المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : Tarjamar suratul qasas


طاهر جبريل دكو
_25 _March _2017هـ الموافق 25-03-2017م, 10:54 AM
SURAR KASASI

Ina farawa da sunan Allah mai rahama mai jin kai

1. DA SIN MIM, Allah ne ya san abin da yake nufi da wannan.
2. Wadannan su ne ayoyin littafi mabayyani.
3. Muna karanta maka labarin Musa da Fir'auna na gaskiya don mutane da suke ba da gaskiya.
4. Hakika Fir'auna ya yi dagawa a bayan kasa ya kuma sanya mutanenta kungiyoyi daban-daban, yana bautar da wata kungiya daga cikinsu, yana yanka 'ya'yansu maza, yana kuma raya mata. Hakika shi ya kasance cikin masu barna.
5. Muna kuma so mu yi baiwa ga wadanda aka wulakanta a bayan kasa mu kuma sanya su shugabanni, kuma mu mayar da su magadan (mulkin Fir'auna).
6. Mu kuma kafa su a bayan kasa, kuma mu nuna wa Fir'auna da Hamana da rundunoninsu abin da suke jin tsoro game da su (mutanen).
7. Muka kuma kimsa wa mahaifiyar Musa cewa: "ki shayar da shi; to yayin da kika ji tsoro game da shi, sai ki jefa shi a cikin gogi, kada kuma ki ji tsoro, kuma kada ki yi bakin ciki; hakika mu masu dawo muki da shi ne, kuma masu sanya shi ne cikin manzanni."
8. Sai mutanen Fir'auna suka tsince shi don (daga baya) ya zama abokin gaba da kuma bakin ciki a gare su. Hakika Fir'auna da Hamana da rundunarsu sun kasance a kan kuskure.
9. Matar Fir'auna kuma ta ce: "(shi) kwanciyar rai ne a gare ni har da kai; kada ku kashe shi; muna fatan ya amfane mu, ko kuma mu dauke shi a matsayin da", alhali kuwa su ba su san (abin da zai faru ba).
10. Zuciyar mahaifiyar Musa kuma ta wayi gari ba komai a cikinta (sai nunaninsa), ba shakka sauran kiris ta bayyana shi, ba don mun sa dauriya a zuciyarta ba don ta zama cikin mumina.
11. Ta kuma ce da 'yar'uwarsa: "ki bi sawunsa", sai ta hango shi daga nesa, su kuwa ba su gane ita ('yar'uwarsa ba ce).
12. Da ma ku can mun haramta masa (nonon) masu shayarwa sai ('yar'uwar tasa) ta ce: "yanzu ba na nuna muku mutanen wani gida da za su shayar muku da shi ba; su kuma za su kyautata masa?"
13. Sai muka dawo da shi wurin mahaifiyarsa don hankalinta ya kwanta kuma don kada ta yi bakin ciki don kuma ta san cewa alkawarin Allah gaskiya ne, sai dai kuma yawancinsu ba sa fahimtar (hakan).
14. Lokacin kuma da ya kai karfinsa ya kuma kammala, sai muka ba shi hukunci da ilimi; kamar haka kuwa muke saka wa masu kyautatawa.
15. Sai ya shiga cikin birnin a lokacin gafalar mutanensa, sai ya sami mutum biyu a cikinsa suna fada; wannan dan kabilarsa ne, wannan kuma abokin gabarsa ne; sai dan kabilar tasa ya nemi taimakonsa a kan abokin gabarsa; to sai Musa ya dan zungure shi, sai kuwa ya kashe shi, (da ya ga haka sai) ya ce: "wannan yana daga aikin Shaidan, hakika shi kuwa makiyi ne bayyananne, mai batarwa."
16. Ya ce: "ya Ubangijina, hakika ni na zalunci kaina, sai ka yi min gafara," shi kuwa mai gafara ne mai jin kai."
17. Ya (kuma) ce: "ya Ubangijina, saboda ni'imar da ka yi min ba zan zama mai taimakon masu laifi ba."
18. Sai ya wayi gari a cikin birnin a tsorace yana dar-dar, sai ga wanda ya nemi taimakon nan nasa a jiya yana sake neman taimakonsa, (sai) Musa ya ce da shi: "hakika kai dai batacce ne sosai".
