طاهر جبريل دكو
_21 _April _2017هـ الموافق 21-04-2017م, 05:42 PM
HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 24/Rajab/1438H
daidai da 21/Afrilu/ 2017M
LIMAMI MAI HUXUBA
DR. ABDULBARIY XAN AWWADH AS-SUBAITIY
TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
BARIN WANI GURBI, A RAYUWAR MUSULMI
Shehin Malami wato: Abdulbariy bn Auwadh As-subaity –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: BARIN WANI GURBI, A RAYUWAR MUSULMI, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan … .
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Bayan haka:
Yana daga manyan ni'imomin Allah ga bawa, YA SANYA MASA WANI GURBI DADDAXA, WANDA ZAI RAYAR DA AMBATONSA, KUMA LADANSA YA RIQA GUDANA DA SHI, SAI RAYUWARSA TA TSAWAITA DA SHI, SABODA DAWWAMAR KYAWAWAN AIYUKANSA A BAYAN MUTUWARSA, Allah (تعالى) yana cewa: "Lallai ne, Mu mu ke raya matattu, kuma mu rubuta abinda su ka gabatar, da gurabensu (wato, abinda su ka bari a bayan mutuwa), kuma kowane abu mun qididdige shi a cikin babban littafi, mabayyani" [Yasin: 12].
Aiki mai kyau, wanda mutum ke aikatawa, a tsawon tafiyar rayuwarsa, yana gadar masa da kasancewar Allah, tare da shi, da samun kiyayewar Allah, kuma a lokacin da wahayin farko, ya zo ga Manzon Allah kwatsam, alhalin Annabi (صلى الله عليه وسلم), tsoro ya dabaibaye shi, ya ce wa matarsa Khadija (رضي الله عنها): "Lallai na ji tsoro ga raina", Sai ta ce masa: "A'a, ka yi bushara, Ina mai rantsuwa da Allah! lallai Allah, ba zai tozarta ka ba, har abada, domin kai kana sada zumunci, kana faxar gaskiyar zance, kana tallafa wa gajiyayye, kuma kana bada abin tarbar baqo, kuma kana taimako kan musibu na gaskiya" Bukhariy ya ruwaito shi.
Kuma idan Allah ya buxe qofofin rahamarSa ga bawanSa, sai ya datar da shi, ga aikin da ke da gurbi mai tasiri da kyau, sai kuma ya sanya masa albarka a cikinsa, ya kuma ninninka amfaninsa, da falalarsa, kuma ya bashi mayewa a cikin dukiyarsa; kaxan xinsa, da mai yawa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Dirhami xaya, ya rigayi dirhami dubu xari", Nasa'iy ya ruwaito shi, da Ibnu-Hibbana a cikin sahihinsa.
Kuma manufar barin wani gurbi a bayanka, ita ce neman yardar Allah, kuma musulmi baya jiran ya gani da kansa, sakamakon aikinsa, kuma baya danganta sakamakon ga qoqarinsa, da jajircewarsa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "An bijiro min da al'ummai (na gan su), sai ga wani Annabi, yana shigewa, a tare da shi akwai mutum xaya, wani Annabin kuma, a tare da shi akwai mutane biyu, wani Annabin kuma, kusan mutane tara, wani Annabin kuma babu wani a bayansa", Bukhariy ya ruwaito shi.
Kuma idan mutane su ka jahilci qoqari, da aiyukan wanda ya bar wani gurbi (a bayan mutuwarsa), to hakan ba zai cutar da shi ba, saboda ilimin Allah, ya kewaye dukkan abinda ya vuya, da wanda ya bayyana, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma, irin abinda kuka gabatar ga kayukanku na alkhairi, za ku same shi a wurin Allah, zai kasance mafifici (akan dukiyar da kuka ajiye), kuma zai fi girma ga sakamako" [Muzzamil: 20]
Kuma duk lokacin da mutum ya gyara zuciyarsa, kuma ya kusanci MahaliccinSa, sai gurbin da ya bari a bayansa, ya amfanar, 'ya'yan itatuwansa, su yi fure, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma, amma wannan bangon, to ya kasance na waxansu yara biyu ne, marayu, a cikin birnin, kuma akwai wata taskar su (ta kuxi) a karkashinsa, kuma Ubansu ya kasance salihin mutum … " [Kahf: 82].
