تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : Tarihin annabi (tsira da amincin allah ya tabbata a gareshi) da sahabban sa goma a taƘaice


طاهر جبريل دكو
_20 _October _2017هـ الموافق 20-10-2017م, 06:30 PM
TARIHIN ANNABI (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI) DA SAHABBAN SA GOMA A TAƘAICE

Wallafar Abu Muhammad Abdul Ganiyyi ɗan Abdul wahid Almaƙdissi (544-600 H)
Fasarar
Muhammad Hassan Usman

مختصر سيرة النبي صلى الله علية وسلم وسيرة أصحابه العشرة
تأليف أبي محمد عبد الغني بن الواحد المقدسي (544-600)

ترجمه بلغة هوسا
محمد حسن عثمان


1439





ABUBUWAN DA KE CIKI


ABUBUWAN DA KE CIKI 2 (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_Toc495849615)
Gabatarwar me fasara: 4 (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_Toc495849616)
Bismillahi-rrahmani-rrahim.. 5 (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_Toc495849617)
]DANGANTAKAR MANZAN ALLAH (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI) DA DANGANTAKAR MAHAIFIYAR SA, DA HAIFUWAR SA, DA RENAN SA, DA MUTUWAR MAHAIFAN SA[. 6 (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_Toc495849618)
FASALI NA SUNAYAN SA (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI). 9 (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_Toc495849619)
FASALI:]Rayuwar sa (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) a Makka, da fitar sa tare da baffan sa Abu ɗalib Zuwa Sham, da auran sa da kadija .[ 10 (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_Toc495849620)
]FARKON WAHAYI[ 10 (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_Toc495849621)
HIJIRAR SA (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI) 11 (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_Toc495849622)
MUTUWAR SA (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI). 11 (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_Toc495849623)
FASALI: YAYAN MANZAN ALLAH (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI)[. 13 (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_Toc495849624)
FASALI NA HAJIN SA DA UMARAR SA (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI). 14 (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_Toc495849625)
FASALI NA YAƘOƘIN SA (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI) 14 (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_Toc495849626)
FASALI NA MARUBUTAN ANNABI (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI) DA MA`AIKAN SA. 15 (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_Toc495849627)
FASALI NA BAFFANNIN MANZAN ALLAH DA GOGGONIN SA (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI). 17 (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_Toc495849628)
MATAYAN ANNABI (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI TARE DA SU). 20 (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_Toc495849629)
HADIMAN MANZAN ALLAH (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI). 23 (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_Toc495849630)
DAWAKAN MANZAN ALLAH (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI). 25 (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_Toc495849631)
]MAKAMAN MAZAN ALLAH (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI)]. 26 (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_Toc495849632)
FASALI NA SIFFOFIN MANZAN ALLAH (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI). 27 (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_Toc495849633)
FASALI NA HALAYAN MANZAN ALLAH (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI). 30 (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_Toc495849634)
MU`UJIZOZIN MANZAN ALLAH (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI). 32 (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_Toc495849635)
FASALI NA TARIHIN SAHABBAN MANZAN ALLAH (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE SU) SU GOMA. 38 (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_Toc495849636)
ABU BAKR SIDDIƘ ALLAH YARDA DA SHI. 38 (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_Toc495849637)
ABU HAFS UMAR ƊAN ALKHAƊƊAB ALLAH YARDA DA SHI. 40 (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_Toc495849638)
BABAN ABDULLAH USMAN ƊAN AFFAN ALLAH YARDA DA SHI. 41 (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_Toc495849639)
ABUL HASAN ALIYYU ƊAN ABU ƊALIB ALLAH YARDA DA SHI. 42 (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_Toc495849640)
ABU MUHAMMAD ƊALHA ƊAN UBAIDULLAH ALLAH YARDA DA SHI. 43 (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_Toc495849641)
ABU ABDILLAH AZZUBAIR ƊAN AWWAM ALLAH YARDA DA SHI. 44 (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_Toc495849642)
ABU IS`HAƘ SA`AD ƊAN ABI WAƘƘAS ALLAH YARDA DA SHI. 45 (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_Toc495849643)
ABUL A`AWAR SA`ID ƊAN ZAID ƊAN AMR ALLAH YARDA DA SHI. 46 (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_Toc495849644)
ABU MUHAMMAD ABDURRAHMAN ƊAN AUF ALLAH YARDA DA SHI. 46 (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_Toc495849645)
ABU UBAIDA AMIR ƊAN ABDULLAH ƊAN ALJARRAH ALLAH YARDA DA SHI. 47 (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_Toc495849646)



Gabatarwar me fasara:

Godiya ta tabbata ga ALLAHubangijin talikai, muna kara gode masa kuma muna neman taimakon sa da gafarar sa, mun shaida babu abin bauta da gaskiya sai ALLAH, kuma mun shaida lalle annabi Muhammadu bawan sa ne kuma ma`aikin sa ne, tsira da amincin ALLAHsu tabbata a gareshi da iyalan gidan sa da sahabban sa da wanda suka biyo baya da kyautatawa. Bayan haka:
Haƙiƙa ALLAHma ɗaukakin sarki ya zabi wannan al`ummar ta kasance mafificiyar al`umma, kuma ya yardar mata musulinci shine addini na gaskiya,ta hanyar fiyayye kuma zaɓaɓɓe, shugaban ɗiyan Adamu baki ɗaya, wato Annabi Muhammdu (tsira da amincin ALLAHya tabbata a gareshi) kenan.
Lalle ne zuwan Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) duniya shiriya ne ga al`umma daga bata, kuma haske ne me kauda duhun shirka da bidi`a da jahilci. ALLAH maɗaukakin sarki ya masa cikakkiyar sura da kuma kyawawan halaye, wanda ya kamata duniya baki ɗaya mu bishi kuma muyi koyi da shi dan mu samu rabo duniya da lahira.
Haƙiƙa babu yadda za`ayi hakan ya samu har sai mun karanci tarihin rayuwar sa da na sahabban sa wanda suka bada kansu da dukiyoyin su dan ɗaukaka wannan addini. Shiyasa malamai suka rubuta manya-manyan litattafai a kan haka, ko kafin su ma Al`ƙur`ani me girma ya bamu cikakken tarihin Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) da sahabban sa.
Ya kai ɗan uwana mai karatu! Wannan littafi dake hannun ka yana ɗaya daga cikin taƙaitattun litattafan tarihin Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) masu fa`ida sosai, shiyasa ma nayi himma dan fasara shi da harshan hausa; domin ka anfana da shi, kuma ya ƙara sa maka san Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) da sahabban sa, da kuma bin tafarkin su.
A ƙarshe ina rokon ALLAH maɗaukakin sarki ya datar damu da yin aiki na ƙwarai da kyakkyawar niyya, kuma ya karɓe su amin…
Sallama da salati su tabbata ga shugaban mu annabi Muhammadu da iyalan sa da sahabban sa da wanda suka biyo bayan su da kyautatawa.
MUHAMMAD HASAN USMAN
12/1/1439
Bismillahi-rrahmani-rrahim

Shehin Malami Kuma Shugaba Masani, Baban Muhammad Abdul Ganiyyi ɗan Abdul Wahid Al maƙdissiALLAHyarda da shi yace: yabo ya tabbata ga ALLAH mahalaccin sama da ƙasa, mahalaccin haske da duhhwai, me tara halittu rana rarrabewa; dan rabautar masu kyautatawa da taɓewar matsiyata.
Na sheda babu abin bauta da gaskiya saiALLAH,shi kaɗai ba shida abokin tarraya, shahada ce wadda mafaɗin ta zai rabauta ranar sakamako. ALLAH yayi daɗin tsira ga shugaban manzanni da annabawa annabi Muhammadu, da iyalan sa da sahabban sa ma su girma.
Wannan taƙaitattun kalmomi ne a kan halayan shugaban mu kuma annabin mu zaɓaɓɓe, Muhammadu (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi), wanda babu wani musulmi da zai wadata da su. ALLAH ya anfanar da mu, da wanda ya karanta ko ya saurara.


]DANGANTAKAR MANZAN ALLAH (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI) DA DANGANTAKAR MAHAIFIYAR SA, DA HAIFUWAR SA, DA RENAN SA, DA MUTUWAR MAHAIFAN SA[.

[DANGARTAKAR SA]:
Sai mu fara da dangantakar sa:
Shine baban Alƙasim, Muhammadu ɗan Abdullahi ɗan Abdul Muɗɗalib ɗan Hashim ɗan Abdu Manaf ɗan ƙusai ɗan kulab ɗan Murra ɗan ka`ab ɗan Lu`ai ɗan Galib ɗan Fihr ɗan Malik ɗan Nadr ɗan kinana ɗan Malik ɗan khuzaima ɗan Mudrika ɗan Ilyas ɗan Mudar ɗan Nizar ɗan Ma`ad ɗan Adnan ɗan Udad ɗan Almuƙawwim ɗan Nahur ɗan Tairah ɗan Ya`rub ɗan Yashjub ɗan Nabit ɗan Isma`il ɗan Ibrahim(badaɗin me rahama) ɗan Tarih( shine Azar) ɗan Nahur ɗan Saru`uɗan Ra`u ɗan Falikh ɗan Aibar ɗan shalikh ɗan Arfakhdash ɗanSam ɗan Nuh ɗan Lamk ɗan Muttushalkh ɗan Akhnukh( shine annbi Idris kamar yadda suke faɗa, kuma shine farkon ɗan Adam wanda ALLAH ya bashi annabta, kuma farkon wanda yayi rubutu) ɗan Yarda ɗan Mahlil ɗan ƙainan ɗan Yanashɗan Shith ɗan Adam (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi).
Muhammadu ɗan Is`haƙ ɗan Yasar Al`madany shine ya ambaci wannan dangantakar a ɗaya daga cikin ruwayoyin sa.
Malamai sun haɗu a kan ingancin dangantakar manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) har zuwa Adnan, kuma sunyi saɓani a waɗan da suka biyo bayan sa.
Ƙuraish shine ɗan fihr ɗan Malik, wasu kuma suka ce shine Annadr ɗan Kinana.


[MAHAIFIYAR ANNABI TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI[
Mahaifiyar Annabi (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) itace Aminatu ɗiyar Wahb ɗan Abdu Manaf ɗan Zuhra ɗan Kulab ɗan Murra ɗan Ka`ab ɗan Lu`ai ɗan Galib.
[HAIHUWAR SHI TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI]
An haifi Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) a Makka a shekarar giwa([1] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn1)), biyu ga watan rabi`ul awwal, a ranar litinin. Wasu kuma suka ce an haife shi shekara talatin bayan shekarar giwa, Wasu kuma suka ce shekara arba`in bayan shekarar giwa. Amma ingantacciyar Magana ita ce Magana ta farko.
]MUTUWAR MAHAIFIYAR MANZAN ALLAH TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI DA MAHAIFIN SA DA KAKAN SA[.
Mahaifin Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) Abdullahi ɗan Abdul Muɗɗalib ya rasu a lokacin da Manzan ALLAHya keda wata ashirin da takwas. Wasu kuma suka ce ya nada wata bakwai, wasu ko suka ce ya rasu a Daru-nnabiga ana ɗauke da cikin sa, wasu ko suka ce ya rasu a Abwa` tsakanin Makka da Madina.
Abu Abdillah Azzubair ɗan Bakkar Azzubaidi yace: Abdullahi ɗan Abdul Muɗɗalib ya rasu a Madina lokacin da Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya keda wata biyu.
Mahaifiyar sa ta rasu ya nada shekara hudu. Sannan kakan sa ya rasu ya nada shekara takwas.
Wasu suka ce: Mahaifiyar sa ta rasu ya nada shekara shida.
[RENAN SA (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI) [.
Suwaiba kuyangar Abu lahab ce ta reni Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi), tare da Hamza ɗan Abdul Muɗɗalib da Abu Salama (Abdullahi ɗan Abdul Asad al`makhzumi). Ta rene su ne da nonon ɗan ta Masruh. Sannan sai Halimatu ɗiyar Abu Zu`aib Assa`adiyya ta rene shi.


FASALI NA SUNAYAN SA (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI).

Jubair ɗan Muɗ `im yayi ruwaya cewa: Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) yace: nine Muhammad, nine Ahmad, nine Al`mahy (wanda ALLAH zai shafe kafirci ta hannu na), kuma nine Al`hashir (wanda ALLAH zai tayar da mutane baya na), kuma nine Al`Akib (wanda babu wani annabi baya na), Bukhari da Muslim suka rawaito shi. Sannan Abu Musa Abdullahi ɗan ƙais yayi ruwaya cewa: Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya zana mana sunayan sa, daga cikin su akwai wanda muka kiyaye, yace: nine Muhammad, nine Ahmad, nine Al`muƙaffi([2] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn2)), nine annbin tuba, nine annabin rahama. A wata ruwaya kuma yace: nine annabin Malhama (shine yaƙi), hadisi ne ingantacce daga Muslim. Sannan Jabir ɗan Abdullahi yayi ruwaya cewa: Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) yace: nine Ahmad, nine Muhammad, nine Al`hashir, nine Al`mahi (wanda ALLAH zai shafe kafirci ta hannu na), idan ƙiyama ta tashi tutar masu godiya tana tare dani, kuma nine shugaban Manzanni, kuma me ceto.
ALLAH me girma da buwaya ya kira shi a cikin littafin sa me girma da Bashiran([3] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn3)), da Naziran([4] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn4)), da Ra`uf([5] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn5)), da Rahim([6] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn6)), da Rahama ga talikai.