19. To lokacin da ya nufi wawurar abokin gabar tasu (sai mai neman taimakon) ya ce: "ya Musa, shin yanzu nufi kake ka kashe ni kamar yadda ka kashe wani rai jiya? Ba abin da kake nifi sai ka zama mai tsaurin rai a bayan kasa; ba ka kuma nufin ka zama cikin masu kyautatawa."
20. Sai wani mutum (mumini daga mutanen Fir'auna) ya zo daga kuryar birnin yana gaggawa, ya ce: " ya Musa hakika manyan gari (suna can) suna shawara game da kai don su kashe ka; to ka fita (daga birnin), hakika ni ina cikin masu yi maka nasiha."
21. Sai ya fita daga cikinsa (watau birnin) a tsorace yana ta dar-dar, ya ce: "ya Ubangijina ka tserar da ni daga azzaluman mutanen nan."
22. Yayin da kuma ya fuskanta wajen (birnin) Madayan, sai ya ce: "ina fatan Ubangijina ya shiryar da ni hanyar da ta fi dacewa."
23. Lokacin da kuma ya gangara wajan ruwan (rijiyar) Madayana sai ya sami wasu mutane masu shayar (da dabbobi), ya kuma sami wasu mata su biyu a gefensu suna kare da (dabbobinsu), sai ya ce (da su): "me ya same ku ne?" sai suka ce: "mu ai ba ma shayarwa har sai duk makiyayan sun juya, kuma mahaifinmu tsoho ne tukuf."
24. To sai ya shayar musu (da dabbobin nasu), sannan ya koma wurin wata inuwa ya ce: "ya Ubangijina, hakika ni mabukacin wani alhairin da za ka saukar mini ne!"
25. Sai dayarsu ta zo masa tana tafiya cikin jin kunya ta ce: "babana yana kiran ka don ya saka maka ladan shayarwar da ka yi mana." To lokacin da ya zo wurinsa ya kuma ba shi labarin (abubuwan da suka faru), sai ya ce da shi: "kada ka ji tsoro, ka tsira daga azzaluman mutane."
26. Sai dayarsu ta ce: "babana, ka dauke shi aiki mana, don kuwa hakika ba wanda ya fi dacewa a dauke shi aiki sai kakkarfa amintacce."
27. Sai ya ce da (Musa): "ina so in aura maka daya daga 'ya'yayen nan nawa guda biyu, a kan ka yi min aiki na shekara takwas, sannan idan ka cika goma to wannan dadin kanka ne; ba na kuwa nufin in kuntata maka, za ka same ni kuwa in Allah ya yarda daga masu cika alkawari."
28. (Musa) ya ce: "wannan tsakanina da kai ne, duk dayan lokutan biyu da na cika babu kwaruwa a gare ni, Allah kuwa shida ne game da abin da muke fada."
29. To yayin da (Musa) ya cika lokacinsa ya kuma tafi da iyalinsa, sai ya hango wuta daga gefen (dutsen) Duri, ya ce da iyalinsa: "ku zauna (a nan), hakika na hango wuta, (zan je don) in zo muku da labari daga wurinta ko kuma wani garwashi na wutar don ku ji dimi."
30. To lokacin da ya zo wurinta (wutar) sai aka yi kira daga gefen kwari na damarsa a wani wuri mai albarka na bishiya, cewa: "ya Musa, hakika ni ne Allah Ubangijin talikai!
31. "Kuma ka jefar da sandarka;" to lokacin da ya gan ta tana mirgina kamar maciji sai ya ba da baya a guje, bai ko waiwaya ba. (Aka ce da shi): "ya Musa dawo, kuma kada ka ji tsoro; hakika kai kana cikin amintattu.
