المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : Tarjamar suratunnajmi zuwa harshen hausa


طاهر جبريل دكو
_5 _April _2017هـ الموافق 5-04-2017م, 04:31 PM
SURAR NAJAMI
A Makka aka saukar da ita
(Ayoyinta 49)
(Muna fara wa da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai).
1. (Allah) Yana rantsuwa da tauraro yayin da ya fadi.
2. Mutuminku bai bata ba kuma bai kauce hanya ba.
3. Kuma ba ya yin Magana bisa son rai.
4. Ba wani abu ba ne shi face wahayi ba ake yuwo (masa).
5. Mai tsananin karfi ne ya sanar da shi.
6. Ma'abocin karfi na boye sannan ya daidaita (a halittar da Allah ya yi masa).
7. Allah kuwa Shi Yana sasanni mai madaukaki.
8. Sannan sai ya kusanta ya kara matsawa.
9. Sai ya kasance kamar kusance tsarkiya da baka ko fiye da haka.
10. Sannan Ya yiwo wahayi abin da ya yi wahayi zuwa bawansa.
11. Zuciya ba ta karyata abin da ta gani ba.
12. Yanzu kwa rika jayayya da shi kana bin da ya gani?
13. Hakika ya gane shi a wani karon.
14. A daidai sidiratul muntaha magaryar tukewa.
15. A daidai ita aljanna (Ma'awa) makoma take.
16. A yayin da abin da yake lullube sidratul (muntaha) yake lullube ta.
17. Gani bai kauce ba kuma bai katare iyaka ba.
18. Hakika ya ga wani abu daga ayoyin Ubangijinsa manya-manya.
19. Shin yanzu bakwa ganin Lata da Uzza.
20. Da kuma Manata ta cikon ukun (gumaka ne).
21. Shin yanzu ku ne kuke da 'ya'ya maza shi kuma yake da mata!
22. Ta wancan shi ne rabon cin zali.
23. Su ba wani abu ba ne face sunaye da kuka sa musu ku da iyayenku, Allah bai saukar da wata hujjaba game da su. Ba kuma abin da suke bi sai zato da son zuciya, hakika kuwa shiriya ta zo musu daga Ubangijinsu.
24. Shin yanzu lallai ne mutum ya sami abin da yake buri!
25. Saboda haka duniya da lahira na Allah ne. (a neme su ta yadda ya ce).
26. Sau da yawa kuma Mala'iku a sammai cetonsu ba ya amfana komai sai bayan Allah Ya yi izini ga wanda ya so ya kuma yarda.
27. Hakika wadanda ba sa ba da gaskiya da ranar Lahira suna kiran mala'iku da sunan mata.
28. Kuma ba su da wani ilimi game da shi, ba abin da suke bi sai zato, kuma zato hakika ba ya wadatar komai a kan gaskiya.
29. Sannan ka yi ko biris ga wanda ya ba da baya ga barin ambatonmu, ba kuma abin da yake so sai rayuwar duniya.
30. Wancan ne iyakacin saninsu. Hakika Ubangijinka Shi ne ya fi sanin wanda ya kauce wa hanyarsa kuma Shi ya fi sanin wanda ya shiriya.
31. Kuma abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin kassai na Allah ne, don zai saka wa wanda suka munana da abin da suka aikata ya kuma sakawa wadanda suka kyautata da kyakkyawa.
32. Wadanda suke gudun manya-manyan zunubai da munanan ayyuka sai abin da ba ka rasa ba wato kanana. Hakika Ubangijinka mayalwacin gafara ne Shi ya fi saninku tun sanda ya fare ku daga kasa sai ga ku kun zama jarirai a cikin mahaifanku, saboda haka kada ku koda kanku, Shi ne ya fi sanin wanda ya ji tsoron Allah.
33. Shin yanzu ba ka ganin wanda ya ba da baya.
34. Kuma ya bayar da dukiya kadan ya kuma dakushe ga ragowar (wato ya hana).
35. Shin yanzu yana sanin gaibu ne saboda haka shi yake gani (yake hangowa).
36. Ko ba a ba shi labarin abin da yake littattafan (Annabi) Musa ba ne?
37. Da (Annabi) Ibrahimu wanda ya cika alkawari! abin da aka umarce shi da shi).
38. Cewa wani ba ba daukar laifin wani.
39. Kuma mutum ba shi da wani abu sai abin da ya aikata.
40. Kuma hakika kuma da sannu za a duba (aikinsa).
41. Sannan a yi masa cikakken sakamako.
42. Hakika kuma wurin Ubangijinka ne matuka.
43. Hakika kuma Shi ne Mai saw a a yi dariya Ya kuma sa ayi kuka.
44. Kuma hakika Shi ne Yake kashewa ya kuma raya wa.
45. Hakika kuma Shi ne wanda Ya halicci abu biyu namiji da mace.
46. Daga maniyi yayin da ake (Barbara) ake zubawa a cikin mahaifa.
47. Kuma hakika ya dora wa kansa sake tashin matattu.
48. Hakika kuma Shi ne Yake wadata wa Yake kuma talauta wa.
49. Kuma hakika Shi ne Ubangijin tauraronnan da ake kira Shi'ira.
50. Hakika kuma ya hallaka Adawan farko.
51. Da kuma Samudawa bai bar saura ba.
52. Da mutanen Annabi Nuhu tun kafin su, hakika su sun kasance su ne (sarakan) mafi zalunci da shisshigi.
53. Da kuma mutanen alkarya da aka kife (su ne mutanen Annabi Ludu).
54. Sannan abin da zai lullube ta ya lullubeta.
55. Sannan da wanne ne daga ayoyin Ubangijinku kake jayayya.
56. Wannan mai gargadi ne daga masu gargadin farko.
57. Alkiyama ta kusa.
58. Ba wani mai yaye ta in ban da Allah.
59. Shin yanzu daga wannan zancen kuke mamaki?
60. Kuke kuma sheka dariya ba kwa kecewa da kuka!
61. Alhali kuma rafkane.
62. Saboda haka sai ku yi sujada ga Allah ku kuma bauta masa.