طاهر جبريل دكو
_1 _November _2017هـ الموافق 1-11-2017م, 03:11 PM
MUƘADDIMAR
RISALA TA IBN ABI ZAID AL ƘAIRAWANI(386)
FASARAR
MUHAMMAD HASAN USMAN
مقدمة رسالة ابن أبي زيد القيرواني المتوفى سنة(386)
ترجمه بلغة هوسا
محمد حسن عثمان
1439
[BISMILLAHI-RRAHMANI-RRAHIM]
Abu Muhammad Abdullahi ɗan Abu Zaid Alƙairawani ALLAH ya jiƙan sa yace:
BABI MAI BAYANI KAN ABUBUWAN DA HARSUNA KE FURTAWA, KUMA ZUKATA KE ƘUDURCEWA DAGA CIKIN AL`AMURRA NA ADDINI NA WAJIBI:
Daga cikin su akwai imani a zuciya da furuci a harshe, cewa ALLAHshine abin bauta ɗaya, babu wani abin bauta face shi kaɗai, baida makamanci, kuma baida tsara, baida ɗa, kuma baida uba, baida abokiyar zama, kuma baida abokin tarayya.
Farkon sa baida farko, sannan ƙarshan sa baida ƙarshe, masu siffantawa baza su iya siffanta yadda yake ba, kuma manazarta baza su iya kewaye sani da al`amurran sa ba, sai dai suyi lura da ayoyin sa, kuma baza su iya nazari ga zatin sa ba, sannan baza su iya mamaya da wani abu na ilimin sa basai dai abin da yaso, kujerar sa ta girmi sammai da ƙassai, kuma kula da su bai masa wahala, dan shi maɗaukakine kuma mai girma.
]ALLAH[ shine masani mai cikakkyan sani, mai juya al`amurra, mai iko akan komai, mai cikakkyan ji da gani, maɗaukaki kuma mai girma, kuma lalle shi ya daidaita a saman al`arshi da zatin sa, kuma yana ko`ina da ilimin sa.
Ya halicci mutun kuma yasan abinda ransa take raya masa ]na alheri ne ko sharri[,yafi kusa da mutun da jijiyar wuyansa, babu wani fure da zai faɗo face ya san da shi, ko wata ƙwaya a ƙarƙashin ƙasa, ko cikin ruwa ko sararin ƙasa face yana rubuce cikin lauhul-mahfuz.
Ya daidaita akan al`arshi, sannan mulkin sa ya mamaye komai, ya nada sunaye kyawawa, da siffofi maɗaukaka, baigushe ba tun azal da dukkan siffofin sa, ya tsarkaka siffofin sa su kasance halittu, ko sunayan sa su kasance farau.
Yayi ma ]annabi [Musa zance, wanda yake ɗaya daga cikin siffofin zatin sa, ba halitta bane daga halittun sa, kuma ya bayyana a dutsi sai ya niƙe saboda girman Ubangiji, kuma lalle Alƙur`ani maganar ALLAHne, ba halitta bane balle yahalaka, ko siffar wata halitta balle ta ƙare.
Ya wajaba yin imani da ƙadara ta alheri ko ta sharri, mai daɗi ko mara daɗi, kuma dukkan su ALLAHUbangijin mu ne ya ƙaddara su, dan shine mai ƙaddara dukkan al`amurra ne, kuma gudanar su na ƙarƙashin hukuncin sa.
Ya san komai kafin kasancewar sa, dan haka sai ya gudana a ƙarƙashin ikon sa, babu wata faɗa ko aiki da bayun sa za suyi face sai ya hukunta shi, kuma ilimin sa ya gabata akan hakan, (ku saurara, mahalicci ya sani, dan shi mai tausayi ne kuma mai cikakkyan sani)([1] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn1)).
Yana ɓatar da wanda ya so, sai ya tozartar da shi cikin adalcin sa, kuma yana shiriyar da wanda ya so, sai ya masa dace na shiriya da falalar sa, kowane ɗaya daga cikin su ana sawwaƙe masa hanyar sa da sanin ALLAH kuma da ikon sa, in ɗan wuta ne ko ɗan aljanna.
ALLAHya tsarkaka wani abu ya kasance cikin mulkin sa wanda bai so shi ba, ko wani ya kasance ya wadatu da shi, ko ya kasance mahaliccin komai face shi, shine Ubangijin bayu da kuma ayyukan su, mai ƙaddara motsawar su da ajalin su.
ALLAH shi ya turo da manzanni dan kafa hujja akan mutane.
Sannan ya cika manzancin sa da gargaɗi da annabta ga annabin sa Muhammad (tsira da amincin ALLAHya tabbata a gareshi), ya sanya shi ƙarshan ma`aika, mai bushara da gargaɗi, mai kira zuwa tafarkin ALLAHbayyananne kamar fitila mai haske da umarnin sa, kuma ya saukar masa da littafin sa tsararre,kuma ya bayyana addinin sa tsayayye da wannan littafin, kuma ya shiriyar da shi zuwa ga hanya meƙaƙƙa.
Ya wajaba yin imani llale ƙiyama zata zo ba kokonto a hakan, kuma lalle ALLAHzai tayar da matattu, zasu dawo kamar halittar su ta farko.
Ya wajaba yin imani lalleALLAHyana riɓinya ladan kyawawan ayyuka, kuma ya yana ma bayu karamci da tuba daga manyan zunubbai, ya gafarta musu ƙananan laifuka in sun nisanci manya-manya, sannan ya sanya wanda bai tuba ba daga manyan zunubbai a cikin ganin damar sa (lalle ALLAH baya gafarta ma wanda ya hadu da shi yana shirka, amma yana gafarta abin da ba shirka ba ga wanda ya so )([2] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn2)) .