32. "Ka sanya hannunka a cikin wuyan rigarka, zai fito fari fat ba tare da wata cuta ba, kuma ka mayar da hannunka (cikin hammatarka) saboda tsoron (farin). To biyu din nan hujjoji ne daga Ubangijinka zuwa ga Fir'auna da mutanensa, hakika su sun kasance mutane ne fasikai."
33. (Musa) ya ce: "ya Ubangijina, hakika ni na kashe musu wani mutum, to ina tsoron su kashe ni.
34. "Kuma dabn'uwana Haruna shi ya fi ni fasahar harshe, sai ka aike shi tare da ni ya taimaka min ya gaskata ni; hakika ni ina jin tsoron su karyata ni,"
35. (Sai Allah) ya ce: "za mu karfafa dantsenka da 'dan'uwanka kuma mu sanya muku nasara, ba za su isa gare ku (da wata cuta) ba. (To ku tafi) da ayoyina ku da wadanda suka bi ku, ku ne masu yin galaba."
36. To lokacin da Musa ya zo musu da ayoyinmu mabayyani sai suka ce: "ai wannan ba wani abu ba ne face kagaggen sihiri; mu kuma ba mu taba jin wannan ba a wurin iyayenmu na farko."
37. Musa kuma ya ce: "Ubangijina (shi ne) ya fi sanin wanda ya zo da sihiri daga wurinsa, da kuma wanda kyakkyawan karshe zai kasance a gare shi, hakika shi dai (al'amarin) kafurai ba sa rabauta."
38. Fir'auna kuma ya ce: "ya ku jama'a ban san kuna da wani Ubangiji ba in ba ni ba, kai ko Hamana shirya min konannen birki sannan ka yi min dogon gini don in hango Ubangijin Musa, ba shakka ni ina tsammanin cewa shi yana cikin makaryata."
39. Ya kuma yi girman kai shi da rundunoninsa a bayan kasa ba da wata hujja ba, suka kuma yi tsammanin cewa su ba za a komar da su zuwa gare mu ba.
40. Sai muka kama shi tare da rundunarsa, sannan muka watsa su a cikin kogi; to ka duba ka ga yadda karshen kafurai ya kasance.
41. Muka kuma mayar da su shugabanni masu kira zuwa ga wuta, ranar alkiyama kuma ba za a taimake su ba.
42. Muka kuma bi su da la'anta a wannan duniyar, ranar alkiyama kuma suna cikin wadanda za a jefa cikin mummunan hali.
43. Hakika kuma mun bai wa Musa littafin (Attaura) baya mun hallaka al'ummun na farko don izina ga mutane da shiriya da rahama ko sa wa'azantu.
44. Kai kuma ba ka kasance a gefen (dutsen Duri) na yamma ba lokacin da muka yo wahayin manzanci zuwa ga Musa, ba ka kuma kasance cikin wadanda suke wurin ba.
45. Sai dai cewa mu mun halicci al'ummu sannan nisan zamani ya tsawaita a gare su, kuma ba ka kasance a zaune cikin mutanen Madayana ba kana karanta musu ayoyinmu, sai dai kuma mu mun kasance masu yi maka wahayi ne (da wadannan labarun).
46. Kuma ba ka kasance a gefen (dutse) Duri ba, lokacin da muka kirawo (Musa), sai dai wata rahama daga Ubangijinka, don ka gargadi wasu mutane da mai gargadi bai zo musu ba gabaninka ko sa wa'azantu.
47. Kuma ba don kada wata masifa ta same su ba saboda abin da suka aikata da kansu sannan su ce: "ya Ubangijinmu, ina ma da ka aiko mana da wani manzo, sannan mu bi ayoyinka mu kuma kasance cikin muminai?"
48. Sannan lokacin da gaskiya ta zo musu daga wajenmu sai suka ce: "ina ma da an ba shi irin abin da aka ba wa Musa?" yanzu ashe tun da can ba su kafirce da abin da aka bai wa Musan ba, suka ce: "su biyun sihiri ne (watau Alkur'ani sa Attaura) da suke taimakon juna?" suka kuma ce: "hakika mu mun kafirce da su gaba daya."
