المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : taqaitaccen bayani game da falalar watan Ramadana


طاهر جبريل دكو
_18 _May _2017هـ الموافق 18-05-2017م, 06:07 PM
خلاصة البيان في فضائل شهر رمضان

taqaitaccen bayani game da falalar watan Ramadana

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
التمهيد
قال أبو جعفر:"والشهر"، فيما قيل، أصله من"الشهرة". يقال منه:"قد شَهر فلانٌ سَيْفه" -إذا أخرجه من غمده فاعترض به من أراد ضربه-"يشهرُه شهرًا". وكذلك"شَهر الشهر"، إذا طلع هلاله،"وأشهرْنا نحن"، إذا دخلنا في الشهر.
وأما"رمضان"، فإن بعض أهل المعرفة بلغة العرب كان يزعم أنه سمى بذلك لشدة الحرِّ الذي كان يكون فيه، حتى تَرْمَض فيه الفِصَال، كما يقال للشهر الذي يُحجّ فيه"ذو الحجة"، والذي يُرتبع فيه"ربيع الأول، وربيع الآخر"
مما يدل على فضل شهر رمضان ما يلي:
Daga abin da ke nuna falalar watan ramadana:
Na farko: Saukar da Alqur'ani mai girma a cikinsa kamar yadda Allah Ya ce:
{شَهْرُ رَمَضَانَ الَّذِي أُنْزِلَ فِيهِ الْقُرْآنُ هُدًى لِلنَّاسِ وَبَيِّنَاتٍ مِنَ الْهُدَى وَالْفُرْقَانِ } [البقرة: 185]
Ma'ana: watan ramadana wanda aka saukar da Alqur'ani a cikinsa da bayani na shariya da rarrabewa tsakanin qarya da gaskiya….
Imamu xxabari ya fitar da hadisi a cikin tafsirinsa da isnadinsa zuwa ga Wasilatu bnu Alsqa'i, رضي الله عنهdaga Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce: an saukar da Suhufi Ibrahima a daren farko na ramadana, kuma an saukar da Attaura bayan shuxewar kwanaki shida a cikin watan ramadana, kuma an saukar da Injila a rana an sha uku an sauke Alqur'ani kuma a ranar ashirin da huxu na ramadana.
Na biyu: Samun dare mai daraja a cikinsa لَيْلَةِ الْقَدْرِ)) wanda ya fi watanni dubu alheri kamar yadda Allah maxaukakin sarki Ya faxa:
{إِنَّا أَنْزَلْنَاهُ فِي لَيْلَةِ الْقَدْرِ (1) وَمَا أَدْرَاكَ مَا لَيْلَةُ الْقَدْرِ (2) لَيْلَةُ الْقَدْرِ خَيْرٌ مِنْ أَلْفِ شَهْرٍ}[القدر:1- 3]
Ma'ana: Lallai Mu Mnu saukar da shi a daren qaddara. Kuma me ya sanar da kai abin da kae cewa daren qaddara? Daren qaddara ya fi watanni dubu alheri.
Na uku: Ana buxe qofofin Aljanna gabaki xayan su a cikinta.
Na huxu: Ana garqme qofoin Wuta a cikinsa ba a barin ko xaya a buxe.
Na biyar: Ana xaure shexanu a da kangararrun shexanu a cikinsa.
Ibnu Awananh Ya ruwaito a cikin littafinsa Almustakhraj daga Abuhuraira رضي الله عنه ya na cewa: Annabi صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ya ce:
«إِذَا جَاءَ رَمَضَانُ فُتِّحَتْ أَبْوَابُ الْجَنَّةِ، وَغُلِّقَتْ أَبْوَابُ النَّارِ، وَصُفِّدَتِ الشَّيَاطِينُ»
وفي لفظ «إِذَا جَاءَ رَمَضَانُ فُتِّحَتْ أَبْوَابُ السَّمَاءِ، وَغُلِّقَتْ أَبْوَابُ جَهَنَّمَ، وَسُلْسِلَتِ الشَّيَاطِينُ»
Ma'ana: Idan Ramadana ta zo sai a buxe qofofin Aljanna, a garqame qofofin Wuta kuma a xaure shexanu. A wani lafazin ya ce: Idan Ramadana ta shigo sai a buxe qofofin sama a garqame qofofin Jahannama kuma a sanya shexanu a cikin ququmi.
Na shida: Kasancewar duk wanda ya azumce ta ya na mai imani da Allah da kuma neman lada, za a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubbansa. Kamar yadda Abu huraira ya ruwaito daga Annabi صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ya ce:
«مَنْ صَامَ رَمَضَانَ إِيمَانًا وَاحْتِسَابًا غُفِرَ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِهِ»
Na bakwai: kasancewar sa yana kankare zunubban da ke tsakaninsa da wata Ramadana kamar yadda Abu huraira ya ruwaito daga Annabi صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ya ce:
«الصَّلَوَاتُ الْخَمْسُ، وَالْجُمُعَةُ إِلَى الْجُمُعَةِ، وَرَمَضَانُ إِلَى رَمَضَانَ مُكَفِّرَاتٌ مَا بَيْنَهُنَّ إِذَا اجْتُنِبَ الْكَبَائِرُ»
Ma'ana: salloli biyar, juma'a zuwa juma'a, da Ramadana zuwa wata Ramadana masu kankarewa ne ga qananan zunubban da ke tsakaninsu matuqar an nisanci manyan laifuka.
ثامنا: أن من صامه وأتبعه ستا من شوال :ان كصيام الدهر فعن أَبَي أَيُّوبَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قال: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
Na takwas: kasancewarduk wanda ya azumce shi tare da kwanaki shida daga cikin watan shawwal kamar ya shekara ne ya na azumi. kamar yadda Abu huraira ya ruwaito daga Annabi صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ya ce:
«مَنْ صَامَ رَمَضَانَ ثُمَّ أَتْبَعَهُ سِتًّا مِنْ شَوَّالٍ فَذَاكَ صِيَامُ الدَّهْرِ»

