المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : A irin wannan wata na sha'aban ! (في مثل هذا الشهر -شعبان-)


طاهر جبريل دكو
_5 _May _2018هـ الموافق 5-05-2018م, 02:46 PM
A IRIN WANNAN WATA NA SHA'ABAN ! (في مثل هذا الشهر -شعبان-) (http://abubakarhamza.blogspot.in/2018/05/a-irin-wannan-wata-na-shaaban.html)

A IRIN WANNAN WATA NA SHA'ABAN !
(في مثل هذا الشهر -شعبان-)
Watan Sha'abana, shine wata na takwas daga cikin watannin shekarar hijira. Kuma a cikinsa ababe dayawa na tarihi na-musamman, suka auku,

A SHEKARA TA 2 BAYAN HIJIRA Allah ya farlanta azumin watan Ramadana akan musulmai, sai hakan ya mayar da azumi ya zama daya daga cikin rukunan guda biyar wadanda aka gina musulunci akansu.

A CIKIN SHA'ABAN NA SHEKARA TA 3 BAYAN HIJIRA Aka haifi Alhasan bn Aliyu –Allah ya kara yarda akansu-; wato jikan Manzon Allah –sallal lahu alaihi wa sallama-, kuma daya daga jagorori biyu na samarin Aljannah.

A RANAR BIYAR GA WATAN SHA'ABAN, A SHEKARAR HIJIRA TA BIYAR Aka haifi Alhusaini bn Aliyu –Allah ya kara yarda a gare su-; wato jikan Manzon Allah –sallal lahu alaihi wa sallama-, kuma daya daga jagorori biyu na samarin Aljannah.

KUMA A WATAN SHA'ABAN NA SHEKARA TA BIYAR KO KUMA SHIDA BAYAN HIJIRA Labarin azamar wasu mushirkai kan yakar Manzon Allah –sallal lahu alaihi wa sallama- ya iske shi, wanda hakan yazama sababin yakin da ke kira da YAKIN BANIL MUSDALIK kuma a wannan yakin Musulmai suka ci nasara akan mushirkai.
KUMA A WATAN SHA'ABAN NA SHEKARA TA CASA'IN DA HUDU (94), AKA HAIFI IMAM LAISU BN SA'AD BN ABDURRAHMAN ALFAHMIY ALMISRIY, wato babban malamin hadisi, masanin ilimin fikihu mahardaci.

KUMA A 25 NA WATAN SHA'ABAN TA SHEKARA TA 625 daga hijira, aka haifi babban malamin fikihu na mazhabar ImamAs-Shafi'iy, Wato, Takiyyudden Muhammadu bn Aliyu bn WAhab, wanda aka sanshi da lakabin Ibnu-dakik Al-id, ma'abucin wallafe-wallafe sanannu, da kuma tarihi abin yabo.

A KUMA RANAR 12 GA WATAN SHA'ABAN NA SHEKARA TA 672 ta hijira, ya rasu a garin Damaskas, Malamin da yayi zurfi cikin ilimin harshen larabci, da sanin fiskoki mabanbanta da ake karanta Kur'ani da su; wato ilimin kiraa-at, wanda shine Imam Ibnu-Malik, ma'abucin shahararrun wallafe-wallafe, daga cikinsu Alfiyyar Ibnu-Malik.

Watan Sha'aban wata ne da aka haifi jigajigan Maluma da manyan mutane.

