المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : HUXUBAR MASALLACIN ANNABI (صلى الله عليه وسلم) JUMA'A, 25/JUMADAL AKHIRAH/1438H Daidai da 24 /MARIS / 2017M


طاهر جبريل دكو
_15 _April _2017هـ الموافق 15-04-2017م, 11:46 AM
HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 25/JUMADAL AKHIRAH/1438H
Daidai da 24 /MARIS / 2017M




LIMAMI MAI HUXUBA
DR. ABDULMUHSIN XAN MUHAMMADU XAN ABDURRAHMAN ALQASIM







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Lallai yabo na Allah ne; muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kayukanmu, da munanan aiyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar, babu mai vatar da shi, Wanda kuma ya vatar, to babu mai shiryar da shi.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke, bashi da abokin tarayya.
Ina kuma shaidawa lallai annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa ne.
Salatin Allah su qara tabbata a gare shi, da IyalanSa da SahabbanSa; da sallamar amintarwa mai yawa.

Bayan haka;
Ku kiyaye dokokin Allah da taqawa -Ya ku bayin Allah- iyakar kiyayewa, kuma ku yi riqo a musulunci da igiya mai qarfi.

Ya ku musulmai …
Allah ya samar da halittu, domin bautarsa da ta game, TSORONSA DA FATAN RAHAMARSA DA SOYAYYARSA, Kuma a kan waxannan ginshiqan ne guda uku, ake gina ibada.
Kuma SON ALLAH shi ne mafi girman waxannan rukunnan (uku).
Kuma tushen kowani aiki da motsawa a duniya shi ne, SO DA NUFI,
Kuma SON ALLAH yana daga cikin manya-manyan abubuwan da imani ke wajabtawa, kuma shi ne babban ginshiqin imani, kuma wanda ya fi girma cikin qa'idodinsa, hasalima domin son Allah ne, aka samar da halittu, kuma shi ne manufar bada umarni,
Kuma son Allah shi ne, ginshiqin kowani aiki daga aiyukan imani da addini,
Kuma gaya ko manufar ibada ita ce, kaiwa maqurawajen son Allah ta'alah, da qanqan-da-kai a gare shi,
Kuma domin soyayyar magabata su ka yi tsere cikin aiki, kasancewar ita ce, mafi girman matakai ko nau'ukan ibadodi, domin babu abinda ya fi soyuwa a wurin lafiyayyun rayuka fiye da Mahaliccinsu da ya qage su, saboda Shi ne Abin bautarsu, Majivinsu, Ubangijinsu, Mai jujjuya lamuransu, Mai azurta su,
Kuma asali ko ginshiqin tauhidi, kuma ruhinsa, shi ne, Tsantsanta son Allah shi kaxai,
Kuma tauhidi baya zama cikakke har sai qaunar bawa ga Ubangijinsa ta cika, kuma ta rigayi son da bawan ya ke yi ga xaukacin ababen so, domin ginshiqin addini, shi ne ikhlasi cikin soyayya, kamar yadda tushen da shirka ke aukuwa kuma shi ne haxa Allah a cikinta.
Kuma lallai imanin bawa, da daidaitarsa a kan addini, ba sa zama cikakku, face ya tabbatar da qaunar Allah, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Na rantse da wanda Raina ke hannunsa! Xayanku ba zai yi Imani ba, har sai na fi soyuwa a gare shi, fiye da ransa", Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.
Kuma son Annabi (صلى الله عليه وسلم) tana biye ne da son Allah.
Kuma Allah ya yabi bayinSa muminai, da tsantsanta sonsu, a gare shi, kuma Ya zargi mushirkai da sanya masa kishiyoyi a cikin soyayya, a inda ya ce: "Kuma akwai daga mutane, wanda yak e riqon kinaye, baicin Allah, kuma waxanda su ka yi imani mafiya so ne ga Allah" .
Kuma Allah ya sanya soyayya, ta zama sifar da masoyanSa su ka fi kevanta da ita, a inda ya ce: "Da sannu, Allah zai zo da wasu mutane, da yak e sonsu, suna sonSa" [Ma'idah: 54].
Kuma idan bawa ya tsantsanta sonsa ga Allah, to lallai ya xanxani halawar imani da zaqinsa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Abu uku, wanda su ka kasance tare da shi, to lallai ya samu halawar imani da zaqinsa, Ya kasance, Allah ne da ManzonSa su ka soyuwa a gare shi fiye da waxanda ba su ba, kuma ya so mutum ba wai yana sons aba ne, sai don Allah, kuma ya qyamaci komawa cikin kafirci, kamar yadda ya ke qin a jefa shi a cikin wuta", Bukhariy da Muslim.
Kuma gaskiyar soyayya ita ce mafi alherin guzuri domin ranar komawa, kuma madalla da ita, ta kasance tanadi domin haxuwa da Allah, saboda wani mutum ya tambayi Annabi (صلى الله عليه وسلم) cewa, yaushe za a yi qiyama? Sai ya ce: "Me ka tanadar mata?", Sai ya ce: Ban mata tanadin salloli dayawa, ko azumi ko sadaka ba, sai dai Ni ina son Allah, da ManzonSa, Sai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Kai, kana tare da waxanda ka ke so", sahabi Anas (رضي الله عنه) ya ce: Bamu yi farin ciki, da wani abu ba, irin farin cikin da muka yi da faxin Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: Kai, kana tare da waxanda ka ke so. Sai Anas (رضي الله عنه) "Ni, ina son Annabi (صلى الله عليه وسلم), da Abubakar, da Umar, Kuma ina fatan na kasance tare da su, saboda son da na ke musu, koda kuwa ban aikata kwatankwacin aikinsu ba" Bukhariy ya ruwaito.

