تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : Sharhin tambayoyin kabari uku الأصول الثلاثة


طاهر جبريل دكو
_10 _February _2018هـ الموافق 10-02-2018م, 02:00 PM
SHARHIN TAMBAYOYIN KABARI UKU الأصول الثلاثة



SHARHIN TAMBAYOYIN KABARI GUDA UKU


Lallai yabo na Allah ne; muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kayukanmu, da munanan ayyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar, babu mai batar da shi, Wanda kuma ya batar, babu mai shiryar da shi.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke, bashi da abokin tarayya.
Ina kuma shaidawa lallai annabi Muhammadu bawanSa ne ManzonSa ne.
Bayan haka;


MATASHIYA GABANIN SHARHI


MAWALLAFIN LITTAFIN USULUS SALASA
Shi ne, Shehin Malami da ake masa lakabi da shehin musulunci, mujaddadin da'awa zuwa ga Tauhidin Allah, Shugaba; abin koyi, jagora; Muhammadu bn Abdulwahhab, dan Sulaiman, daga kabilar Tamim.
Alkunyarsa: Abul-Husain.
An haife shi, a garin Uyaynah, a shekarar hijira ta 1115H.
Ya yi wafati a garin Dir'iyyah, a shekarar 1206H.


ME YASA MUKE KARANTA TAUHIDI
(ILIMIN SANIN YADDA AKE KADAITA ALLAH)?
Saboda Allah ya halitta mu, domin kadaita shi.
Saboda Allah baya karbar kowane aiki, sai idan an kadaita shi da shi.
Babu mai shiga Aljannah sai mai tauhidi.
Sababi ne na yawaitar lada.
Sababi ne na kankare laifuka.
Sababi ne na samun shiriya, da tabbatuwan zaman lafiya.
Sababi ne na samun natsuwa.
Sababi ne na samun ceton Annabi صلى الله عليه وسلم



DALILAN DA SUKA SABBABA ZABAN WANNAN LITTAFI, A FARKON NEMAN ILIMI
Yadda Magabatanmu na-kwarai, da Malumanmu; na Ahlus-Sunnah Wal Jama'ah su ka baiwa wannan littafi mai albarka kulawa; saboda abinda ke cikinsa na amfani da fa'idodi masu girma, wanda hakan ya mayar da shi, wani ginshikin da 'Dalibin ilimi zai fari tafiyarsa ta kan wannan littafi, ya kuma gina neman ilimin shari'a da ya ke yi akan wannan littafi, Wannan ya sanya mu –a wannan zamanin- mu ke koyi da su, kuma muke binsu sau-da-kafa, akan wannan manhaji.


* Suma sauran mutane –wadanda ba daliban ilimi ba- ba za su dena bukatar wannan littafin ba, da kuma abinda littafin ya ginu akansu na-ginshikai, wadanda babu makawa, dole Mutum ya yi imani da su, irin imanin da baya karbar kokwanto da shakku.




WANNAN LITTAFIN –DA SAURAN LITTATAFAN SHEHIN MUSULUNCI; MUHAMMADU BN ABDULWAHHAB رحمه الله- YA YI FICE DA WADANNAN:


Saukin ma'ana da fitowa fili
Ambaton mas'aloli tare da dalilansu
Hada mas'aloli da jeranta su, da fadin adadinsu, gabanin fara sharhinsu
Yawaita addu'a ga mai karanta ko sauraron littatafansa.



BAYANIN MENENE الأصول الثلاثة
"Usulus Salasa", a takaice, sune: Tambayoyin kabari guda uku;
Wanene Ubangijinka?
Menene Addininka?
Wanene Annabinka?



WANE FA'IDA ZA MU SAMU, IDAN MUKA KARANTA "USULUS SALASA"
Lallai idan ka karanci wadannan ginshikan uku, sai ka yi aiki da su, sa'annan ka yi da'awarka zuwa gare su, sai kuma ka yi hakuri kan, neman ilimi, da aiki da shi, da kuma da'awa zuwa ga hakan, to lallai –da izinin Allah- za ka iya amsa tambayoyin kabari.
























ABINDA KE CIKIN LITTAFIN "USULUS SALASA"
Wannan littafin ana kasa abinda ke cikinsa zuwa kashi biyar;
MAS'ALOLI GUDA HUDU
(da suke cikin suratul Asr)
MAS'ALOLI GUDA UKU
(da suke magana kan karkasuwar Tauhid)
MUHIMMANCIN KARANTA TAUHIDI
"GINSHIKAI GUDA UKU"
(Tambayoyin kabari)
RUFEWA



1. MAS'ALOLI GUDA HUDU
1- ILIMI
2- AIKI DA ILIMI
3- DA'AWA ZUWA GA ILIMI DA AIKI
4- JURIYA GA CUTARWAR DA TAKE CIKINSU



2. MAS'ALOLI GUDA UKU
1- Tauhidin Rububiyyah da Tauhidin Asma'u was Sifatu
2- Tauhidin Uluhiyyah
3- Barranta daga Shirka da ma'abutansa
(a zuciya da harshe, da sauran gabbai)



3. MUHIMMANCIN KARANTA ILIMIN TAUHIDI
(Shine abinda ya gabata, na amsar: Me ya sanya muke karanta ilimin Tauhidi?).


4. GINSHIKAI GUDA UKU NA "USULUS SALASA"
"Usulus Salasa", a takaice, sune: Tambayoyin kabari guda uku;
Wanene Ubangijinka?
Menene Addininka?
Wanene Annabinka?

5. RUFEWA;
Wannan kuma yana farawa ne daga fadin Mawallafin "والناس إذا ماتوا يبعثون" har zuwa karshen littafin.




NA FARKO: MAS'ALOLI GUDA HUDU


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ (Bismil Lahir Rahmanir Rahim)
اعْلمْ رَحِمَكَ اللهُ (Ka sani –Allah ya yi maka rahama-)
أَنَّهُ يَجِبُ عَلَيْنَا تَعَلُّمُ أَرْبَع مَسَائِلَ:
(Lallai yana wajaba akanmu mu koyi mas'aloli guda hudu)
الأُولَى: الْعِلْمُ: (Mas'alar farko: ILIMI)
وَهُوَ مَعْرِفَةُ اللهِ، وَمَعْرِفَةُ نَبِيِّهِ صلى الله عليه وسلم، وَمَعْرِفَةُ دِينِ الإِسْلامِ بالأَدِلَّةِ
)ILIMI Shine ilimin sanin Allah, da sanin AnnbinSaصلى الله عليه وسلم da sanin addinin Musulunci, tare da dalilai).
الثَّانِيَةُ: الْعَمَلُ بِهِ (Mas'ala ta biyu: AIKI DA ILIMIN).


(1) SABABIN DA YA SANYA MAWALLAFINMU YA FARI LITTAFINSA DA "BISMILLAH"
1. Domin koyi da littafin Allah, da Annabawa عليهم السلام.
2. Domin koyi da Maluman da suka gabace shi, da magabatan kwarai; wadanda cikin al'adarsu akwai bude littatafansu da sunan Allah (Bismillah).
3. Domin neman albarkar farawa da sunan Allah Mai-karamci.



(2) Kamar yadda muka yi nuni, a "MUKADDIMAH" cewa yana daga al'adar Malam cikin wallafe-wallafensa, ya kan fara addu'a ga 'Daliban ilimi, kuma ya roka musu rahamar Allah; kuma cikin aikata haka, akwai dalili akan:
Rahamar Maluman Ahlus-Sunnah Wal Jama'a ga 'Dalibansu.
Lallai addinin Musulunci ga asalinsa ya ginu ne akan jin-kai da rahama.



ILIMI: Shine: Sanin gaskiya, da dalilinsa. Kishiyan ilimi kuma shine Jahilci.


(3) Domin bayanin alakar da ke tsakanin "ILIMI" da "AIKI DA SHI" wani ke cewa: "ILIMI YANA HUKUNTA AIKI' IDAN HAR YA AMSA MASA SHI KENAN, IDAN KUMA BA HAKA BA, SAI ILIMIN YA YI KAURA"; Don haka, babu wata fa'ida ga ilimin da ba a yi aiki da shi ba, kuma idan mutum ya koyi ilimi, to wajibi ne ya yi aiki da shi, idan kuma ba haka ba, to ya yi koyi da Yahudawa; saboda Yahudu ne, suke da ilimi babu aiki, "SUNA SANINSA KAMAR YADDA SUKE SANIN 'YA'YANSU" . Kuma farkon wadanda za a fara babbakawa a cikin wuta sune mutane uku; daga cikinsu, akwai wanda ya koyi ilimi, sai bai yi aiki da shi ba


KUMA MALAMIN DA BAI YI AIKI DA ILIMINSA BA
ZA A AZABTA SHI GABANIN MASU BAUTAR GUMAKA
الثَّالِثَةُ: الدَّعْوَةُ إِلَيْهِ
(Mas'ala ta uku: YIN DA'AWA ZUWA GA ILIMI DA AIKI).


DA'AWA TANA DA SHARUDDA DA KA'IDODI, WANDA YA WAJABA TA GINU AKANSU, Wanda suka fi muhimmanci daga cikinsu sune:
1. Dole da'awar ta kasance an nufi Allah Ta'alah da ita.
2. Dole a gina da'awa akan ilimin shari'a.
3. Dole da'awa ta kasance da hikima, da hakuri.
4. Sai kuma a kula da yanayin wadanda ake musu da'awar.

DALILI AKAN WADANNAN SHARUDDAN
Fadin Allah Ta'alah: "KA CE: WANNAN CE HANYATA; INA KIRA ZUWA GA ALLAH; AKAN BASIRA NI DA WADANDA SUKA BI NI, KUMA TSARKI YA TABBATA GA ALLAH, KUMA NI BAN ZAMA DAGA CIKIN MASU SHIRKI BA" [Yusuf: 108].
"WANNAN CE HANYATA": Abinda ake nuni da shi a nan shine abinda Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya zo da shi; na shari'a.
"INA KIRA ZUWA GA ALLAH": Mai yin kira zuwa ga Allah, shine Mai ikhlasin niyya wanda ke son isar da mutane zuwa ga Allah.
"AKAN BASIRA" Basira it ace ilimi, kuma a nan tana kunsar sanin:
1. Sanin shari'a
2. Sanin yanayin wanda kake masa da'awa
3. Sanin hanyar da zata kaika ga manufarka.

Kai ka ce, Mawallafin yana cewa: Idan ka nemi ilimi, sa'annan ka yi aiki da ilimin, to wajibi ne akan abinda Annabi صلى الله عليه وسلم da Sahabbai da Magabatan kwarai suka kasance akansa, kamar yadda Allah yake cewa:
"KA CE: WANNAN CE HANYATA; INA KIRA ZUWA GA ALLAH; AKAN BASIRA NI DA WADANDA SUKA BI NI"; Kenan babu makawa kan da'awa.