FASALI:]Rayuwar sa (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) a Makka, da fitar sa tare da baffan sa Abu ɗalib Zuwa Sham, da auran sa da kadija .[

Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya rayu maraya a wajan kakan saAbdul Muɗɗalib sannan baffan sa Abu ɗalib ɗan Abdul Muɗɗalib ya karɓe shi.
Haƙiƙa ALLAH maɗaukakin sarki ya tsarkake shi daga dauɗar jahiliyya da kuma dukkan aibi, sannan ya bashi dukkan kyawawan halaye, har ya kasance ba a sanshi da wani suna a cikin mutanan sa ba face Al`amin([7] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn7)); saboda abinda suka gani na amanar sa da gaskiyar sa da tsarkakar sa.
A lokacin da ya kai shekara sha biyu ya fita zuwa garin Sham tare da baffan sa Abu ɗalib, har suka isa Busra, sai Bahira(me bauta a addinin nasara) ya ganshi kuma ya gane shi da siffofin sa, sai ya kama hannun sa yace: wannan shine shugaban talikai, wannan shine Manzan ubangijin talikai, wannan shi ne wanda ALLAH zai aiko rahama ga talikai. Sai aka ce masa: waya sanar da kai haka? Sai yace: lokacin da kuka gabato daga wannan dutsan Babu wata itaciya ko dutse face sai da yayi sujada, alhali basa yin sujada sai ga Annabi, kuma muna da labarin sa a cikin litattafan mu. sannan ya nemi Abu ɗalib ya mayar da shi saboda kar yahudawa su cutar da shi.
Sannan ya fita karo na biyu garin Sham tare da Maisara (yaran kadija ALLAH ya yarda da ita) wajan kasuwanci kafin ya aure ta, har suka isa garin Busra, sai ya sayar da hajar sa.
A lokacin da ya kai shekara ashirin da biyar ya auri kadija amincin ALLAH ya tabbata gareta.
]FARKON WAHAYI[

A lokacin da Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya kai shekara arba`in ALLAH ya keɓance shi da karamar sa, kuma ya aiko shi da manzanci.
Jibrilu yazo masa da wahayi yana cikin kogon Hira (wani dutse ne a garin Makka). Ya zauna a garin Makka shekara goma sha uku. Wasu ko suka ce shekara goma sha biyar, wasu kuma su kace shekara goma, amma maganar farko tafi inganci.
Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya kasance yana fuskantar baitul maƙdis idan yana salla tsawan zaman sa a Makka, amma duk da haka baya juya ma Ka`aba baya, yana hadawa da saitin ta. Bayan da Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) yazo Madina ya fuskanci baitul maƙdis wata goma sha bakwai ko sha shida yana salla.
HIJIRAR SA (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI)

Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) yayi hijira zuwa Madina tare da Abu bakr siddiƙ da yaran sa Amir ɗan fuhaira (ALLAH yarda da su). Abdullahi ɗan Uraiƙiɗ shine jagoran su, kafiri ne be musulun ta ba. Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya zauna a Madina shekara goma.
MUTUWAR SA (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI).

Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya rasu ya nada shekara sattin da uku, wasu ko suka ce sattin da biyar, wasu kuma suka ce sattin, amma maganar farko tafi inganci. Ya rasu ne ranar litinin bayan hantsi ya ɗaga,sha biyu ga watan rabi`ul awwal, wasu ko suka ce a biyu ga wata, wasu kuma suka ce a farkon watan ne ya rasu, (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi).
An binne shi a daran laraba, wasu ko suka ce a daran talata. Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) yayi jinya kwana goma sha biyu kafin ya rasu, wasu ko suka ce kwana goma sha huɗu ne.
Aliyyu ɗan Abu ɗalib ne ya masa wanka, tare da baffan saAl`abbas da Alfadlu ɗan Al`abbas da ƙusam ɗan Al`abbas da Usama ɗan Zaid da shuƙran,sannan Aus ɗan khauli Al`Ansari ma ya halarta. Sannan a ka masa likafani da yadi guda uku yan Suhuliyya (wani gari ne a yaman) babu riga balle rawani. Sannan musulmi suka masa salla ɗaya bayan ɗaya ba tare da limami ba. An shunfiɗa masa wata shunfiɗa ja wadda yake rufa da ita.
Al`abbas da Aliyyu da Alfadlu da ƙusam da shuƙran ne suka shiga cikin ƙabarin sa, sannan a ka rufe da birgi tara.
An binne shi ne a gurin da ALLAH ya karɓi ran sa, dai-dai shunfiɗar sa. ALLAHad ([8] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn8)) shi ne irin ƙabarin da a ka gina masa a ɗakin A`isha (ALLAH yarda da ita). Sannan a ka binne Abu Bakr da Umar(ALLAH yarda da su) a tare da shi cikin dakin.


FASALI: YAYAN MANZAN ALLAH (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI)[.

Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya nada yaya maza uku:
Alƙasim: wanda da sunan sa a kema Manzan ALLAH alkunya. An haife shi a Makka kafin annabta, kuma ya rasu ya nada shekara biyu.
Abdullahi: ana ce masa Aɗɗayyib da Aɗɗahir; saboda an haife shi a cikin musulinci, wasu ko suka ce wani ɗan ne da wannan sunan. Amma maganar farko it ace dai-dai.
Ibrahim: an haife shi a Madina kuma ya rasu a cikin ta a shekara ta goma, yana da wata goma sha bakwai ko sha takwas.
Wasu sun ce Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya nada ɗa me suna Abdul uzza, amma de ALLAH me girma da buwaya ya tsarkake shi daga hakan, kuma ya mishi tsari.
YAYA MATA:
Zainab: Abul`As ɗan Arrabi`u ɗan Abdul Uzza ɗan Abdu shams ne ya aure ta, shi ko ɗan yar uwar mahaifiyar ta ne, sunan mahaifiyar sa hala yar khuwailid.
Ta haifa masa Aliyyu (ya rasu yana ƙarami), da Umama wacce Annabi (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya ɗauke ta yana salla. Ta girma har Aliyyu ya aure ta bayan rasuwar Faɗima (ALLAH ya yarda da su ).
Faɗima: ɗiyar Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi), Aliyyu ɗan Abu ɗalib ne ya aureta. Ta haifa masa Alhasan da Alhusaini da Muhassin (ya rasu yana ƙarami), da Ummu Kulsum wadda Umar ɗan khaɗɗab ya aura, da Zainab wadda Abdullahi ɗan ja`afar ɗan Abu ɗalib ya aura.
Ruƙayya: ɗiyar Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi),Usman ɗan Affan ne ya aure ta har ta rasu a wajan sa, sannan ya auri Ummu Kulsum ita ma ta rasu a wajan sa.
Ruƙayya ta haifi ɗa me sunan Abdullah,wanda ake ma Usman alkunya da shi.
A kan haka yayan Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) mata haudu ne, babu saɓani,sannan maza uku ne a magana mafi inganci. Farkon wanda a ka haifa shi ne Alkasim sannan Zainab sannan Ruƙayya sannan Faɗima sannan Ummu Kulsum, sannan a cikin musulinci an haifi Abullahi da Ibrahim a Madina.
Duka yayan Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) daga kadija ne banda Ibrahim, shi ɗan Mariya Alkibɗiyya ne. Kuma dukkan su sun rasu kafin Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) banda Faɗima, dan ita ta rayu bayan sa da wata shida.
FASALI NA HAJIN SA DA UMARAR SA (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI).

Hammam ɗan yahya yayi ruwaya daga ƙatada cewa: na tambayi Anas: so nawa Annabi (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) yayi haji? Sai yace: yayi haji guda da umara hudu, umara ta farko lokacin da mushirikai suka tsare shi zuwa ka`aba, ta biyu ko a shekara me zuwa lokacin da yayi sulhu da su, da umarar sa wadda ya ɗau harami a ji`irrana, inda a ka raba ganimar yaƙin hunaini a watan zulƙi`ida, da umarar sa wadda yayi tare da hajin sa. Bukhari da Muslim suka rawaito shi. Wannan duk ya kasance ne a Madina, amma ba`a san yayi haji ko umara ba lokacin yana makka. Kawai yayi hajin ban kwana ne, har yace ma mutane: tana yuwa baza ku sake gani na ba daga wannan shekarar.
FASALI NA YAƘOƘIN SA (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI)

Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) yayi yaki ashirin da biyar da kan sa, wannan ita ce shahararriyar magana. Abu Ishaƙa ne ya faɗa, da Abu ma`shar da Musa ɗan Uƙba da sauran su.
wasu ko su ka ce ashirin da bakwai ne.
Akwai ƙananan yaƙoƙi da tura yan rundunoni da yayi kimanin hamsim ko kusan haka.
A cikin su Ya shiga hilin daga so tara, a yaƙin Badar da yaƙin Uhud da yaƙin Khandaƙ da yaƙin Bani ƙuraiza da yaƙin Almusɗaliƙ da yaƙin Khaibar da Fathu Makka da yaƙin Hunaini da yaƙin Ɗa`if.
Wasu suka ce haƙiƙa yayi yaƙin wadil ƙura da yaƙin algaba da yaƙin bani-nnadir.
FASALI NA MARUBUTAN ANNABI (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI) DA MA`AIKAN SA.

Abu Bakr siddiƙ ya yima annabi (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) rubutun ]wahayi[, da Umar ɗan Alkhaɗɗab da Usman ɗan Affan da Aliyyu ɗan Abu ɗalib da Amir ɗan Fuhaira da Abdullahi ɗan Al`arƙam azzuhri da Ubayyu ɗan Ka`ab da sabit ɗan ƙais ɗan shammas da Khalid ɗan Sa`id ɗan Al`as da Hanzala ɗan Arrabi`u Al`asadi da Zaid ɗan sabit da Mu`awiya ɗan Abu Sufyan da shurahbilu ɗan Hasana.
Amma Mu`awiya ɗan Abu Sufyan da Zaid ɗan sabit sunfi lazimtar sa.
Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya aiki Amr ɗan Umayya addamri wajan Annajashi] sarkin Habasha[, sunan sa As`hama (ma`anar sa kyauta), sai ya amshi wasiƙar Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) yana karanta ta har ya sauka daga gadan sarauta sannan ya zauna a ƙasa. Sai ya musulinta kuma ya kyautata musulincin sa. Hakan ya kasance ne lokacin da Ja`afar ɗan Abu ɗalib ya je da abokanan sa. Ya inganta cewa annabi (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) yayi masa salla ranar da ya rasu. Anyi ruwaya cewa ba a gushe ba a na ganin haske cikin ƙabarin sa.
Sannan Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya aiki Dihya ɗan khalifa Alkalbi zuwa ga ƙaisar sarkin Rum, sunan sa Hiraƙl, sai ya nemi sani kan annabi (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi), bayan haka ya tabbatar da gaskiyar annabtakar sa. Yayi nufin shiga musulinci amma rumawa basu yarda ba, dan haka sai yaƙi dan gudun gushewar mulkin sa.
Sannan Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya aiki Abdullahi ɗan Huzafa Assahami zuwa ga Kisra sarkin Farisa, sai ya ciccira wasiƙar Annabi (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi), daga jin haka sai Manzan ALLAH yace: ALLAH ya tarwatsa mulkin sa. Sai ALLAH ya tarwatsa mulkin sa da na mutanan sa.
Sannan Annabi (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya aiki Haɗib ɗan Abu Balta`a Allakhmi zuwa ga Almuƙauƙis sarkin Iskandariyya da Masar, sai ya faɗi kyakyawar Magana, amma be musulinta ba, sannan ya ba Annabi (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) kyautar Mariyatul Ƙibɗiyya da yar uwar ta Sirin. Sai Manzan ALLAH ya ba Hassan ɗan Sabit kyautar Sirin, har ta haifar masa Abdu-rrahman.
Sannan Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya aiki Amr ɗan Al`as zuwa ga sarakunan Umman Jaifar da Abd yayan Aljulandi,yan ƙabilar Al`azd ne, amma Jaifar shine shugaba , sai suka musulinta kuma suka bada gaskiya, sannan suka barwa Amr kula da lamarin zakka, amma yin hukunci a tsakanin su. Be gushe ba a can har sai da Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya rasu.
Sannan Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya aiki Saliɗ ɗan Amr Al`amiri zuwa Yamama wajan Hauza ɗan Aliyyu Alhanafi, sai ya girmama shi kuma ya bashi kyakkyawan masauki, sannan ya rubuta ma Manzan ALLAH cewa: lalle kayi kira zuwa ga kyakkyawan abu, ni kuma nine me magane da sunan mutane na kuma mawaƙin su, ina so ka bani ragamar wasu al`amurra , sai Annabi (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya ki, dan haka be musulinta ba. Ya rasu a lokacin fatahu Makka.
Sannan Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya aiki Shuja`u ɗan Wahb Al`asadi zuwa ga Alharis ɗan Abu Shamir Algassani sarkin Al`balƙa`u ta ƙasar Sham. Shuja`u yace: sai na iske shi a Guɗatu Dimashƙ([9] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn9)), ya karanta wasiƙar Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) sannan yayi wurgi da ita, kuma yace zanje gare shi. Haƙiƙa yayi nufin haka amma ƙaisar ]sarkin Rum[ ya hana shi.
Sannan Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya aiki Al`muhajir ɗan Abi Umayya Almakhzumi zuwa ga Alharis Alhimyari ɗaya daga cikin sarakunan ƙasar Yaman.
Sannan Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya aiki Al`ala`u ɗan Alhadrami zuwa ga Almunzir ɗan Sawi Al`abdi sarkin Bahrain,ya rubuta masa wasiƙa ta kira zuwa ga musulinci, sai ya musulinta kuma ya bada gaskiya.
Sannan Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya aiki Abu musa Al`ash`ari da Mu`az ɗan Jabal ALLAH yarda da su zuwa ƙasar Yaman baki daya da kira zuwa ga musulinci, sai mutanan ƙasar da sarakunan su suka musulinta ba tare da yaƙi ba.
FASALI NA BAFFANNIN MANZAN ALLAH DA GOGGONIN SA (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI).

Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya nada baffani goma sha ɗaya, daga cikin su akwai:
Alharis: shine babban ɗan Abdul Muɗɗalib, kuma da shi ake masa alkunya. An samu sahabbai daga cikin yayan sa da jikokin sa.
Ƙusam: ya rasu yana ƙarami. Shi ɗan uwa ne ga Haris na wajan uwa.
Azzubair ɗan Abdul Muɗɗalib: yana daga cikin manya manyan ƙuraishawa. Ɗan sa Abdullahi ɗan Azzubair ya halarci yaƙin Hunaini tare da Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) kuma ya tabbata. Yayi shahada a Ajnadaini([10] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn10)). An rawaito cewa yayi gumurzu da mutun bakwai, ya kashe su suma suka kashe shi.
Sannan daga cikin yayan Azzubair akwai Adduba`a, sahabiyace, Da Ummul hakam wadda ta rawaito hadisai daga Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi).
Hamza ɗan Abdul Muɗɗalib: zakin ALLAH da Manzan sa, kuma ɗan uwa ga Manzan ALLAH na shayarwa. Ya musulinta a farkon musulinci, sannan yayi hijira zuwa Madina, ya halarci yaƙin Badar, sannan yayi shahada a yaƙin Uhudu. Ya nada ɗiya ɗaya.
Baban Alfadlu Al`abbas ɗan Abdul Muɗɗalib: ya musulinta kuma ya kyautata musulincin sa,sannan yayi hijira zuwa Madina. Ya girmi Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) da shekara uku.
Al`abbas ya nada yaya maza goma: Alfadlu da Abdullah da ƙusam, dukkan su sahabbai ne. Ya rasu a MAdina shekara ta talatin da biyu hijira a halifancin Usmane ɗan Affan.
Al`abbas da Hamza su kaɗai ne suka musulinta a cikin baffanninManzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi).
Abu ɗalib ɗan Abdul Muɗɗalib: sunan sa Abdu manaf, ɗan uwa ne na wajan uwa ga Abdullahi(mahaifin Manzan ALLAH tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi), da kuma Atika(wadda tayi mafarki na yaƙin Badar). Mahaifiyar su ita ce Faɗima ɗiyar Amr ɗan A`iz ɗan Imran ɗan Makhzum.
Daga cikin yayan Abu ɗalib akwai Ɗalib (ya rasu yana kafiri), da Aƙilu da Ja`afar da Aliyyu da Ummu Hani, dukkan su sahabbai ne. Sunan Ummu Hani Fatikha, wasu ko su kace Hindu.
Sannan ance Jumana tana daga cikin yayan sa.
Abu Lahab ɗan Abdul Muɗɗalib: sunan sa Abdul Uzza, mahaifin sa ya masa wannan alkunyar ne saboda kyawan fuskar sa. Daga cikin yayan sa akwai Utba da Mu`attib, wanda suka tabbata tare da Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) a ranar Hunaini, da Durratu, dukkan su sahabbai ne. sannan akwai Utaiba wanda zaki ya hallaka shi a Zarƙa`u cikin ƙasar Sham, saboda kafircewar sa ga kiran Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi).
Abdul Ka`aba.
Hajal: sunan sa Almugira.
Dirar: ɗan uwa ne na wajan uwa ga Al`abbas.
Algidaƙ: an yi masa wannan sunan ne saboda yawan kyautar sa da ciyarwar sa.
Goggonnin Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) su shida ne:
Safiyya ɗiyar Abdul Muɗɗalib: ta musulinta kuma tayi hijira. Ita ce mahaifiyar Azzubair ɗan Awwam. Ta rasu a halifancin Umar ɗan Alkhaɗɗab. Ta kasance yar uwa ta wajan uwa ga Hamza.
Atika ɗiyar Abdul Muɗɗalib: ance ta musulinta, ita ce wadda tayi mafarki na yaƙin Badar. Abu Umayya ɗan Almugira ɗan Abdullahi ɗan Umar ɗan Makhzum ne ke auranta. Ta haifar masa Abdullahi da Aslam, dukkan su sahabbai ne, da kuma Zuhaira da Ƙariba Alkubra.
Urwa ɗiyar Abdul Muɗɗalib: Umair ɗan Wahb ɗan Abduddar ɗan Ƙusai ne ke auranta, ta haifar masa Ɗulaib ɗan Umair, yana daga cikin wanda suka yi hijira na farko, yayi shahada a Ajnadaini, sannan be bar yaya ba.
Umaima ɗiyar Abdul Muɗɗalib: Jahash ɗan Ri`ab ne ke auranta, kuma ta haifar masa Abdullahi wanda yayi shahada a yaƙin Uhudu, da Abu Ahmad Al`a`amaAshsha`ir, sunan sa Abdu, da Zainab matar Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi), da Habiba da Hamna,dukkan su sahabbai ne, da Ubaidullah ɗan Jahash, ya musulinta sannan ya zama kirista, ya rasu a Sham yana kafiri.
Barra ɗiyar Abdul Muɗɗalib: Abdul Asad ɗan Hilal ɗan Abdullahi ɗan Umar ɗan Makhzum ne ya aure ta. Ta haifar masa Abu salama, sunan sa Abdullahi, shine mijin Ummu salama kafin annabi (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi). Sannan Abu Ruhm ɗan Abdul Uzza ɗan Abu ƙais ya auri Barra bayan Abdul Asad, ta haifar masa Sabra.
Ummu Hakim: sunan ta Albaida`u ɗiyar Abdul Muɗɗalib. Kuraiz ɗan Rabi`a ɗan Habib ɗan Abdu Shams ɗan Abdu Manaf ne ya aure ta. Ta haifar masa Urwa, wadda ita ce mahaifiyar Usman ɗan Affan.


MATAYAN ANNABI (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI TARE DA SU).

Farkon wadda Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya aura itace Khadija ɗiyar Khuwailid ɗan Asad ɗan Abdul Uzza ɗan ƙusai ɗan kulab. Ya aure ta ya nada shekara ashirin da biyar. Ta kasance tare da shi har lokacinda ALLAH ya aikoshi. Ta kasance me temakon sa da gaskiya . ta rasu kafin hijira da shekara uku a mafi ingancin zance. Wasu ko suka ce kafin hijira da shekara biyar, Wasu kuma suka ce shekara huɗu.
Sannan Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya auri Sauda ɗiyar Zam`a ɗan ƙais ɗan Abdu shamsɗan Abdu wudd ɗan Nasr ɗan Malik ɗan Hisl ɗan Amir ɗan Lu`ai bayan Khadija a Makka kafin hijira. Ta kasance tana aure da Assakran ɗan Amr (ɗan uwa ne ga Suhail ɗan Amr). girma ya cimmata, har Manzan ALLAH ya so ya saketa, amma sai taba A`isha kwanakin ta, sai ya riƙe ta.
Sannan Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya auri A`isha ɗiyar Abu Bakr siddiƙ kafin hijira da shekara biyu a Makka. Wasu ko suka ce kafin hijira da shekara uku, ita ko ta nada shekara shida, Wasu ko suka ce ta nada shekara bakwai, amma maganar farko tafi inganci. Sannan ya tara da ita ta nada shekara tara a Madina bayan hijira a wata na bakwai, Wasu ko suka ce a wata na sha takwas ne. Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya rasu ta nada shekara goma sha takwas. Ta rasu a Madina, kuma an binne ta a maƙabartar baƙi`a, bayan tayi wasiyya da hakan, a shekara ta hamsin da takwas. Wasu ko suka ce a shekara ta hamsin da bakwai ne, amma maganar farko tafi inganci.Abu Huraira ne ya mata salla. Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) be auri budurwa ba inba ita ba. Ana mata alkunya da Ummu Abdillah. Anyi ruwaya cewa ta taɓa yin ɓari,sai dai be tabbata ba.
Sannan Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya auri Hafsa ɗiyar Umar ɗan Alkhaɗɗab ALLAH ya yarda da su. Khunais ɗan Khuzafa ne ke auran ta kafin haka, shi kuma sahabi ne na Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi), ya rasu a Madina,kuma ya halarci yaƙin Badar. Anyi ruwaya cewa Annabi (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya sake ta, sai Jibrilu (amincin ALLAH ya tabbata a gare shi) ya zo yace masa ALLAH yana umartar ka ka maida Hafsa, saboda me yawan azumi da salla ce , kuma matar ka ce a aljanna.
Uƙba ɗan Amir Aljuhani yayi ruwaya cewa: Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya saki Hafsa ɗiyar Umar, da Umar yaji haka sai ya watsa ma kan sa ƙasa yana me cewa: daga yau ALLAH be damu da Umar da ɗiyar sa ba, washe gari sai Jibrilu ya zo ma Manzan ALLAH yana me cewa: ALLAHmaɗaukakin sarki yana umartar ka ka maida Hafsa saboda tausayama Umar. Ta rasu a shekara ta ashirin da bakwai, wasu ko suka ce a shekara ta ashirin da takwas, shekarar da a ka buɗe garin Ifriƙiya
Sannan Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya auri Ummu Habiba ɗiyar Abu Sufyan, sunan ta Ramla ɗiyar Sakhr ɗan Harb ɗan Umayya ɗan Abdu Shams ɗan Abdu Manaf.
Tayi hijira tare da mijin ta Ubaidullai ɗan Jahash zuwa Habasha, sai ya zama kirista, amma ita ko ta tabbata a musulinci. Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya aure ta ne tana Habasha. Annajashi ne ya bada sadakin, dinare ɗari huɗu, sannan Manzan ALLAH ya aiki Amr ɗan Umayya Addamri ya taho da ita, kuma Usman ɗan Affan ne waliyin ta, wasu ko suka ce Khalid ɗan Sa`id ɗan A`s ne. Ta rasu a shekara ta arba`in da huɗu.
Sannan Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya auri Ummu Salama, sunan ta Hindu ɗiyar Abu Umayya ɗan Almugira ɗan Abdullahi ɗan Umar ɗan Makhzum ɗan Yaƙza ɗan Murra ɗan Ka`ab ɗan Lu`ai ɗan Galib.
Abu Salama Abdullahi ɗan Abdul Asad ɗan Hilal ɗan Abdullahi ɗan Umar ɗan Makhzum ne ke Aure da ita kafin haka. Ta rasu a shekara ta sittin da biyu, sannan a ka binne ta a maƙabartar baƙi`a a Madina. Ita ce ƙarshan rasuwa cikin matan Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi), wasu ko suka ce Miamuna ce.
Sannan Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya auri Zainab ɗiyar Jahash ɗan Ri`ab ɗan Ya`amur ɗan Sabira ɗan Murra ɗan Kabirɗan Ganm ɗan Dudan ɗan Asad ɗan Khuzaima ɗan Mudrika ɗan Ilyas ɗan Mudar ɗan Nizar ɗan Ma`ad ɗan Adnan. Ta kasance ɗiya ce ga goggon sa Umaima ɗiyar Abdul Muɗɗalib. yaran sa Ziad ɗan Harisa ne ke aure da ita kafin haka, sannan ya sake ta, sai ALLAH da kan sa ya aura masa ita, ba shi ba ya ɗaura auran.
Ya zo a cikin ruwaya ingantata Zainab ta kasance tana cewa ga sauran matan Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi): uwayan ku ne suka aurar da ku, ni kuma ALLAH ne ya aurar da ni daga saman bakwai. Ta rasu a Madina shekara ta ashirin, kuma an binne ta a maƙabartar baƙi`a.
Sannan Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya auri Zainab ɗiyar Khuzaima ɗan Alharisɗan Abdullah ɗan Amrɗan Abdu Manaf ɗan Hilal ɗan Amir ɗan Sa`sa`a ɗan Mu`awiya. Ana ce mata Ummul Masakin saboda tana yawan ciyar da talakawa.
Abdullahi ɗan Jahash ne ke aure da ita kafin haka, wasu ko suka ce Abdullaɗif ɗan Alharis ne, amma maganar farko tafi inganci. Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya aure ta ne a shekara ta uku bayan hijira, amma ba ta jima sosai da shi ba, tayi wata biyu ko uku ne kaɗai ta rasu.
Sannan Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya auri Juwairiyya ɗiyar Alharisɗan Abu dirar ɗan Habib ɗan A`iz ɗan Malik ɗan Almusɗaliƙ Alkhuza`iyya. An kamota ne a yaƙin Banil musɗaliƙ, sai ta faɗo a raban sabit ɗan ƙais ɗan Shammas, sai ya nemi da ta fanshi kan ta, sai Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya biya mata sannan ya aure ta, a shekara ta sida bayan hijira. Ta rasu a watan rabi`ul Awwal shekara ta hamsin da shida.
Sannan Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya auri Safiyya ɗiyar Huyai ɗan Akhɗab ɗan Yahya ɗan Ka`ab ɗan AlkhazrajAnnadriyya, tana daga cikin zuriya Annabi Haruna ɗan Imran (ɗan uwan annabi Musa tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gare su). An kamota ne a yaƙin Khaibar shekara ta bakwai bayan hijira. Kafin haka Kinana ɗan Abul Huƙaiƙ ne ke auran ta, sai Manzan ALLAH ya kashe shi sannan ya yanta ta, kuma yasa yantawar ita ce sadakin ta. Ta rasu a shekara ta talatin, wasu ko sukace a shekara ta hamsin.
Sannan Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya auri Maimuna ɗiyar Alharis ɗan Hazn ɗan Bujair ɗan Alharamɗan Ruwaiba ɗan Abdullahi ɗanHilal ɗan Amir ɗan Sa`sa`a ɗan Mu`awiya. Maimuna ta kasance yar uwar uwa ce ga Khalid ɗan Walid da Adbullahi ɗan Abbas.
Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya aure ta ne a wani wuri da ake cema Sarif, kuma ya tara da ita a can, sannan kuma ta rasu a can. Sarif wani ruwa ne da ke nisan mil tara da Makka. Maimuna ita ce ƙarshan wadda ya aura cikin matan sa uwayan muminai. Ta rasu a shekara ta sittin da uku.
Wannan sune matayan da Annabi (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya aura kuma ya tara dasu, su goma sha ɗaya ne. sannan ya auri wasu mata bakwai amma be tara da su ba.
HADIMAN MANZAN ALLAH (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI).