Kuma matsayin bayi, yana kasancewa ne, gwargwadon qaunarsu ga Allah, Bakar Almuzaniy –رحمه الله- ya ce: "Abubakar (رضي الله عنه) ba wai ya samu fifiko ba ne, saboda yawan sallah, ko azumi, sai dai da wani abinda ya kasance a cikin zuciyarsa".
Ibnu-Ulaiyah –رحمه الله- ya ce: "Abinda ya kasance a cikin zuciya Abubakar shi ne, son Allah, da kuma nasiha ga halittun Allah".

Kuma duk wanda ya xanxana daga cikakken son Allah, to sai hakan ya shagaltar da shi, daga dukkan ababen so, kuma ba zai xebe kewa ba, face ubangijinSa, kuma ba zai rataya ba, sai da shi.

Kuma Allah ya tanadi narko ga masu kawar da kai, ga soyayyarSa, a inda ya ce: "Ka ce, idan Ubanninku, da xiyanku, da 'yan'uwanku, da matanku, da danginku, da dukiyoyi, waxanda ku ka yi tsiwirwirinsu, da fataucin da ku ke tsoron tasgaronsa, da gidaje waxanda ku yarda da su, sun kasance mafiya soyuwa, a gare ku, daga Allah da ManzonSa, da yin jihadi ga hanyarSa, to, ku yi jira har Allah, Ya zo da lamarinSa! Lallai Allah bay a shiryar da mutane fasiqai" [Taubah: 24].
Kuma samun irin wannan soyayyar kan kasance ne, da abinda Allah da ManzonSa su ka sunnanta.

KUMA MAFI GIRMAR SABBUBA, WANDA KE HUKUNTA BAWA YA SO UBANGIJINSA, shi ne: SAMUN ILIMIN SANIN SUNAYEN ALLAH DA SIFOFINSA, Domin Allah shi ne, abin so, domin zatinSa, da kuma saboda kamalar sifofinSa, kuma kyan Allah ta'alah, da kamalarSa, da sunayenSa, da sifofinSa, suna hukunta bayinSa da son da ya kai maqura, da qanqan-da-kai, da biyayya a gare shi. Kuma kowani SUNA na Allah ta'alah, da SIFA, a tattare da shi, akwai fiskokin dalilai da su ke nuni akan Allah, waxanda saboda su, Allah ke cancantar cikakkiyar soyayya daga bayinSa, kuma da waxannan sunayen Allah ya nemi sanu a wurin bayinSa, kuma ya yawaita ambatonsu a cikin littafinSa, da kuma a harshen AnnabinSa, domin a riqa ambaton Ubangiji da su, ana gode masa.
Kuma fifikon martabobin halittu cikin son Allah, gwargwadon fifikon martabarsu ne, wajen saninSa da samun ilimi akanSa, kuma wanda ya fi halittu sanin Allah, shi ne wanda ya fi tsoronSa.