49. Ka ce (da su): "to ku zo da wani littafin daga wajen Allah wanda yafi su nuna hanyar shiriya (watau Alkur'ani da Attaura), zan bi shi idan kun kasance masu gaskiya."
50. To idan ba su amsa maka ba, sai ka tabbatar da cewa ba abin da suke bi sai soye-soyen ransu kawai; ba kuwa wanda ya fi bacewa kamar wanda ya bi son ransa ba tare da wata shiriya daga Allah ba. Hakika Allah ba ya shiryar da mutane kafurai.
51. Hakika kuma mun sadar musu da fadi (na bin wani na Alkur'ani) don su wa'azantu.
52. (Wasu daga) wadanda muka bai wa littafi a gabaninsa (Alkur'ani) su suna ba da gaskiya da shi.
53. Idan kuma ana karanta musu (Alkur'ani) sai su ce: "mun ba da gaskiya da shi, ba shakka shi gaskiya ne daga Ubangijinmu, hakika mu mun kasance musulmi tun gabanisa."
54. Wadancan za a ba su ladan su niki biyu saboda hakurin da suka yi, kuma suna kawar da mummunan aiki da kyakkyawa, suna kuma ciyar wa daga abin da muka azurta su (da shi).
55. Idan kuma suka ji maganar banza sai su kau da kai daga gare ta, su kuma ce: "(sakamakon) ayyukanmu yana gare mu, ku kuma na ayyukanku yana gare ku. Mun kubuta daga gare ku; ba ruwanmu da wawaye!"
56. Hakika kai ba ka shiryar da wanda ka so, sai dai Allah yana shiryar da wanda ya so. Shi kuma ne ya san masu shiryuwa.
57. Suka ce: "idan muka bi shiriyar tare da kai, to za a kame mu (ribattatu) daga kasarmu", (ka ce da su): "yanzu ashe ba mu ne muka tanadar musu Harami amintacce ba da ake kawo kowanne irin (nau'i) na 'ya'yan itace gare shi don azurtawa daga gare mu?" sai dai kuma yawancinsu ba sa sanin (haka).
58. Kuma da yawa al'umma da muka hallakar wanda ta butulce wa rayuwarta. To ga gidajensu can ba a zaune su ba a bayansu sai kadan, muka kuma kasance mu ne magadan.
59. Kuma Ubangijinka bai zamanto mai hallakar da alkaryu ba har sai ya aiko da manzon a cikin manyan biranensu, yana karanta musu ayoyinmu. Kuma ba mu kasance masu hallaka alkaryu ba sai idan mutanensu sun zama azzalumai.
60. Abin da kuma aka ba ku na kowanne irin abu, to jin dadin rayuwar duniya ne da adonta. Abin da yake wurin Allah kuwa (shi) ya fi alhairi da kuma wanzuwa. Me ya sa ne ba kwa hankalta?
61. Yanzu wanda muka yi wa alkawari kyakkyawa sannan zai same shi, zai zama kamar wanda muka jiyar dadin rayuwar duniya sannan kuma shi yana daga wadanda za a kai wuta? (A'a, ba za su yi daidai ba).
62. Kuma (ka tuna) ranar da (Allah) zai kirawa su sannan ya ce: "ina abokan tarayyar nawa wadanda kuka kasance kuna riyawa?"
63. Sai wadanda fadar (alkawarin Allah na azaba) ya tabbata a kansu suka ce: "ya Ubangijinmu, wadannan da muka batar, mun batar da su ne kamar yadda mu ma muka bata, muna neman kubuta zuwa gare ka, don kuwa ba su kasance suna bauta mana ba."
64. Kuma aka ce: "ku kirawo abokan tarayyar naku", sannan suka kirawo su, sai ba su amsa musu ba, suka kuma ga azaba (suka rika burin) ina ma sun kasance shiryayyu!
65. (Ka tuna) kuma ranar da (Allah) zai kirawo su sannan ya ce: "me zaku amsa wa manzanni (da shi?)."