Anas ɗan Malik ɗan Annadr Al`ansari.
Hindu da Asma`u ɗiyan Harisa daga ƙabilar Al`aslami.
Rabi`a ɗan Ka`ab Al`aslami.
Abdullahi ɗan Mas`ud ya kasance me kula da takalmin Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi), idan zaiyi tafiya yana sa masa su, sannan idan ya zauna sai ya hudda masa su, kuma ya riƙe su tsakanin hannayan sa.
Sannan Uƙba ɗan Nafi`u ya kasance me kula da alfadarin sa, yana jaye da ita a lokacin balaguro.
Da Bilal ɗan Rabah, me kiran salla.
Da Sa`ad yaran Abu Bakr.
Da Zu Mikhmar ( ko Zu Mikhbar), ɗan ɗan uwan Annajashi, wasu ko suka ce ɗan yar uwar sa ne.
Da Bukair(ko Bakr) ɗan shaddakh Allaisi.
Da Abu Zarr Algifari.
Da waƙid, da Abu waƙid da Hisham, da Abu Dumaira, da Hunain, da Abu Asib (sunan sa Ahmar), da Abu Ubaid.
Da Safina, ya kasance bawa ne ga Ummu Salama matar Annabi (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi), sai ta yantar da shi, da sharaɗin zaiyi hidima ga Annabi (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) iya rayuwar sa, sai yace mata: ai koda baki min wannan sharadin ba to ni ba zan rabu da Manzan ALLAH ba.
Wannan da aka zano sune wanda suka shahara. Wasu ma sun ce sunkai har arba`in.
Daga cikin bayu mata akwai:
akwai Salma Ummu Rafi`u, da Baraka Ummu Aiman wadda ya gada daga mahaifin sa, kuma ita ce mahaifiyar Usama ɗan Zaid. Da Maimuna ɗiyar Sa`ad, da khadira, da Ridwa.
YARAN GIDAN SA MAZA
Zaid ɗan Harisa ɗan Sharahil Alkalbi, da ɗan sa Usama ɗan Zaid wanda ake masa kirari da masoyi ɗan masoyi.
Da Sauban ɗan Bujdud, ɗan asalin ƙasar Yaman ne.
Da Abu Kabsha, haifaffan Makka ne. sunan sa Sulaim, ya halarci yakin Badar. Wasu ko suka ce haifaffan Daus ne.
Da Anasa, haifaffan Assarat ne.
Da Salih wanda ake cema Shuƙran.
Da Ribah, baƙi ne.
Da Yasar, ɗan yankin Nuba ne.
Da Abu Rafi`u, sunan sa Aslam, wasu ko suka ce Ibrahim, bawane ga Al`abbas, sai ya baiwa Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) shi, shi kuma sai ya yantar da shi.
Da Abu Muwaihiba, haifaffan Muzaina ne.
Da Fudala, wanda ya sauka ƙasar Sham.
Da Rafi`u, ya kasance bawane ga Sa`ad ɗan Al`as, sai yayan sa suka gaje shi, sai wasu suka yantar da shi, wasu ko suka riƙeshi, sai yazo wajan Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) yana neman temakwan sa, sai suka ba Manzan ALLAH shi kyauta. Rafi`u ya kasance yana cewa: ni yaran gidan Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ne.
Da Mid`am, baƙi ne, Rifa`a ɗan Zaid Aljuzami ne ya bashi shi kyauta. Haifaffan Hisma ne, an kashe shi a Wadil ƙura.
Da Kirkira, wanda ke kula da kayan Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) a balaguro.
Da Zaid, kakan Hilal ɗan Yasar ɗan Zaid.
Da Ɗuhman ko Kaisan ko Mihran ko Zakwan ko Marwan.
Da Ma`bur Alƙibdi, sarki AlMuƙauƙis ne ya bashi kyautar sa.
DAWAKAN MANZAN ALLAH (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI).

Farkon dokin da Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya mallaka shine Assakb([11] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn11)), ya saye shi ne daga wani balaraban ƙauye ɗan ƙabilar Bani Fazara da uƙiyya goma([12] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn12)), lokacin da yake wajan balaraban ƙauye ana ce masa Addaris, sai Manzan ALLAH ya masa suna da Assakb, ya nada farin goshi da ƙafafuwa, me tsananin gudu ne, shine farkon dokin da Manzan ALLAH yayi yaƙi a saman shi. Ingarman doki ne, me cikakkiyar sura. Shine wanda Manzan ALLAH yayi tsere a saman shi kuma ya shige gaba, dalilin haka Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) yayi farin ciki.
Almurtajaz: shine dokin da Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya saye shi a wajan wani balaraban ƙauye, har Huzaifa ɗan Sabit yayi sheda da haka. Balaraban ɗan ƙabilar Bani Murra ne.
Sahal ɗan Sa`ad Assa`idi yace: Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya nada dawakai uku a wajena:Lizaz, da Azzarib, da Alluhaif.
Lizaz: sarki AlMuƙauƙis ne ya masa kyautar sa, shi kuma Alluhaif Rabi`a ɗan Abul Bara` ne ya masa kyautar sa,sai Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya saka masa a cikin dukiyar bani kilab, shi kuma Azzarib Farwa ɗan Amr Aljuzami ne ya bashi shi kyauta.
Haka kuma Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya nada wani dokin da ake cema Alward wanda Tamimu-ddari ne ya masa kyautar sa, shi kuma Manzan ALLAH ya ba Umar shi, shi ko Umar yayi sadaka da shi, bayan wani lokaci sai yaga a na tallar sa.
Kamar yadda Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya nada alfadari me suna Adduldul wadda yake hawan ta a balaguro. Ta rayu har bayan Manzan ALLAH kuma ta girma sosai har haƙoran ta suka zube, dan haka ma ake niƙa mata gari. Ta mutu a Yambu`.
Haka kuma Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya nada jaki me suna Ufair wanda ya mutu a hajin ban kwana.
Haka kuma ya nada taguwa ashirin a daji, wanda ake kawo masa salka biyu ta nonon su a kowane dare. Daga ckin taguwoyi masu yawan nono akwai Alhinna`u, da Assamra`u, da Al`urayyas da Assa`adiyya, da Bagum, da Alyusaira, da Arrayya.
Akwai wata taguwar sa me suna Alburda wadda Addahhak ɗan Sufyan ya masa kyautar ta, ana tatsar nonon taguwa biyu a gareta.
Haka kuma ya nada wata goɗiya wadda Sa`ad ɗan Ubada ya aika masa tare da wani doki me suna A`shshaƙra`daga cikin dabobin bani Aƙil.
Haka kuma Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya nada wata taguwa me suna Al`adbawadda Abu Bakr ya saya daga cikin dabobin banil harish, da wata taguwar da dirhami ɗari takwas, sai Manzan ALLAH ya saye ta da dirhami ɗari huɗu. Al`adba`u ita ce taguwar da Manzan ALLAH yayi hijira a samanta, sannan ruba`iyya([13] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn13)) ce. Kuma ana ce mata Alƙaswa`u da Aljadba`u. wata rana anyi tserere da ita, da aka tsere mata sai musulmi suka shiga damuwa.
Akwai wasu dabobi wanda yake anfana da nonon su, bakwai daga ciki ƙananan dabobi ne, sune: Ajza da Zamzam da Suƙya da Baraka da Warisa da Aɗlal da Aɗraf.
Haka kuma Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya nada ƙanan dabobi guda ɗari.
]MAKAMAN MAZAN ALLAH (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI)].

Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) nada mashi uku wanda ya samo daga ganimar Bani ƙainuƙa`u. haka kuma ya nada kibiya uku: Arrauha`u, da Shauhaɗ, da kuma wata masara me suna Assafra`u.
Kamar yadda ya nada hular kariya me gunkin kan rago, dalilin haka Manzan ALLAH ya ƙyamace ta, sai aka wayi gari ya ɓace.
Haka kuma ya nada takobi me suna Zul-ƙifarwanda ya same shi a ganimar yaƙin Badar, kuma shine takobin da yayi mafarkin sa ranar Uhudu, kafin haka takobin na Munabbih ɗan Hajjaj Assahami ne.
Kamar yadda ya samu takobi uku a cikin ganimar yaƙin Bani ƙainuƙa`u: Ƙula`i da Battar da Alhanif. Ya nada wasu takubban kuma bayan haka:Almikhdam da Rusub, ya same su ne a yaƙin Alfals (wani gunki ne na ƙabilar ɗai).
Anas ɗan Malik yana cewa: gindin gidan takobin Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) na azurfa ne, sannan kan makamin ma na azurfa ne, sannan abinda ke tsakanin su yan ƙarahuna ne na azurfa.
Haka kuma ya samu rigar kariya biyu da makaman Bani Ƙainuƙa`u, ɗaya a na ce masa Assugdiyya, ɗayan ko Fidda. Anyi ruwaya daga Muhammad ɗan Salama yace: naga Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) a ranar yaƙin Uhudu da rigar kariya biyu, daya me suna Zatul Fudul da kuma Fidda. Haka kuma na gansa a ranar yaƙin Khaibar da rigar kariya biyu: Zatul Fudul da Assa`adiyya.
FASALI NA SIFFOFIN MANZAN ALLAH (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI).

