المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : Kwanaki goman zulhijjah (وليال عشر)


طاهر جبريل دكو
_19 _August _2017هـ الموافق 19-08-2017م, 03:54 PM
KWANAKI GOMAN ZULHIJJAH
(وليال عشر)




TANADAR
(زاد)




TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA





Yana daga falalar Allah ta'alah akan bayinsa, yadda ya sanya musu lokaitai na qara yin ayyukan xa'a, waxanda a cikinsu ake ninnika lada, sai su yi ta tsere a cikin lokatan da ayyukan za su kusantar da su zuwa ga Ubangijinsu,
Kuma yana daga cikin waxannan lokatan MASU FALALA:
KWANAKI GOMAN FARKO NA WATAN ZUL-HIJJAH, Wannan kuma ya kasance ne, saboda abinda Allah ya ajiye a cikinsu, na falalarSa, da kuma yadda yak e karrama bayinsa,
Saboda a cikinsu ne;
Ake samun YININ TAKWAS (TARWIYAH), da YININ ARAFAH, da YININ LAYYAH,
Kuma domin girman sha'anin kwanakin nan guda goma ne, Allah ya yi rantsuwa da su, a cikin faxinsa:
"INA RANTSUWA DA ALFIJIR * DA KUMA DARARE GUDA GOMA" [Fajr: 1-2].
Kuma Manzon Allah (sallal lahu alaihi wa sallama) ya bada labarin cewa, su ne mafifitan yinin da ake da su a duniya, a cikin faxinsa:
"Mafifitan kwanakin duniya su ne, yinin kwanakin goma", yana nufin: goman farkon zulhijjah.
[Ibnu-Hibban ya rawaito shi, kuma Albaniy ya inganta shi].

Abu-Usman An-Nahdiy yana cewa:
"Sun kasance, -yana nufin magabatan kwarai- suna girmama, gwammai guda uku, wato: GOMAN QARSHE NA WATAN RAMADHANA, da GOMAN FARKO NA WATAN ZULHIJJAH, da GOMAN FARKON WATAN MUHARRAM".

TO, DA ME ZA MU TARBI WAXANNAN KWANAKIN?

Ya zo daga Abdullah ibn Abbas ya ce:
Manzon Allah –sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce:
"Babu wasu yini wanda aiki nagari ya fi soyuwa a cikinsu, a wurin Allah Mabuwayi da xaukaka, fiye da waxannan kwanakin", Yana nufin, kwanakin nan guda goma.
Sai su ka ce: Ya Ma'aikin Allah! Koda jihadi ne, fi sabilillah?
Sai ya ce: "Koda jihadi ne, fi sabilillah, sai ga mutumin da ya fita da Ransa, da kuma dukiyarsa, sai bai dawo da komai ba". .

Shi kuma, AIKI NA KWARAI Ya qunshe dukkan nau'oin ibadodi mabanbanta, na azumi, da sallah, da zikiri, da yin kabbara domin girmama Allah ta'alah, da tilawar Alqur'ani, da ciyarwa ta fiskokin biyayya, da makamantan haka,

Kuma yana daga cikin ibadodin da ake qarfafa YINSU A WAXANNAN KWANAKIN

YIN AZUMI:[B] In banda yinin goma, daga cikinsu, saboda y azo daga wata daga cikin Matan Annabi –sallal lahu alaihi wa sallama- ta ce:
"Manzon Allah –sallal lahu alaihi wa sallama- ya kasance yana azumtar yini tara a watan zulhijjah".

[Abu-dawud ya ruwaito shi, 2437, da An-Nasa'iy, 2372, kuma Albaniy ya inganta shi, a cikin littafin SAHIHU ABIY-DAWUD, 2106].

Musamman kuma yinin da azumtarsa, ke kankare zunaban shekaru biyu (yinin Arafah).

Kuma YANA DAGA CIKINSU:
AMBATON ALLAH (ZIKIRI) DA KABBARORI,
Allah ta'alah ya ce:
"KUMA SU AMBACI SUNAN ALLAH, A CIKIN WASSU YINI SANANNU, AKAN ABINDA YA AZURTA SU, NA BAHIMATUL AN'AAM (dabbobin ni'ima)" [Hajj, 28].
Wanda kuma sune YININ NAN GUDA GOMA.

Kuma YANA DAGA CIKINSU:
YIN AIKIN HAJJI,
Kuma shine mafificin abinda aka aikata, a cikin kwanakin nan guda goma, kuma Manzon Allah –sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce:
"Hajji kuvutacce, bashi da wani sakamako, face Aljannah" [Bukhariy da Muslim].

Kuma DAGA CIKINSU AKWAI:
YIN LAYYAH,
Kuma duk wanda ya yi nufin ya yi Layyah, to sai ya kame, daga yanke gashinsa da faratunsa (akaifa),tun daga shigar watan zulhijjah, har zuwa lokacin da zai yanka, abar layyarsa.