خطوات إلى الاستعداد لدخول رمضان
Matakai bakwai domin shirya wa shigan Ramadana
Mataki na farko: yawaita addu'ar Allah Ya kai ka ramadana saboda duk yadda ka kai ga son isa ga wani alheri ba ka iyawa har sai Allah Ya kai ka.
Mataki na biyu: godiya ga Allah Idan ya kai ka watan Ramadana godiya da ta haxa da aikin gavvai da zuciya da harce, saboda duk sa'adda bawa ya gode wa Allah game da ni'imar da Ya yi masa to Allah Ya yi alqawarin qara masa.
Mataki na huxu: Murna da shigowar Ramadana kamar yadda Allah Ya ce:
(قُلْ بِفَضْلِ اللَّهِ وَبِرَحْمَتِهِ فَبِذَلِكَ فَلْيَفْرَحُوا هُوَ خَيْرٌ مِمَّا يَجْمَعُونَ) [يونس:58]
Ma'ana: Ka ce: da falalar Allah da RahamarSa to da wannan ne za ku yi murna da farinciki sama da abin da ku ka tara na duniya.
Mataki na huxu: tsara yadda za ka gudanar da rayuwarka a cikin watan Ramadana ta fuskar sallolin nafila dare da rana, tilawar Alqur'ani, sauran nau'uka na zikiri, sadaka, halartan wuraren karatu kamar wuraren tafsiri ziyara da sauransu. Domin duk abin da ka yi shi ba bisa tsari ba to ba ka ribatan shi yadda ya kamata ko ma ka yi asarar sa gaba xaya.
Mataki na baiyar: Karantan hukunce-hukuncen watan Ramadana, kama daga abin da ke da alaqa da hukuncin ganin wata, hukuncin azumin watan Ramadan, sanin abubuwan da ke jawo kaffara, sanin saruxxan azumi, sanin abubuwan da ke vata azumi, sanin hukunce-hukuncen I'tikafi, da sanin hukunce-hukuncen zakkan fidda kai da hukunce-hukuncen sallan idi da sauransu. Allah Ya ce:
(فَاسْأَلوا أَهْلَ الذِّكْرِ إِنْ كُنْتُمْ لا تَعْلَمُونَ)[الأنبياء:7].
Ma'ana: Ku tambayi ma'abuta sani idan har ba ku sani ba.
Mai ahalari na cewa:
((ولا يحل له أن يفعل فعلا حتى يعلم حكم الله فيه))
Ma'ana: kuma bai halatta gare shi ya aikata wani aiki har sai ya san hukuncin Allah akai.
Mataki na shida: Tuba zuwa ga Allah tuba ta gaskiya saboda zunubbai su ne sabubban haramta wa bawa alheran duniya da lahira. Allah maxaukakin sarki Ya ce:
{وَمَا أَصَابَكُمْ مِنْ مُصِيبَةٍ فَبِمَا كَسَبَتْ أَيْدِيكُمْ وَيَعْفُو عَنْ كَثِيرٍ} [الشورى: 30]
Duk abin da ya same ku na musiba to daga abin da hannayenku su ka aikata ne kuma Allah Ya na yafe abubuwa masu yawa.
Mataki na bakwai: buxe sabon shafi a rayuwa ta gari, sai bawa ya yi qoqarin kyautata hainsa tun kafin shigar ramadana saboda ya ribaci fursa da ganiman da ke cike a cikin watan sannan ya qudurta aniyan tabbata akan hakan har qarshen rayuwarsa.
Rubutu da tarjamar Xahiru Jibril Dukku.