Kyakkyawan aikin da aka assasa shi da niyya tagari, yana sanya gurbin tasirinsa ya qara tabbatuwa, ya qara xaukan shekaru, tare da qara samun karvuwa, Allah (تعالى) yana cewa: "Zuwa ga Allah ne, kalmomi daxa-xa ke hawa, kuma aiki nagari ke xaukaka" [Faxir: 10].
Kuma duk aikin da ba a gina shi akan imani ba, to qarshensa shi ne gushewa da lalacewa, duk kuma yadda (a farkonsa) ya kai ga girma da bunqasa.
Addinin musulunci yana qara dasa lamarin barin gurbi mai tasiri (bayan mutuwa), wanda zai gina rayuwa, ya kuma tsayu wajen isar da saqonta, domin rayuwar ta ci gaba da ginuwa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Idan qiyama ta zo, tsayuwa, sai a hannun xayanku ya kasance akwai bishiyar da zai dasa, to idan ya samu damar ya yi dashen gabanin tsayuwarta, to ya dasa shi", Bukhariy ya ruwaito shi a cikin Adabul Mufrad, kuma Albaniy ya inganta shi.
Saboda dashen da mutum ke dasawa, koda bai tsinki 'ya'yansa a cikin rayuwarsa ba, to ana qirga shi cikin gurbin da ya bari wanda ladansa ke wanzuwa a gare shi, a lokutan da al'ummar da ta zo a bayansa, ta ke amfanuwa, saboda Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Babu wani musulmi da zai yi wani dashe, ko ya yi wata shuka, sai wani tsuntsu ko mutum ya ci daga cikinsa, ko kuma dabba, face ya kasance sadaka a gare shi", Bukhariy ya ruwaito shi.
Kuma, Duk wanda ya san tasirin samar da abinda zai bar wani gurbi (bayan mutuwarsa), to sai ya hau ga qololuwar qoqari, ya kuma shiga tsere (cikin aiki), Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Wanda a cikin musulunci ya sunnata wata sunna mai kyau, to yana da ladanta, da ladan wanda ya yi aiki da ita a bayansa, ba tare da an tauye komai daga ladansu ba", Muslim ya ruwaito shi.
Musulmi mai kyakkayawan imani, ma'abucin tarihi mai kyau, shi ne abin buga misali, mai amfani, wanda duk inda ya sauka ya kan amafanar, saboda halayyansa abin koyi ne, tarihinsa kuma fitila ce mai haskawa, Ga Annabin Allah; Ibrahim (عليه السلام) a inda ya ke roqon UbangijinSa, da cewar: "Ya Ubangina ka bani hukunci, kuma ka riskar da ni ga salihai * kuma ka sanya mini harshen gaskiya, a cikin mutanen qarshe * kuma ka sanya ni daga magadar aljannar ni'ima" [Shu'ara'i: 83-85].
Sai Allah ya amsa masa addu'arsa, ya ce: "Kuma muka bar masa (yabo) a cikin jama'ar qarshe" [As-safaat: 78].
Don haka ne, babu wani mahalukin da zai yi salati ga annabinmu Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) face ya yi salati ga annabi Ibrahim (عليه الصلاة والسلام).
Kuma bayyanar gurbin musulmi mai tasiri, a cikin rayuwarsa, da bayan mutuwarsa yana daga busharorin gaggawa, kan datarwar da Allah ya yi ga bawa, da yadda ya karvi aiyukansa, An ce wa Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم), Mutum ne ya ke aikata aikin alkhairi, sai mutane su gode masa akansa –ko su riqa sonsa- (shin hakan riya ne?) Sai ya ce: "Wannan ai, bushara ce ta gaggawa (tun daga duniya) ga mumini", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma FAGAGEN DA AKE IYA BARIN GURBI A CIKINSU (a rayuwa) NAU'I-NAU'I NE, shakalinsu kuma masu yawa ne, Sai kowani mutum ya zavi abinda zai dace da damammakinsa, da abinda ya yi daidai da ikonsa, da baiwawwakinsa, kamar yadda sahabban Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) su ka kasance, waxannan da su ka bar gurbi mai tasiri, a dukkan vangarorin rayuwa; kamar, a wajen kawo gyara, da alqalanci, da ciyarwa, da jihadi, da kuma ilimi.