الرَّابِعَةُ: الصَّبْرُ عَلَى الأَذَى فِيهِ.
(Mas'ala ta hudu: Hakuri kan cutarwa a cikinsa).
وَالدَّلِيلُ قَوْلُهُ تَعَالَى:
(وَالْعَصْرِ * إِنَّ الإِنسَانَ لَفِي خُسْرٍ * إِلاَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ وَتَوَاصَوْا بِالْحَقِّ وَتَوَاصَوْا بِالصَّبْرِ).
Dalili akan abinda ya gabata shine fadinsa Madaukaki:
"INA RANTSUWA DA ZAMANI * LALLAI MUTUM YANA CIKIN HASARA * FACE WADANDA SUKA YI IMANI, KUMA SUKA AIKATA AYYUKAN KWARAI, KUMA SUKA YI WA JUNA WASIYYA DA BIN GASKIYA, KUMA SUKA YI WASIYYA DA YIN HAKURI" [Asr: 1-3].
(1) Mawallafin –Allah ya yi masa rahama- ya ambaci HAKURI bayan da'awa, wato kamar yana ce maka: Lallai wanda zai bi hanyar da'awa, to lallai wasu lamura (marasa dadi) za su kasance masa, kamar yadda suka kasance ga Annabawa da Manzanni عليهم السلام; kenan babu makawa sai an yi hakuri.
HAKURI
Kalmar (الصبر) a harshen Larabci: tana nufin killacewa.
A shari'a kuma: Hana rai wasu abubuwa.

Imam Ibnul-kayyim –رحمه الله- ya kasa hakuri zuwa kasha uku:
1. Yin hakuri wajen biyayya ga Allah; har a iya aikata bauta.
2. Hakuri kan sabo, har a nisance su.
3. Hakuri kan ababen da Allah ya kaddara masu radadi.



(2) Bayan Ambato mas'alolin nan guda hudu, Sai Mawallafin –رحمه الله- ya koro musu dalili daga littafin Allah, wanda shine suratul Asr.
Kuma lallai Mawallafin –رحمه الله- ga dabi'arsa ya kan ambaci mas'ala, tare da dalilinta, Saboda me?
Domin ya tarbiyyantar da 'Dalibi akan bin dalilai; ba taklidi (ko makauniyar bin maluma) ba.
Har ya zama akwai hujja a wurin 'dalibi, wanda zai iya mayar da martini ga wanda ya saba wa gaskiya.
Har 'Dalibi ya iya samun ciro hukunce-hukunce, daga dalilansu, akan lafiyayyun ka'idodi.



قَالَ الشَّافِعيُّ -رَحِمَهُ اللهُ-: لَوْ مَا أَنْزَلَ اللهُ حُجَّةً عَلَى خَلْقِهِ إِلا هَذِهِ السُّورَةَ لَكَفَتْهُمْ (1).
(Shafi'iy –رحمه الله- ya ce: Da Allah bai saukar da wata hujja ga halittunsa ba, sai wannan sura, to da ta isar musu).
وَقَالَ البُخَارِيُّ -رَحِمَهُ اللهُ-: بَابُ: العِلْمُ قَبْلَ القَوْلِ وَالْعَمَلِ؛
(Kuma Bukhariy –رحمه الله- ya ce: Babin da ya kunshi bayani kan: Ilimi shine gabanin zance da aiki).
وَالدَّلِيلُ قَوْلُهُ تَعَالَى: (فَاعْلَمْ أَنَّهُ لاَ اله إِلاَّ اللَّهُ وَاسْتَغْفِرْ لِذَنبِكَ)[محمد:19]، فَبَدَأَ بِالْعِلْمِ قَبْلَ القَوْلِ وَالعَمَلِ) (2).
(Dalili akan haka shine fadin Allah Ta'alah: SABODA HAKA, KA SANI, BABU ABIN BAUTAWA DA GASKIYA, FACE ALLAH, KUMA KA NEMI GAFARAR ZUNUBANKA) [Muhammadu: 19]. Sai Allah ya fara da batun ilimi gabanin zance da aiki).
(1) Maksudin Mawallafin –رحمه الله- shine lallai wannan surar (wato, Asr) ita kadai, ta wadatar wajen tsayuwar hujja akan halittu, kan su yi ilimi, su yi aiki da shi, su yi da'awa, su yi hakuri.
(2) Amirul-mu'uminina a ilimin hadisi; wato, Imamul Bukhariy ya kulla babi a cikin littafinsa (na Sahihul Bukhariy) ya ce: BABIN DA KE BATU KAN YADDA ILIMI KE RIGAYAR ZANCE DA AIKI, Sai ya ambaci dalilinsa; don haka, babu makawa, dole sai an samu ilimi a farko gabanin zance da aiki; Kuma lallai baya inganta bawa ya yi aiki ba tare da ilimi ba, idan kuma ya aikata hakan, to yay i kamantacceniya da Nasara.


NA BIYU: MAS'ALOLI GUDA UKU
اعْلَمْ رَحِمَكَ اللهُ أَنَّه يَجِبُ عَلَى كُلِّ مُسْلِمٍ وَمُسْلِمَةٍ، تَعَلُّمُ هَذِهِ الثَّلاثِ مَسَائِل، والْعَمَلُ بِهِنَّ (1):
(Ka sani, Allah ya yi maka rahama; Lallai yana wajaba akan kowane musulmi namiji da mace, su koyi wadannan mas'alolin guda uku, kuma su yi aiki da su).
(1) Mawallafin ya fara magana kan wannan bangaren ne, da yin addu'a ga 'Dalibi.
Kuma lallai Mawallafin –رحمه الله- a cikin littafin Usulus salasa, ya yi addu'a har a wurare uku ga 'dalibi, A farkon mas'aloli guda hudu, sai kuma a nan, inda ke magana kan mas'aloli uku, Wuri na ukun kuma shine inda ya ce: Ka sani, Allah ya shiryar da kai zuwa ga 'da'arsa, lallai mikakken addini wato tafarkin Annabi Ibrahima...




MATASHIYA GABANIN SHARHIN MAS'ALOLIN UKU
TAUHIDI
A harshen larabci, Tauhidi –kadaita Allah- tushen kalmar ya kadaita, yana kadaitawa, akan ce: ya kadaita abu, idan mutum ya kudurci kasancewarsa guda daya.
A shari'a kuma, Tauhidi, kadaita Allah ne –سبحانه وتعالى- cikin abinda ya kebantu da su, na Rububiyyah, da Uluhiyyah, da Sunaye da Sifofi.

TAUHIDI YA KASU KASHI UKU
TAUHIDUR RUBUBIYYAH
Shine kadaita Allah –سبحانه وتعالى- cikin ayyukansa.
Ko a ce:
Kadaita Allah –سبحانه وتعالى- cikin halitta, da mulki, da juya lamari.
TAUHIDUL ULUHIYYAH
Shine kadaita Allah –سبحانه وتعالى- da bauta.
TAUHIDUL ASMA'U WAS-SIFAAT
Shine, kadaita Allah cikin abinda ya sanya wa kansa, na suna da sifa, a cikin littafinsa, ko ta harshen ManzonSa–صلى الله عليه وسلم-, ta hanyar tabbatar masa abinda ya tabbatar wa kansa, da kore abinda ya kore wa kansa, ba tare da karkatar da su, ko wofintar da su ba, kuma ba tare da fadar yanayinsu ko misaltawa ba.



Lamarin sunayen Allah da sifofinsa abu ne da ake tsayawa kawai ga abinda ya zo cikin littafin Allah, da sunnah; Wannan kuma ya kan kasance ta hanyar:
- Tabbatar wa Allah abinda ya tabbatar wa kansa, a cikin littafinsa, da kuma abinda, ManzonSa صلى الله عليه وسلم ya tabbatar masa.
- Da kuma kore abinda Allah –سبحانه وتعالى- ya kore wa kansa, a cikin littafinsa, haka kuma ManzonSa –صلى الله عليه وسلم- ya kore masa, misalin fadinsa: "GYANGYADI BAYA KAMA SHI, KUMA BARCI BAYA KAMA SHI" . "KUMA 'YAR WAHALA BATA SHAFE MU" [Kaf: 38].
Za a tabbatar masa da wadannan, ba tare da karkatar da su, ko wofintar da su ba, kuma ba tare da fadar yanayin sifofin ko misaltawa ba.
الأُولَى: أَنَّ اللهَ خَلَقَنَا، وَرَزَقَنَا، وَلَمْ يَتْرُكْنَا هَمَلا، بَلْ أَرْسَلَ إِلَيْنَا رَسُولاً، فَمَنْ أَطَاعَهُ دَخَلَ الجَنَّةَ، وَمَنْ عَصَاهُ دَخَلَ النَّارَ، وَالدَّلِيلُ قَوْلُهُ تَعَالَى: (إِنَّا أَرْسَلْنَا إِلَيْكُمْ رَسُولاً شَاهِداً عَلَيْكُمْ كَمَا أَرْسَلْنَا إِلَى فِرْعَوْنَ رَسُولاً * فَعَصَى فِرْعَوْنُ الرَّسُولَ فَأَخَذْنَاهُ أَخْذاً وَبِيلاً) [المزمل: 15، 16] (1).
(MAS'ALAR FARKO: Lallai Allah ya halitta mu, kuma ya azurta mu, kuma bai bar mu kara zube ba, sai ya aiko mana da wani Manzo; wanda ya masa biyayya ya shiga Aljannah, wanda kuma ya saba masa ya shiga wuta).
Dalili akan haka, shine fadinSa Madaukaki: "Lallai ne Mu, mun aiko wani Manzo zuwa gare ku, Mai shaida akanku, kamar yadda muka aika wani Manzo zuwa ga Fir'auna * Sai Fir'auna ya saba wa Manzon, saboda haka Muka kama shi, kamu mai tsanani" [Muzammil: 15-16].
MAS'ALOLI UKU, A TAKAICE
MAS'ALAR FARKO:
Tauhidin Rububiyyah da Tauhidil Asma'i was sifaat
MAS'ALA TA BIYU:
Tauhidil Uluhiyyah
MAS'ALA TA UKU:
Barranta daga shirka, da ma'abutansa

(1) Mas'alar farko: Mawallafin –رحمه الله- ya tabbatar wa Allah, tauhidin Rububiyyah, da Tauhidil Asma'i was sifaat, cikin fadinsa: (Lallai Allah ya halitta mu), saboda shine Mahalicci, (Kuma ya azurta mu) saboda shine Mai azurtawa. (Kuma bai kyale mu kara-zube ba); babu umarni da hani ba, (Saidai ya turo mana da Manzo).