Anyi ruwaya daga Anas ɗan Malik ALLAH yarda da shi yace: Abu Bakr Siddiƙ ALLAH yarda da shi ya kasance idan yaga Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya gabato yana waƙe yana cewa:Musɗafa amintacce ne yana kira zuwa ga alheri, tamkar farin wata wanda babu duhu tare da shi.
Kuma Anyi ruwaya daga Abu Huraira ALLAH yarda da shi yace: Umar ɗan Alkhaɗɗab ALLAH yarda da shi ya kasance yana yaban Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) da waƙar Zuhair ɗan Abu Salma ga Hiram ɗan Sinan, inda ya ke cewa: inda kai wani abu ne ba mutun ba, da ka kasance farin wata me haskakawa adaran goma sha huɗu. sannan bayan haka sai Umar da fadawan sa suce: haka Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) yake, babu kuma wanda keda wannan siffar face shi.
An samo daga Aliyyu ɗan Abi ɗalib ALLAH yarda da shi yace: Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya kasance fari ne, me launi ja, me baƙin ƙwayar ido, gashin sa a meƙe yake, me cikakkyan gemu, gashin kan sa ya sauka zuwa ƙasan kunnuwan sa, ya nada yan gashi tsakanin ƙirji zuwa cibiya, wuyan sa yana haske kamar takobin azurfa, daga saman ƙirjin sa zuwa cibiyar sa akwai gashi ya taho kamar siririn icce, babu wasu gashi a cikin sa ko ƙirjin sa banda waɗannan, tafin hannun sa da ƙafafuwan sa masu kauri ne, idan yana tafiya yana tafiya da kuzari kamar me gangarowa,in zai juya yana juyawa gaba ɗaya, zufar sa kamar lu`u-lu`u, ƙanshin zufar sa yafi na almiski me tsananin ƙanshi, shi ba dogo ba kuma ba gajere ba, ba fajiri ba kuma ba lalatacce ba, ban taɓa ga kamar sa ba a gabanin sa ko bayan sa.
A wata ruwaya ko yace: tsakanin kafaɗun sa akwai alamar annabta, wanda shine hatimin annabawa, yafi kowa kyauta, yafi kowa walwala, yafi kowa gaskiyar magana, yafi kowa cika alƙawwali, sannan yafi kowa kyawawan halaye, yafi kowa kyawan zamantakewa, wanda ya gansa kai tsaye zai girmama shi, idan ko yayi mu`amala da shi zai so shi. Me kamanta shi yace: ban taɓa ga kamar sa ba a gabanin sa ko bayan sa (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi).
Albara`u ɗan Azib yana cewa"Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya kasance tsakatsakiya ne, me faɗin kafaɗu ne, gashin kan sa ya kai kunnuwan sa, na ganshi sanye da tufa ja, ban taɓa ganin mafi kyan sa ba (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi).
Ummu Ma`abad Alkhuza`iyya ta siffan ta Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) tana cewa: naga wani mutun kyakkyawa, fuskar sa na ƙyalli, me kyan sura, me faɗin ciki, ba me ƙaramin kai ba, shahararre wajan kyau,me kyan fuska, me baƙin ƙwayar idanu, gashin idanun sa su nada tsawo, muryar sa a bayyane take, me dogon wuya, me cikakkyan gemu, girar sa nada lanƙwasa kamar iccan kibiya, doguwa ce kuma da gashi, sannan kuma sun haɗu da juna, ya nada nutsuwa lokacin da yayi shuru, yana ɗaga muryar sa in zayi magana, mafi kyan mutane, me kwarjini daga nesa, me kyakkyawan hali daga kusa, me daɗaɗan kalamai, kalaman sa a bayyane suke, ba kaɗan ba wanda ba a ganewa, ko dayawa wanda za a ƙosa, kalaman sa a tsare suke kuma a jere kamar zubar tsakiyar da aka jera, tsakatsakiya ne, shi ba dogo ba, kuma ba gajere ba wanda idanuwa zasu rena, mafi cika da kamala tsakanin abokan sa biyu([14] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn14)), sannan mafi matsayi. Ya nada abokai wanda suke kewaye da shi, in yana magana suna saurarawa, in ya umarce su suna gaugawar aikatawa, suna masa hidima, sannan ana kewaye da shi kowane lokaci, ba me tsamin rai ba ne, kuma baida wauta.
Anas ɗan Malik Al`ansari ALLAH yarda da shi ya siffanta Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) yana me cewa:Manzan ALLAH mutun ne tsakatsakiya, ba dogo ba kuma ba gajere ba, me farin launi ne, wanda be ciza ba, kuma ba me baƙi ba, ba me yamutsatstsan gashi ba ne, kuma ba watsatstse ba, me kyan gashi ne.
Hindu ɗan Abu hala yana cewa: Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya kasance me girma ne abin girmamawa, fuskar sa na haskawa kamar wata daran sha huɗu, ba dogo ba kuma ba gajere ba, me babban kai ne, me kyan gashi, idan gashin kan sa ya rabu biyu da kan sa sai ya barshi, amma shi da kansa be raba shi([15] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn15)), tsawan gashin sa be huce ƙarƙashin kunnan sa. Me farin launi ne, me faɗin goshi ne, girar sa nada lanƙwasa kamar iccan kibiya, doguwa ce kuma da gashi, sannan kuma sun kusa haɗuwa da juna, tsakanin su akwai jijiya wadda take bayyana lokacin da yayi hushi, me dogon hanci wanda ke haskakawa,wanda be lura da kyau ba zai ce ya nada dogon karan hanci, me cikakkyan gemu, me baƙin ƙwayar ido, me dedetaccan kumci, me babban baki, haƙoran sa a jere suke, sannan kuma sun ɗan rarrabe, ya nada yan gashi tsakanin ƙirji zuwa cibiya,wuyan sa(na haske da ƙyalƙyali)kamar wuyan gunkin da aka ƙera da haƙoran giwa, me matsakaiciyar halitta ne, me babban jiki kuma riƙaƙƙe, cikin sa da ƙirjin sa sun dedeta da juna, me faɗin ƙirji, me faɗin kafaɗu ne, me manyan gaɓai ne, fari ne, daga saman ƙirjin sa zuwa cibiya akwai gashi kamar jan layi , babu gashi a nonon sa da cikin sa imba wanda aka ambata ba, ya nada gashi a zira`in sa da kafaɗun sa, me faɗin ƙirji, me dogayan ƙasusuwan hannu, me faɗin tafin hannu, me kaurin tafin hannu da ƙafafuwa, me dogon yatsu, ƙasusuwan sa na hannu da ƙwabri a meƙe suke, gefen da be taɓa ƙasa na ƙafar sa ya ɗagu, ƙafafuwan sa masu silɓi ne in an zuba ruwa yana hucewa da gaugawa, idan yana tafiya yana ɗaga ƙafar sa sosai, yana sassaka a takun sa, sannan kuma cikin nutsuwa, me dogon taki ne, kamar wanda ke gangarawa, idan zai juya yana juyawa gaba ɗaya,yana kai kallan sa ƙasa, duban sa zuwa ƙasa yafi yawa fiye da duban sa zuwa sama, be ƙwara ido, yana sanya sahabban sa a gaba lokacin tafiya, kuma yana fara sallama ga wanda yaɗu da shi.
FASALI NA HALAYAN MANZAN ALLAH (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI).

Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) yafi kowa jarumta. Aliyyu ɗan Abu ɗalibALLAH yarda da shi yace: mun kasance idan yaƙi yayi yaƙi, mazaje suka haɗu da mazaje, sai muyi kariya da Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi). Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) yafi kowa kyauta, ba a tambayar sa wani abu ya hana. Yafi kowa dattako, me tsananin kunya ne, har yafi budurwa wadda ke cikin ɗakinta kunya. Baya ƙwara ma mutun ido.
Baya ramuwa dan karan kan sa, kuma baya hushi, sai dai in an keta shari`ar ALLAH. Kuma idan yayi hushi a kan addinin ALLAH babu me tarbar sa.
Makusanci da na nesa, me ƙarhi da me rauni dai-dai suke wanjan neman hakki a wajan sa.
Baya aibata abinci, in ya so shi ya ci, in kuma be so shi ba ya barshi. Baya cin abinci a kishingiɗe, haka kuma baya cin abinci a saman wani abu. Baya hana kan sa abubuwan halak. Idan ya samu dabino sai ya ci, in kuma ya samu gurasa sai ya ci, in kuma ya samu nama me shuyi sai ya ci. Ya sha malo tare da maga.
Yana san kayan zaƙi da zumuwa.
Abu Huraira ALLAH yarda da shi yace: Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya bar duniya be taɓa ƙoshi ba da gurasa ta sha`ir. Akanyi wata guda har ma biyu ba a ɗora girki ba a gidan iyalan sa, sede su ci dabino da ruwa.
Yana amsar kyauta, amma be cin sadaka, kuma yana saka ma wanda ya masa kyauta.
Bayada dogon buri cikin abincin sa ko tufar sa. Yana cin abinda ya samu, kuma yana sa tufar da ya samu. Yana ɗinke takalmin sa, da rigar sa, kuma yana hidima ga iyalan sa a cikin gida, sannan kuma yana gaida mara lafiya.
Yafi kowa ƙasƙantar da kai, yana amsa kiran wanda ya kiraye shi me kuɗi ko talaka, me matsayi ko mara matsayi.
Yana san talakawa, yana halartar jana`izar su, yana zuwa gaida mara lafiyar su. Be walaƙanta talaka, kuma me mulki be masa kwarjini dan mulkin sa.
Yana hawan doki da raƙumi da jaki da alfadari. Yana goya bawan sa ko wani a saman dabba. Baya yarda wani yayi tafiya a bayan sa, har ma yana cewa: ku bar ma Mala`iku baya na. yana sanya kayan audiga, da takalmin fata.
Mafi kayan da yafi so sune Alhibara([16] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn16)), alkybba ce ta ƙasar Yaman masu zane ja da fari.
Zoban sa na azurfa ne, sannan zanan tsaka ma na azurfa ne , yana sa shi a ƙaramar yatsa ta dama, wani lokaci kuma a hagu.
Ya kasance yana ɗaura dutse a cikin sa saboda yinwa, alhali ALLAH ya bashi mabuɗi na taskokin ƙasa, yaƙi karɓa kuma ya zaɓi rayuwar lahira.
Ya kasance me yawan zikiri, baya yasassar magana. Yana tsawaita salla kuma ya gajarta huɗuba.
Yafi kowa murmushi, da fara`aduk da kasancewar sa kullun cikin taka-tsantsan da da tunani.
Ya kasance yana san turare kuma yana ƙin iska me wari. Yana kyautata alaƙar sa da masu matsayi dan ya jayo hankalin su, kuma yana girmama masu falala, yana sakin fuska ga kowa, sannan be jafa`i. idan yaga wasanni na halak baya ƙyamar su. yana zolaya amma da gaskiyar magana, kuma yana karɓar uzurin me uzuri.
Ya nada bayu maza da mata amma be fifita kansa a gare su wajan ciyarwa ko tufafi. Baya ɓata lokacin sa sai dai a ayyukan ɗa`a ko nasa ko na iyalan sa.
Yayi kiwan dabobi har ma yana cewa: babu wani annabi face sai yayi kiwo. An tambayi A`isha ALLAH ya yarda da ita halayan Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi), sai tace: halayan sa sune Alƙur`ani, yana hushi da abinda yake hushi da shi, kuma yana yarda da abinda yake yarda da shi. Yazo a cikin hadisi ingantacce daga Anas ɗan Malik ALLAH yarda da shi yace: ban taɓa taɓa wani dibaje ko alhariri me laushi fiye da tafin hannun Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi), kuma ban taɓa shinshina wani ƙanshi ba fiye da ƙanshin Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi), haƙiƙa na masa hidima shekara goma, be taɓa kyara ta ba, ko yace min dammi kayi kaza, ko dammi ba kayi kaza ba.
Haƙiƙa ALLAH maɗaukakin sarki ya tattara masa kyawawan halaye, da kyawawan ayyuka. Kuma ALLAH maɗaukakin sarki ya bashi sani na mutanan farko da na ƙarshe, wanda ke tattare da tsira da rabo, alhali shi Ummiyi ne, baya karantawa kuma baya rubutawa, sannan kuma ba yada malami a cikin mutane. Ya rayu a cikin gari me cike da jahilci da yanayi da sahara.
ALLAH ya bashi abinda be bawa kowa ba a cikin duniya, kuma ya zaɓe shi akan mutanan farko da na ƙarshe. Sallama da salati su tabbata a gare shi har ya zuwa ranar sakamako.
MU`UJIZOZIN MANZAN ALLAH (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI).