Duk wanda ALLAH ya masa azaba a wutar sa to zai fitar da shi da imanin sa, sannan ya sa shi aljannar sa (wanda yayi aiki gwargwadan ƙwayar zarra zai gan shi)([3] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn3)). Kuma za`a fitar da masu manyan zunubbai na al`ummar annabi (tsira da amincin ALLAHya tabbata a gareshi) daga cikin wuta da cetan sa.
Ya wajaba yin imani cewa lalle ALLAHya halicci aljanna, gidan dawwama ne wanda ya tanadar da shi ga masoyan sa, kuma ya girmama su a cikin ta da duba zuwa ga fuskar sa mai girma da ɗaukaka, itace aljannar da ya sauko da annabin sa kuma halifan sa Adam (tsira da amincin ALLAHya tabbata a gareshi) daga cikin ta zuwa ƙasa, kuma sanin sa ya gabata tun tuni da hakan. Kuma ya halicci wuta, sai ya sanya ta gidan dawwama ga wanda ya kafirce masa kuma ya kauce ma ayoyin sa da litattafan sa da manzannin sa, sannan zai sanya su abin katangewa daga ganin sa.
Ya wajaba yin imani lalle ALLAHmaɗaukakin sarki zai zo ranar ƙiyama da mala`iku sahu-sahu, dan yin sakamako na zunubi ko na lada ga al`ummomi, sannan a tsaida skeli dan auna ayyukan bayu, duk wanda nasa yayi nauyi to yana daga cikin masu rabo, sannan za a basu takardun su gwargwadan ayyukan su, wanda aka bashi takardar sa a hannun dama to za a masa hisabi mai sauƙi, amma wanda aka bashi takardar sa a hannun hagu to zai shiga wutar Sa`ira.
Ya wajaba yin imani lalle siraɗi gaskiya ne, bayu zasu ƙetara shi gwargwadan ayyukan su, akwai masu tsira daga gare shi, wanda suka sha banban wajan gaugawar wucewa daga wutar jahannama, wasu ko munanan ayyukan su zasu dirmiyar da su a cikin ta.
Ya wajaba yin imani da ƙoramar alkausar ta Annabi (tsira da amincin ALLAHya tabbata a gareshi),al`ummar sa zata sha shi,duk wanda ya sha ba zaiyi ƙishirwa ba har abada, sannan za a kori duk wanda ya canza addinin Manzan ALLAH(tsira da amincin ALLAHya tabbata a gareshi) daga gare shi.
Ya wajaba yin imani cewa lalle shi imani ya ƙunshi faɗa da baki, da tsarkake zuciya, da kuma aiki da gaɓɓai, yana ƙaruwa da ƙaruwar ayyuka, kuma yana raguwa da raguwar su, dan haka raguwar ayyuka sababi ne na raguwar imani kamar yadda ƙaruwar su sababi ne na ƙaruwar imani. Faɗar imani bai cika sai da aiki, kamar yadda faɗa da aiki basa cika sai da kyakkyawar niyya, haka kuma faɗa da aiki da kyakkyawar niyya ba su cika sai sunyi dai-dai da sunnar Manzan ALLAH(tsira da amincin ALLAHya tabbata a gareshi).
Ya wajaba yin imani cewa ba a kafirta mai kallan alƙibla -musulmi- dan ya aikata zunubi.
Ya wajaba yin imani cewa shahidai suna raye a wajan Ubangijin su ana arzuta su, kuma lalle rayukan mutanan kirki na cikin ni`ima har zuwa tashin ƙiyama, su kuma rayukan matsiyata na cikin azaba har zuwa ranar sakamako.
Ya wajaba yin imani cewa lalle muminai za a fitine su cikin ƙabari kuma za a tambaye su ( ALLAH na tabbatar da muminai da faɗar kalmar shahada a nan duniya da kuma lahira)([4] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn4)).
Ya wajaba yin imani lalle akwai mala`iku masu tsaro wanda ke tare da bayu suna rubuta ayyukan su, duk da haka babu abinda zai ɓuya na ayyukan su ga ilimin Ubangiji, kuma lalle mala`ikan mutuwa na karɓar rayuka da izinin Ubangijin sa.
Ya wajaba yin imani cewa mafificin zamani shine wanda suka yi zamani da Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) kuma suka yi imani da shi, sannan zamani mai bi masa, sannan mai bi masa.
Ya wajaba yin imani cewa mafi girma da ɗaukaka a cikin sahabbai sune halifofi shiriyayyu:Abubakr sannan Umar sannan Usman sannan Aliyyu ALLAH yarda da su.
Kada a ambaci ɗaya daga cikin sahabban Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a garesu) sai dai ambato mai kyau, sannan a bar tattauna abinda ya faru tsakanin su na yaƙe-yaƙe, dan su suka cancanci a nema musu uzuri, da kuma yi musu kyakkyawan zato.
Ya wajaba yin ɗa`a ga shuwagabanni na musulmi da kuma malamai, da bin magabata na ƙwarai da koyi da su, da nema musu gafara, da barin jayayya da gardama a addini, da barin abinda yan bidi`a suka ƙirƙira.
ALLAH yayi daɗin tsira ga shugaban mu annabin mu Muhammad da iyalan sa da matan sa da zuriyar sa baki ɗaya.
٭٭٭
[/URL]([1]) Suratl mulk, aya: 14.
(http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftnref1)([2])Suratu nisa`i, aya: 48.
([3])Suratul zalzala, aya: 7.
[URL="http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftnref4"] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftnref3)([4])Suratu Ibrahim, aya: 27.