[B]MANUFAR TURO MANZANNI –عليهم السلام-
Domin tsayar da hujja ga halittu; "BAMU KASANCE MASU AZABTARWA BA FACE, MUN TAYAR MANZO" [Isra'i: 15].
Domin jin-kai da rahama, "BAMU AIKO KA BA FACE, JIN-KAI GA TALIKAI" [Anbiya'i: 107].



الثَّانِيَةُ: أَنَّ الله لا يَرْضَى أَنْ يُشْرَكَ مَعَهُ أَحَدُ فِي عِبَادَتِهِ، لا مَلَكٌ مُقَرَّبٌ، وَلا نَبِيٌّ مُرْسَلٌ؛
(MAS'ALA TA BIYU: Lallai ne Allah, baya yarda a hada shi da wani cikin bautarsa; Mala'ika ne makusanci, ko kuma Annabi Manzo).
وَالدَّلِيلُ قَوْلُهُ تَعَالَى: (وَأَنَّ الْمَسَاجِدَ لِلَّهِ فَلاَ تَدْعُوا مَعَ اللَّهِ أَحَدًا).
(Dalili akan haka kuma shine fadinSa Madaukaki: "KUMA LALLAI WURAREN SUJJADA NA ALLAH NE; SABODA HAKA, KADA KU ROKI WANI TARE DA ALLAH (A CIKINSU)" [Jinn: 18]).
Dangane da ma'anar "MASAJID a cikin ayar" akwai maganganu guda uku, kuma za a iya hada maganganun
Masallatan da ake ginawa domin ayai bautar Allah a cikinsu.
Gabban da ake yin sujjada da su.
Doron kasa, saboda hadisin: "Kuma an sanya min kasa ta zama wurin sujjada, mai tsarki".

fadinSa: "NA ALLAH NE; SABODA HAKA, KADA KU ROKI WANI TARE DA ALLAH (A CIKINSU)" kalmar, "WANI" tana game kowa-da-kowa, don haka ne Imam Muhammad bn Abdulwahhab –رحمه الله-, a farkon mas'alar ya ce: "Lallai ne Allah baya yarda a hada shi ko a masa shirka da wani"; wato: ko-wanene shi, Annabi ne, ko Waliyyi, ko Aljani, ko Salihi.




الثَّالِثَةُ: أَنَّ مَنْ أَطَاعَ الرَّسُولَ، وَوَحَّدَ اللهَ لا يَجُوزُ لَهُ مُوَالاةُ مَنْ حَادَّ اللهَ وَرَسُولَهُ، وَلَوْ كَانَ أَقْرَبَ قَرِيبٍ؛ وَالدَّلِيلُ قَوْلُهُ تَعَالَى: (لاَ تَجِدُ قَوْمًا يُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الآخِرِ يُوَادُّونَ مَنْ حَادَّ اللَّهَ وَرَسُولَهُ وَلَوْ كَانُوا آبَاءَهُمْ أَوْ أَبْنَاءهُمْ أَوْ إِخْوَانَهُمْ أَوْ عَشِيرَتَهُمْ أُوْلَئِكَ كَتَبَ فِي قُلُوبِهِمُ الإِيمَانَ وَأَيَّدَهُم بِرُوحٍ مِّنْهُ وَيُدْخِلُهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا عَنْهُ، أُوْلَئِكَ حِزْبُ اللَّهِ، أَلاَ إِنَّ حِزْبَ اللَّهِ هُمُ الْمُفْلِحُونَ).
(MAS'ALA TA UKU: Lallai duk wanda yay i da'a ga Manzo, kuma yay i tauhidin Allah, baya halatta a gare shi, ya so ko ya jibinci wanda ya saba wa Allah da ManzonSa, koda kuwa dangin da yafi kusanci ne).
Dalili kan wannan mas'alar shine fadinSa madaukaki: "BAZA KA SAMU MUTANEN DA SUKA YI IMANI DA ALLAH, DA RANAR KARSHE SUNA YIN SOYAYYA DA WANDA YA SABA WA ALLAH DA MANZONSA BA; KODA KUWA SUN KASANCE UBANNINSU NE, KO 'YA'YANSU, KO 'YAN'UWANSU, KO DANGINSU, WADANNAN ALLAH YA RUBUTA IMANI A CIKIN ZUKATANSU, KUMA YA KARFAFA SU DA WANI RUHI DAGA WURINSU, KUMA ZAI SHIGAR DA SU ALJANNONI WADANDA KORAMU KE GUDANA KARKASHINSU, SUNA MASU DAWWAMA A CIKINSU, ALLAH YA YARDA DA SU, KUMA SUMA SUN YARDA DA SHI, WADANNAN SUNE KUNGIYAR ALLAH, KUMA LALLAI KUNGIYAR ALLAH SUNE MASU BABBAN RABO" [Mujadalah: 22].
Mas'ala ta uku: Mawallafin –رحمه الله- a cikinta ya bayyana wajabcin barranta daga shirka da ma'abutanta.
BARRANTA DAGA SHIRKA DA MA'ABUTANSA KAN KASANCE DA;
Da zuciya
Da harshe
Da kuma gabbai

1- Da zuciya: Ta hanyar kin kafirai da idinsu, da bukukuwansu, musamman shirkoki da bidi'oin da suke wurinsu.
2- Da harshe: "LALLAI NE NI, NA BARRANTA DAGA ABABEN DA KUKE BAUTAWA" [Zukhruf: 26].
"KA CE: YA KU KAFIRAI * BA ZAN BAUTA WA ABINDA KUKE BAUTAWA BA * KUMA KU BAKU KASANCE MASU BAUTA WA ABINDA NAKE BAUTAWA BA * KUMA NIMA BAN ZAMA MAI BAUTA WA ABINDA KUKE BAUTAWA BA * KUMA BAKU ZAMA MASU BAUTA WA ABINDA NAKE BAUTAWA BA * SABODA ADDININKU NAKU NE, NIMA ADDININA NAWA NE" [Kafiruna: 1-6].
3- Da gabbai: Ta hanyar kin tarayya da su cikin bukukuwansu da alamomin ibada, ko tufafi, ko abinda suke kansa na akida.


NA UKU: MUHIMMANCIN KARANTA TAUHID
اعْلَمْ أَرْشَدَكَ اللهُ لِطَاعَتِهِ، أَنَّ الْحَنِيفِيَّةَ مِلَّةَ إِبْرَاهِيمَ: أَنْ تَعْبُدَ اللهَ وَحْدَهُ، مُخْلِصًا لَهُ الدِّينَ. وَبِذَلِكَ أَمَرَ اللهُ جَمِيعَ النَّاسِ، وَخَلَقَهُمْ لَهَا؛ كَمَا قَالَ تَعَالَى: (وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالإِنْسَ إِلاَّ لِيَعْبُدُونِ). وَمَعْنَى يَعْبُدُونِ: يُوَحِّدُونِ، وَأَعْظَمُ مَا أَمَرَ اللهُ بِهِ التَّوْحيِدُ، وَهُوَ: إِفْرَادُ اللهِ بِالْعِبَادَةِ(3). وَأَعْظَمُ مَا نَهَى عَنْه الشِّركُ، وَهُوَ: دَعْوَةُ غَيْرِهِ مَعَهُ، وَالدَّلِيلُ قَوْلُهُ تَعَالَى (وَاعْبُدُواْ اللّهَ وَلاَ تُشْرِكُواْ بِهِ شَيْئًا).
Ka sani –Allah ya shiryad da kai zuwa ga biyayya a gare shi-, Lallai mikakken addini; tafarkin annabi Ibrahima, shine: Ka bauta wa Allah, shi kadai, kana mai tsantsanta addinni a gare shi, kuma da aikata haka, Allah ya umarci dukkan mutane, kuma ya halitta su don haka, kamar yadda Allah Ta'alah ya ce: "KUMA BAMU HALITTA MUTUM DA ALJANI BA, FACE SU BAUTA MIN".
Ma'anar: "SU BAUTA MIN", shine su min tauhidi (kadaita Allah).
Kuma mafi girman abinda Allah ya yi umarni da shi, shine, Tauhidi, wanda kuma shine: kadaita Allah a cikin bauta.
Kuma mafi girman abinda Allah ya yi hani akansa, shine shirka, wanda kuma ita ce: Rokon wanin Allah tare da Allah.
Dalili shine fadinSa Madaukaki: "KU BAUTA WA ALLAH, KADA KU HADA SHI DA KOWA" [Nisa'i: 36].


HANIYFIYYA –addinin Annabi Ibrahim (A.S)
A harshen larabci kalmar an ciro ta ne, daga "hanaf", mai ma'anar, karkata.
A shari'a kuma, "haniyfiyyah" ita ce addinin da ya karkata, daga shirka, ya fiskanci ikhlasi da tauhidi da imani, "MAI 'DA'A NE GA ALLAH, WANDA YA KARKATA YA BAR SHIRKA"; wato, wanda ya fiskanci Allah, ya juya baya ga shirka, saboda kalmar "hanif" tana nufin mutumin da da'iman ke komawa ga tauhidi, mai nisantar shirka.

(3)A nan Mawallafin –رحمه الله- da yake magana akan mafi girman abinda Allah yayi umarni da shi, shine tauhidi, yana gaya mana dalilin da ya sanya muke karanta Tauhidi ne, kuma a baya, mun yi bayanin muhimmancin Tauhidi.


BAYANI AKAN TAUHIDI –kamar yadda muka gabatar-
A harshen larabci, Tauhidi –kadaita Allah- tushen kalmar ya kadaita, yana kadaitawa, akan ce: ya kadaita abu, idan mutum ya kudurci kasancewarsa guda daya.
A shari'a kuma, Tauhidi, kadaita Allah ne –سبحانه وتعالى- cikin abinda ya kebantu da su, na Rububiyyah, da Uluhiyyah, da Sunaye da Sifofi.

Mawallafin yace: Ma'anar: "SU BAUTA MIN", shine su min tauhidi (kadaita Allah). Wannan maganar Abdullahi bn Abbas –رضي الله عنهما- ne, a inda yake cewa:
إنَّ كل عبادة في القرآن معناها التوحيد، واعبدوا الله: وحدوا الله، "يأيها الناس اعبدوا ربكم": يا أيها الناس وحدوا ربكم.
Lallai kowace ibada a cikin Alkur'ani, ma'anarta shine: Tauhidi. "KU BAUTA WA ALLAH"; Wato, ku yi tauhidin Allah. "YA KU MUTANE, KU BAUTA WA UBANGIJINKU"; Wato, Yak u mutane, ku kadaita Ubangijinku.