2018/05/02
YA MAI NEMAN ALKHAIRI; KA SHIRYA!! (يا باغيَ الخير استعدْ) (http://abubakarhamza.blogspot.in/2018/05/ya-mai-neman-alkhairi-ka-shirya.html)

YA MAI NEMAN ALKHAIRI; KA SHIRYA!!
(يا باغيَ الخير استعدْ)
'Yan kasuwa, ma'abuta kasuwanci su kan yi cikakken shiri, a lokutan kasuwanci, domin fatan samun fiyayyen riba.
Su kuma Muminai, suna yin shiri domin fiskantar watan azumi na Ramadhana (wato, WATA MAI TARIN ALBARKA) da nau'ukan bauta, Sai su
1- Yawaita yin azumi a Sha'aban, domin ya kasance shiri ga azumtar watan Ramadana.
2- Da kuma yin Tuba ta gaskiya, da ficewa daga ayyukan zunubai, da mayar da kayan da suka zalunta, izuwa ga Ma'abutansu.
3- Da yafiya da yin sulhu, da kawar da dukkan sabani, da warware jayayya, domin mu kasance mun cancanci samun gafarar Allah.
4- Da kuma, koyan hukunce-hukuncen azumi, da laddubansa, da ababen da suke bata azumi, da abinda ke halatta ga mai azumi, da wanda baya halatta, domin azuminmu ya kasance ingantacce.
5- Da nisantar ayyuka masu shagaltarwa, gwargwadon iko, domin mu samar da lokacin yin ibadodi a cikin watan Ramadana, Kuma hakika Sufyan As-Sauriy idan watan azumi ya shigo, ya kan bar kowane abu; domin ya fiskanci karatun Alkur'ani.
6- Kuma lallai watan azumi, dama ce mai matukar girma domin nisantar munanan al'adu, da azizita halaye ababen yabo, Allah Ta'alah ya ce:
(يا أيها الذين ءامنوا كُتب عليكم الصيامُ كما كُتب على الذين من قبلكم لعلكم تتقون) [البقرة: 183].
Ma'ana: "YA KU WADANDA SUKA YI IMANI AN WAJABTA AZUMI AKANKU, KAMAR YADDA AKA WAJABTA SHI GA WADANDA SUKE A GABANINKU, TSAMMANINKU ZA KU SAMU TAKAWA" .
SHA’ABAN WATAN DAGA AYYUKAN BAYI NA SHEKARA GA UBANGIJIN TALIKAI فضائل شعبان (http://abubakarhamza.blogspot.in/2018/05/shaaban-watan-daga-ayyukan-bayi-na.html)

SHA’ABAN WATAN DAGA AYYUKAN BAYI NA SHEKARA GA UBANGIJIN TALIKAI
فضائل شعبان
Watan Rajab ya shude, Sai Sha’aban ya fiskanto
Kuma an sanya masa suna SHA’ABAN ne, saboda yadda kabilu ke yin kungiya-kungiya domin fita yaki da kai farmaki, bayan ficewan watan Rajab Mai alfarma (wanda ba a yaki cikinsa).
Sha’aban, Me ya sanar da kai abinda ake kiransa: WATAN SHA’ABAN?
Wata ne na yi tanadi da shiri ga watan Ramadhana,
Watan yawaita azumi ne (nafila), da tilawar Alkur’ani; domin Annabi –sallal lahu alaihi wa sallama- ya kasance yana yawaita azumi a cikinsa, saboda wata ne da mutane ke gafala akansa, kuma shine watan da ake daga ayyukan bayi na tsawon shekara; gaba dayansu; Usamah bn Zaid –radiyal Lahu anhu- yana cewa:
“NACE: YA MANZON ALLAH, BAN GA KANA AZUMTAR WANI WATA BA, IRIN YADDA KAKE AZUMTAR WATAN SHA’ABAN, SAI YA CE: SABODA SHI, WATA NE DA MUTANE KE GAFALA AKANSA, DA KE TSAKANIN RAJAB, DA WATAN RAMADHANA, KUMA SHINE WATAN DA AKE DAGA AYYUKAN BAYI GA UBANGIJIN TALIKAI; SAI NAKE SON A DAGA AIKINA GARE SHI ALHALIN INA AZUMI”.
Ibnul kayyim -rahimahulLahu- yace:
“LALLAI AYYUKAN SHEKARA ANA DAGA SU ZUWA GA ALLAH NE A CIKIN WATAN SHA’ABAN”.
Kuma Magabatan kwarai sun kasance, suna yawaita karatun Alkur’ani a cikin watan Sha’aban, domin a cikinsu akwai wadanda suke rufe shagunansu domin su shagaltu da yawaita karatun Alkur’ani;
Salamah bn Kuhailin yana cewa:
“ANA FADIN CEWA: WATAN SHA’ABAN, WATAN MASU KARATUN KUR’ANI NE”.
Kuma Magabatan kwarai sun kasance suna kwadayin taimakon miskini a cikin watan Sha’aban, domin ya fiskanci watan Ramadhana da abinda zai jiyar da iyalansa da ‘ya’yansa dadi; domin an ruwaito daga wasu daga cikin magabantan kwarai cewa, sun kasance idan watan Sha’aban ya shigo, sai su fitar da zakkar dukiyarsu, domin su karfafa wa mai rauni da miskini, akan azumtar watan Ramadhana.
Kuma a cikin watan Sha’aban akwai sabar wa Rai, da shirya ta, saboda ta iya fiskantar watan Ramdhana da mafificin zantuka da kuma ayyuka.