Daga cikin manya manya mu`ujizozin Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) bayyanannu shine Alƙur`ani me girma, wanda ƙarya bata zo masa daga gaban sa ko baya, shi kuma saukakke ne daga me hikima kuma abin godiya, shine wanda ya gagari masu fasaha, ya ɗimautar da masu balaga, sannan suka gaza kawo sura goma kwatamkwacin sa, ko ma sura guda kacal. Har mushirikai ma sun shaida da mu`ujizar Alƙur`ani, kuma har masu jayayya da shi da zindiƙai sun gaskanta da abinda ke cikin shi.
Wata rana mushirikai sun tambayi Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya nuna musu aya, sai ya nuna musu tsagewar wata, har ya rabu gida biyu. Wannan shine ma`anar faɗar ALLAH maɗaukakin sarki cewa: alƙiyama ta kusanto kuma wata ya tsage([17] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn17)).
Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) yace: ALLAH ya tattaro mini ƙasa baki ɗaya, sai naga duk abin ke gabacin ta da wanda ke yammacin ta, haƙiƙa mulkin al`umma ta zai kai har iya inda aka nunamin.
Haƙiƙa ALLAH ya gaskanta faɗar Manzan sa, dan ko mulkin sa ya kai har ƙarshan gabas da yamma, amma be watsu ba a kudu da arewa([18] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn18)) .
Ya kasance yana huɗuba a kan wani kututture, lokacin da aka yi masa minbari yake tsayuwa a kan sa, sai wannan kututturan ya riƙa kuka irin na taguwa me ciki, har seda Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) yazo masa, ya same shi yana kuka irin na jariri, sanan yayi shuru.
Sannan ruwa ya ɓuɓɓugo a tsakanin yatsun sa so diyawa.
Anji tsakuwa na tasbihi a hannun sa, har ma ya miƙa ma Abu Bakr sannan Umar sannan Usman. Wani lokaci ma suna jin tasbihin abinci alhali yana cin sa. Duwatsu da itatuwa sun masa sallama a lokacin da aka aiko sa. Kuma karfata da aka sama guba ta masa magana, wanda yaci karfatar tare da shi ya mutu shi kuma Annabi ya rayu bayan sa shekara huɗu. kyalkeci ma ya sheda annabcin sa. Wata rana ya huce wani raƙumi ana ban ruwa a saman shi, lokacin da raƙumin ya gansa sai yayi kuka sannan ya shunfiɗa wuyan sa a ƙasa, sai Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) yace: wannan raƙumin ya kawo kukan ana ɗora masa aiki dayawa kuma ana bashi abinci kaɗan. Haka kuma wata rana ya shiga wata garka da raƙumi a ciki, da raƙumin ya ganshi sai yayi kuka har hawaye suka fito masa, sai Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya cema me shi: ya kawo kukan kana barin shi da yinwa kuma kana bashi wahala. Sannan ya shiga wata garkar kuma sai yaga wasu raƙuma biyu sun gagara kamawa, lokacin da ɗaya daga cikin su yaga Annabi sai yazo ya durƙusa, Manzan ALLAH ya ɗaura masa igiya kuma ya miƙa ma me shi, ɗayan ma da yaga haka sai shi ma yayi kamar na farko.
Wata rana kuma a cikin balaguro yana barci wata itaciya ta tsaga ƙasa har tazo gare shi, lokacin da ya tashi aka bashi labarin abinda ya faru sai yace: ai ta nemi uzinin Ubangijin ta dan tazo tayi mini sallama kuma aka bata.
Ya umarci itaciya biyu da su haɗu[da ya ƙare biyan buƙatar sa[ sai ya umarce su da su rabu.
Wani balaraban ƙauye ya nemi ya gwada masa aya sai ya umarci wata itaciya tazo ta tsaya a gaban sa, sannan ta koma inda take.
Yayi niyya yanka raƙuma shida sai sukayi rigai-rigai zuwa gare shi wanne za`a fara da shi.
Ya shafi nonon wata ƙaramar dabba mara nono, sai ya ciko sannan ya tasta ya sha kuma ya ba Abu Bakr shima ya sha. Irin wannan ƙissar ta taɓa aukuwa a runfar Ummu Ma`abad.
Sannan ƙatada ɗan Annu`uman Azzafari idan sa ya fita har seda ya kasance a hannun sa, sai Manzan ALLAH ya maida shi, har ma yafi idan ɗaya kyau da gani sosai. Wasu ma sun ce ba a gane shi.
Yayi tofi a idanuwan Aliyyu ɗan Abu ɗalib masu ciwo, sai ya warke nan take, kuma daga rannan be sake ciwan ido ba. Kuma Ya taɓa masa addu`a wata rana yana rashin lafia, sai ya warke, sannan be sake yin irin wannan cutar ba.
Ƙafar Abdullahi ɗan Atik Al`ansari ta kare, da ya shafa ta ta warke nan take.sannan ya bada labari cewa zai kashe Ubayyu ɗan Ka`ab Aljumahi ranar Uhudu, daya sarce shi kaɗan sai ya mutu.
Sa`ad ɗan Mu`az yace ma ɗan uwan sa Umayya ɗan Khalaf: naji Muhammadu yana cewa shi zai kashe ka, sai ko aka kashe shi a yaƙin Badar yana kafiri.
Ya bada labarin guraran da za a kashe mushirikai a ranar Badar, yana cewa: anan za a kashe wane gobe in ALLAH ya yarda, sannan anan za a kashe wane gobe in ALLAH ya yarda. Babu wanda ya kauce gurin da Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya gwada.
Ya bada labarin cewa wata jama`a a cikin al`ummar sa zasu yi yaƙi a teku, kuma Ummu Haram ɗiyar Milhan tana daga cikin su, sai ko haka ya kasance kamar yadda ya faɗa.
Ya faɗa ma Usman cewa wata musiba zata same shi, sai ko aka kashe shi.
Ya faɗa ga Alhasan ɗan Aliyyu cewa: wannan yaran nawa shugaba ne, kuma haƙiƙa ALLAH zai dedeta tsakanin ƙungiyoyi na musulmi manya manya guda biyu ta hanyar sa. Hakan ko ya faru.
Ya bada labarin kashe Al`aswadul Ansi (babban maƙaryacin nan) a daran da a kashe shi da kuma wanda ya kashe shi a can San`a`a cikin ƙasar Yaman. Haka ma ya bada irin wannan labarin lokacin da aka kashe Kisra]sarkin Farisa[.
Haka kuma ya bada labarin Ashshaima`u ɗiyar Buƙaila Al`azdiyya lokacin da aka nuna masa ita tana sanye da mayafi baƙi a kan alfadari fari, sai ko rundunar Khalid ɗan Walid suka kamo ta kamar yadda Manzan ALLAH ya faɗa, hakan ya auku a zamanin halifancin Abubakar.
Wata rana ya cema Sabit ɗan ƙais ɗan Shammas: ka rayu kana me godiya, kuma zaka mutu shahidi,saiko ya rayu me godiya, sannan yayi shahada a yaƙin Yamama.
Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) yace ma wani mutun (wanda yake rayawa shi musulmi ne) da yake tare da shi a cikin yaƙi: yana daga cikin yan wut, Sai ALLAH ya gaskata faɗar Manzan sa, saboda mutuman ya soki kan sa da kan sa.
Yayi ma Umar ɗan Alkhaɗɗab addu`ar shiriya, sai aka wayi gari ya musulin ta.
Yayi ma Aliyyu ɗan Abu ɗalib addu`a ta ALLAH ya kareshi daga jin zafi da sanhi, sai ya kasance baya jin zafi ko sanhi.
Yayi ma Abdullahi ɗan Abbas addu`a ta ALLAH ya fahimtar da shi addini kuma ya sanar da shi tawili, hakan ko ya auku har ma ana kiran sa da Alhabru([19] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn19)) da Albahru([20] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn20)) saboda yawan ilimin sa.
Yayi addu`a ga Anas ɗan Maliki ALLAH ya masa tsawan kwanaki da yawan dukiya da yaya, kuma ALLAH yayi albarka cikin su. Haƙiƙa ko ya samu ɗiya maza ɗari da ashirin daga tsatsan shi, kuma ana cirar garkar dabinan sa so biyu a shekara, sannan kuma ya rayu shekara ɗari da ashirin ko kusan haka.
Da Utaiba ɗan Abu Lahab ya cira masa riga kuma ya cutar da shi, sai ya masa addu`a ta ALLAH ya haɗa shi da kare daga cikin karnukan sa, saiko zaki ya hallaka shi a Zarƙa`u cikin ƙasar Sham.
Wata rana an kawo masa kukan fari yana saman minbari, sai ya roƙi ALLAH maɗaukakin sarki, a lokacin babu komi a sama, saiko hadari ya gamu nan take kamar duwatsuna, akayi musu ruwa har wata juma`a, sannan aka kawo masa kukan yawan sa, sai ya roƙi ALLAH ya tseda shi,sai ya tsaya har sahabbai suka riƙa tafiya cikin rana.
Ya ciyar da wanda suka gina ramin khandaƙ su dubu daga sa`i na sha`ir ko ƙasa da haka da karama dabba, suka ci suka ƙoshi alhali abincin yana nan kamar ba a taɓa shi ba. Haka kuma ya ciyar da su dabino kaɗan wanda ɗiyar Bashir ɗan Sa`ad ta kawo ma baban ta da ɗan uwan uwan ta Abdullahi ɗan Rawaha.
Ya umarci Umar ɗan Alkhaɗɗab yaba wasu mutane ɗari hudu guzuri daga dabino kaɗan, tilin sa kamar zaunannan ƙaramin raƙumi , bayan ya gama basu sai dabinan ya kasance kamar ma ba a taɓa shi ba.
Haka kuma ya ciyar da mutane tamanin a gidan Abu Ɗalha da gurasa kaɗan wadda Anas ya mallaƙeta a hamatar sa saboda ƙarancin ta, har suka ƙoshi dukkan su.
Ya ciyar da runduna guda da dabinan da ke cikin jakar guziri ta Abu Huraira har suka ƙoshi dukkan su sannan aka maida saura cikin jakar, sai Manzan ALLAH ya masa addu`a a cikin ta, sai ya riƙa ci cikin abinda yayi saura tsawan rayuwar Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) da zamanin Abu Bakr da Umar da Usman ALLAH ya yarda da su, lokacin da aka kashe usman sai akayi kyautar sa. ya bada wusuƙi([21] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn21)) hamsin saboda ALLAH a cikin ta.
Ya ciyar da mutane dayawa da abincin da ke cikin bukuru wanda Ummu Sulaim ta masa kyautar sa a lokacin walima ta auran sa da Zainab. Bayan an gama ba a iya gane yawan abincin ba, kafin a ci shi ko bayan an ci shi.
Sannan ya jefi runduna da jimƙar hannu ta ƙasa a yaƙin Hunaini, sai ALLAHmaɗaukakin sarki ya tarwatsa su. Wasu ma daga cikin su suka ce: babu wani daga cikin mu face seda idanun sa suka cika da ƙasa. Dan hakama ALLAHmaɗaukakin sarki ya saukar da aya: ba kai bane kayi jifa lokacin da kake jifa, amma de ALLAH ne yake jefawa([22] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn22)) .
Ya bi tsakanin ƙuraishawa ɗari wanda suke jiran sa, ya watsa ƙasa a kawunan su, sannan ya bi ya huce basu ganshi ba.
Suraƙa ɗan Malik ɗan Jush`um ya bi shi dan ya kashe shi ko ya kama shi, daya kusanto gare shi sai Manzan ALLAH yayi addu`a a gare shi, sai ƙafafuwan dokin sa suka nitse cikin ƙasa, sai ya ba Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) aminci, sai Manzan ALLAH ya masa addu`a, sannan ALLAH ya kuɓutar da shi.
Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) nada mu`ujizozi bayyanannu, da hujjoji zahiri ,da halaye tsarkakakku, mun taƙaita a kaɗan daga cikin su.


FASALI NA TARIHIN SAHABBAN MANZAN ALLAH (TSIRA DA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE SU) SU GOMA.

ABU BAKR SIDDIƘ ALLAH YARTDA DA SHI.