Kuma duk amfanin da ke kaiwa ga wasu, ya ke shuka alheri, wanda kuma rayuwa ke gyaruwa da shi, to zai kasance yana da gurbin tasiri mai daxi, da lada madawwami, misalinsa kamar karantarwa, da da'awa, da biyan buqatu (ga mabuqata), da taimakon wanda aka zalunta.
Kuma lallai mafifici, daga cikin nau'ukan bauta, shi ne wanda ya fi yawan amfanarwa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Wanda ya yi da'awa zuwa ga wata shiriya, to zai kasance yana da lada kwatankwacin na wanda ya bi shi, ba tare da an tauye komai daga ladansu ba", Muslim ya ruwaito shi.
Don haka, Mai hankali ko zurfin tunani, shi ne wannan da ke barin wani gurbi, don bayan mutuwarsa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Yana daga abinda ke riskar mumini na aikinsa da ladansa kyawawa, bayan mutuwarsa, Ilimin da ya karantar da shi, da mus-hafin Qur'ani wanda ya gadar da shi, ko masallacin da ya gina shi, ko gidan da ya gina ga matafiyi (xan hanya), ko kogin da ya jawo wutsiyarsa, ko sadakar da ya fitar da ita daga dukiyarsa, a halin lafiyarsa da rayuwarsa, wanda za ta riske shi, a bayan mutuwarsa", Ibnu-Majah ya ruwaito shi, kuma Albaniy ya inganta shi.
YANA DAGA ALAMOMIN WANDA ZAI BAR GURBI MAI TASIRI; Ya sanya lahira a gaban idanunsa biyu, kuma ya riqa gina baxini (zuciya), da kuma zahirinsa, yana mai tsarkake ransa da aikinsa, zancensa kuma ya riqa daidaita shi da aikinsa, Allah (تعالى) yana cewa: "Na'am, Wanda ya sallama fiskarsa ga Allah, alhali kuwa yana mai kyautatawa, to, yana da ladansa a wurin Ubangijinsa, kuma babu tsoro a kansa, kuma ba za su zama suna baqin ciki ba" .
YANA DAGA ALAMOMIN WANDA ZAI BAR GURBI MAI TASIRI; Lallai manufofinsa da halayyarsa su kan zama tabbatattu, rayuwarsa kuma, akan ma'auni madaidaici, yana yin aiki, cikin yarda da ransa, da jin buwayar addininsa.
Kuma waxanda ke barin wani gurbi a cikin mutane da rayuwa, sune waxanda su ka shuka/ ko dasa soyayyarsu, a cikin zukata, tare da yin sabo da mutane, ya zo cikin hadisi cewa, "Idan Allah ya so bawa, sai ya kirayi mala'ika Jibrilu, cewa: Allah yana son wane, ka so shi, sai Jibrilu ya so shi, daga nan sai mala'ika Jibrilu ya yi kira a cikin ma'abuta sama, cewa: Lallai Allah yana son wane, ku so shi, sai ma'abutan sama, su so shi, sa'annan sai a sanya masa karvuwa a bayan qasa", Bukhariy ya ruwaito shi.
Mutum yana wayan gari, ya bar wani gurbi (mai babban tasiri ne), a lokacin da ya keve kansa da wani aiki, ya kuma gina/ ko zana dukkan abinda ya ke son ya cimma, tare da iyakance manufofinsa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Mafi soyuwan aiyuka a wurin Allah, shi ne wanda ya fi dawwama, koda ya zama kaxan", Bukhariy ya ruwaito shi, da Muslim.
Kuma alqur'ani mai karamci yana kwaxaitarwa kan (musulmi) ya keve kansa da wani aikin, a cikin faxinsa: "Baya kasancewa ga muminai, su fita zuwa yaqi gaba xaya, saboda haka, don me, wata jama'a daga kowane vangare a cikinsu, ba za ta fita (ga neman ilimi ba) domin neman fahimtar addini, kuma domin su yi gargaxi ga mutanensu, idan sun komo zuwa gare su, tsammaninsu su zama masu kiyayewa" [Tauba: 122].
Da kuma, a cikin faxinSa, "Sai ka tambayi masani mai bada labari a kansa" [Furqan: 59].
Da kuma, a cikin faxinSa: "Kuma babu mai baka labari, kamar wanda ya sani" [Faxir: 14].
Kuma wannan gurbin, ya kan kasance mai girman tasiri ne, a lokacin da za mu sanya son inganta aiki, a matsayin jagora, kyautatuwar aikin kuma da kwalkwale shi, a matsayin hanya, matakin ihsani kuma, a matsayin turba, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Lallai Allah ya rubuta kyautatawa, akan komai".
Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima, Ina faxar abinda ku ke ji wannan, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa, lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
[B]HUXUBA TA BIYU
Akwai wanda ke samar da gurbi, mai nakasasshen haske, wanda kuma aka jahilci hanyar da ya xauko shi, kuma babu wata manufa a bayansa da ke waqen cimma ta, kuma ba wani abu mai qima ake son assasawa ba, abun da aka qunsa, xan jebu ne, da gini karkatacce, wanda kuma neman shahara ce ke tunkuxa shi, ko neman tara dukiya.
Kuma abinda ya fi wannan muni, shi ne idan wancan gurbin ya samar da rugujewar addini, da kuma rushewa, ko gurvata halayya, "Sune waxanda aikinsu ya vace, a cikin rayuwar duniya, alhalin suna zaton suna kyautata aiki" [Kahf: 104].
Gurbin da aka bari tasirinsa yana tozarta, haka kuma qimarsa, idan sahibinsa da ya aikata shi ya buge da aikata savo a lokacin da ya kevanta, ko ya riqa bayyanar da laifuka na savo, domin Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Lallai na san wasu mutane daga al'ummata, waxanda za su zo da kyawawan aiyuka, kwatankwacin duwatsun tihama, farare, sai Allah Mabuwayi da xaukaka ya sanya su, su zame kamar qura abar sheqewa",
Sai sahabi Sauban, ya ce: Ya Ma'aikin Allah, Sifanta mana su, fito da lamarinsu a fili, domin kada mu kasance daga cikinsu, alhalin bamu sani ba?
Sai ya ce: "Lallai su, 'yan'uwanku ne, kuma daga irin fatarku, kuma suna sallar dare kamar yadda kuke yi, sai dai su, mutane ne waxanda idan su ka kevanta da ababen da Allah ya haramta, sai su keta alfarmarsu", Ibnu-Majah ya ruwaito shi, kuma Albaniy ya inganta shi.
Mafi sharri daga cikin masu barin wani gurbi, lallai su ne waxanda, su ka toshe qofofin kyawawan aiyuka ga kayukansu, kana su ka buxe tarin munanan aiyuka -a takardun aiyukansu-, har ya kasance, mutumin da ya samar da wannan gurbin ya mutu, alhalin aikinsa yana cigaba da wanzuwa, a matsayin zunubi; ga wanda ya samar da shi, Allah (تعالى) yana cewa: "Domin su xauki zunubansu cikakku, a ranar qiyama, da kuma zunuban waxanda su ke vatar da su ba tare da ilimi ba" [Nahl: 25].
Kuma, ya ce: "Kuma lallai suna xaukar kayan nauyinsu, da waxansu nauyayan kayan, tare da kayan nauyinsu" [Ankabut: 13].
Mai aikata mummunan aiki, lallai yana cutar da al'ummarsa, yana keta kariyar qasarsa, kuma yana yayyaga alfarmar al'ummarsa, saboda abin nan da ke aikatawa; na vatarwa, da yaudara, da qawata mummunan aiki, ta hanyar kafofin laturoni (da intanet), wanda ya ke qawata sha'awowi da waxannan kafofin, ko ta hanyar teburan da ya ke yaxa shubuhohi daga gare su, da yadda ya ke yin da'awa zuwa ga aikin savo, da qetare iyaka, ko kuma tallen laifuka, ko kuma ta hanyar kafofi masu rusa ladduba, da halayya (nagartattu), Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Duk wanda ya yi da'awa zuwa ga wata vata, lallai akansa akwai zunubi, kwatankwacin na wanda ya bishi, kuma hakan ba zai tauye komai daga zunubansu ba", Muslim ya ruwaito shi.
TA QARE….