NA HUDU: GINSHIKAI GUDA UKU
فَإِذَا قِيلَ لَكَ: مَا الأُصُولُ الثَّلاثَةُ التِي يَجِبُ عَلَى الإِنْسَانِ مَعْرِفَتُهَا؟
فَقُلْ: مَعْرِفَةُ الْعَبْدِ رَبَّهُ، وَدِينَهُ، وَنَبِيَّهُ مُحَمَّدًا صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ (1).
فَإِذَا قِيلَ لَكَ: مَنْ رَبُّكَ؟
فَقُلْ: رَبِّيَ اللهُ الَّذِي رَبَّانِي، وَرَبَّى جَمِيعَ الْعَالَمِينَ بِنِعَمِهِ، وَهُوَ مَعْبُودِي لَيْسَ لِي مَعْبُودٌ سِوَاهُ؛ وَالدَّلِيلُ قَوْلُهُ تَعَالَى: (الْحَمْدُ للَهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ)(2). وَكُلُّ مَنْ سِوَى اللهِ عَالَمٌ، وَأَنَا وَاحِدٌ مِنْ ذَلِكَ الْعَالَمِ(3).
Idan aka ce maka: Menene ginshikai uku, wadanda ya zama wajibi mutum ya sansu?
Sai ka ce: Bawa, ya san UbangijinSa, da addininSa, da AnnabinSa; Muhammadu –صلى الله عليه وسلم-.
Idan aka ce maka: Wanene Ubangijinka?
Sai ka ce: Ubangijina, shine Allah, wanda ya ke rainona, kuma ya reni dukkan talikai, da ni'imominSa, kuma shine abin bautata, bani da wani abin bauta, idan ba shi ba.
Dalili akan haka shine fadinSa Madaukaki:
"GODIYA TA TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN TALIKAI". Kuma dukkan abinda ba Allah ba halitta ne, Ni kuma daya ne daga cikin wadannan halittun
(1) Mawallafin –رحمه الله- ya fara da ambaton ginshikai guda uku, wadanda kuma sune tambayoyin kabari guda uku, kuma ya yi tambaya ne, domin ya waigo da fadakar makaranci, ko mai sauraro da tambayar da ya jefo, Sai kuma ya masar tambayar.
(2) Mawallafin –رحمه الله- ya bada haske kan ginshikin farko, a inda ya bayyana cewa, Lallai Ubangiji kuma wanda ya cancanci a masa bauta shine Allah –سبحانه وتعالى-, sai kuma ya ambaci dalili, wanda kuma shine fadin Allah Ta'alah: "GODIYA TA TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN TALIKAI"; saboda Ubangiji shine abin bauta.
"GODIYA TA TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN TALIKAI" Wannan ayar ta hada nau'ukan tauhidi guda uku
"[B]ALHAMDU" cikinsa akwai tabbatar wa Allah Tauhidin Asma'u was-sifaat
"LILLAHI" cikinsa akwai tabbatar masa da Tauhidin Uluhiyyah.
"RABB" cikinsa akwai tabbatar masa da Tauhidin Rububiyyah

(3) Yana nufin dukkan abinda Allah ba, halittarsa aka yi, Idan kuwa na kasance, halitta, to dole ne na tsayu wajen godiya ga Mai halitta, Mai ni'ima, Mai falala –سبحانه وتعالى-.


فَإِذَا قِيلَ لَكَ: بِمَ عَرَفْتَ رَبَّكَ؟
فَقُلْ: بِآيَاتِهِ وَمَخْلُوقَاتِهِ، وَمِنْ آيَاتِهِ: اللَّيْلُ، وَالنَّهَارُ، وَالشَّمْسُ، وَالْقَمَرُ، وَمِنْ مَخْلُوقَاتِهِ السَّمَاوَاتُ السَّبْعُ وَالأَرَضُونَ السَّبْعُ وَمَنْ فِيهِنَّ، وَمَا بَيْنَهُمَا؛ وَالدَّلِيلُ قَوْلُهُ تَعَالَى: (وَمِنْ آيَاتِهِ اللَّيْلُ وَالنَّهَارُ وَالشَّمْسُ وَالْقَمَرُ لاَ تَسْجُدُوا لِلشَّمْسِ وَلاَ لِلْقَمَرِ وَاسْجُدُوا لِلَّهِ الَّذِي خَلَقَهُنَّ إِن كُنتُمْ إِيَّاهُ تَعْبُدُونَ).
وَقَوْلُهُ تَعَالَى: (إِنَّ رَبَّكُمُ اللّهُ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ ثُمَّ اسْتَوَى عَلَى الْعَرْشِ يُغْشِي اللَّيْلَ النَّهَارَ يَطْلُبُهُ حَثِيثاً وَالشَّمْسَ وَالْقَمَرَ وَالنُّجُومَ مُسَخَّرَاتٍ بِأَمْرِهِ أَلاَ لَهُ الْخَلْقُ وَالأَمْرُ تَبَارَكَ اللّهُ رَبُّ الْعَالَمِينَ)(1).
وَالرَّبُ هُوَ الْمَعْبُودُ، وَالدَّلِيلُ قَوْلُهُ تَعَالَى: (يَا أَيُّهَا النَّاسُ اعْبُدُواْ رَبَّكُمُ الَّذِي خَلَقَكُمْ وَالَّذِينَ مِن قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ * الَّذِي جَعَلَ لَكُمُ الأَرْضَ فِرَاشاً وَالسَّمَآء بِنَآءً وَأَنزَلَ مِنَ السَّمَآءِ مَآءً فَأَخْرَجَ بِهِ مِنَ الثَّمَرَاتِ رِزْقاً لَّكُمْ فَلاَ تَجْعَلُواْ لِلّهِ أَندَاداً وَأَنتُمْ تَعْلَمُونَ)(2).
قَالَ ابْنُ كَثِيرٍ ـ رَحِمَهُ اللهُ تَعَالَى: الخَالِقُ لِهَذِهِ الأَشْيَاءَ هُوَ الْمُسْتَحِقُّ لِلْعِبَادَةِ(3).
Idan kuma aka ce maka: Da me ka san Ubangijinka?
Ka ce: Da ayoyinSa da halittunSa, Kuma daga cikin ayoyinsa, akwai dare da yini, da rana da wata, Daga cikin halittunsa, akwai sammai bakwai, da kassai bakwai, da abinda suke cikinsu da abinda suke cikinsu.
Kuma dalili shine fadinSa Madaukaki: "DAGA AYOYINSA AKWAI DARE DA YINI DA RANA DA WATA, KADA KU YI SUJJADA GA WATA KO RANA, KU YI SUJJADA GA ALLAN DA YA HALITTA SU, IDAN KUN KASANCE GA SHI KADAI KUKE YIN BAUTA".
Da fadinSa: "LALLAI NE UBANGIJINKU SHINE ALLAN DA YA HALITTA SAMMAI DA KASA, A CIKIN YINI GUDA SHIDA, SA'ANNAN YA DAIDAITA A SAMAN AL'ARSHI, YANA SHIGAR DA DARE YA RUFA YINI, YANA NEMANSA DA GAGGAWA, KUMA RANA DA WATA DA TAURARI HORARRU NE DA UMARNINSA, KUMA HALITTA TASA CE, UMARNI NASA NE, ALBARKAR ALLAH UBANGIJIN HALITTU TA BAYYANA".
Kuma Ubangiji shine abin bauta, dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "YA KU MUTANE KU BAUTA WA UBANGIJINKU DA YA HALITTA KU, DA WADANDA SUKE GABANINKU, DOMIN KU SAMU KARIYA * WANDA YA SANYA MUKU KASA SHIMFIDA, SAMA KUMA GINI, KUMA YA SAUKAR DA RUWA DAGA SAMA, SA'ANNAN YA FITAR DA ABINCI DAGA 'YA'YAN ITACE, DA SHI, SABODA KU, DON HAKA, KADA KU SANYA WA ALLAH KISHIYOYI, ALHALI KUNA SANE".
Ibnu-kasir –رحمه الله- ya ce: "Wanda ya halicci wadannan ababen shine ya cancanci bauta".
(1) Mawallafin ya ambato tarin ayoyi cikin duniya da halittu, wadanda suke nuni kan samuwar Allah, kuma suke tabbatar da cewa, babu Ubangiji kuma babu Mahalicci, babu abin bauta, da gaskiya face Allah, sai kuma ya kawo dalilai daga Alkur'ani, kamar yadda suka zo cikin maganarsa.
· Kowace halitta aya ce da take nuna samuwar Allah –سبحانه وتعالى-, Saidai Sheikhul Islma Muhammdu bn Abdulwahhab –رحمه الله- ya banbance tsakanin aya, da halitta, saboda aya tana caccanzawa, misalin dare da yini, kuma wanda ke caccanza yanayi yafi karfin dalili, akan halittar da bata canzawa.
(2) Wanan ayar, da take cikin suratul Bakarah, Wasu daga cikin Maluma, suka ce, a cikinta akwai kira na farko a cikin Alkur'ani "YA KU MUTANE...", Kuma a cikinta, akwai umarni na farko "KU YI BAUTA"; Ma'ana: Ku yi Tauhidi. Kuma a cikinta akwai, farkon hani a cikin Alkur'ani, "KADA KU SANYA KISHIYOYI GA ALLAH, ALHALIN KUNA SANE"; Wannan kuma hani ne kan shirki.
(3) Yana nufin, Wanda ya kadaitu cikin Rububiyyah, ya zama wajibi a kadaita shi cikin Uluhiyyah.


