تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : HUXUBAR MASALLACIN ANNABI (صلى الله عليه وسلم) JUMA'A, 09/SHA'ABAN/1438h


طاهر جبريل دكو
_15 _May _2017هـ الموافق 15-05-2017م, 11:32 PM
HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 09/SHA'ABAN/1438h








LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHIN MALAMI ALIYU XAN ABDURRAHMAN AL-HUZAIFIY














TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
Yabo ya tabbata ga Allah Wanda ke rayawa da kashewa, kuma Shi mai iko ne akan komai, sunayensa sun tsarkaka, kuma sifofinSa sun xaukaka, Babu abin bautawa face Shi, Mai hikima, Mai bada labari, wanda ya rayar da zukata da Alqur'ani, da wa'azozi, da hikima, da kuma kyakkyawan aiki abin godiya, Ya kuma dogarar da wanda ya kauce daga gaskiya ga ransa, sai ya kasance cikin hasara, da gafala, da ruxu.
Ina yin yabo ga Ubangijina, a kan ni'imominSa gaba xaya, kuma ina yin godiya a gare shi, a kan falalarSa mai girma,
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; Shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, Mai ji Mai gani,
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu annabi Muhammadu bawanSa ne kuma manzonsa; Mai bushara Mai gargaxi, kuma fitila mai haskakawa, Ya Allah ka yi qarin salati da sallama da albarka, ga bawanka kuma manzonka annabi Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa, waxannan da su ababen koyi ne ga dukkan muminin da ke da basira a cikin addininsa.


Bayan haka:
Ku kiyaye dokokin Allah da taqawa, ta hanyar aikata dukkan aikin da Allah ke yarda da shi, da nisantar kowani aikin da Ya ke qinsa, saboda taqawar Allah ita ce, rabauta a duniya, kuma sababin samun rabauta da aljannar dawwama, a gidan lahira, kuma lallai daxi ya tabbata ga wanda ya yi riqo da taqawa, bone kuma ya tabbata ga wanda ya nisanci taqawa; ya qi yin aiki da ita,


Ya ku bayin Allah …
Ku gyara zukatanku, da ababen da su ke gyara zukata, kuma ku kula da ababen da su ke zuwa ga zukata; sai su vata su, saboda zuciya ita ce sarki ko jagora ga sauran gavvai, kamar yadda Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai a cikin jiki akwai wata tsoka, idan ta gyaru dukkan jiki ya gyaru, idan kuma ta lalace, to dukkan jiki ya vaci, wannan ita ce zuciya", Bukhariy ya ruwaito shi da Muslim, daga hadisin An-nu'uman bn Bashir (رضي الله عنه).


Shin, ko kun san mafi girman cutukan zuciya, wanda idan aka jarrabi mutum da ita, za a haramta masa alkhairi gaba xayansa, ko a haramta wa mutumin da aka jarraba da ita, dayawa daga qofofin alheri,,, to, Ku saurara!
Lallai mafi girman cutukan zukata, shi ne GAFALA, Saboda cikakkiyar gafala, ita ce wanda kafirai da munafiqai su ka tave, saboda ita, kuma ita ce, ta wajabta musu dawwama a cikin wuta, Allah (تعالى) yana cewa: "Wanda ya kafirta da Allah, bayan imaninsa, face wanda aka tilasta, alhali kuwa zuciyarsa tana natse da imani, kuma wanda ya yi farin ciki da kafirci, to, akwai fushi akansa daga Allah, kuma suna da wata azaba mai girma * waxannan ne kafirai, saboda sun fifita son duniya a kan lahira, kuma lallai ne Allah ba Ya shiryar da mutane kafirai * Waxannan ne waxanda Allah Ya yi rufin zukatansu, da jinsu da gannansu, kuma waxannan su ne gafalallu" [Nahli: 106-108].


