مبطلات الصيام
ABABEN DA SUKE LALATA AZUMI
(مبطلات الصيام)
Azumi wanda shine bauta wa Allah, ta hanyar kamewa daga ci da sha da jima'i, daga fudowar alfijir na gaskiya, har zuwa faduwar rana.
Kuma WAJIBI NE Musulmi ya kiyaye azuminsa daga ababen da za su lalata shi, wanda kuma sune, ci da sha, da abinda ke daukar ma'anarsu daga ababen da suke baiwa jiki abinci, kamar ruwan da ake dorawa ko allurai masu dauke da abinci, da daukan jini da karinsa, da yin jima'i, da fitar maniyyi ba a cikin barci ba, ko ta hanyar wasa da al'aura (istimna'i), da makamancinsu.
Amma yin mafarkin saduwa (da fitar maniyyi), to lallai basu karya azumi da ijma'in maluma. Haka shima fitan maziyyi –ga zancen da yafi inganci-.
Haka Yin Amai –da ganganci-, Amma idan amai ya rinjaye shi, to azuminsa ingantacce ne, saboda fadinSa –sallal lahu alaihi wa sallama-:
"من ذرعه القيء فليس عليه قضاء، ومن استقاء عمدًا فليقضِ". رواه أبو داود والترمذي وصححه الألباني في إرواء الغليل.
Ma'ana: "Wanda amai ya rinjaye shi, babu ramuko akansa, Wanda kuma ya janyo amai da ganganci, to ya rama azumi" Abu-dawud da Tirmiziy suka ruwaito, kuma Albaniy ya inganta shi, a cikin littafin Irwa'ul galil.
Yin Kaho, haka kuma bada taimakon jini, Kuma duk wanda ya bukaci bayar da taimakon jini a cikin yini, to ya karya azuminsa, sai kuma ya biya azumi daya, a madadinsa.
Yana daga abinda ke lalata azumi, da ijma'in maluma Fitan jinin haila ko haihuwa a cikin kowane dakika cikin yini, koda kuwa fitan nasa gabanin faduwar rana ne, da minti daya.
Wanda ya aikata wani abu daga cikin ababen da suke karya azumi, yana mai jahiltar hukuncin, ko a halin manta shi, ko a halin tilascin da aka masa, to azuminsa ingantacce ne. sai dai haila da jinin biki (nifasi)su kam suna lalata azumi ta ko-yaya.
Lallai azumi yana da FARILLAI da IYAKOKI, wadanda wajibi ne a kiyaye su. Kuma Allah Ta'alah yana cewa a karshe-karshen jerin ayoyin azumi:
"تلك حدود الله فلا تقربوها، كذلك يبين الله آياته للناس لعلهم يتقون"، [البقرة: 187].
Ma'ana: "WADANCAN SUNE IYAKOKIN ALLAH, KADA KU KUSANCE SU, KAMAR HAKA NE ALLAH KE BAYYANA AYOYINSA GA MUTANE, LA'ALLA SU SAMU TAKAWA", [Bakara: 187].