طاهر جبريل دكو
_13 _November _2017هـ الموافق 13-11-2017م, 12:25 PM
ترجمة أعلام السنة المنشورة لاعتقاد الطائفة الناجية المنصورة للشيخ الحافظ الحكمي رحمه الله إلى لغة الهوسا
A'lamussunnatil manshurah li'itiqadidda'ifatinnajiyatil mansurah
matashiya
بسم الله الرحمن الرحيم
المقدمة
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya halicci sammai da qasa, kuma Ya sanya duffai da haske sannan kafirai da ubangingijinsu su ke daidaitawa. Kuma Shi ne wanda Ya halicce ku daga laka sannan Ya qaddara (wani) ajali, da wani ajali ambatacce a wurinSa sannan ku kuma kuna tantama. Kuma Shi ne (kadai) Allah a cikin sammai haka nan ma a cikin qasa. Ya na sanin sirrinku da abinda ku ka bayyana kuma Ya na sanin abinda ku ke aikatawa.
Kuma ina shedawa babu abin bauta bisa cancanta sai Allah Shi kadai ba Shi da abokin tarayya, (Shi ne) daya tilo abin nufi da bukatu, bai Haifa ba kuma ba a haife Shi ba, kuma babu wani da ya ke tsara gare Shi, kai! Duk abinda ke cikin sammai da qasa ma na Shi ne, dukkanin su masu bauta ne gare Shi, maqagin sammai da qasa, idan Ya hukunta wani al'amari kawai cewa zai yi da shi kasance sai ya yi ta kasancewa. Kuma Uabangijinka Shi ke halitta kuma Shi ke zaben (wanda Ya so) zabi ba nasu bane. Ya tsarkaka Ya daukaka daga abinda su ke yi na shirka (gare Shi) ba a tambayarShi game da abin da Ya yi, su kuma ana tanbayar su.
Kuma ina shedawa lallai shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa ne. Ya aiko shi da shiriya da addinin gaskiya domin Ya rinjayar da shi bisa dukkanin addinai ko da kuwa mushirikai sun qi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa da sahabbansa wadanda su ka yi hukunci da gaskiya kuma da shi su ka kasance suna adalci.
Da wadanda su ka biyo bayansu bisa kyautatawa, wadanda ba su karkata daga sunna kuma basu daidaita ta da komai, a'a! ita kadai su ke bi kuma da ita su ke riko kuma akanta su ke kashe dukiyoyinsu da lokutansu kuma ita su ke karewa. Da dukkanin wadanda su ka shiga tafarkinsu kuma su ka bi hanyarsu har zuwa ranan da za a sake raya su.
Bayan haka: wannan (littafi ne) takaitacce mai girma mai anfani, mai yawan fa'idoji mai yawan anfani, ya qunshi qa'idoji na addini, kuma ya na kunshe da asalin tauhidin da annabawa su ka yi kira zuwa gare shi, kuma aka sauke littattfai akan shi, (wanda) babu tsira ga wanda ya yi addini da wanin sa, kuma ya na shiryarwa zuwa ga shiga tafarki mai haske kuma hanyar gaskiya mabayyani, a cikin shi (wato littafin) na yi sharhin al'amuran imani da halayensa, da abin da ya ke gusar da shi dukkanin shi ko kuma ya ke kore cikar sa, a cikin sa na ambaci ko wace mas'ala da dalilin ta saboda al'amarinsa ya bayyana kuma hakikaninsa ya fito fili, kuma na takaita akan mazhabar ahlussunna mabiya tafarkin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma na yi watsi da mazhabar masu bin son ziciya 'yan bidi'a saboda ita (mazhabar 'yan bidi'a) ba a ambaton ta sai domin mai da martani da bayanin bacin ta, da kuma aika kifiyoyin sunna akanta. Haqiqa manyan malamai sun dauki nauyin tona asirinta kuma sun yi wallafe – wallafe na musamman akan mai da martani akan ta da nisantar da mutane daga barin ta. Tare da cewa kishiya akan fahimce ta ne da ambaton kishiyar ta, kuma ya fito fili da sanin ka'idojin shi da ma'anarshi. Idna rana ta fito to ba a bukatar wata sheda don nuna cewa gari ya waye.
Kuma idan gaskiya ta bayyana ta fito fili to babu wani abu bayanta in banda bata.
Kuma na rattaba shi akan tsarin tambaya saboda dalibi ya farka ya ankara, sannan sai na biyar da amsar da zai fito da al'amarin fili kuma ba zai rikitar ba. Kuma na ambace shi da suna A'ALAMUSSUNNATIL MANSHURA LI'TIQADIDDA'IFATINNAJIYATIL MANSURA kuma Allah madaukaki na ke roko da Ya sanya shi don neman yardar Shi, kuma ya amfanar da mu da abin da mu ka sani kuma Ya sanar da mu abin da zai anfane mu don ni'ima da falala daga gare Shi. Lallai Shi akan komai mai iko ne kuma game da bayin Shi masani ne mai sassautawa. Kuma gare shi makoma ta ke, kuma Shi ne majibincin mu saboda haka madalla da majibinci kuma madalla da mai taimako.