وَأَنْوَاعُ الْعِبَادَةِ الَّتِي أَمَرَ اللهُ بِهَا، مِثْلُ: الإِسْلامِ، وَالإِيمَانِ، وَالإِحْسَانِ، وَمِنْهُ: الدُّعَاءُ، وَالْخَوْفُ، وَالرَّجَاءُ، وَالتَّوَكُّلُ، وَالرَّغْبَةُ، وَالرَّهْبَةُ، وَالْخُشُوعُ، وَالْخَشْيَةُ، وَالإِنَابَةُ، وَالاسْتِعَانَةُ، وَالاسْتِعَاذَةُ، وَالاسْتِغَاثَةُ، وَالذَّبْحُ، وَالنَّذْرُ، وَغَيْرُ ذَلَكَ مِنْ أَنْوَاعِ الْعِبَادَةِ الَّتِي أَمَرَ اللهُ بِهَا، كُلُّهَا للهِ تَعَالَى.
وَالدَّلِيلُ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (وَأَنَّ الْمَسَاجِدَ لِلَّهِ فَلاَ تَدْعُوا مَعَ اللَّهِ أَحَدًا).
فَمَنْ صَرَفَ مِنْهَا شَيْئًا لِغَيْرِ اللهِ؛ فَهُوَ مُشْرِكٌ كَافِرٌ؛ وَالدَّلِيلُ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (وَمَن يَدْعُ مَعَ اللَّهِ الهاً آخَرَ لاَ بُرْهَانَ لَهُ بِهِ فَإِنَّمَا حِسَابُهُ عِندَ رَبِّهِ إِنَّهُ لاَ يُفْلِحُ الْكَافِرُونَ).
وَفِي الْحَدِيثِ: (الدُّعَاءُ مخ الْعِبَادَةِ).
وَالدَّلِيلُ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (وَقَالَ رَبُّكُمُ ادْعُونِي أَسْتَجِبْ لَكُمْ إِنَّ الَّذِينَ يَسْتَكْبِرُونَ عَنْ عِبَادَتِي سَيَدْخُلُونَ جَهَنَّمَ دَاخِرِينَ).
Kuma nau'ukan ibada wadanda Allah ya yi umarni da su, misalinsu shine: musulunci, da imani, da ihsani, kuma daga cikin ibada akwai, addu'a, tsoro, fata, tawakkali, bayyana kwadayi, da tsoro, da khushu'i, da khashyah, da maida lamari ga Allah, da neman taimako, da neman tsari, da neman agaji, da yanka, da bakance, da abinda wannan ba daga cikin na'ukan ibada, wadanda Allah ya yi umarni da su, dukkansu ana yinsu ga Allah Ta'alah.
Dalili kuma shine: FadinSa Madaukaki: "KUMA LALLAI WURAREN SUJJADA NA ALLAH NE; SABODA HAKA, KADA KU ROKI WANI TARE DA ALLAH (A CIKINSU)".
Kuma duk wanda ya aiwatar da wani abu na ibada ga wanin Allah shi mushriki kafiri, dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "KUMA DUK WANDA YA ROKI WANI ABIN BAUTAR TARE DA, BASHI DA HUJJA AKAN HAKA, TO LALLAI HISABINSA YANA WURIN UBANGIJINSA, KUMA LALLAI SHA'ANIN, KAFIRAI BASA SAMUN RABO".
Ya zo a cikin hadisi, "Addu'a itace ibada".
Dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "KUMA UBANGIJINKU YACE, KU ROKE NI, ZAN AMSA MUKU, LALLAI WADANDA SUKE GIRMAN KAI, BASA MIN BAUTA ZASU SHIGA JANNAMA, SUNA KASKANTATTU"
Mawallafin ya yi ta'aliki ga maganar Ibnu-Kasir (da ta gabata) ta hanyar ambato wani adadi (mai yawa) na ibadodin zuciya, da ibadodin gabbai, tare da ambato dalilinsu daga littafin Allah, ga kowane aikin, kamar yadda bayaninsu zai zo:
ADDU'A –kuma ya kasu zuwa kashi biyu-
ADDU'A TA IBADA
Addu'ar ibada shima kamar rokon bukata ne a fakaice, kamar sallah da azumi da hajji.
Yin wannan addu'ar ga wanin Allah shirka ne mai girma (da take fitarwa da ga musulunci).


ADDU'AR ROKON BUKATU
Wannan kuma shine rokon bukata, da harshe, kamar mutum yace: Ya Allah! Ka gafarta min, Ya Allah ka mini rahama.
Hukuncin wannan addu'ar ya kasu kashi-kashi, kamar yadda ke tafe:



ADDU'AR ROKON BUKATU TANA KASUWA KASHI BIYU NE:
Rokon abinda babu mai iko akansa in banda Allah.


Wannan kuma rokon wanin Allah shirka ne mai girma.
Rokon abinda bawa ke da ikon samar da shi,


Wannan yana halatta, idan aka cika sharuddan da ke tafe:



Wanda za a rokan ya kasance rayayye;


Wannan ya haramta rokon ya kasance ga matacce.
Wanda za a rokan ya kasance halartacce;


Wannan ya haramta rokon wanda baya halarce.
Wanda za a rokan ya kasance yana da iko;


Wannan ya haramta rokon gajiyayye.
Sai kuma ya kudurta cewa, wanda yake rokonsa sababi ne kawai, bashi da wani tasiri a karan-kansa.



Amma idan ya kudurta cewa wanda yake rokon, yana da wani ikon juya abu a dukiya a boye, ko ya ji cewa, akwai wani ion janyo amfani ko tunkude cuta a hannunsa, to wannan shirka ne.
· Abin lura a nan:
Muna bayanin hukunci ne akan aiki (muka ce hakan kafirci ne shirka), amma hukunci ga mutumin da yayi aikin, shi kam yana bukatar tsayar masa da hujja, tare da kawar masa shubuha, gabanin a kafirta shi.
Kuma Maluma sune wadanda ke yin hukunci ga wanda ya yi aikin, suce, wannan mumini ne, ko kafiri.


KARKASUWAN MUTANE KAN AKIDARSU DANGANE DA SABABI ZUWA KASHI UKU
Wadanda suka sanya ko kudurta abinda Allah –سبحانه وتعالى- ya sanya shi sababi a matsayin sababi.


Wannan ya halatta.
Masu sanya ko kudurta abinda Allah bai sanya shi sababi ba, sababi.


Kudurta hakan karamar shirka ce.
Sai wadanda suke kudurta cewa, shi sababi yana da tasiri a karan-kansa, kuma janyo amfani da tunkude cuta tana hannun sababin.
Wannan kuma babbar shirka ne.



SABUBBA NA SHARI'A
Kamar karatun addu'oin ruk-ya, da yadda Allah –سبحانه وتعالى- ya sanya shi ya zama sababin dauke cuta.
SABUBBAN DA AKA SANI
Kamar shan magani, shima Allah ya sanya shi, a matsayin sababin samun waraka.

Hadisin "Addu'a itace bargon ibada" hadisi ne mai rauni, Wanda ya inganta shine fadin Annabi –صلى الله عليه وسلم- "Addu'a itace bauta".


Yaya addu'a zata zama itace ibada?
Aya tana nuna wannan, "UBANGIJINKU YACE: KU ROKE NI ZAN AMSA MUKU, LALLAI NE WADANDA SUKE GIRMAN KAN BAUTA A GARE NI ZASU SHIGA JAHANNAMA SUNA KASKANTATTU".
A nan Allah –سبحانه وتعالى- ya ce: "YIN BAUTA A GARE NI", wannan sai ya nuna cewa lallai addu'a ibada ce.


وَدَلِيلُ الْخَوْفِ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (فَلاَ تَخَافُوهُمْ وَخَافُونِ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ) (1).
وَدَلِيلُ الرَّجَاءِ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (فَمَن كَانَ يَرْجُو لِقَاءَ رَبِّهِ فَلْيَعْمَلْ عَمَلاً صَالِحاً وَلاَ يُشْرِكْ بِعِبَادَةِ رَبِّهِ أَحَدًا) (2).
Dalili kan ibadar tsoro shine, fadinSa Madaukaki: "KUMA KADA KU JI TSORONSU, KU JI TSORONA IDAN KUN KASANCE MUMINAI".
Dalilin ibadar fata kuma shine fadinSa Madaukaki: "DUK WANDA YA KASANCE YANA FATAN HADUWAR UBANGIJINSA, TO YA AIKATA AIKI NAGARI, KUMA KADA YA HADA WANI CIKIN BAUTAR UBANGIJINSA".
(1) TSORO: Ji ne a jika, wanda ke kasancewa a lokacin tsammanin aukuwar abinda zai kawo halaka, ko cuta, ko cutarwa.
Kuma hakika Allah –سبحانه وتعالى- ya yi hani, kan jin tosron majibintan Shedanu, sai kuma ya yi umarnin a ji tsoronsa shi kadai.
TSORO KASHI UKU NE:
Tsoro na bauta da girmamawa, a asirce
Tsoro na dabi'a (wanda ake halittar bawa da shi)
Tsoro na haram



Shine tsoron mai bauta da yake yinsa ga wanda yake bautawa, kuma a cikinsa akwai kan-kan-da kai, da tawali'u, da girmama wanda ake masa bauta.
Wannan nau'in tsoron wajibi ne, kautar da zuwa ga wanin Allah shirka ne babba.
Misalinsa shine kamar mutum ya ji tsoron wuta, da abokin adawa, da dabbar da take farauta... ko makamancin haka.
Wannan nau'in tsoron halal ne.
Misalinsa kamar tsoron da ya kai ga debe tsammani daga rahamar Allah, ko ya ji tsoron mutum sai ya masa biyayya cikin sabon Allah.



(2) FATA: Mutum ya yi kwadayin wani lamarin da samunsa a kusa yake, kuma zai iya kasancewa samunsa a nesa yake; amma sai ya ajiye shi a matsayin abinda samunsa yake kusa.
Fatan da ya kunshi kan-kan-da kai da tawali'u, baya kasancewa, sai ga Allah –سبحانه وتعالى-.
Kuma kautar da shi ga wanin Allah –سبحانه وتعالى- shirka ne babba.
Kuma ibadar fata abar yabo, bata kasancewa sai ga wanda ya yi aikin biyayya ga Allah, sai ya yi fatan samun ladanta, ko kuma ya tuba daga sabo, sai ya yi fatan karbar tubansa.
Amma fatan da aka yi ba tare da aiki ba, to rudu ne, da guri, abin zargi.
ودَلِيلُ التَّوَكُلِ: قَوْلُهُ تَعَالَى: ( وَعَلَى اللّهِ فَتَوَكَّلُواْ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ ). وقوله: (وَمَن يَتَوَكَّلْ عَلَى اللَّهِ فَهُوَ حَسْبُهُ) (1).
وَدَلِيلُ الرَّغْبَةِ، وَالرَّهْبَةِ، وَالْخُشُوعِ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (إِنَّهُمْ كَانُوا يُسَارِعُونَ فِي الْخَيْرَاتِ وَيَدْعُونَنَا رَغَباً وَرَهَباً وَكَانُوا لَنَا خَاشِعِينَ ) (2).
Dalilin Tawakkali shine fadinSa Madaukaki: "GA ALLAH NE, ZA KU DOGARA, IDAN KUN KASANCE MUMINAI".
Da fadinSa: "KUMA DUK WANDA YA DOGARA GA ALLAH, TO YA ISAR MASA".
Dalilin ibadar kwadayi da fargaba da khushu'i, shine fadinSa Madaukaki: "LALLAI NE, SU, SUN KASANCE SUNA YIN SAURIN AIKATA ALKHAIRORI, KUMA SUNA ROKONMU CIKIN KWADAYI DA FARGABA, KUMA SUN KASANCE A GARE MU MASU KHUSHU'I".
(1) Hakikanin Tawakkali
A harshen larabci: Tawakkali ga abu na nufin, dogaro akansa.
A shari'a kuma: Tawakkali, shine gaskiyar dogaro ga Allah, tare da amintuwa da Allah, da riko da sabubba na shari'a.