KUMA YANA DAGA ABUBUWAN DA SU KE HUKUNTA SON ALLAH: YAWAITA AMBATONSA, Domin dawwamar da ambatonSa yana gadar da soyayyarSa, Allah ta'alah ya ce: "Ya ku waxanda su ka yi imani ku ambaci sunan Allah, Ambato mai yawa" [Ahzab: 41].
Kuma ibadodi suna rataya ne akan zikiri, domin halittu su rataya da Ubangijinsu, zukatansu kuma su cika da sonSa.
Kuma sunnar Allah ta'alah (ta bbatar da cewa), lallai wanda ya yawaita ambaton wani abu, ya kan so shi, kuma duk wanda ya so, wani mutum yak an yawaita ambatonsa, Kuma Allah, shi ne ya fi cancantar a so, shi, kuma a ambace shi. Kuma sakayya ya kan kasance ne daga jinsin aiki. Allah ta'alah y ace, a cikin hadisin Qudusiy, "Ni, ina yadda bawana ya yi zatona, kuma Ni ina tare da shi idan ya ambace ni, Idan ya ambace Ni, a cikin ransa, to zan ambace shi a cikin raina, idan kuma ya ambace Ni a cikin wata jama'a, to zan ambace shi a cikin jama'ar da ta fi tasa alkhairi" Bukhariy da Muslim.

KUMA RAYUKA SUNA SON WANDA YA KYAUTATA MUSU, Allah kuma shi ne, mai bayar da ni'ima, mai kyautata wa bayinSa –ga haqiqa-, kuma shi yak e bayar da dukkan ni'imomi, koda kuwa sun gunada ta hannun wasu, to amma shi ne, mai sauqaqe su, wanda ke sabbaba sabubansu; shi kaxai. "Yak u, mutane! Ku tuna ni'imomin Allah, a kanku, Shin akwai wani mai halitta, baicin Allah, da zai arzutta ku daga sama da qasa? Babu wani abin bautawa da gaskiya face, shi. Ta yaya ake karkatar da ku?" [Faxir: 3].
Saboda qoqarin leqen ni'imomi, da yin tunani a cikinsu, yana hukunta son wanda ya bada kyautar ni'imomin, da gode masa akansu. Kuma son Allah, yana cikin godiyar da ta wajaba ga Allah a cikinsu, kuma yin hakan sababi ne na dawwamar ni'imomi da qaruwarsu, Allah Mabuwayi da xaukaka yana cewa: "Lallai ne, idan ku ka gode sai na qara muku" [Ibrahim: 7].

KUMA YIN TUNANI CIKIN MULKIN DA KE SAMMAI DA QASA YANA SANYA MA'ABUCINSA SON ALLAH DA GIRMAMA SHI, Saboda zukata an halicce su, a kan son kamala, kuma babu wata kamala, ta haqiqa, sai ga Allah (سبحانه).

KUMA FISKANTAR AIYUKAN BIYAYYA CIKIN GASKIYA DA IKHLASI, SABABI NE NA ALLAH YA YI FALALA GA BAWANSA, Sai kuma Allah ya yi masa sakayya da jin daxin soyayyarSa, da kuma xebe kewar da ta ke cikin ganawa da Shi, har ya zama ba zai nemi canji akan hakan ba, kuma ba zai tava qinsa ba, har abada, sai kuma ya rayu a cikin aljannar duniya, gabanin ya shiga aljanna a lahira, Annabi (صلى الله عليه وسلم) "Ya Bilal! Ka tsayar da ikamar sallah, kuma ka hutar da mu da ita". Abu-dawud ya ruwaito shi.

KUMA TILAWAR LITTAFIN ALLAH, DA TADABBURIN MA'ANONIN AYOYINSA, RAYUWA NE GA ZUKATA, kuma (Qur'ani) tsarkaka ga rayuka, kuma tunatarwa da shiriya, kuma wa'azi da waraka. Wanda ya lazimci ce shi, yak an so UbangijinSa, kuma ya kan kawar da kai ga abinda bas hi ba.

KUMA BABU HANYAR ISA KO KAIWA GA SAMUN SOYAYYAR ALLAH, DA SAMUN KUSANCI GARE SHI, SAI TA HANYAR QANQAN DA KAI GA ALLAH SUBHANAHU, da karayar zuciya a gaba gare shi.
Wannan kuma gaba xayansa addu'a ta haxe su.

KUMA nisantar cutukan shubuhohi da sha'awowi, hanya ne na samun gyaruwa da daidaituwa (istiqama).
KUMA samun abokai nagari, mai taimako ne na alkhairi, kan aikata abinda Allah yak e so, kuma ya yarda.
Shi KUMA ambaton aljanna da abinda ke cikinta na ni'imah, wanda kuma ni'imar da ta fi xaukaka ita ce, ganin Ubangiji mai karamci = yana tayar da lamarin son Allah (a zuciya), da kuma lamarin son ganawa da shi. Kuma duk wanda ya so ganawa da Allah, sai Allah ya qaunaci ganawa da shi.

Lallai kuma soyayya ta gaskiya tana bayyana akan gavvai, kuma ma'abucinta baya kasancewa face mai ikhlasin bautarsa ga Allah, mai bin Manzon Allah (S.A.W), Hasanul Basariy –رحمه الله- ya ce: "Wasu mutane sun riya cewa suna son Allah, sai Allah ya jarrabe su, da faxinsa: Ka ce, idan kun kasance kuna son Allah, to ku bi Ni, Allah zain so kuma ya gafarta muku zunubanku" [Ali-imrana: 31].

Kuma idan soyayya ta ingantu, sai abinda ta ke hukuntawa ya tsayu, sai bawa ya yi soyayya domin Allah, kuma ya qi don Allah.
Kuma Allah ya siffanta waxanda ya ke sonsu, a cikin faxinsa: "masu tawali'u ga muminai, masu izza akan kafirai" [Ma'idah: 54].
Kuma duk wanda ya so, wanda Allah ya so, to lallai haqiqa ya so Allah.

Kuma duk wanda soyayyarsa ta zama ta gaskiya to sai ya so aiyukan xa'a, kuma ya yi aiki da su, ya kuma qi savo, kuma ya nisance shi.

KUMA YANA DAGA CIKIN ALAMOMIN SON ALLAH, YAWAITA AMBATONSA, Kuma duk wanda ya so Allah, sai ya so maganar Allah, kuma ba zai qosa daga tilawarsa ba.
Kuma idan son Allah ya samu gindin zama a cikin zuciya, sai bawa ya fiskanci Allah, yana mai fatan samun rahamarSa, yana kuma tsoron fushinSa, sai kuma jiki gaba xayansa ya zama salihi, baya qosawa da aiyukan kusantar Allah, kuma baya gajiyawa da yin xa'a, yana mai yarda da hukuncin Allah da qaddararSa, yana samun yaqini cewa lallai zavin da Allah ya yi masa ya fi alkhairi akan abinda ya zava shi da kansa, sai ya yi ta hauhawa ga matakin ihsani, har zuwa lokacin da gaibu zai kasance kamar abinda ya ke bayyane.

Allah ya siffanta da sifofin girma, da kyawu, "Kuma babu wani abu da ya zama kamar tamkarsa, kuma shi ne Mai ji Mai gani" [Shura: 11].
Kuma yana daga CIKIN SIFOFINSA: SOYAYYA, Yana son biyayya, kuma yana son ma'abuta biyayya, irin soyayyar da ta dace da girmanSa da matsayinSa,
(Allah) yana son addinin musulunci, kuma ya yarje mana shi (a matsayin addini), kuma yana son annabawanSa da manzanninSa da bayinSa salihai, kuma Allah shi ne, ALWADUDU ma'abucin soyayya mai tsanani ga waliyyanSa, su kuma bayinSa muminai duk wanda ya yi adawa da su, to lallai Allah ya bada shelar yaqi da shi.
Allah WUTURI shi kaxai yana son abu guda xaya, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai ne Allah yana da sunaye casa'in da tara (99); wato xari saura xaya, wanda ya kiyaye su ya shiga aljanna, kuma shi Wutri ne yana son abi wutri" . Muslim ya ruwaito shi.
Don haka, Allah yak e son wutri daga cikin xa'ar bayi, kuma Yana son a kaxaita shi da wannan xa'an; ba tare da an haxa shi da abokin tarayya ba.
Kuma ita SALLAH ganawa ce tsakanin bawa da UbangijinSa, kuma Allah yana son tsayar da ita a kan lokacinta.
Kuma mafi soyuwar sallar nafila da azuminsu a wurin Allah shi ne wanda Annabi Dawud (عليه السلام) ya kasance a kansu. "Domin ya kasance yana azumtar yini, sai ya sha ruwa a xaya yinin". Bukhariy ya ruwaito shi, da Muslim. "Kuma ya kasance yana yin barcin rabin dare, ya yi sallar xaya bisa ukunsa, sai ya yi barcin xaya bisa shidansa" Ibnu-majah.

Kuma Allah yana son qanqan-da-kan bayinSa a gare shi, da karayar zukatansu a gaba gare shi, Wani mutum ya ce wa Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ka bani labarin aikin da Allah ya fi so, sai ya ce: "Na hore ka da yawaita sujjada ga Allah", Muslim ya ruwaito shi.

Kuma mafi gaskiyar zance shi ne wanda ya zama, yabo ne ga Allah, kuma Allah yana son hakan daga bayinSa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Babu wani da yabo ya fi soyuwa a gare shi, fiye da Allah, kuma domin haka ne ya yaba wa kanSa", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma "mafi soyuwan Magana a wurin Allah shi ne: SUBHANALLAHI WA BI HAMDIHI", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma "Kalmomi biyu, suna da sauqi akan harshe, suna da nauyi a ma'auni, Allah mai rahama yana sonsu, SUBHANALLAHIL AZIM, SUBHANALLAHI WA BI HAMDIHI", Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.
Kuma kalmomi huxu (4) su ne maganar da ta fi soyuwa a wurin Allah, "SUBHANALLAHI, WALHAMDU LILLAHI, WA LA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR", Muslim ya ruwaito shi.
"Kuma sunayen da Allah ya fi sonsu, su ne: Abdullahi da Abdurrahma", Abu-dawud ya ruwaito shi.

Waxanda su ka fi dukkan mutane cancantar biyayya su ne iyaye, kuma yin biyayya a gare su, Allah yana sonsa, kuma ya yarda da shi, "An tambayi, wani aiki Allah ta'alah ya fi so? Sai Annabi ya ce: Salla a kan lokacinta, da biyayya wa iyaye, da kuma jihadi fiy sabilillahi", Nasa'iy ya ruwaito shi.

Kuma "Aikin da Allah ya fi so, shi ne farin ciki, da ka shigar da shi zuciyar musulmi", Tirmiziy ya ruwaito shi.

Tausasawa dukkansa alkhairi ne, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai ne Allah yana son tausasawa a cikin lamura gaba xaya", Bukhariy daMuslim su ka ruwaito shi.
Kuma Allah yana son haquri da natsuwa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce, wa Ashaj (Ashajin Abdulqais): "Lallai ne kana daxabi'u biyu, waxanda Allah ke so, haquri, da natsuwa", Muslim ya ruwaito shi.
Kunyar da za ta hana aikata savo, da suturar mace, da kamewarta, abubuwa ne da Allah ke son su, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم): "Lallai ne Allah Mai kunya ne Mai suturcewa, kuma yana son kunya da sutura, don haka idan xayanku zai yi wanka, sai ya vuya", Abu-dawud ya ruwaito shi.

Kuma shi Allah, "Mai kyau ne, yana son kyau", Muslim ya ruwaito shi.

Kuma Allah Mai afuwa ne, yana son afuwa ga halittunSa, Annabi (صلى الله عليه وسلم): "Ya Allah, lallai ne kai mai afuwa ne, kana son afuwa, ka min afuwa", Tirmiziy ya ruwaito shi.
Kuma "Babu wani wanda bada uzuri ya fi soyuwa a gare shi, fiye da Allah", Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.
Atishawa itama Allah yana sonta, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai Allah yana son atishawa, kuma yana qin hamma", Bukhariy ya ruwaito shi.
Kuma bayyanar da ni'ima yana daga abubuwan da Allah ke so, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai Allah yana son garin alamar ni'amar da ya yi ga bawanSa", Tirmiziy ya ruwaito shi.
Kuma "Babu wani daga cikinku da ya ci wani abinci wanda Allah ya fi so, fiye da abinda hannayensa suka aikata", Ahmad ya ruwaito shi.

Kuma Allah yana qara son aiyukan kwarai, a lokuta masu alkhairi, "Babu wani aiki wanda ya fi so, fiye da goman qarshe", Bukhariy ya ruwaito shi.

Kuma aiki da shari'a, ta vangaren rangwamensu da masu azamarsu, shi ne sha'anin mumini, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai ne Allah yana son ayi aiki da rangwamenSa, kamar yadda yak e qin ayi aiki da savonSa", Ahmad ya ruwaito shi.
Kuma tabbata akan xa'a dace ne daga Allah, kuma tabbatuwa, kuma "mafificin aiyuka a wurin Allah, shi ne wanda aka fi dawwama akansa, duk qarancinsa", Bukhariy ya ruwaito shi.
Kuma lazimtar zikiri yana taimako, wurin samun kyakkyawar qarshe, kuma "mafi soyuwar aiki a wurin Allah, shi ne ka mutu, alhalin harshenka yana xanye da ambaton Allah", Ibnu-hibbana ya ruwaito shi.
Kuma wuraren da xa'a ke yawaita sun fi soyuwa ga Allah, fiye da wassunsu, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "kuma a cikin garurruka, wuraren da su ka fi soyuwa a wurin Allah, sune masallatansu, wanda kuma Allah ya fi qinsu, su ne kasuwanninsu", Muslim ya ruwaito shi.

Kuma kamar yadda Allah ke son xa'a da aiki, to kuma yana son mai aiki da xa'a, kuma mafi soyuwan bayi a wurin Allah sune badaxinSa biyu; "Kuma Allah ya riqi Ibrahima badaxi", [Nisa'i: 125]. Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai ne Allah ta'alah ya riqe ni badaxi, kamar yadda ya riqi ibrahima badaxi", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma ya jefa soyayyarSa ga annabi Musa (عليه الصلاة والسلام) a inda ya ce: "Kuma na jefa wani so daga gare Ni, a kanka, kuma domin a riqe ka da kyau a kan idoNa", [Xaha: 39].

Kuma duk wanda ya so, sunayen Allah da sifofinSa, sai Allah ya so shi, Wani mutum ya kasance yana yin karatu ga abokansa a cikin sallah, sai ya rufe karatunsa da QUL HUWAL LAHU AHAD, yayin da su ka dawo sai su ka ambaci hakan ga Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) sai ya ce"Ku tambaye shi don me ya sa ya ke aikata hakan?" sais u ka tambaye shi, sai ya ce: Saboda ita sifar (Allah) Mai rahama ne, kuma ni ina son na riqa karanta ta, Sai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Ku bashi labari, cewa Allah yana sonsa", Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.
Kuma lallai ne shi Allah subhanahu yana son masu bin annabinSa (صلى الله عليه وسلم); masu gaskiya cikin son AnnabinSa, "Kuma idan kun kasance kuna son Allah, sai ku bi ne" [Ai-imrana: ].
Kuma yana son masu taqawa, yana son masu kyautatawa.
Kuma lallai tawakkai Imani ne da yaqini, kuma Allah yana son masu tawakkali.
Shi kuma adalci da shi sammai da qasa su ka tsayu, kuma ma'abutansa Allah yana sonsu, Allah ya ce: "Kuma ku yi adalci, saboda Allah yana son masu adaci" [].
Kuma duk wanda ya bayar da dukiyarsa da ransa ga addini sai Allah ya so, shi kuma ya karrama shi, Allah (سبحانه) yana cewa: "Lallai ne Allah yana son waxanda su ke yi yaqi, domin xaukaka kamarsa, cikin sahu, kamar su, gini ne mai xamfarar juna", [Saff: 4].
Kuma haquri wajen yin xa'a, da barin savo, da lokacin bala'i, biyayyar Alah ne kuma addini, kuma Allah yana son masu haquri.
Kuma duk wanda ya aikata nafilfili bayan farillai, sai Allah ya so shi, Allah ta'alah a cikin hadisi qudusi yana cewa: "Kuma bawana ba zai kusance ni da wani abu (na ibada ba) wanda ya fi soyuwa a wurina fiye da abinda na farlanta akansa, kua bawana ba zai gushe ba yana kusantata da nafilfii face na so shi", Bukhariy ya ruwaito shi.
Kuma waxanda su ke qauracewa duniya, su ke yin aiki domin lahira, Allah yana sonsu, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Ka guji duniya, sai Allah ya so ka", Ibnu-majah ya ruwaito shi.
Kuma zama da salihan bayi albarka ce ga a'abutanta, Allah ta'alah yana faxa a cikin hadisin qudusiy: "Soyayyata ta sauka (wajaba) ga masu yin soyayya domin Ni, da masu zama domin Ni, da masu ziyara domin Ni, da masu bayarwa domin Ni".
Kuma voye aikin xa'a sababi ne na samun soyayyar Allah ga ma'abutan hakan, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai Allah yana son bawa, mai taqawa, mai wadaci (a zuciya), voyayye", Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.
Kuma "Mumini qaqqarfa (cikin imani), ya fi alheri, kuma ya fi soyuwa a wajen Allah, fiye da mumini mai rauni", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma "alamar imani ita ce, son ansarawa, alamar munafurci kuma qin ansarawa, kuma su Ansar babu mai sonsu face mumini, kuma babu mai qinsu face munafiqi, kuma wanda ya so su Allah zai so shi", Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.
Kuma duk wanda ya so waliyyan Allah da bayinSa salihai, sai Allah ya so shi, Wani mutum ya ziyarci xan'uwansa a wata alqarya ta daban, sai Allah ya sanya wani Mala'ika akan hanyarsa ya jira shi, a yayin da ya zo wurinsa sai ya ce: Ina ka nufa? Sai ya ce: na nufi wani xan'uwana ne a wannan aqaryar. Sai ya ce: Shin kana da wata ni'ima ce a kansa (haqqi) da ka ke neman bunqasarta? Sai ya ce: a'a, sai dai ina sonsa ne domin Allah Mabuwayi da xaukaka, Sai ya ce: "Lallai Ni manzon Allah ne zuwa gare ka, cewa: Allah yana sonka kamar yadda ka so shi", Muslim ya ruwaito shi.
Mai tuba, mai komawa zuwa ga Allah, Allah yana sonsa, kuma yana karvar tubansa, Allah (سبحانه) ya ce: "Lallai ne Allah yana son masu tuba, kuma yana son masu tsarkaka", [].
Kuma duk wanda ya so haxuwa da Allah, sai Allah ya so haxuwa da shi. Kuma soyayyar Allah ita ce, qololuwar abinda rayuka ke neman hawa ko samunsa, sai zukata su wanzu cikin tsoro da fata.
Kuma yana daga rahamar Allah, yadda ya sanya alamomin sonsa a duniya, suna faranta ran mumini basa ruxinsa.
Kuma shiriya bata kasancewa sai ga wanda Allah ke so, Allah ta'alah a cikin hadisin qudusiy yana cewa: "Kuma bawana ba zai gushe ba yana kusanta ta da nafilfili face na so shi, kuma idan na so shi, sai in kasance jinsa da yak e ji da shi, da ganinsa da yak e gani da shi", Bukhariy ya ruwaito shi.

Kuma bada kariya daga fitinar duniya alama ce ta so da karramawa.
Kamar yadda karvuwa a bayan qasa kuma da son da halittu su ke yi ga musulmi shi kuma dalilin son Allah ne a gare shi, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai Allah tabaraka wa ta'alah ida ya so wani bawa, sai ya kira mala'ika Jibrilu, cewa: Alah yana son wane; ka so shi, sai mala'ika Jibrilu ya so shi, Sai kuma Jibrilu ya yi qolo ga halittun sama, cewa lallai Aah yana son wane, ku so shi, sai ma'abuta sama su so shi, sai kuma a sanya masa karvuwa a bayan qasa", Bukhariy ya ruwaito shi.
Kuma kyakkyawar qarshe baiwa ce daga Allah, da ya ke yi ga wanda ya ke so, "Kuma idan Allah ya nufi bawansa da alkhairi, to sai ya datar da shi ga wani aiki na kwarai, sai kuma ya karvi ransa, a cikinsa", Ahmad ya ruwaito shi.

BAYAN HAKA, YA KU MUSULMAI!
Lallai son da Allah ke yi wa bawansa matsayi ne mai girma, wanda mai xa'a a gare shi ke samun wannan matsayin, tare da xa'a ga ManzonSa (صلى الله عليه وسلم), cikin aqida da zance da aiki.
Kuma duk wanda Allah ya so shi, sai ya tunkuxe masa kowani sharri da bala'i. ya kuma shiryar da shi, ya datar da shi, ya amsa addu'arsa, Allah yana faxa a cikin hadisi qudusiy: "Kuma wallahi idan ya roqe ni, lallai zan bashi", Bukhariy ya ruwaito shi.
Kuma, lallai wanda aka masa dace, zai yi aiki domin samun soyayyar Allah, ta hanyar aikata kowace xa'a ga Allah, da nisantar kowane savo.

A UZU BILLAHI MINASH SHAIXANIR RAJIM:
"Na'am! Wanda ya cika alqawarinsa, kuma ya yi taqawa, to lallai ne Allah yana son masu taqawa" [Ali-imrana: 76].

ALLAH YAYI MINI ALBARKA NI DA KU CIKIN ALQUR'ANI MAI GIRMA. …


[B]HUXUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah kan kyautatawarSa; Godiya kuma tasa ce bisa ga datarwarSa da kuma ni'imominSa,
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya; Ina mai girmama sha'aninSa.
Ina kuma shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawansa ne, kuma manzonSa ne.
Allah yayi daxin salati a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da kuma sallama mai ninnukuwa.

Ya ku musulmai…
Kuma lallai masoyi yak an nisanci abinda Majivinsa (Allah) ke qi, ya yi nesa da kafirci da kasha-kashensa, "Domin Allah baya son kafirai" [Ali-imarana: 32].
Kuma zai kasance mai nisantar varna da ma'abutansa, "Lallai ne Allah baya son masu varna",[Qasas: 77].
Zai kuma nisaci, zalunci qaraminsa da babbansa, saboda Allah baya son azzalumai.
Yana mai taka-tsan-tsan da qetare iyaka, domin Allah baya son masu qetare iyaka.
Kuma zuciyarsa, za ta zama kuvutacciya daga girman kai, qanqan-da-kai ya kasance ya bayyana masa, domin Allah baya son masu girman kai.
Ba zai zama mai girma kai, ko mai alfahari ba, Allah (تعالى) yana cewa: "Kada ka yi alfahari, domin Allah baya son masu alfahari", [Qasas: 76].
Yana mai nisantar ji-ji-da-kai ko alfahari ga wani, saboda "Allah baya son dukkan mai taqama mai alfahari", [Hadid: 23].
Yana mai taka-tsan-tsan daga xabi'ar ha'inci


Ya Allah! Ka yi salati da sallama da albarka, ga annabinmu Muhammadu,
Kuma Ya Allah! Ka yarda da khalifofi shiryayyu, waxanda suka yi hukunci da gaskiya, kuma da shi, su ka kasance suke yin adalci, Abubakar da Umar da Usman da Aliyu, da kuma sauran sahabbai gabaxaya, Ka haxa da Mu tare da Su, da kyautarka da karamarka, Ya Mafi kyautar masu kyauta.
Ya Allah! Ka xaukaka Musulunci da Musulmai, ka qasqantar da shirka da Mushirkai, kuma ka ruguza maqiyan addini, Kuma ka sanya –Ya Allah!- Wannan qasar cikin aminci da nitsuwa, da wadaci da walwala, da kuma sauran qasashen Musulmai.
Ya Allah! Ka gyara halin Musulmai a kowani wuri.
Ya Allah! Ka mayar da su izuwa ga addininka, mayarwa mai kyau.
Ya Allah! Ka sanya qasashensu su zama garurrukan aminci da zaman lafiya, Ya Mai qarfi, Ya Mabuwayi!
Ya Allah! Ka tabbatar da rundumarmu, Ya Allah! Ka tabbatar da dugadugansu, Ya Allah! Ka daidaita jifansu, kuma ka azurta su da yi don kai (ikhlasi), Ya Ma'abucin girma da Baiwa.
Ya Allah! Ka datar da shugabanmu, kuma ka sanya aikinsa ya zama cikin yardarka. Kuma ka datar da sauran jagororin Musulmai wajen yin aiki da littafinka, da hukunta shari'arka, Ya ma'abucin girma da yin baiwa.
"Ya UbangijinMu ka bamu mai kyau a duniya, ka bamu mai kyau a lahira, kuma ka kare mu daga azabar Wuta" [Baqarah: 201].
Ya Allah! Lallai ne Mu muna roqonka ilimi mai amfani da kuma aiki mai kyau.
Ya Allah! Lallai kai ne abin bautawa; Babu wani abin bauta face kai, Kai ne Mawadaci, mu kuma mune Faqirai, Ka saukar mana da ruwan sama kada ka sanya mu daga cikin masu xebe tsammani, Ya Allah! Ka bamu ruwan sama!
Ya Allah! Ka bamu ruwan sama!!
Ya Allah! Ka bamu ruwan sama!!!
"Ya Ubangijinmu lallai ne Mu mun zalunci kayukanmu, idan har baka gafarta mana, ka yi rahama a gare mu ba, za mu kasance daga cikin masu hasara" [A'araf: 23].
Bayin Allah!!!
"Lallai Allah yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanci, kuma yana yin hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah Mai girma da daraja zai ambace ku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari, kuma ambaton Allah shine mafi girma, kuma lallai Allah ya san abinda kuke aikatawa.