Sunan sa Abdullah ɗan Abu ƙuhafa. Shi ko Abu ƙuhafa sunan sa Usman ɗan Amir ɗan Amr ɗan Ka`ab ɗan Sa`ad ɗan Taim ɗan Murra ɗan Ka`ab ɗan Lu`ai ɗan Galib Attaimi Alƙurashi. Dangantakar sa tana haɗuwa da Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) daga Murra ɗan Ka`ab.
Mahaifiyar sa ita ce Ummul Khair Salma ɗiyar Sakhr ɗan Amir ɗan Ka`ab ɗan Sa`ad ɗan Taim ɗan Murra.
Ya rayu shekara sittin da uku,dai-dai shekarun Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi).
Shine farkon wanda ya musulinta cikin wannan al`umma, kuma shine mafi alherin su bayan Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi). Yayi halifanci tsawan shekara biyu da rabi, wasu suka ce shekara biyu da wata huɗu ba kwana goma ne yayi halifanci, wasu suka ce wata ashirin ne yayi.
Daga cikin yayan sa akwai:
Abdullah: ya musulinta da jimawa kuma sahabi ne. ya kasance yana zuwa wajan Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) da Abu Bakr lokacin da suke cikin kogo. Mashi ya same shi a yaƙin Ɗa`if, sannan ya rasu a halifancin mahaifin sa.
Asma`u -ma`abuciyar ƙyalle biyu-: ita ce matarAzzubai ɗan Awwam. Tayi hijira zuwa Madina ta nada cikin Abdullah ɗan Azzubair, shine farkon ɗan da aka haifa cikin musulinci bayan hijira.
Mahaifiyar ta ita ce Ƙutaila ɗiyar Abdul Uzza, daga ƙabilar Bani Amir ɗan Lu`ai. Bata musulinta ba.
A`isha assiddiƙa: matar Annabi (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi). Ta nada ɗan uwa shaƙiƙi me suna Abdurrahman ɗan Abu Bakr. Ya halarci yaƙin Badar tare da mushirikai sannan ya musulinta bayan haka.
Mahaifiyar ta ita ce Ummu Ruman ɗiyar Amir ɗan Uwaimirɗan Abdu Shamsɗan Attab ɗan Uzaina ɗan Subai`u ɗan Duhman ɗan Alharis (ɗan Ganm) ɗan Malik ɗan Kinana. Ta musulinta sannan tayi hijira, ta rasu a zamanin Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi).
Abu Atiƙ Muhammad ɗan Abdurrahman: an haife shi zamanin Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi).
Bamu san ba wasu sahabbai hudu wanda sashan su ɗiya ne ga sashe in ba waɗannan ba.
Muhammad ɗan Abu Bakr: an haife shi a hajin ban kwana, an kashe shi a Misra, ƙabarin sa ma yana can. Mahaifiyar sa ita ce Asma`u ɗiyar Umais Alkhas`amiyya.
Ummu Kulsum ɗiyar Abu Bakr: an haife ta bayan rasuwar Abu Bakr. Mahaifiyar ta itace Habiba, wasu suka ce sunan ta Fatikha ɗiyar Kharija ɗan Zaid ɗan Abu Zuhair Al`ansari. Ɗalha ɗan Ubaidullah ne ya aure ta.
Kenan Abu Bakr nada yaya maza uku da mata uku, dukkan su sahabbai ne, banda Ummu Kulsum. Shi kuma Muhammad an haife shi ne a zamanin Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi).
Abu Bakr ALLAH yarda da shi ya rasu watan Jumadal Akhira saura kwana uku ya ƙare shekara ta goma sha uku.



ABU HAFS UMAR ƊAN ALKHAƊƊAB ALLAH YARDA DA SHI.

]Sunan sa Umar ɗan Alkhaɗɗab[ ɗan Nufail ɗan Abdul Uzza ɗan Riyah ɗan Abdullah ɗan Ƙurɗ ɗan Razah ɗan Adiyyu ɗan Ka`ab ɗan Lu`ai ɗan Galib. Dangantakar sa tana haɗuwa da Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) daga Ka`ab ɗan Lu`ai.
Mahaifiyar sa ita ce Hantama ɗiyar Hashim, wasu ko suka ce Hisham ɗan Mugira ɗan Abdullah ɗan Umar ɗan Makhzum.
Ya musulinta a Makka, kuma ya halarci dukkan yaƙuna tare da Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi).
Yayan sa sune:
Abu Abdurrahman: Abdullah, ya musulinta da jimawa, kuma yayi hijira tare da ɗan uwan sa. Yana daga cikin zaɓaɓɓun sahabbai.
Hafsa: Matar Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi). Mahaifiyar ta ita ce Zainab ɗiyar Maz`un.
Asim ɗan Umar:an haife sa a zamanin Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi). Mahaifiyar sa ita ce Ummu Asim Jamila ɗiyar Sabit ɗanAbul Aƙlah.
Zaidul Akbar da Ruƙayya: mahaifiyar su ita ce Ummu Kulsum ɗiyar Aliyyu ɗan Abu ɗalib.
Zaidul Asgar da Ubaidullah ɗiyan Umar: mahaifiyar su ita ce Ummu Kulsum ɗiyar Jarwal Alkhuza`iyya.
Abdurrahmanul Akbar ɗan Umar, da Abdurrahmanul Ausaɗ, shi ne Abu Shahma wanda aka ma bulala saboda ya sha giya. Mahaifiyar sa baiwa ce sunan ta Luhayya.
Abdurrahmanul Asgar ɗan Umar: Mahaifiyar sa baiwa ce a na ce mata Fukaiha.
Iyad ɗan Umar: Mahaifiyar sa ita ce Atika ɗiyar Zaid ɗan Amr ɗan Nufail.
Abdullahil Asgar ɗan Umar: Mahaifiyar sa ita ce Sa`ida ɗiyar Rafi`u Al`ansariyya daga ƙabilar Bani Amr ɗan Auf.
Faɗima ɗiyar Umar: Mahaifiyar ta ita ce Ummul Hakim ɗiyar Alharis ɗan Hisham.
Ummul Walid ɗiyar Umar: sai dai be tabbata ba kasancewar ta ɗiyar sa.
Zainab ɗiyar Umar: yar uwa ce ga Abdurrahmanul Asgar ɗan Umar.
Umar ɗan Alkhaɗɗab yayi halifanci shekara goma da wata sida da rabin wata. An kashe shi a ƙarshan watan zulhijja a shekara ta ashirin da uku hijira.Ya nada shekaru sittin da uku, dede shekarun Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi). Amma malamai sunyi saɓani kan shekarun sa.
BABAN ABDULLAH USMAN ƊAN AFFAN ALLAH YARDA DA SHI.

]Shine usman ɗan affan[ ɗan Abul As ɗan Umayya ɗan Abdu Shams ɗan Abdu Manaf.Dangantakar sa tana haɗuwa da Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) dagaAbdu Manaf, wanda shine kaka na biyar. Mahaifyar sa ita ce Ummu Urwa ɗiyar Kuraiz ɗan Rabi`a ɗan Habib ɗan Abdu Manaf. Mahaifiyar ta (Ummu Urwa) ita ce Ummu Hakin Albaida`u ɗiyar Abdul Muɗɗalib.
Ya musulinta da jimawa, kuma yayi hijira zuwa habasha sannan Madina. Ya auri yayan Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) biyu. Yayi halifanci shekara goma sha biyu ba kwana goma, wasu suka ce ba kwana goma sha biyu.
An kashe shi a sha takwas ga watan Zul hijja bayan sallar la`asar yana azumi shekara ta talatin da biyar, ya nada shekara tamanin da biyu.
Daga cikin yayan sa akwai:
Abdullahil Akbar: mahaifiyar sa ita ce Ruƙayya ɗiyar Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi), ya rasu ya nada shekara shida. Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ne ya shiga ƙabarin sa.
AbdullahilAsgar: mahaifiyar sa ita ce Fatikha ɗiyar Gazwan, yar uwa ce ga Utba.
Umar da Khalid da Aban da Maryam: mahaifiyar su ita ce Ummu Amr ɗiyar Jundub ɗan Amr ɗan Humama daga Azd daga Kabilar Daus.
Alwalid da Sa`id da Usman: mahaifiyar su ita ce Faɗima ɗiyar Alwalid ɗan Abdu Shams ɗan Almugira ɗan Abdullahi ɗan Umar ɗan Makhzum.
Abdul Malik: bayada zuriya,ya rasu lokacin da yake cikin kuzarin sa, mahaifiyar sa ita ce Ummul Banin ɗiyar Uyaina ɗan Hisn ɗan Huzaifa ɗan Zaid.
A`isha da Ummu Aban da Ummu Amr: mahaifiyar su ita ce Ramla ɗiyar Shaiba ɗan Rabi`a.
Ummu Khalid da Urwa da Ummu Aban Assugra: mahaifiyar su ita ce Na`ila ɗiyar Al`ahwas ɗan Amr ɗan Sa`alaba ɗan Alharis ɗan Hisn ɗan Damdam ɗan Adiyyu ɗan Junab daga ƙabilar Kalb ɗan Wabra.
ABUL HASAN ALIYYU ƊAN ABU ƊALIB ALLAH YARDA DA SHI.

]Shine Aliyyu ɗan Abu Ɗalib[ ɗan baffan Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi). mahaifiyar sa ita ce Faɗima ɗiyar Asad ɗan Hashim ɗan Abdu Manaf. Ita ce farkon Hashimiyya wadda ta haifi bahashime. Ta musulinta kuma tayi hijira Madina. Ta rasu a zamanin Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi). Ya auri Faɗima ɗiyar Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi), ta haifa masa Alhasan da Alhusain da Muhassin wanda ya rasu yana ƙarami.
Haka kuma daga cikin yayan sa akwai:
Muhammad Alhanafiyya: mahaifiyar sa ita ce Khaula ɗiyar Ja`afar, daga kabilar Bani Hanifa.
Umar ɗan Aliyyu da yar uwar sa Ruƙayya Alkubra: tagwayyu ne. mahaifiyar su yar ƙabilar taglib ce.
Al`abbasul Akbar ɗan Aliyyu: wanda ake cema Assaƙƙa`u, an kashe shi tare da Husain. Yan uwan sa shaƙiƙai sune: Usman da Ja`afar da Abdullah ɗiyan Aliyyu: mahaifiyar su baiwa ce kuma Alkilabiyya ce.
Ubaidullah da Abu Bakr ɗiyan Aliyyu: basu bar baya ba. mahaifiyar su ita ce Laila ɗiyar Mas`ud Annahshaliyya.
Yahya ɗan Aliyyu: ya rasu yana ƙarami, mahaifiyar sa ita ce Asma`u ɗiyar Umais.
Muhammadul Akbar ɗan Aliyyu:ɗan baiwa ne, ya rasu be bar baya ba.
Ummul Hasan da Ramla: mahaifiyar su ita ce Ummu Sa`id ɗan Urwa ɗan Mas`ud Assaƙafi.
Zainab Assugra da Ummu Kulsum Assugra da Ruƙayya Assugra da Ummu Hani da Ummul Kiram da Ummu Ja`afar (sunan ta Jumana) da Ummu Salama da Maimuna da Khadija da Faɗima da Umama ɗiyan Aliyyu: ɗiyan bayu ne, kuma uwayan su daban-dabanne.
Halifancin Aliyyu yayi shekara huɗu da wata bakwai da wasu kwanaki. akwai saɓani wajan tantance kwanakin. An kashe shi ya nada shekara sittin da uku. Wasu suka ce shekara sittin da biyar ne, Wasu ko suka ce hamsin da takwas ne, sannan Wasu ko suka ce hamsin da bakwai ne.wannan ya auku ne a shekara ta arba`in hijira wadda ake cema shekarar jama`a.
ABU MUHAMMAD ƊALHA ƊAN UBAIDULLAH ALLAH YARDA DA SHI.

]Shine Ɗalha ɗan Ubaidullah[ɗan Usman ɗan Amr ɗan Ka`ab ɗan Sa`ad ɗan Taim ɗan Murra ɗan Ka`abɗan Lu`ai ɗan Galib. Dangantakar sa tana haɗuwa da Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) dagaMurra ɗan Ka`ab.mahaifiyar sa ita ceAssa`aba ɗiyar Alhadrami, yar uwa ce ga Ala`u ɗan Alhadrami.
Sunan Alhadrami Abdullah ɗan Abbad ɗan Akbar ɗan Auf ɗan Malik ɗan Uwaif ɗan Khazraj ɗan Iyadɗan Assadaf. Mahaifiyar sa ta musulinta kuma ta mutu musulma.
Ɗalha ya musulinta da jimawa kuma ya halarci yaƙin Uhudu da na bayan sa.Amma be halarci yaƙin Badar ba saboda yana Sham wajan kasuwanci, sai Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya bashi kaso da cikin ganimar sannan kuma ya nada ladan wanda suka je wannan yaƙin.
Daga cikin yayan sa akwai:
Muhammad Assajad: wanda aka kashe shi tare da shi.
Imran: mahaifyar sa ita ce Hamna ɗiyar Jahash.
Musa ɗan Ɗalha: ɗan Khaula ɗiyar ƙa`ƙa`u ɗan Ma`abad ɗan Zurara.
Ya`aƙub da Isma`il da Ishaƙ: mahaifyar su ita ce Ummu Aban ɗiyar Utba ɗan Rabi`a.
Zakariya da A`isha: mahaifyar su ita ce Ummu Kulsum ɗiyar Abubakar siddiƙ ALLAH yarda da su.
Isa da Yahya: mahaifyar su ita ce Su`uda ɗiyar Auf Almuriyya.
Ummu Ishaƙ ɗiyar Ɗalha: mahaifyar ta ita ce Ummul Haris ɗiyar ƙasama ɗan Hanzala Aɗɗa`iya.
Dan haka yayan Ɗalha goma sha ɗaya ne. wasu suka ce akwai wasu yayan biyu: Usman da Salih. Amma de ba tabbata ba.
An kashe Ɗalha a shekara ta talatin da shida a yaƙin Jamal, ya nada shekara sittin da biyu.
ABU ABDILLAH AZZUBAIR ƊAN AWWAM ALLAH YARDA DA SHI.