YAYA ZAKA SAMAR DA YARO MAI SON KARATU كيف تصنع طفلا قارئًا؟ (http://abubakarhamza.blogspot.in/2018/05/yaya-zaka-samar-da-yaro-mai-son-karatu.html)

YAYA 'DANKA ZAI ZAMA MAI YAWAN KARANCE-KARANCE?
(كيف تصنع طفلا قارئا)
1- [B]Sanin dabarun hadda, da fahimta, da kwankwadar ilimi.
2- Yarda da kai da samun karfin hali, da sanin kai.
3- Kyautata karfin kwakwalwa.
Damammaki ne da kuma dabarun wanda 'danka zai koye su; idan har dan yaro ne mai yawaita karatu, mai kuma son littafafai.
Sai ka yi kwadayi ya zama hakan, ta hanyar///

a. Samar wa yaro littatafai da majalloli da kissoshi masu kayatarwa a cikin hotuna wadanda suka dace da irin shekarunsa, a cikin dakinsa, ko inda hannayensa za su iya dauka.
b. Yin tarayya da shi cikin karance-karancen littatafansa da kissoshin da ya ke so.
c. Tafiya da shi dakunan karatu ko laburare, da karfafa shi kan zaban wasu kissoshi da kansa.
d. Amsa masa wasu daga cikin tambayoyinsa, da kuma nusar da shi wasu littatafan da za su amsa masa sauran tambayoyin.
e. Yin amfani da salo mai cike da hikima, ta hanyar hakaito masa kissoshi masu dadi, sai kuma a nuna masa littatafan da suka kunshi kissoshin da suka fi nasan dadi.
f. Karfafar yaro da kyaututtuka, da kuma kalmomin karfafa guiwa da yabawa, ga dukkan cigaban da yaron ya samu ta bangaren karatu.
g. Sai kuma kulla alaka tsakanin nashadodin da yaron ya ke so, da karance-karance.
Kuma da wadannan hanyoyin ne yaronka zai mallaki mabudan ilimi da masaniya, Da fatan ya samu kansa cikin wadanda Allah ke magana akansu cikin fadinSa: "ALLAH NA DAUKAKA DARAJOJIN WADANDA SUKA YI IMANI, DAGA CIKINKU, DA NA WADANDA AKA BAIWA ILIMI" [Mujadilah: 11].