BABU MAKAWA SAI LAMURA UKU SUN TABBATA GA TAWAKKALI
Gaskiya cikin dogaro ga Allah –سبحانه وتعالى-.
Amintuwa da Allah –سبحانه وتعالى- cewa zai cika abinda ya alkawarta.
Riko da sabubban shari'a.



(2) Ibadar kwadayi: Son isa zuwa ga abinda kake so.
Ibadar fargaba: ita ce, nau'in tsoron da ke haifar da gujewa abinda kake tsoro, don haka "Rahbah" tsoro ne da ke hade da aiki.
Ibadar khushu'i: Kan-kan-da kai ne da ke cakude da jin girman Allah, ta yadda mutum zai mika-wuya ga abinda Allah ya hukunta na kaddara, da shari'a.
· Mai tafiya zuwa ga Allah –سبحانه وتعالى- babu makawa, sai ya hada tsakanin ibadar tsoro da fata, kuma ba zai rinjayar da sashe akan sashe ba; tsoron kada ya samu zamiya sai ya halaka; don haka babu makawa sai an samu ibadar tsoro da fata a wurinsa, kuma kamar fukafikan tsuntsu biyu suke a gare shi.


وَدَلِيلُ الْخَشْيَةِ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (فَلاَ تَخْشَوْهُمْ وَاخْشَوْنِي...) الآية.
وَدَلِيلُ الإِنَابَةِ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (وَأَنِيبُوا إِلَى رَبِّكُمْ وَأَسْلِمُوا لَهُ...) الآية.
وَدَلِيلُ الاسْتِعَانَةِ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (إِيَّاكَ نَعْبُدُ وإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ). وَفِي الْحَدِيثِ: (...وإِذَا اسْتَعَنْتَ فَاسْتَعِنْ بِاللهِ).
وَدَلِيلُ الاسْتِعَاذَةِ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ الْفَلَقِ). وَ(قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ النَّاسِ).
وَدَلِيلُ الاسْتِغَاثَةِ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (إِذْ تَسْتَغِيثُونَ رَبَّكُمْ فَاسْتَجَابَ لَكُمْ...) الآية.
وَدَلِيلُ الذَّبْحِ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (قُلْ إِنَّنِي هَدَانِي رَبِّي إِلَى صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ دِيناً قِيَماً مِّلَّةَ إِبْرَاهِيمَ حَنِيفاً وَمَا كَانَ مِنَ الْمُشْرِكِينَ * قُلْ إِنَّ صَلاَتِي وَنُسُكِي وَمَحْيَايَ وَمَمَاتِي لِلّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ * لاَ شَرِيكَ لَه وَبِذَلِكَ أُمِرْتُ وَأَنَا أَوَّلُ الْمُسْلِمِينَ). وَمِنَ السُنَّةِ: (لعَنَ اللهُ مَنْ ذَبَحَ لِغَيْرِ اللهِ).
Dalilin ibadar tsoro: shine fadinSa Madaukaki: "KADA KU JI TSORONSU, KU JI TSORONA" (1).
Dalilin ibadar maida lamari ga Allah: shine fadinSa Madaukaki: "KUMA KU MAYAR DA LAMARI ZUWA GA ALLAH, KU MIKA WUYA A GARE SHI"(2).
Dalilin ibadar neman taimako: shine fadinSa Madaukaki: "A GARE KA MUKE YIN BAUTA, KUMA DAGA GARE KA MUKE NEMAN TAIMAKO".
Ya zo cikin hadisi: "Idan zaka nemi taimako, ka nemi taimakon Allah"(3).
Dalilin ibadar neman tsari: shine fadinSa Madaukaki: "KA CE: INA NEMAN TSARIN UBANGIJIN SAFIYA".
Da "KA CE: INA NEMAN TSARIN UBANGIJIN MUTANE"(4).
Dalilin ibadar neman agaji: shine fadinSa Madaukaki: "A YAYIN DA KUKE NEMAN AGAJIN UBANGIJINKU, SAI YA AMSA MUKU"(5).
Dalilin ibadar bakance: shine fadinSa Madaukaki: "KA CE: LALLAI NE SALLATA DA YANKANA, DA RAYUWATA, DA MUTUWATA, NA ALLAH NE UBANGIJIN TALIKAI * BASHI DA ABOKIN TARAYYA".
Ya zo cikin sunnah: "Allah ya tsine wa wanda ya yi yanka, ga wanin Allah"(6).
(1) Ibadar khashyah: Shine tsoron da ya ginu akan ilimi ko sanin girman wanda ake tsoronsa da sanin cikakken ikonsa.
(2) Ibadar inabah: Shine komawa ga Allah Ta'alah; ta hanyar yin da'a a gare shi, da nisantar saba masa, saboda ma'anar "Wa aniybuw" shine, ku koma "zuwa ga Ubangijinku"; ta hanyar sallama lamarinka ga Allah –سبحانه وتعالى-; saboda kai bawansa ne, shi kuma bawa babu makawa dole ya sallamawa shugabansa, shugaban kuma shine Allah, kamar yadda Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Shugaba shine Allah".
(3) Ibadar isti'anah: tana nufin, neman taimako, "A KAI KADAI MUKE BAUTAWA, KUMA A GARE KA MUKE NEMAN TAIMAKO". A cikin wannan ayar an gabatar da abinda hakkinsa shine a jinkirta shi, wannan kuma yana nuni kan takaicewa, wato, Baza mu yi bauta ba, sai a gare ka, kuma baza mu nemi taimako ba, sai a wurinka.
(4) Ibadar isti'azah: tana nufin, neman tsari, daga abin ki, saboda kalmar "A'uzu" tana nufin, ina neman mafaka, ina neman kariya.
(5) Ibadar istigasah: tana nufin, neman agazawa, wanda kuma shine tsamar da mutum daga tsanani da halaka.
Ibadodin neman taimako, da neman tsari da neman agaji da ceto, ya halatta a neme su daga halitta cikin abinda ke da iko akansa, da sharudda guda hudu; wato ya zama rayayye, halartacce, mai iko, kuma kudurta shi sababi ne.

(6) Ibadar yanka: Fitar da rai, ta hanyar zubar da jinin dabba, a wani yanayi kebantacce.
YANKA YA KASU KASHI UKU
Yanka don Allah, kamar hadaya, da lahiya, da yanka domin sadaka.
Yanka ba don Allah ba, cikin so da girmamawa, kamar yanka wa Aljanu, da ma'abuta kabari.
Wannan shirka ne babba.
Yanka na halal, kamar yanka akuya don cin nama, ko girmama bako, ko yanka domin sayar da nama.

· Abin lura: Akwai karin bayani kan mas'alar yanka, wanda zai zo a littafin Tauhid, da izinin Allah.


وَدَلِيلُ النَّذْرِ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (يُوفُونَ بِالنَّذْرِ وَيَخَافُونَ يَوْماً كَانَ شَرُّهُ مُسْتَطِيرًا).
Dalilin ibadar bakance: shine fadinSa Madaukaki: "SUNA CIKA BAKANCE, KUMA SUNA TSORON YININ DA SHARRINSA KE YADUWA" (1).
(1) HAKIKANIN BAKANCE (ALWASHI)
A harshen larabci: nazr yana nufin, alkawartawa da lazimtawa.
A shari'ance: Bakance, shine mai hankali ya lazimta wa kansa wani abinda ba wajibi ba ne, akansa.

· Abin lura: Bakance yana da kashe-kashe, da sharudda, da kaffara, wanda karin bayani akansu zai zo a littafin Tauhid, da izinin Allah.
NAU'UKAN BAKANCE
Alwashi don Allah
Alwashi da bakance ga wanin Allah



· Mawallafin, ya ambaci ibadodin da suka gabata, ba wai a matsayin sune kadai ibadodi ba, saidai a matsayin misali, domin akwai dinbin ibadodin da ba a ambata ba. Saidai kuma darasin a nan shine, duk wanda ya kautar da wani abu na wadannan ibadodin ko wasunsu ga wanin Allah, to lallai ya yi shirka.


الأَصْلُ الثَّانِي: مَعْرِفَةُ دِينِ الإِسْلامِ بِالأَدِلَّةِ.
وَهُوَ: الاسْتِسْلامُ للهِ بِالتَّوْحِيدِ، وَالانْقِيَادُ لَهُ بِالطَّاعَةِ، وَالْبَرَاءَةُ مِنَ الشِّرْكِ وَأَهْلِهِ، وَهُوَ ثَلاثُ مَرَاتِبَ: الإسْلامُ، وَالإِيمَانُ، وَالإِحْسَانُ. وَكُلُّ مَرْتَبَةٍ لَهَا أَرْكَانٌ.
المرتبة الأولى: الإسلام(1). فَأَرْكَانُ الإِسْلامِ خَمْسَةٌ: شَهَادَةُ أَن لا اله إِلا اللهُ(2)، وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللهِ، وَإِقَامُ الصَّلاةِ، وَإِيتَاءِ الزَّكَاةِ، وَصَوْمُ رَمَضَانَ، وَحَجُّ بَيْتِ اللهِ الْحَرَامِ.
ASALI NA BIYU: SANIN ADDININ MUSULUNCI, DA DALILAI.
SHINE, Mika wuya ga Allah, da tauhidi, da jawuwa gare shi da da'a, da barranta daga shirka da ma'abutansa.
Kuma addini martabobi uku ne, musulunci, da imani, da ihsani. Kuma kowace martaba tana da rukunnai.
Martabar farko: Musulunci.
Kuma rukunnan musulunci guda biyar ne:
Shaidawa babu anin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma annabi Muhammadu manzon Allah ne, da tsayar da sallah, da bada zakkah, da azumin ramadhana, da hajjin dakin Allah mai alfarma.
(1) Mawallafin ya shiga Magana kan ginshiki na biyu, wanda shine, bawa ya san addininsa, sai kuma ya fara bayanin hakikanin musulunci, a inda y ace:
MARTABAR FARKO: MUSULUNCI
Mika wuya ga Allah, da tauhidi, da jawuwa gare shi da da'a, da barranta daga shirka da ma'abutansa.