]Shine Azzubair ɗan Awwam[ ɗan Khuwailid ɗan Asad ɗan Abdul Uzza ɗan Ƙusai ɗan Kulab . Dangantakar sa tana haɗuwa da Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) daga Ƙusai ɗan Kulab, kaka na biyar kenan. mahaifyar sa ita ce Safiyya ɗiyar Abdul Muɗɗalib Goggon Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi). Ta musulinta kuma tayi hijira zuwa Madina.
Azzubair yayi hijira sau biyu, kuma yayi salla a ƙibla biyu.
Shine farkon wanda ya zare takobin sa saboda ALLAH. Shine Hawari([23] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn23)) na Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi).
Daga cikin yayan sa akwai:
Abdullah: shine farkon ɗan da aka haifa a musulinci bayan hijira.
Almunzir da Urwa da Asim da Almuhajir da Khadija Alkubra da Ummul Hassan da A`isha: mahaifyar su ita ce Asma`u ɗiyar Abu Bakr Siddiƙ.
Khalid da Amr da Habiba da Sauda da Hind: mahaifyar su ita ce Ummu Khalid ɗiyar Khalid ɗan Sa`id ɗan Al`as.
Mus`ab da Hamza da Ramla: mahaifyar su ita ce Arrabab ɗiyar Unaif Alkalbiyya.
Ubaida da Ja`afar da Hafsa:mahaifyar su ita ce Zainab ɗiyar Bishr daga ƙabilar ƙais ɗan Sa`alaba.
Zainab ɗiyar Azzubair: mahaifyar ta ita ce Ummu Kulsum ɗiyar Uƙuba ɗan Abi Mu`iɗ.
Khadijatu- ssugra: mahaifyar ta ita ce Aljalal ɗiyar ƙais, daga ƙabilar Asad ɗan Huzaima.
Dan haka yayan Azzubair maza da matasu ashirin da ɗaya ne. an kashe shi a yaƙin Jamal shekara ta talatin da shida.Ya nada shekara sittin da bakwai ko da shida.
ABU IS`HAƘ SA`AD ƊAN ABI WAƘƘAS ALLAH YARDA DA SHI.

]Shine Sa`ad ɗan Abi waƙƙas[. Sunan Abu waƙƙas Malik ɗan Uhaib ɗan Abdu Manaf ɗan Zuhra ɗan Kulab . Dangantakar sa tana haɗuwa da Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) daga Kulab ɗan Murra. mahaifiyar sa ita ce Hamna ɗiyar Sufyan ɗan Umayya ɗan Abdu Shams ɗan Abdu Manaf.
Ya musulinta da jimawa. Ya kasance yana cewa: nine na ukun shiga musulinci. Ya halarci yaƙin Badar da sauran yaƙuna tare da Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi). Shine farkon wanda ya jefa mashi dan ɗaukaka addinin ALLAH. Ya jefa mashi cikin runduna wadda keda Abu Sufyan, inda suka haɗu a wani guri da ake cema Rabig a shekarar farko da Annabi ya zo Madina.
Daga cikin yayan sa akwai:
Muhammad: Hajjaj ne ya kashe shi.
Umar: Almukhtar ɗan Abu Ubaid ne ya kashe shi.
Amir da Mus`ab: anyi ruwayar hadisan Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) daga gare su.
Umair da Salih da A`isha yayan Sa`ad.
Ya rasu a babban gidan sa dake Aƙiƙ wanda yake nisan mil goma da Madina. Mazaje ne suka ɗauko gawar sa har zuwa Madina, a shekara ta hamsin da biyar, yana ɗan shekara saba`in da yan ka, kuma shine ƙarshan sahabbai goma (wanda aka ma albishir ƙin shiga aljanna)rasuwa.
ABUL A`AWAR SA`ID ƊAN ZAID ƊAN AMR ALLAH YARDA DA SHI.

Shine Sa`id ɗan Zaid ɗan Amr ɗan Nufail ɗan Abdul Uzza ɗan Riyah ɗan Abdullah ɗan Ƙurɗ ɗan Razah ɗan Adiyyu ɗan Ka`ab ɗan Lu`ai ɗan Galib. Dangantakar sa tana haɗuwa da Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) daga Ka`ab ɗan Lu`ai. Mahaifiyar sa ita ce Faɗima ɗiyar Ba`aja ɗan Umayya ɗan Khuwailid, daga ƙabilar Bani Mulaih daga Khuza`a.
Sa`id ya kasance ɗan baffan Umar ɗan Alkhaɗɗab ne, sannan ya auri yar uwar sa Ummu Jamil ɗiyar Alkhaɗɗab.
Ya musulinta da jimawa, sannan be halarci yaƙin Badar ba.
Daga cikin yayan sa akwai:
Abdullah: mawaƙi ne.
Azzubair ɗan Bakkar yana cewa:yayan sa kaɗan ne, kuma babu wanda yake Madina.
Sa`id ɗan Zaid yarasu a shekara ta hamsin da ɗaya, yana ɗan shekara saba`in da yan ka.

ABU MUHAMMAD ABDURRAHMAN ƊAN AUF ALLAH YARDA DA SHI.

]Shine Abdurrahman ɗan Auf[ ɗan Abd ɗan Alharis ɗan Zuhra ɗan Kulab . Dangantakar sa tana haɗuwa da Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) daga Kulab ɗan Murra. Mahaifiyar sa ita ce Ashshifa, wasu ko suka ce sunanta Al`anƙa`u ɗiyar Auf ɗan Abdul Haris ɗan Zuhra.tayi hijira.
Abdurrahman ya musulinta da jimawa, kuma ya halarci yaƙin Badar da sauran yaƙuna tare da Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi). Ya zo cikin ruwaya ingantatta cewa Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) yayi salla bayan Abdurrahman ɗan Auf a yaƙin Tabuka.
Daga cikin yayan sa akwai:
Salim Al`akbar: ya rasu kafin musulinci.
Ummul ƙasim: an haife ta cikin jahiliyya.
Muhammad: da sunan sa ake masa alkunya, an haife sa a cikin musulinci.
Ibrahim da Humaid da Isma`il: Mahaifiyar su ita ce Ummu Kulsum ɗiyar Uƙba ɗan Abu Mu`iɗ ɗan Amr ɗan Umayya ɗan Abd Shams ɗan Abd Manaf. Tana daga cikin masu hijira da kuma wanda suka yi mubaya`a ga Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi). Dukkan yayan sa wanda suka zo daga gareta an rawaito hadisai daga gare su.
Urwa ɗan Abdurrahman: an kashe shi a Ifriƙiya. Mahaifiyar sa ita ce Nuhaira ɗiyar Hani` ɗan Ƙaisa ɗan Mas`ud ɗan Sha`aban.
Salim Al`asgar: an kashe shi a Ifriƙiya. Mahaifiyar sa ita ce Sahla ɗiyar Suhail ɗan Amr. Ya kasance ɗan uwa ne na wajan uwa ga Muhammad ɗan Abu Huzaifa ɗan Utba.
Abdullahil Akbar: an kashe shi a Ifriƙiya. Mahaifiyar sa yar ƙabilar Bani Abdul Ash`hal ce.
Abu Bakr ɗan Abdurrahman.
Abu Salama Alfaƙih: wanda ake cema Abdullahil Asgar: Mahaifiyar sa ita ce Tumadir ɗiyar Al`asbag Alkalbiyya. Ita ce farkon kalbiyya wadda baƙuraishe ya aura.
Abdurrahman ɗan Abdurrahman.
Mus`ab ɗan Abdurrahman: ya kasance daga cikin sojojin Marwan ɗan Alhakam a Madina.
Abdurrahman ɗan Auf ya rasu a Madina, Kuma an binne shi a baƙi`a shekara ta talatin da biyu a halifancin Usman ɗan Affan. Sannan Usman ɗan Affan ne ya masa salla, yana da shekara saba`in da biyu.
ABU UBAIDA AMIR ƊAN ABDULLAH ƊAN ALJARRAH ALLAH YARDA DA SHI.

]Shine Amir ɗan Abdullah ɗan Aljarrah[ ɗan Hilal ɗan Uhaib ɗan Dabba ɗan Alharis ɗan fihr ɗan Malik. Mahaifiyar sa ita ce Gunm ɗiyar Jabir ɗan Abdul Uzza ɗan Amir ɗan Umaira ɗan Wadi`a ɗan Alharis ɗan fihr. Wasu suka ce sunan ta Umaima ɗiyar Gunm ɗan Jabir ɗan Abdul Uzza. Dangantakar sa tana haɗuwa da Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) daga fihr ɗan Malik. Ya musulinta da jimawa, tun kafin Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) ya shiga Darul Arƙam. Ya halarci yaƙin Badar da sauran yaƙuna tare da Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi). Shine wanda ya cire yan ƙarahuna na hular kariya daga fuskar Manzan ALLAH (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) a ranar Uhudu, har seda haƙoran sa na gaba suka zube, duk da haka bakin sa ya kasance me kyan gani, har ma ake cewa: ba a taɓa ganin faɗuwar haƙora me kyau kamar ita ba.
Daga cikin yayan sa akwai:
Yazid da Umar.
Yayan Abu Ubaida sun rasu, dan haka be bar baya ba. Ya rasu a annobar Amawas a shekara ta goma sha takwas.Ƙabarin sa yana Gaur Baisan a ƙauyan Amta, ya nada shekara hamsin da takwas. Mu`azu ɗan Jabal ne ya masa salla, wasu ko suka ce Amr ɗan Al`as.
Abu Ubaida ne ya kashe mahaifin sa kafiri a yaƙin Badar, kuma a kan sa ne ALLAH ya saukar da aya: ba zaka samu waɗan da su kayi imani da ALLAH da ranar lahira suna ƙaunar wanda suke kangare ma ALLAH da Manzan sa ba, ko da mahaifan su ne, ko yayan su, ko yan uwan su, ko dangin su, irin waɗannan sune wanda ALLAH ya sa imani a zukatan su, kuma ya ƙarfafa su da nasara daga gare shi, sannan zai sanya su aljanna wadda ƙoramu ke gudana a ƙarƙashin su, suna madawwama a cikin su, ALLAH ya yarda da su suma sun yarda da shi,waɗannan sune ƙungiyar ALLAH, ku saurara lalle ƙungiyar ALLAH sune masu rabo([24] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn24)) .


Na ƙare rubuta tarihin annabi (tsira da amincin ALLAH ya tabbata a gareshi) da tarihin sahabban sa goma(ALLAH yarda da su da wanda suka biyo baya da kyautatawa har zuwa ranar ƙiyama) a ranar laraba kwanaki goma na farko na watan Jumadal Awwal shekara ta ɗari bakwai da talatin da biyu.
ALLAH yayi sallamada daɗin tsira me yawa ga shugaban mu ]annabi[Muhammad da iyalan sada sahabban sa.

•••





[/URL]([1])shekarar giwa: ita ce shekarar da ALLAH ya hallaka rundunar da. tazo kashe ɗakin Ka`aba.

(http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftnref1)(1) shine wanda yazo bayan annabawa,ko kuma Al`Akib.

(2) Me bushara.

(http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftnref3)(3) Me gargaɗi.

(4) Me tausayi.

(http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftnref5)(5) Me jin ƙai.

([7]) shine amintacce.

(http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftnref7)([8]) ƙabari ne wanda akeyin ɗiyar ƙabarin a gefan alƙibla.

([9])wani guri ne a Dimashƙ me tarin garakai da itace da ƙoramu.

(http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftnref9)([10])guri ne Sham.

([11])me tsananin gudu.

(http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftnref11)([12]) uƙiyya: ita ce dirhami arba`in.

([13])ita ce taguwar da ta shiga shekara ta bakwai.

(http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftnref13)([14])tana nufin Abu Bakr da Amir ɗan Fuhaira.

([15])wannan ya kasance a farkon musulinci, amma daga baya ya kasance yana raba shi.

(http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftnref15)([16])wasu nau`in kaya ne masu kyau da a ke ɗinkawa da audiga a ƙasar Yaman,su nada zane.

([17])suratul ƙamar,aya:1.

(http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftnref17)([18]) Haƙiƙa addinin musulinci ya yaɗu ko`ina a duniya, gabas da yamma kudu da arewa.

([19])malami.

(http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftnref19)([20]) me yawan ilim.

([21])shi ne sa`I sattin.

(http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftnref21)([22])suratul anfal,aya: 17.

([23])matemaki.

[URL="http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftnref24"] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftnref23)([24])suratul mujadala, aya: 22.