WATAN AZUMI RAMADANA YA KARANTO واقترب شهر رمضان (http://abubakarhamza.blogspot.in/2018/05/watan-azumi-ramadana-ya-karanto.html)

WATAN AZUMI YA KUSANTO
(واقترب رمضان)
'Yan kwanaki kadan suka rage gabanin shigan watan azumi!
LAMURAN DA SUKA DACE GA MUSULMI YA KULA DA SU A WATAN SHA'ABAN
DAGA CIKINSU: Akwai biyan bashin watan azumin da ya shude; Duk wanda akwai ramukon azu,im Ramadanan da ya shude, sakamakon halin tafiya ko jinya ko haila da makancinsu, to sai yay i gaggawan biyan wannan bashin gabanin shigowan watan Ramadana, saboda A'ishah –Allah ya kara yarda a gare ta- ta ce:
(كان يكون علي الصوم من رمضان، فما أستطيع أن أقضيَه إلا في شعبان).
Ma'ana: "NA KASANCE, AZUMI YA KAN KASANCE A KAINA, NA RAMADANA, SAI NA KASA SAMUN DAMAN BIYANSA, SAI A WATAN SHA'ABAN".
Kuma baya halatta a yi bikin daren tsakiyan watan Sha'aban (15), ko kebance wannan daren da wata ibada ta musamman, Imam An-Nawawiy –Allah ya yi rahama a gare shi- yake cewa, dangane da sallar RAGA'IB da ake yinta a watan Rajab, da sallar daren tsakiyan watan Sha'aban raka'oi dari:
((وهاتان الصلاتان بدعتان منكرتان)).
Ma'ana: "Wadannan salloloin guda biyu, bidi'oi ne ababen kyama".
Kuma yana daga cikin hadisai raunana na karya wadanda suka yadu, kan falalar wannnan sallah:
(إذا كانت ليلة النصف من شعبان فقوموا ليلها وصوموا نهارها) ((السلسلة الضعيفة، برقم: 2132، قال الشيخ الألباني: ضعيف جدا أو موضوع)).
Ma'ana: "IDAN DAREN RABIN WATAN SHA'ABANA -15- YA ZO, SAI KU KWANA KUNA SALLAR DAREN, KUMA KU AZUMCI YININSA".
Shekh Albaniy yake cewa (a cikin littafin AS-SILSILATUS SAHIHAH, 2132): Hadisi ne mai rauni sosai, ko na karya.
Da kuma hadisin da ke cewa:
(خمس ليال لا تُرد فيهن الدعوة: أول ليلة من رجب، وليلة النصف من شعبان، وليلة الجمعة، وليلة الفطر، وليلة النحر). ((السلسلة الضعيفة، برقم: 1452، قال الشيخ الألباني: موضوع)).
Ma'ana: "DARARE GUDA BIYAR, BA A KIN AMSA ADDU'A A CIKINSU; DAREN FARKO A WATAN RAJAB, DA DAREN TSAKIYAN WATAN SHA'ABAN, DA DAREN JUMA'A, DA DAREN SALLAN AZUMI, DA DAREN SALLAR LAYYAH".
Shekh Albaniy yake cewa (a cikin littafin AS-SILSILATUS SAHIHAH, 1452): Hadisi ne na karya.
Shekh IbnuBazin –Allah yay i rahama a gare shi- ya ce:
((كل الأحاديث الواردة فيها موضوعة وضعيفة لا أصل لها)).
Ma'ana: ((Dukkan hadisan da suka zo kan wannan dare, na karya ne, da masu rauni, wanda basu da wani asali)).

Sannan idan karshen watan Sha'aban ya zo, to baya halatta ya azumci rana daya ko biyu na karshen watan Sha'aban, saidai idan ya dace da yi9nin da mutum ya saba yin azuminsu, ko kuma idan ya kasance cikin ramukon azumin Ramadana, saboda fadinsa –عليه الصلاة والسلام-:
((لا تقدموا رمضان بصوم يوم ولا يومين، إلا رجل كان يصوم صومًا فليصم)). متفق عليه
Ma'ana: "KADA KU RIGAYI WATAN RAMADANA DA AZUMIN YINI DAYA, KO YINI BIYU, SAIDAI MUTUMIN DA YA KASANCE YAKE YIN WANI AZUMI, TO YA AZUMCE SHI". Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma babu laifi, a rika yin murna, kan shigowan watan Ramadana; saboda abinda ke cikin shiga watan na ni'ima da alkhairi.