Wannan shine hakikanin musulunci; wato, ka sallama lamarinka ga Allah –سبحانه وتعالى- saboda kai bawa ne, kuma bawa dole ne ya sallama ga shugabansa, shugaban kuma shine Allah, kamar yadda Annabi –صلى الله عليه وسلم-.
Sa'annan sai ya kasa addini izuwa ga martabobi guda uku:
Musulunci
Imani
Ihsani



(2) Rukunnan musulunci guda biyar ne, Na farkonsu:
Kalmar shahada


فَدَلِيلُ الشَّهَادَةِ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (شَهِدَ اللّهُ أَنَّهُ لاَ اله إِلاَّ هُوَ وَالْمَلاَئِكَةُ وَأُوْلُواْ الْعِلْمِ قَآئِمَاً بِالْقِسْطِ لاَ اله إِلاَّ هُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ).
وَمَعْنَاهَا: لا مَعْبُودَ بِحَقٍّ إلا اللهُ، لا إله نَافِيًا جَمِيعَ مَا يُعْبَدُ مِنْ دُونِ اللهِ.
إِلا اللهُ مُثْبِتًا الْعِبَادَةَ للهِ وَحْدَهُ لا شَرِيكَ لَهُ فِي عِبَادَتِهِ، كَمَا أَنَّهُ لَيْسَ لَهُ شَرِيكٌ فِي مُلْكِهِ.
وَتَفْسِيرُهَا الَّذِي يُوَضِّحُهَا قَوْلُهُ تَعَالَى: (وَإِذْ قَالَ إِبْرَاهِيمُ لأَبِيهِ وَقَوْمِهِ إِنَّنِي بَرَآء مِّمَّا تَعْبُدُونَ * إِلاَّ الَّذِي فَطَرَنِي فَإِنَّهُ سَيَهْدِينِ * وَجَعَلَهَا كَلِمَةً بَاقِيَةً فِي عَقِبِهِ لَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ).
Dalilin Kalmar shahada shine fadinSa Madaukaki: "ALLAH YA SHAIDA CEWA: LALLAI NE BABU ABIN BAUTAWA DA CANCANTA FACE SHI, KUMA MALA'IKU DA MA'ABUTA ILIMI SUN SHAIDA, YANA TSAYE DA ADALCI, BABU ABIN BAUTAWA DA GASKIYA FACE SHI, MABUWAYI MAI HIKIMA".
Kuma ma'anar kalmar (LA ILA ILLAL LAHU) shine babu abin bautawa da cancanta, face Allah, saboda "LA ILAHA" tana kore cancanta ne ga dukkan ababen da ake bauta musu, koma bayan Allah. "ILLAL LAHU" kuma, yana tabbatar da cancantar bautan ne ga Allah shi kadai; bashi da abokin tarayya cikin bautarsa, kamar yadda bashi da abokin tarayya cikin mulkinsa.
Kuma tafsirin (LA ILAHA ILLAL LAHU) wanda ke fito da ma'anarta a sarari shine, fadinSa Madaukaki: "KA AMBATA, LOKACIN DA IBRAHIMU YA CE GA BABANSA DA MUTANENSA, LALLAI NE NI NA BARRANTA DAGA ABINDA KUKE BAUTAWA * FACE WANDA YA KAGI HALITTA TA, LALLAI SHINE ZAI SHIRYAR DA NI * KUMA YA SANYA (WANNAN MAGANAR) KALMA MAI WANZUWA, A CIKIN ZURIYARSA TSAMMANINSU SU KOMA DAGA BATA".


A wannan wuri, Sai Mawallafin –رحمه الله- ya ambaci dalilin Kalmar shahada (LA ILAHA ILLAL LAHU), ya kuma bayyana hakikanin ma'anarta, a inda yace:
BABU ABIN BAUTAWA DA GASKIYA SAI ALLAH
Don haka; babu makawa Kalmar shahada sai ta kunshi
KOREWA
TABBATARWA

Korewa da ya zo cikin "LA ILAHA".
Tabbatarwa, wanda ya zo cikin fadin "ILLAL LAHU".
Kuma wannan sigar, tana nuna takaicewa, da tabbatarwa; ta yadda ta takaice, kuma ta tabbatar da cancantar bauta ga Allah; shi kadai, kuma take kore ta ga wanin Allah, don haka ne, Mawallafin –رحمه الله- ya ce: Kuma tafsirin (LA ILAHA ILLAL LAHU) wanda ke fito da ma'anarta a sarari shine, fadinSa Madaukaki: "KA AMBATA, LOKACIN DA IBRAHIMU YA CE GA BABANSA DA MUTANENSA, LALLAI NE NI NA BARRANTA DAGA ABINDA KUKE BAUTAWA * FACE WANDA YA KAGI HALITTA TA".
"NA BARRANTA DAGA ABINDA KUKE BAUTAWA" wannan shine ma'anar "LA ILAHA".
"FACE WANDA YA KAGI HALITTA TA" Wannan shine ma'anar "ILLAL LAHU".


وقَوْلُهُ تَعَالَى: (قُلْ يَا أَهْلَ الْكِتَابِ تَعَالَوْاْ إِلَى كَلَمَةٍ سَوَاءٍ بَيْنَنَا وَبَيْنَكُمْ أَلاَّ نَعْبُدَ إِلاَّ اللّهَ وَلاَ نُشْرِكَ بِهِ شَيْئاً وَلاَ يَتَّخِذَ بَعْضُنَا بَعْضاً أَرْبَاباً مِّن دُونِ اللّهِ فَإِن تَوَلَّوْاْ فَقُولُواْ اشْهَدُواْ بِأَنَّا مُسْلِمُونَ) (1).
Da fadinSa: "KA CE, YA KU MA'ABUTA LITTAFI, KU TAFO, ZUWA GA KALMA MAI DAIDAITAWA, A TSAKANINMU DA KU, KADA MU BAUTA WA KOWA, FACE ALLAH, KUMA KADA MU HADA KOME DA SHI, KUMA KADA SASHENMU YA RIKI SASHE, UBANGIJI, BAICIN ALLAH, IDAN KUMA SUKA BIJIRE, SAI KACE: KU YI SHAIDA CEWA, LALLAI NE MU MASU SALLAMAWA NE".
· Da mai yin magana zai ce: Hakikanin shaidawa babu abin bautawa, da gaskiya sai Allah, shine babu wanda ake bauta masa face Allah?
Sai mu ce, wannan maganar kuskure ce, saboda idan yace duk abinda ake bauta masa Allah ne, kenan yana halatta yin bauta ga dukkan ababen bautawa. Saidai idan ya ce, abin bautawa da cancanta, to wannan dalili ne na cewa, ya kafirce kuma baya tare da dukkan ababen bautawa wadanda wasu suke bauta musu, koma bayan Allah, kuma yana jin cewa babu wanda ake masa bauta da gaskiya ko cancanta face Allah.


· Da mai magana zai ce: ma'anar LA ILAHA ILLAL LAHU, shine babu Ubangiji Mahalicci na gaskiya face Allah?
Sai muce: Wannan maganar gaskiya ce, saidai kuma ba itace ma'ana ko tafsirin LA ILAHA ILLAL LAHU ba, domin babu Mahalicci sai Allah, tauhidin Rububiyyah ne, wanda kafiran da aka tayar da Annabi –صلى الله عليه وسلم- a cikinsu, suka yarda da shi, saidai hakan bai shigar da su cikin musulunci ba.
(1) "KA CE, YA KU MA'ABUTA LITTAFI, KU TAFO, ZUWA GA KALMA MAI DAIDAITAWA, A TSAKANINMU DA KU" Wannan ayar ta nuna cewa, akidar masu kawo kusanci tsakanin addinai kuskure ce.


وَدِليلُ شَهَادَةِ أَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللهِ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (لَقَدْ جَآءكُمْ رَسُولٌ مِّنْ أَنفُسِكُمْ عَزِيزٌ عَلَيْهِ مَا عَنِتُّمْ حَرِيصٌ عَلَيْكُم بِالْمُؤْمِنِينَ رَؤُوفٌ رَّحِيمٌ).
وَمَعْنَى شَهَادَة أَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللهِ: طَاعَتُهُ فِيمَا أَمَرَ، وَتَصْدِيقُهُ فِيمَا أَخْبَرَ، واجْتِنَابُ مَا نَهَى عَنْهُ وَزَجَرَ، وأَلا يُعْبَدَ اللهُ إِلا بِمَا شَرَعَ.
Dalili akan shaidawa lallai annabi Muhammadu manzon Allah ne, shine fadinSa Madaukaki: "HAKIKA WANI IRIN MANZO DAGA CIKIN KAYUKANKU YA ZO MUKU, ABINDA KE WAHALAR DA KU YANA BUWAYARSA, KUMA MAI KWADAYI NE A GARE KU, GA MUMINAI KUMA MAI TAUSHI NE, MAI JIN KAI".
Ma'anar shaidawa lallai annabi Muhammadu manzon Allah ne, shine: Yin da'a a gare shi cikin abinda yayi umarni, da gaskata shi cikin abinda ya bada labari, da nisantar abinda ya yi hani akansa; ya tsawatar, da cewar kada a bauta wa Allah sai da abinda wannan annabin ya kawo na shari'a.


(1) Mawallafin –رحمه الله- ya ambaci wannan ayar a matsayin dalili kan shaidawa lallai annabi Muhammadu –صلى الله عليه وسلم- Manzon Allah ne, kuma lallai Allah ya karfafa wannan shaidar a cikin ayar da abubuwa uku na karfafa zance, sune: rantsuwar da ake kaddara ta, harafin, da kalmar "kad; wato lallai hakika".
(2) Mawallafin –رحمه الله- ya bayyana, hakikanin ma'anar shaidawa lallai Annabi Muhammadu –صلى الله عليه وسلم- manzon Allah ne, da cewar lallai yana wajaba, ga kowane musulmi namiji da mace, domin tabbatar da wannan kalma;
Yin da'a a gare shi cikin abinda yayi umarni, da gaskata shi cikin abinda ya bada labari, da nisantar abinda ya yi hani akansa; ya tsawatar, da cewar kada a bauta wa Allah sai da abinda wannan annabin ya kawo na shari'a, kuma ya bayyana, salatin Allah da sallamarSa, su kara tabbata a gare shi.
Abinda shaidawa lallai Annabi Muhammadu –صلى الله عليه وسلم- manzon Allah ne ke hukuntawa, shine lallai shi, bawa ne da ba za a bauta mas aba, kuma manzo ne da ba za a karyata shi ba, Wannan kuma yana hukunta:
Mu yi da'a a gare shi cikin dukkan abinda yay i umarni da shi –صلى الله عليه وسلم-.
Saboda shi mai isar da sako ne daga Allah.
Gaskata shi, cikin abinda ya bada labari –صلى الله عليه وسلم-.
Saboda shi mai gaskiya ne, abin gaskatawa –صلى الله عليه وسلم-.
Nisantar abinda ya yi hani, kuma ya yi tsawa;
Ta hanyar ka sanya abinda Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya yi hani akansa ta bangare guda, kai kuma ta wani bangare.
Kada a bauta wa Allah –سبحانه وتعالى- sai da abinda Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya zo da shi;
Cikin wannan kuma akwai raddi ko maida martini ga masu kirkiro addini ('Yan bidi'a).


