تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : Tarjamar suratu-ddur zuwa harshen hausa


طاهر جبريل دكو
_5 _April _2017هـ الموافق 5-04-2017م, 04:28 PM
SURAR DURI
A Makka aka saukar da ita
(Ayoyinta 49)
(Muna fara wa da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai).
1. (Allah Ya rantse da dutsen Duri sina'a.
2. Da kuma littafi abin rubutawa.
3. Cikin fata, abin budewa.
4. Da kuma Baitul Ma'amuri.
5. Da kuma rufi abin dagawa.
6. Da kuma kogi mai ruwa makil.
7. Hakika azabar Ubangijinka lallai za ta afku.
8. Ba wani nai hana ta.
9. Ranar da sama za ta yi tambal-tambal sosai.
10. Duwatsu kuma su tafiyar (su su bar wurinsu).
11. Saboda haka tsananin azaba ya tabbatar ga masu karyata a wannan ranar.
12.Wadanda su suna cikin kutsawa suna wasa.
13. Ranar da za a ingiza su zuwa wutar Jahannama mugum ingizawa.
14. (A ce da su) wannan ce wutar da kuka kasance kuna karyata ta.
15. Yanzu sihiri ne wannan ko kuwa ku ne ba kwa gani?
16. Ku shigeta kuna konuwa sannan ku yi hakuri ko kada kuyi hakuri duk daya a gare ku. Hakika za a saka muku abin da kuka kasance kuna aikatawa ne.
17. Hakika masu tsoron Allah suna cikin aljannoni da ni'ima.
18. Suna masu fantamawa (morewa) da abin da Ubangijinsu ya ba su, Ubangijinsu ya kuma ya kare su azabar (wutar) Jahannama.
19. (Sai a ce da su) ku ci ku sha cikin murna saboda abin da kuka kasance kuna aikatawa.
20. Suna kashingide a kan gadaje a jere Muka kuma aura musu Hurul'aini (matar aljanna).
21. Wadanda kuwa suka ba da gaskiya zuriyarsu kuma suka bi su da imani, za Mu hada su da zuriyarsu, ba kuma za Mu rage musu komai ba daga aikinsu, kowane mutum jingina ne na abin da ya tsuwurwurta.
22. Muka kuma kawo musu 'ya'yan itatuwa da nama daga abin da suke sha'awa.
23. Suna mikekeniyar kofin (giya) a cikinta babu zancen banza a cikinta kuma babu alfahasha. (ba kamar giyar duniya ba).
24. Kuma yan yara suna kaiwa da komowa a garesu, kai ka ce su wani daiman ne abin keyayewa.
25. KUma shashinsu ya gabata a bisa shashi suna tambayeyeniya.
26. Suka ce: "Hakika mu mun kasance kafin wannan ababan tsoro a cikin iyalinmu.
27. Sai Allah Ya yi mana baiwa ya kuma kare mu azaba mai cutarwa. Mai shiga kofar gashi.
28. Hakika mu mun kasance tin kafin wannan muna rokonsa Hakika Shi Mai kyautatawa ne Mai jinkai.
29. Sannan ka yi wa'azi ai kai ba ka kasance da ni'imar Ubangijin ka (ace) boka ko mahaukaci ba ne.
30. Ko kuwa suna cewa mahaki ne muna saurara masa musibar zamani kamar mutuwa.
31. Ka ce: "Ku saurara, sannan hakika ni ma mai sauraro tare da ku.
32. Ko kuwa mafarke-mafarkensu ne suke umartarsu da wannan ko kuwa su mutane ne masu shisshigi.?
33. Ko kuwa suna cewa kagarsa ya yi? A'a ba haka ba ne ba, dai, su ne ba sa ba da gaskiya.
34. Saboda haka su zo da zance irinsa idan sun kasance masu gaskiya.
35. Ko kuwa an halicce su ne daga babu, ko kuwa su ne masu halittar?
36. Ko kuwa su suka halicci sammai da kassai? Ba haka ba ne ba sa san sakankancewa ne.
37. Ko kuwa a wurinsu taskokin Ubangijinka suke ko kuwa su ne masu rinjaye? (kan komai).
38. Ko kuwa suna da tsani ne da suke ji ta cikinsa sannan mai jiyo musu ya zo da hujjoji mabayyana?
39. Ko kuwa shi ne yake da 'ya'ya mata ku kuma kuke da 'ya'ya maza?
40. Ko kuwa kana tambayarsu lada ne saboda haka abin da aka dora musu ya yi masu nauyi?
41. Ko kuwa a wurinsu gaibu yake saboda haka su suke rubutawa?
42. Ko kuwa suna nufin makirci ne? Saboda haka wadanda suka kafirce su ne wadanda kaidinsu zai koma kansu.
43. Ko kuwa suna da wani abin bautawa ne wanin Allah? Tsarki ya tabbata ga Allah da abin da suke tara (shi da Shi).
44. Idan kuma suka ga wani yanki daga sama mai fadowa sais u ce: "hadari ne mai hauhawa juna.
45. Saboda haka ka rabu da su har sai sun hadu da ranarsu wadda za a kashe su a cikinta.
46. Ranar da kaidinsu ba zai Magana musu komai ba, kuma su ba za'a taimake su ba.
47. Hakika kuma wadanda suka yi zalunci suna da wata azabar ban da waccan, sai dai kuma mafi yawansu ba su sani ba.
48. (Kuma ka yi hakuri da hukuncin Ubangijinka saboda hakika kai kana cikin kiyayewarmu. Kuma ka yi tasbihi da godiyar Ubangijinka lokacin da za ka tashi.
49. Da daddare kuma sai ka yi tasbihi a gare shi da kuma lokacin da tauraro ya ba da baya.