Wani lokacin kuma GAFALAR ta kan kasance, daga musulmi, sai ya gafala bai aikata wasu aiyukan alheri ba, ko ya gafala ya bar aiki da sabuban da su ke janyo amfani, ko tseratarwa daga sharri, sai kuma ladan alkhairan su kuvuce masa, gwargwadon abinda ya same shi na gafala, sannan sai ayi masa uquba, da ababen da rai ke qi, na sharri gwargwadon gafalarsa, saboda ya bar sabubban tsira, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma ga kowane mutum, akwai darajoji, saboda abinda su ka aikata, kuma domin Allah Ya cika musu sakamakon aiyukansu, alhali kuwa su, ba za a zalunce su ba” [Ahqaf: 19].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Kuma mutum bashi da kome face abin da ya aikata * Kuma lallai aikinsa, za a gan shi * sa'annan a saka masa da sakamako wanda ya ke mafi cika" [Najm: 39-41].
Kuma Manzo (صلى الله عليه وسلم) ya ruwaito daga Ubangijinsa maxaukaki, lallai ya ce: "Ku shiga aljanna da rahamata, ku raba abinda ke cikinta, gwargwadon aiyukanku".
Kuma Manzon Allah (عليه الصلاة والسلام) yana cewa: "Kuma wasu ba za su gushe suna jinkiri ba, face Allah ya jinkirtar da su, koda kuwa sun shiga aljannah".


Kuma Allah ya faxa, dangane da sakamakon gafala kan aiki da sabbuban tsira: "Shin, kuma a lokacin da wata masifa ta same ku, alhali kuwa kun samar da biyunta, sai ku ka ce: Daga ina wannan ta ke? Ka ce: daga rayukanku ta ke, Lallai ne Allah a kan dukkan komai Mai iko ne" [Ali-imrana: 165].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Kuma duk abin da ya same ku, na masifu, to sakamakon abin da hannayenku su ka aikata ne, kuma Allah yana yafewar wasu laifukan dayawa" [Shurah: 30].
Shi kuma wannan afuwar,ga musulmi ne kawai, saboda kafiri ba a yafe zunubansa, sai ya tuba (ya shiga musulunci).