وَدَلِيلُ الصَّلاةِ، وَالزَّكَاةِ، وَتَفْسِيرُ التَّوْحِيدِ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (وَمَا أُمِرُوا إِلاَّ لِيَعْبُدُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ حُنَفَآءَ وَيُقِيمُوا الصَّلاةَ وَيُؤْتُوا الزَّكَاةَ وَذَلِكَ دِينُ الْقَيِّمَةِ)(1).
ودَلِيلُ الصِّيَامِ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ كُتِبَ عَلَيْكُمُ الصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى الَّذِينَ مِن قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ)(2).
ودَلِيلُ الْحَجِّ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (وَلِلّهِ عَلَى النَّاسِ حِجُّ الْبَيْتِ مَنِ اسْتَطَاعَ إِلَيْهِ سَبِيلاً وَمَن كَفَرَ فَإِنَّ الله غَنِيٌّ عَنِ الْعَالَمِينَ)(3).
Kuma dalili kan sallah da zakkah da kuma fassarar tauhidi shine fadinSa Madaukaki: "BA A UMARCE SU DA KOMAI BA, FACE BAUTA WA ALLAH SUNA MASU TSARKAKE ADDININSU A GARE SHI KUMA MASU KARKATA ZUWA ADDINI GASKIYA, KUMA SU TSAYAR DA SALLAH, SU BADA ZAKKAH, KUMA WANNAN SHINE ADDINI MIKAKKE".
Kuma dalilin azumi shine fadinSa Madaukaki: "YA KU WADANDA SUKA YI IMANI, AN WAJABTA MUKU AZUMI KAMAR YADDA AKA WAJABTA SHI GA WADANDA KE GABANINKU, LA'ALLA KO ZA KU SAMU TAKAWA".
Kuma dalilin hajji shine fadinSa Madaukaki: "KUMA ALLAH YA WAJABTA WA MUTANE HAJJIN DAKINSA GA WANDA YA SAMU HANYAR ZUWA GARE SHI, KUMA WANDA YA KAFIRCE, TO LALLAI ALLAH YA WADATA DAGA TALIKAI".
(1) RUKUNI NA BIYU: SHINE SALLAH:
Sallah itace, Bauta wa Allah ta hanyar aikata ayyuka da zantuka kebantattu, wadanda ake fara su da kabbara, a gama su da yin sallama, kuma itace kashin bayan wannan addinin, kuma hakika an farlanta ta, daga Allah –kai tsaye- zuwa ga AnnabinSa –صلى الله عليه وسلم-, a lokacin da aka yi mi'iraji aka tafi sama da shi.
RUKUNI NA UKU: ZAKKAH:
A harshen larabci, zakkah tana nufin, bunkasa abu da tsarkake shi.
Kuma zakka nau'uka biyu ce, zakkar jiki, da zakkar cikin dukiya.
(2) RUKUNI NA HUDU: AZUMI:
Azumi, a harshen larabci, na nufin kamewa.
A shari'a kuma, ana wani bauta ne ga Allah, ta hanyar kamewa daga ababen da suke karya azumi, tare da niyya, daga ketowar alfijir, zuwa ga faduwar rana.
Kuma azumi yana daga cikin mafi falalar na'ukan ibadodi; domin tattaruwan nau'ukan hakuri guda uku, kuma saboda girman sha'anin azumi ne, ya sanya Allah –سبحانه وتعالى- ya nasabta wa kansa, bada sakamako ga mai azumi.
(3) RUKUNI NA BIYAR: HAJJI:
Hajji, a harshen larabci, yana nufin, ka nufi wani wuri.
A shari'a kuma, Hajji bauta ne ga Allah, ta hanyar zartar da wasu ayyukan harama, daidai da yadda sunnar Annabi –صلى الله عليه وسلم- ta zo da shi.
Kuma hajji, farilla ne aka kowane musulmi, ya yi shi sau daya a tsawon rayuwarsa.


الْمَرْتَبَةُ الثَّانِيَةُ: الإِيمَانُ، وَهُوَ: بِضْعٌ وَسَبْعُونَ شُعْبَةً، فَأَعْلاهَا قَوْلُ لا اله إِلا اللهُ، وَأَدْنَاهَا إِمَاطَةُ الأَذَى عَنِ الطَّرِيقِ، وَالْحَيَاءُ شُعْبَةٌ مِنْ الإِيمَانِ.
وَأَرْكَانُهُ سِتَّةٌ: كما في الحديث (أَنْ تُؤْمِنَ بِاللهِ، وَمَلائِكَتِهِ، وَكُتُبِهِ، وَرُسُلِهِ، وَالْيَوْمِ الآخِرِ، وَتُؤْمِنَ بِالْقَدَرِ خَيْرِهِ وَشَرِّهِ).
وَالدَّلِيلُ عَلَى هَذِهِ الأَرْكَانِ السِّتَةِ: قَوْلُهُ تَعَالَى: (لَّيْسَ الْبِرَّ أَن تُوَلُّواْ وُجُوهَكُمْ قِبَلَ الْمَشْرِقِ وَالْمَغْرِبِ وَلَكِنَّ الْبِرَّ مَنْ آمَنَ بِاللّهِ وَالْيَوْمِ الآخِرِ وَالْمَلآئِكَةِ وَالْكِتَابِ وَالنَّبِيِّينَ).
ودليل القدر: قَوْلُهُ تَعَالَى: (إِنَّا كُلَّ شَيْءٍ خَلَقْنَاهُ بِقَدَرٍ).
MARTABA TA BIYU: ITACE; IMANI;
Kuma imani sifofi ko rassa saba'in da wani abu ne, mafi kololuwarsu shine, fadin LA ILAHA ILLAL LAHU, Kuma mafi kankantarsu itace, kautar da abu mai cutarwa daga hanya, Kuma kunya reshe ne na imani.
Kuma rukunnan imani guda shida ne, kamar yadda ya zo cikin hadisi, "Ka yi imani da Allah, da Mala'ikunSa, da LittatafanSa, da ManzanninSa, da Ranar karshe, kuma ka yi imani da kaddara na alkhairinsa da sharrinsa".
Kuma dalili akan wadannan rukunnan guda shida, fadinSa Madaukaki: "BA KAWAI SHINE ADDINI BA, KU JUYAR DA FISKOKINKU, WAJEN GABAS KO YAMMA BA, AMMA ADDINI SHINE GA WANDA YA YI IMANI DA ALLAH, DA RANAR KARSHE, DA MALA'IKU, DA LITTATAFAI, DA ANNABAWA".
Kuma dalilin kaddara FadinSa Madaukaki: "LALLAI NE MU, KOWANE ABU MUN HALICCE SHI DA KADDARA".
Martaba ta biyu: Imani
Imani a harshen larabci: Sakankancewa cikin gaskatawa.
A shari'a kuma: Imani zance ne na harshe, da kudurin zuci, da aikin gabbai –har da zuciya-, yana karuwa da aikin da'a, kuma yana tawaya da sabo.
Shi imani na shari'a babu makawa, sai ya hada lamura guda biyar.
Ta yadda idan daya daga cikinsu ya samu tasgaro, to an fita daga hakikanin imani, a wurin Ahlus-Sunnah wal Jama'ah.


Menene dalili akan wadannan lamuran guda biyar?
Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "mafi kololuwarsu shine, fadin LA ILAHA ILLAL LAHU", wannan dalili ne, akan zancen baka.
"mafi kankantarsu itace, kautar da abu mai cutarwa daga hanya", wannan kuma aikin gabbai.
"Kunya kuma…", wannan aikin zuciya ne.
Da fadinSa Madaukaki: "WANENE DAGA CIKINKU WANNAN SURAR TA KARA MASA IMANI?" WAnnan dalili ne akan mas'alar karuwar imani, to kuma idan ya zama yana karuwa, to babu makawa zai samu tawaya, kuma batun tawayar addini ya zo karara, cikin fadinSa –صلى الله عليه وسلم-: "Ban ga masu tawayar hankali da addini ba,…", wannan ya nuna addini yana samu tawaya, ko nakasa.


RUKUNNAN IMANI GUDA SHIDA
Imani da Allah
Imani da Mala'iku
Imani da littatafai
Imani da Manzanni
Imani da Ranar karshe
Imani da kaddara mai kyansa da mummunansa


RUKUNIN FARKO: IMANI DA ALLAH, yana hukunta lamura guda hudu:
Imani da samuwar Allah –سبحانه وتعالى-, kuma yak an kasance da lamura guda hudu:
Imani da tauhidin Rububiyyah
Imani da Tauhidin Uluhiyyah
Imani da Tauhidin sunaye da siffofi


Da dalilan hankali
Saboda ahankalce ba zai yiwu ayi tunanin samun halitta ba tare da samuwar wanda ya halicce shi ba, "KO AN HALITTA SU BA DA WANI ABU BA NE, KO KUMA SUNE MASU HALITTAR?".
Da dalilai da ake iya ji ko gani, saboda mutum yakan iya kasancewa cikin bakin ciki da tsanani, sai ya daga hannayensa sama yana cewa, Ya Ubangijina, sai wannan bacin ran yak au, da izinin Allah –سبحانه وتعالى-.


Da dalilai na halitta; saboda "kowane halitta aka haifuwarsa akan akidar musulunci, iyayensa biyu suke mayar da shi bayahude ko banasare, ko bamajuse".


Da dalilai na shari'a; Ibnul kayyim –رحمه الله- ya ambata cewa, lallai babu wata aya a cikin littafin Allah, face a cikinta akwai dalili akan tauhidi.




RUKUNI NA BIYU: IMANI DA MALA'IKU
Mala'iku: Halittu ne da suke boye, Allah ya halitta su daga haske, suna yin da'a wa Allah basa saba masa, suna da rayuka "RUHI MAI TSARKI", da gangan jiki "YA SANYA MALA'IKU JAKADODI, MA'ABUTA FUKA-FUKAI, BIBBIYU, DA UKU-UKU, DA HUDU-HUDU, YANA YIN KARI CIKIN HALITTA, DA ABINDA YA YI NUFI", Suna da hankula da zukata, "HAR IDAN AKA JIJJIGA ZUKATANSU SAI SUCE, MENENE UBANGIJINKU YA FADA?". Muna yin imani da Mala'iku, da kuma abinda Allah ya sanar da mu na sunayensu, (kamar Jibrilu, da Mika'ilu, da Isra'ila), da sifofinsu (BASU SABA WA ALLAH CIKIN ABINDA YA UMARCE SU, KUMA SUNA AIKATA DUKKAN ABINDA AKA UMARCE SU), da ayyukansu (misalin, daukar al'arshi), da dukkan labarum da suka zo, a kansu, a dunkule, da labaru na dalla-dalla.


RUKUNI NA UKU: IMANI DA LITTATAFAI: