المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : HUXUBAR MASALLACIN ANNABI (صلى الله عليه وسلم) JUMA'A, 10/Rajab/1438H daidai da 07/Afrilu/ 2017M


طاهر جبريل دكو
_15 _April _2017هـ الموافق 15-04-2017م, 11:43 AM
HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 10/Rajab/1438H
daidai da 07/Afrilu/ 2017M




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEIKH ABDULLAHI BN ABDURRAHMAN ALBU'AIJAN





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA

RAJAB TSAKANIN BIN SUNNAH, DA BIDI'A
Shehin Malami wato: Abdullahi bn Abdurrahman Albu'aijan –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: RAJAB TSAKANIN BIN SUNNAH, DA BIDI'A, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah; mai jujjuya kwanaki da watanni, Mai tafiyar da shekaru da zamannai, Mai haxa halittu domin hisabi,
Ina yin yabo a gare Shi, a kan dukkan lamura, tsawon kanaki da shekaru da watanni, a lokacin kaxawar iskar gabashi (الصبا) ko ta yamma (الدبور),

Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya, sai Allah; shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, Ya kammala mana addini, kuma ya cika ni'ima a gare mu, kuma ya yarda da musulunci ya zama addini a gare mu, shaidawar gaskiya da yaqini wanda ta ke warkar da qiraza, kuma ta amfanar da mu a cikin qaburbura, kuma ta xaga darajarmu a ranar da za a yi busa cikin qaho,

kuma ina shaidawa lallai annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa, ya isar da saqon manzanci, kuma ya sauke amana, ya yi nasiha ga al'ummah, kuma ya yi jihadi don xaukaka kalmar Allah iyakar jihadi,
Allah ka yi daxin salati a gare shi, da kuma iyalansa da sahabbansa, gaba xaya.

Bayan haka:
Lallai mafi alherin zance shine littafin Allah, Kuma mafi alherin shiriya ita ce shiriyar annabi Muhammadu (صلى الله عليه وسلم), kuma mafi sharrin lamura sune qirqirarrunsu, kuma kowace bidi'a va tace, kuma kowace bata tana cikin wuta,

Ya ku bayin Allah !! …
Ku bi dokokin Allah da taqawa kuma ku yi masa xa'a, saboda taqawa ita ce wasiyyar Allah ga na farko da qarshe, "Kuma haqiqa Mun yi wasiyya ga waxanda aka baiwa littafi gabaninku, da kuma ku, cewa, ku bi Allah da taqawa" [Nisa'i: 131].

Ya ku musulmai !! …
Lallai ne jinsin mutum ba a halicce shi don wasa ba, kuma ba a kyale shi kara-zube ba, domin an bashi umarni da hani, kuma lallai za a yi masa hisabi, "Kuma duk wanda ya aikata daidai da kwayar zarra na alheri, to lallai zai ganshi * kuma duk wanda ya aikata daidai da kwayar zarra na sharri, to zai gan shi" [Zalzala: 7-8].

Kuma haqiqa Allah Mabuwayi da xaukaka ya karrama mu da addinin musulunci, kuma ya keve mu da turo mafificin manzo, tare da mafificin littafi, kuma ya sanya mu ka kasance mafi alherin al'umma, Yabo da godiya da jinjina su qara tabbata ga Allah, akan wannan.

Ya ku musulmai !! …
Lallai ne Allah ya fifita, sashin lokuta, da kuma sashin kwanaki, da sashin watanni, akan sashe, kuma wannan fifikon yana hukunta jin alfarmarsu da girmama su, kuma a wani lokacin, hakan ya kan hukunta, a kevance lokutan da wasu ibadodi, Sai dai kuma hakan gaba xayansa, a dabaibaye ya ke da shari'a, haka kuma an dabaibaye shi da koyi da annabi (SAW), ba da bidi'a ba.

Kuma haqiqa, girman watanni masu alfarma (guda huxu) da falalarsu da fifikonsu akan sauran watanni ya tabbatu a cikin shari'a, Allah ta'alah ya ce: "Lallai qidayar watanni a wurin Allah wata goma sha biyu ne a cikin littafin Allah, a ranar da ya halicci sammai da qassai, cikinsu akwai huxu masu alfarma, wannan ne addini madaidaici, saboda haka, kada ku zalunci kayukanku a cikin watannin" [Tauba: 36].
Hadisi ya zo daga Abu-bakrata (رضي الله عنه), lallai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya yi huxuba, a hajjinsa na bankwana, sai ya faxa a cikin huxubar tasa cewa, "Lallai zamani ya juya izuwa ga yanayinsa, a ranar da ya halicci sammai da qassai, Shekara, watanni ne goma sha biyu, daga cikinsu akwai guda huxu masu alfarma, uku a jejjere; wato; ZULQA'ADAH, DA ZUL HIJJAH, DA MUHARRAM, da RAJAB xin kabilar Mudar, wanda ke tsakanin JUMADAH da SHA'ABAN", Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.
Kuma watannin nan, an sanya su suka zama masu alfarma ne, domin a samu damar yin hajji da umrah (ba tare da wata qabila ta hana hakan ba).

Bayin Allah … !!!
Ga mu nan, a cikin kwanakin watan Rajab, kuma Rajab yana cikin watanni masu alfarma, wanda mu ke bauta wa Allah, da jin haramcinsa, muna kuma sanin falalarsa da girmansa, kuma muna roqon Allah, ya datar da mu a cikinsa zuwa ga abinda ya ke so, kuma ya yarda.
Sai ku girmama abinda Allah ya girmama, saboda duk "Wanda ya girmama alfamomin Allah, to shi ne mafifici a gare shi, a wurin Ubangijinsa" [Hajj: 30].

Bayin Allah … !!!
Lallai ginshiqin addini kuma tushensa, shi ne shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma annabi Muhammadu manzon Allah ne, Kuma abinda waxannan kalmomin su ke hukuntawa shi ne, ikhlasi ga Allah, da kuma bin Manzon Allah, saboda haka, Allah ba ya karvar aiki, face wanda aka yi ikhlasinsa ga Allah, kuma ya dace da shiryarwar AnnabinSa (صلى الله عليه وسلم); "Kuma duk wanda ya kasance yana fatan saduwa da UbangijinSa, to sai ya aikata aiki nagari, kuma kada ya yi shirka da wani, a cikin bautar UbangijinSa" [Kahf: 110].
Don haka, ibadodi an tsayar da shar'anta su ga shari'a, kuma babu fagen sanya ra'ayi ko hankali a cikinsu, kuma dukkan alheri yana cikin bin waxanda su ka gabata (na kwarai), kamar yadda dukkan sharri ya tattaru cikin bidi'ar mutanen qarshe.

Kuma baya halatta ga wani mutum ya kevance wata ibada da wani lokaci ko wuri, wanda Allah da manzonSa (SAW) ba su kevance ta da shi ba, saboda Mu, an bautar da mu ne, da yin aiki da shari'ar Allah, ba da son zuciyarmu, ko kuma ganin dama ba, don haka, wajibin da ya ke kanmu, shi ne mu ce mun ji, mun bi, kuma mu aikata abinda Allah ya umarce mu da aikata shi, "Abin sani, kawai zancen muminai idan aka kira su zuwa ga Allah da manzonSa domin su yi hukunci a tsakaninsu, shi ne su ce: Mun ji, mun bi, kuma waxannan su ne masu samun babban rabo" [Nur: 51].

Ya ku taron musulmai … !!!
Lallai watan RAJAB watah ne mai albarka, lura da kasancewarsa cikin watanni masu alfarma, sai dai kuma hakan baya hukunta a keve watan, da wata ibadar da shari'a bata yi izini da ita ba.
A kan hakan, ba za a keve watan Rajab da wata sallah kevantacciya, ko a kwana ana raya wani dare a cikinsa (da ibadodi) ba, ko a yi bikin wani dare a cikinsa. Saboda watan Rajab daidai ya ke da sauran watanni, masu alfarma.
Kuma dukkan hadisan da su ka nuna a yi wata ibada kevantacciya, ko a kwana ana raya wani dare, ko kuma bikinsa, to hadisai ne masu rauni wanda ba a gina hukuncin shari'a akansu.
Kuma duk abinda ke hannun mutane, na wannan, to lallai qura ne, daga cikin abubuwan da zamanin jahiliyya ya wanzar da su.
Sai ku yi riqo da Sunnah, sai ku yi riqo da Sunnah, kuma ku nisanci bidi'a, kuma ku riqa yin nasiha ga juna, kuna yin wasiyya da gaskiya, kuma kuna wasiyya da yin haquri.
Kuma ku saurari mai kira zuwa ga Allah, a inda ya ke kiran ma'abuta littafi, "Ka ce: Ya ku ma'abuta littafi, kada ku yi guluwwi (wuce iyaka) a cikin addininku, abinda ba gaskiya ba, kuma kada ku bibiyi son zuciyar wasu mutane, waxanda su ka riga su ka bace a gabani, kuma su ka vatar da wasu masu yawa, kuma su ka vace daga tsakar hanya" [Ma'idah: 77].
Kuma gaskiya, lallai ita ce, ta fi cancantar a bi, ita kuma varna varna ce, bata canzawa bata jirkita.
Su kuma bidi'oi fitintinu ne da bala'oi, kuma jarabawa ne da musibu, da savo da zunubi, da laifuka da ququmi, waxanda su ke kange mutane daga bin Sunnah, kuma su ke rarraba kayukan al'umma, kuma su ke lalata addini, da hankula, da fixra.
Kuma mutane ba za su qirqiri wata bidi'a ba, face sun bar kwatankwacinta daga Sunnah.
Kuma haqiqa Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya bar mu akan addini mai haske, darensa da yininsa xaya su ke.

Kuma manzanci, lallai an rufe shi, "A yau, na kammala mu ku addininku, kuma na cika ni'imata a kanku, kuma na yarda da musulunci ya zama addini a gare ku" [Ma'idah: 3].
Don haka, duk wanda ya ke son cin nasara, da samun sakamako da lada, to sai ya taqaitu, akan abinda Allah (سبحانه) ya halatta, domin hadisi ya zo daga Irbadhu bn Sariya (رضي الله عنه) ya ce "Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya yi mana wa'azi mai shiga jiki, mai ratsawa, wanda zukata suka tsorata daga gare shi, kuma idanu su ka fitar da hawaye, Sai mu ka ce, kamar wa'azin mai bankwana, to ka yi mana wasiyya, sai ya ce: Ina muku wasiyya da bin dokokin Allah da taqawa, da kuma, ji da biyayya, koda kuwa bawa ne ya shugabance ku, kuma lallai duk wanda ya rayu daga cikinku a bayana, to lallai zai ga savani dayawa, sai ku yi riqo da sunnata da sunnar khalifofina shiryayyu, masu shiryarwa, ku riqe su da fiqoqi, kuma kashedinku da riqo da qirqirarrun abubuwa, saboda kowace bidi'a vata ce".
Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma, kuma ya azurta mu da bin sunnar AnnabinSa mai karamci, da kuma lazimtar shiriyarsa miqaqqa, ina faxin abinda ku ke ji wannan, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai, sai ku nemi gafararSa, lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,

HUXUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah wanda ya shiryar da mu zuwa ga musulunci, kuma ba mu kasance za mu shiryatu ba, ba don Allah ya shiryar da mu ba,
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya.
Kuma ina shaidawa lallai annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa, babu wani alkhairi face ya nusatar da mu a gare shi, kuma babu wani sharri face ya tsawsatar da mu daga aikata shi,
Allah ya qara salati da sallama a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da wanda ya yi riqo da sunnarsa, kuma ya bibiyi shiriyarsa, har zuwa ranar sakamako.

Ya ku bayin Allah !! …
Ina haxa ku da Allah, kan riqo da shiriyar Annabi (صلى الله عليه وسلم), da lazimtar umarninsa da hani, da kuma koyi da sunnarsa.
Kuma ina tsawatar da ku, kan yin bidi'oi da dangogin vata.

Imam As-shaxibiy –رحمه الله- yana cewa: "Lallai xan bidi'a ya yi taurin kai ga shari'a, kuma ya sava mata, saboda mai shari'a (wato Allah), Ya Ayyana hanyoyi kevantattu ga ababen da ya nema daga bayinsa, da kuma wasu fiskoki kevantattu, sai kuma ya taqaice halittu akan waxannan hanyoyi da fiskoki, da umarninsa cewa, abi su, da kuma hanin kada a ketare su, haka kuma, da alqawarin bada rahama ko horo (na, wa'adi da wa'idi), kuma Allah ya bada labarin cewa, lallai alkhairori, (dukkansu) su na kan wannan hanyaoyin, sharri kuma, yana cikin qetare su, izuwa ga waninsu, kuma ya bada labarin cewa, lallai ya turo manzo ne domin rahama ga talikai. Sai dai shi kuma xan bidi'a, ya shure wannan gaba xayansa, domin xan bidi'a yana riya cewa, lallai akwai wasu hanyoyin na daban, kuma (a ganin xan bidi'a), abinda mai shari'a ya iyakance, ba iyakantacce ba ne, haka abinda ya Ayyana shima ba aiyananne ba ne, don haka; kamar yana cewa, mai shari'a ya sani, muma kuma mun sani, kuma za a iya fahimta, daga yadda xan bidi'a ke qara cusa wasu hanyoyi a cikin addini, cewa shi, yana jin ya san wasu abubuwa wanda mai shari'a bai sansu ba, Wannan kuma, idan har xan bidi'an ya yi nufin hakan a zuciyarsa, to lallai hakan kafirce wa shari'ar ne, da (kafircewa) mai shari'ar. Idan kuma ya kasance bai nufi hakan ba, to vata ne bayyananna" . maganarsa ta qare –رحمه الله-.

Ya Allah! Ka nuna mana gaskiya, a matsayinta na gaskiya, kuma ka azurta mu, da binta, kuma ka nuna mana varna a matsayinta na varna, kuma ka azurta mu da nisantar ta, kuma kada ka sanya varna ta zama ta cakuxe mana da gaskiya, har ta kaimu ga vata,
Ya Allah ka azurta mu da riqo da sunna a lokacin lalacewar al'umma,
Ya Allah! Ubangijin mala'ika Jibrila da Mika'ila da Isra'fila wanda ya qagi sammai da qassai, masani gaibu da abinda ke bayyane, kai ne ka ke hukunci tsakanin bayinka cikin abinda su ka kasance su ke savani, ka shiryar da mu gaskiya cikin abinda aka yi savani, da izininka, lallai ne kai kana shiryar da wanda ka ke so, izuwa hanya madaidaiciya.
Ya Allah! Ka daukaka musulunci da musulmai, kuma ka qasqantar da shirka da mushirkai, ka taimaki bayinka masu tauhidi, kuma –Ya Allah- ka sanya wannan qasa cikin aminci, da zaman lafiya, da sauran qasashen musulmai.
Ya Allah! Ka bamu aminci a qasashenmu, kuma ka gyara shugabanninmu, kuma jagororin lamuranmu.
Ya Allah! Ka datar da majivincin lamuranmu da datarwarka, kuma ka qarfafe shi da qarfafawarka, ya ma'abucin girma da karramawa,
Ya Allah! Ka kiyaye iyakokin qasarmu, ka taimaki rundunoninmu, Ya Ubangijin halittu.
Ya Allah! Ka gyara halayen musulmai a kowani wuri, Ya Allah ka kasance (mai taimakon) 'yan'uwanmu a qasar Somaliya, Ya Allah ka xauke abinda ya sauka akansu na tsananin bala'oi, da quncin rayuwa, da tsananin musibu. Ya Allah! Lallai su, suna jin yunwa ka ciyar da su, tsirara su ke, ka tufatar da su, kuma suna cikin bala'in jarabawa, ka tausasa musu.
Ya Allah! Shekarun yunwa sun addabe su, har duwatsunsu su ka lulluve, qasarsu ta cika da qura, dabbobinsu su ka faxi saboda qishi, har sautin kukan matan da suka rasa 'ya'yansu ya yi ta tashi.
Ya Allah! Ka ji qan sautin haniniyar marasa lafiya, da kuma masu kuka,
Ya Allah! Ka yaxa rahamarka a cikinsu da gajimare mai bubbuxewa, da kuma bazara mai ruwa dayawa, da ciyawi masu ganye, da kuma ruwa mai zubar mamako mai tarin yawa, wanda za ka raya abinda ya mutu da shi, kuma ka dawo da abinda aka rasa da shi

Bayin Allah
"Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallama ta aminci" [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati da sallama wa Annabi Muhammadu, kuma ka yarda da khalifofinsa shiryayyu masu shirayarwa; Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu, da sauran sahabbai gabaxaya, ka haxa da mu, da baiwarka, ya mafi baiwar masu kyauta.