GAFALA ita ce, Rashin nufan alkhairi ta fiskar niyya, da qin son alkhairi, tare da wofantar zuciya daga ilmi mai amfani, da aikata aiki nagari. Wannan kuma ita ce, gafala cikakkiya, mai halakarwa, kuma ita ce gafalar da ake samu daga kafirai da munafiqai, wanda kuma mutum ba zai samu rabo da ita ba, sai in har ya tuba zuwa ga Allah, kuma mutum ba zai bi komai ba -idan wannan gafalar ta dabaibaye shi- face zato, da abinda ransa ke so (wato, son rai), wanda kuma shi ne abinda shexaninsa ya qawata masa, ko abinda ransa ta so, na sha'awowi. Kuma wannan gafalar da ita ce, Allah ya yi uquba ga kafirai da munafiqai, a duniya da lahira, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma haqiqa, mun halitta, saboda Jahannama, dayawa daga aljanu da mutane, suna da wasu zukata, amma basa fahimta da su, kuma suna da idanu, basa gani da su, kuma suna da kunnuwa, ba su ji da su, waxancan kamar dabbobi su ke, A'a, su ne mafi vacewa, waxancan su ne gafalallu" [A'araf: 179].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Kuma a lokacin da mu ka kwaranye azaba daga barinsu, zuwa ga wani ajali, wanda su ke masu iske shi, sai ga su suna warwarewa * Sai mu ka yi azabar ramuwa, daga su, saboda haka mu ka nitsar da su, a cikin teku, domin lallai sun qaryata ayoyinmu, kuma sun kasance daga barinsu, gafalallu" [A'araf: 135-136].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Kuma lallai ne dayawa daga mutane, dangane da ayoyinmu gafalallu ne" [Yunus: 92].
Kuma Allah yana faxa dangane da munafiqai: "Kurame, bebaye, makafi, saboda haka ba su komawa" [Baqara: 18].
Kuma Allah (سبحانه) ya ce: "Kuma ka yi musu gargaxi, da ranar nadama, a lokacin da aka hukunta al'amari, alhalin kuwa suna a cikin gafala, kuma su ba su yin imani" [Maryam: 39].
An ruwaito daga Abu-Sa-id (رضي الله عنه) ya ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Idan ma'abuta aljanna su ka shiga aljanna, ma'abuta wuta suma su ka shiga wuta, sai a zo da mutuwa, da yanayin wani rago, mai kyau, sai mai kira ya yi kira, cewa: Ya ma'abuta aljannah! Sai su miqa wuya suna yin dubi, sai ya ce: Shin ko kun san wannan? Sai su ce, e, wannan ai mutuwa ce, alhalin kowane mutum daga cikinsu ya ganta, sai kuma ya ce: Ya ku ma'abuta wuta, Sai su miqe wuya suna yin dubi, sai ya ce: Shin ko kun san wannan? Sai su ce, e, na'am, wannan ai mutuwa ce, alhalin kowane mutum daga cikinsu ya ganta, Sai a yanka mutuwa a tsakanin wuta da aljanna, Sai a ce: Ya ma'abuta aljannah, ku dawwama; babu mutuwa, Ya ku ma'abuta wuta, ku dawwama babu mutuwa. Sai Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya karanta wannan ayar: (Kuma ka yi musu gargaxi, da ranar nadama, a lokacin da aka hukunta al'amari, alhalin kuwa suna a cikin gafala, kuma su ba su yin Imani)", Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.
Kuma ya zo, a wasu riwayoyin, cewa: "Ba domin Allah ya rubuta wa 'yan aljanna dawwamammen rayuwa ba, to da sun mutu, saboda farin ciki. Kuma ba domin Allah ya rubuta dawwamammiyar rayuwa ga ma'abuta wuta ba, da sun mutu saboda baqin ciki, da nadama"
Kuma ma'anar faxin Allah (تعالى): "alhalin suna cikin gafala", yana nufin: a nan duniya, saboda gidan lahira, babu wata gafala a cikinta.
Don haka, gafala irin ta kafirai da munafiqai, gafala ce mai dabaibayi, kuma cikakkiya, wanda ta ke wanzar da ma'abucinta a cikin wuta, kuma ita ce: RASHIN NUFAN ALKHAIRI KO NIYYATARSA, DA RASHIN SONSA, DA WOFANTUWAR ZUCIYA DAGA ILIMI MAI AMFANI, DA AIKI NA KWARAI, TARE DA BIN SON ZUCIYA, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma kada ka yi xa'a ga wanda mu ka shagaltar da zuciyarsa daga ambatonmu, kuma ya bi son zuciyarsa, sai al'amarinsa ya kasance a lalace" [Kahf: 28].
Maluman tafsiri su ka ce:
Ma'ana: Kada ka yi biyayya ga wanda mu ka sanya zuciyarsa ta gafala, da barin Qur'ani da musulunci, sai lamarinsa ya kasance a tozarce, a walaqance.


Amma ita kuma GAFALAR MUSULMI, ta kan kasance ne, wajen barin wasu daga cikin ayyuka nagari, waxanda kuma barin yin aiki da su, bai warware masa musuluncinsa ba. Ko kuma ta hanyar aukawa cikin savon da basa kafirtarwa, da rafkana daga tuna uqubobin da aka tanada musu.
Kuma lallai samun rafkana daga musulmi, sharri ne mai girma akansa, kuma cutarwa ne mai hatsari, wanda ke jefa shi cikin halaka, kuma su tottoshe masa hanyoyin alkhairi.


KUMA LALLAI GAFALA TANA CUTARWA MAI YAWA, tana kuma xauke da sharrin da basu da iyaka, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma kada ku kasance, kamar waxanda su ka manta da Allah, sai ya mantar da su rayukansu, Waxannan su ne fasiqai" [Hashr: 19],
Kuma Allah ya ce: "Sun mance Allah, sai ya manta da su, lallai ne munafiqai su ne fasiqai" [Tauba: 67].
Kuma Allah (عز وجل) ya ce: "Kuma ka ambaci Ubangijinka, a cikin ranka, da qanqan-da-kai, da tsoro, da koma-bayan bayyanawar magana, da safe da maraice, kuma ka kasance daga gafalallu", [A'araf: 205].


Kuma da gafala ne, wajen sanin cikar tauhidi, musulmi ke aukawa cikin tauye cikar tauhidi, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma mafi yawansu ba su yin imani da Allah, face suna masu shirka" [Yusuf: 106].


Kuma da gafala kan koyan rukunnan sallah ne, da wajibanta, ake samun tawaya a cikin sallar, kamar yadda ya zo cikin hadisin Abiy-hurairah (رضي الله عنه) lallai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ga wani mutum, yana sallah, sai ya gajerce sallarsa, sannan ya juyo ya yi sallama wa Annabi (صلى الله عليه وسلم), sai ya ce masa: "Koma ka yi sallah; domin kai baka yi sallah ba", ya aikata hakan har sau uku, Sai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya karantar da shi, yadda zai natsu a cikin ayyukan sallah. Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.


Kuma da gafala ne daga tuna ladan da ke cikin sallar jam'i, hakan ke janyo sakaci kan halartar jam'in, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Sallolin da su ka fi nauyi ga munafiqai, sune sallar isha da sallar asuba, kuma da mutane sun san abinda ke cikinsu na lada, da sun zo musu koda da jan ciki", Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi, daga Abu-hurairah.


Kuma da gafala ne kan ladan da zakka ke da shi, da kuma gafala kan uqubar da aka tanada ga wanda ya hana zakka, sakaci kan bada ita ya ke kasancewa: saboda ya zo cikin hadisi cewa: "Babu wani ma'abucin taskar da baya bada zakkarta, face a ranar qiyama an suranta masa wani maciji mai kora, yana cizon muqamuqansa biyu, sai ya riqa cewa: Ni ne taskarka, Nine dukiyarka" Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi, daga hadisin Abu-hurairah.
Ma'ana dukiyar za ta zama macijiya, wanda za ta riqa lasar kanxarsa biyu, tana zuba dafinta a ciki.


Kuma da gafala ne, daga tunani kan uqubobin rashin biyayya ga iyaye, to sai hakan ya sanya yaro yin rasar kunya ko rashin biyayya a gare su, sai abinda Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya bada labari ya auku a kansa, a inda ya ce: "Kuma mutane uku, ba za su shiga aljanna ba; mai qin biyayya ga iyayensa, da maras kishi, da matar da ta ke qoqarin zama namiji", An-nasa'iy da Alhakim suka ruwaito shi, daga Abdullah ibn Umar.
Shi kuma Dayyus; maras kishi, shi ne, wanda ke tabbatar da iyalansa akan zina, da kuma macen da ta ke kwaikwayar mazaje.


Kuma da gafala ne daga uqubar da aka tanada ga mai yanke zumunci, sai narkon azabar ta auku akan wanda ya yanke zumuncin, saboda ya zo cikin hadisin Jubair bn Mux'im, daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Baya shiga aljannah, Mai yanke zumunta", Bukhariy ya ruwaito shi.


Kuma da gafala ne daga uqubobin da aka tanada kan zalunci, zalunci a bayan qasa ke yawaita, har a yi ta kwararar da jini, ana xaukar dukiyar wani, ko a yi ta'a'danci ga mutunci, sai kuma gine-gine su zama rusassu, qasa kuma ta zama wanda aka qaurace mata, sai kuma a halaka shuka da 'ya'ya, sai lamarin tsoro ya yaxu, daga nan kuma, sai uquba ta sauka ga azzalumi, kamar yadda Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai ne Allah yana jinkirtawa ga azzalumi, har idan ya zo kama shi, to ba zai kuvuce masa ba, sai ya karanta, wannan ayar: (Kuma haka kamun Ubangijinka ya ke, idan ya kama alqaryoyi alhali suna masu zalunci, lallai ne kamunSa, mai raxaxi ne mai tsanani" [Hud: 102]. Bukhariy ya ruwaito shi da Muslim, daga hadisin Abu-Musa.


Kuma lallai gafala mabuxi ne na sharrori, kuma da ita ne, ake haramtawa musulmi ladaddaki masu yawa.
Kuma naqasa bata shiga wa musulmi, face ta qofar gafala.
Kuma tsira daga gafala shi ne samun rabo, nisantarta kuma hawa ne ga matakai, ko darajojin ibada.
Kiyayar gafala shi ne garkuwa daga uqubobi a cikin wannan rayuwa, da rabauta da samun ni'imomi bayan mutuwa.
Kuma samun kariya daga gafala, da samun tsira daga gare ta baya kasancewa face, ta hanyar nisantar sabubban da su ke jawo ta, da qin karkata ga duniyar da ta ke ruxar mutum, har ya bar lahirarsa.


Yana daga ababen da su ke taimakon musulmi wajen nisantar gafala, KIYAYE SALLOLIN JAM'I da khushu'i, da halarto da zuciya, saboda sallah ta qunshi rayuwar zukata, saboda abinda ke cikinta na ma'anoni masu girma, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma ka tsayar da sallah domin ambatona", [Xaha: 14].


Kuma yana daga ababen da su ke tseratarwa daga gafala: AMBATON ALLAH, a cikin kowane hali, saboda zikiri yana raya zuciya, kuma yana koran shexan, kuma yana tsarkake ruhi, kuma yana qarfafa jiki, wajen ayyukan xa'a, kuma yana tayarwa daga barcin mantuwa. Dawwama kan ambaton Allah (da zikiri) kuma, yana kiyaye bawa daga aikata savo, saboda ya zo daga Abu-Musa (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Misalin wanda ke ambaton UbangijinSa, da wanda baya ambaton UbangijinSa, misalin rayayye ne da matacce", Bukhariy ya ruwaito shi, da Muslim.


Yana daga abinda ke kare bawa daga gafala: ZAMA DA MALAMAI DA SALIHAI, saboda suna tunatarwa ga lamarin Allah, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma ka haqurtar da ranka, tare da waxanda ke kiran Ubangijinsu, safe da maraice, suna nufin fiskarSa, kuma kada idanunka su juya daga barinsu, kana nufin qawar rayuwar duniya" [Kahf: 28].


Kuma yana daga ababen da su ke tseratarwa daga gafala: NISANTAR WURAREN WARGI DA FASIQANCI, DA MUMMUNAN ABOKI, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma lallai ne an sassaukar muku a cikin littafi, cewa, idan kun ji ayoyin Allah, ana kafirce musu, kuma ana izgili da su, to kada ku zauna tare da su, sai sun shiga cikin wani taxin na daban, lallai ne ku, a lokacin nan misalinsu ku ke" [Nisa'i: 140].
Kuma ya zo cikin hadisi, cewa: "Misalin abokin zama na banza, kamar mai fura zuga-zugi ne".


Kuma yana daga ababen da su ke tseratarwa daga gafala: SANIN QASQANCIN DUNIYA, DA GUSHEWARTA, DA RASHIN RUXUWA DA KAYAN KYALKYALINTA, DAGA LAHIRA, saboda duniya ita ce, ta kange mafi yawan mutane daga lahira, da kuma bin shiriya.


Kuma yana daga ababen da su ke tseratarwa daga gafala: NISANTAR ZUNUBAI DA SAVO, saboda kasancewar duk savon da bawa ya auka cikinsa, to hakan ya kasance ne da sababin gafala, Allah (تعالى) yana cewa: "Lallai ne waxanda su ka yi taqawa, idan wani ruxi daga shexan ya tava su, sai su tuna, sai ga su sun zama masu basira * kuma 'yan'uwansu (shexanu) suna taimakonsu a cikin vata, sa'an nan ba su taqaitawa", [A'araf: 201-202].


Allah yayi mini albarka Ni da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da mu da abinda ke cikinsa na ayoyi da tunatarwa mai hikima, kuma ya amfanar da mu da shiriyar shugaban manzanni, da kuma maganganunsa miqaqqu, Ina faxar maganata wannan, kuma ina neman gafarar Allah Mai girma Mai daraja wa Ni da Ku, da kuma sauran musulmai da muminai, Ku nemi gafararSa; lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.





HUXUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah, Ubangijin talikai, Mai rahama mai jin qai, Ina yin yabo a gare shi, kuma ina gode masa, akan ni'imominSa na zahiri da baxini gaba xaya, kuma ina yaba masa akan alkhairi gaba xaya, Shi kamar yadda ya yi yabo ne wa kansa,
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Shi; Mabuwayi Mai hikima.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shigabanmu Muhammadu bawan Allah ne kuma Manzonsa, wanda ya shiryar zuwa ga hanya madaidaiciya,
Ya Allah ka yi qarin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa, ma'abuta taqawa, da kuma halaye masu karamci.


Bayan haka;;;
Ku kiyaye dokokin Allah iyakar taqawa, kuma ku yi riqo a musulunci da igiya mai qarfi,


Ya ku bayin Allah…
Lallai mafi girman abinda zai tsamar da musulmi daga gafala, da ababen da ta ke haifarwa masu cutarwa shi ne: TUNA MUTUWA, DA ABINDA KE BAYAN MUTUWAR, saboda mutuwa mai wa'azi ne mai gamsarwa, kuma ana ganinta ana jinta, kuma yaqinin ne da xanxana ta ya ke a kurkusa, haxuwa da ita kuma lamari ne mai aukuwa, An ruwaito daga Abu-hurairah (رضي الله عنه) yana cewa: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Ku yawaita ambaton mai yanke jin daxi, yana nufin mutuwa" Tirmiziy ya ruwaito shi, kuma ya ce: hadisi ne hasan.
Kuma duk wanda ya yawaita ambaton mutuwa, sai zuciyarsa ta gyaru, aikinsa kuma ya tsarkaka, sai kuma ya kuvuta daga cutar gafala.
A lokacin mutuwa kuma, mumini yana farin ciki, fajiri kuma yana gurin komowa duniya, sai dai kuma, fau-fau ba za a amsa masa ba, Allah (تعالى) yana cewa: "Har idan mutuwa ta je wa xayansu sai ya ce: Ya Ubangijna, ku mayar da ni (duniya) * Tsammanina in aikata aiki na kwarai cikin abin da na bari, Kayya! Lallai ne ita kalma ce, shi ne mafaxinta, kuma a baya gare shi akwai wani shamaki, har ranar da za a tayar da su" [Mu'uminuna: 99-100].


Kuma shekarun mutum, shi ne abinda ya shuxe cikin aikin biyayya.
Wanda kuma ya shuxe cikin savo, to wannan hasarar rayuwarsa ne


Bayin Allah,,,


"Lallai ne Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa" [Ahzab: 56].


Manzon Allah kuma (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Duk wanda yayi mini salati guda xaya to Allah zai yi masa salati guda goma ".
Sai ku yi salati da sallama ga shugaban mutanen farko da na qarshe, kuma jagoran manzanni;
Ya Allah! Ka yi salati wa annabi Muhammadu da iyalan annabi Muhammadu kamar yadda ka yi salati wa annabi Ibrahima da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai a cikin talikai, Abun godiya ne, Mai girma.
Ya Allah! Ka yi albarka wa annabi Muhammadu da iyalan annabi Muhammadu kamar yadda ka yi albarka wa annabi Ibrahima da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai a cikin talikai, Abun godiya ne, Mai girma.
Kuma ka yi musu sallama; tsiratarwa mai yawa.
Ya Allah! Ka yarda da sahabbai gabaxaya, da kuma khalifofi shiryayyu, kuma shugabanni masu shiryarwa; Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu, da sauran sahabban annabinka gabaxaya, da waxanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar qarshe,
Ya Allah! Ka yarda da mu tare da su, da baiwarka, da rahamarka ya mafi rahamar masu rahama.
Ya Allah! Ka xaukaka musulunci da musulmai, ka kuma qasqantar da kafirci da kafirai,
Ya Allah ! ka kashe bidi'oi har zuwa ranar tashi qiyama;
Ya Allah! Ka dusar da wutar bidi'a; wacce ta ke cin karo da addininka, kuma take cin karo da shari'arka,
Ya Allah! Ka kashe bidi'oi, har zuwa tashin qiyama, lallai kai mai iko ne akan komai.
Ya Allah!
Ya Allah!
Ya Allah!
Addu'oi;;;;;;;;;;;;;;;;