66. Sai abubuwan da za su fada suka bace musu a wannan ranar, sannan (kuma) su ba sa tambayar (juna).
67. To amma wanda ya tuba ya ba da gaskiya ya kuma yi aiki nagari to ana kaunar ya zama cikin marabauta.
68. Kuma Ubangijinka yana halittar abin da yake so yana kuma zabar (abin da yake so), ba su suke da zabi ba. Tsarki ya babbata ga Allah, ya kuma daukak dag abin da suke tara (shi da shi).
69. Kuma Ubangijinka ya san abin da zukatansu suke boyewa da kuma abin da suke bayyanawa.
70. Kuma shi Allah, babu wani abin bauta wa da gaskiya sai shi, yabo ya tabbata a gare shi a duniya da lahira; hukunci kuma nasa ne, kuma zuwa gare shi ne kawai za a komar da ku.
71. Ka ce: "ku ba ni labari, (yanzu) idan Allah ya sanya muku dare tutur har zuwa ranar alkiyama, wane sarki ne in ba Allah ba zai zo muku da wani haske? To me ya sa ba kwa ji?"
72. Ka ce: "ku ba ni labari (yanzu) idan Allah ya sanya muku rana tutur har zuwa ranar alkiyama, wane sarki ne in ba Allah ba zai zo muku da dare da za ku samu nutsuwa a cikinsa? To me ya sa ba kwa lura.
73. Daga rahamarsa ne kuma ya sanya muku dare da rana don ku samu nutsuwa a cikinsa (watau dare) kuma don ku nema daga falalarsa (da rana), don ku rika yin godiya.
74. Kuma ka tuna ranar da (Allah) zai kirawo su nannan ya ce: "ina abokan tarayyar nawa wadanda kuka kasance kuna riyawa?"
75. Muka kuma ware wani shaida dag kowacce al'umma (watau annabinsu) sannan muka ce: "to ku kawo dalilinku (na yin tarayya da Allah)." Sannan suka san cewa lallai gaskiya tana ga Allah, kuma abin da suka kasance suna kirkira ya bace musu.
76. Hakika Karuna yana dag mutanen Musa, sai ya yi musu dagawa muka kuma ba shi daga taskoki (na dukiya), abin da makullansu suka zama kaya niki-niki ga tarin jama'a karfafa, yayin da mutanensa suka ce da shi: "kada ka yi homa, hakika Allah ba ya son masu fariya.
77. "Kuma ka nemi gidan lahira ta hanya abin da Allah ya ba ka, kada kuma ka manta rabonka na duniya; kuma ka kyautata kamar yadda Allah ya kyautata maka, kada kuma ka nemi yin barna a bayan kasa. Hakika Allah ba ya son masu barna."
78. Ya ce: "ai ni an ba ni ita (watau dukiyar) ta hanyar ilimin da nake da shi ne." shin yanzu bai sani ba ne cewa hakika Allah ya hallaka wasu al'ummun da suke a gabansa wadanda suka fi shi karfi da kuma yawan tarin (dukiya)? Ba kuwa za a tambayi kafurai game da laifukansu ba.
79. Sai ya fito wa mutanensa a cikin adonsa; sai wadanda suke burin rayuwar duniya suka ce: "ina ma da za mu mallaki irin abin da aka bai wa Karuna? Hakika shi mai babban rabo ne."
80. Wadanda kuwa aka bai wa ilimi (mai amfani) sai suka ce: "kaiconku, ai ladan Allah shi ya fi alheri ga wanda ya ba da gaskiya, ya kuma yi aiki nagari, ba kuwa wanda ake wa katari da shi sai masu hakuri."
81. Sanna muka kifar da shi (Karuna) tare da gidansa cikin kasa, kuma ba shi da wata jama'a da za su taimake shi in ba Allah ba, kuma bin kasance daga masu cin nasara ba.
82. Kuma wadanda suka yi burin matsayinsa a jiya suka wayi gari suna cewa: "wai yau mun ga abin al'ajabi! Allah yana yalwata arziki ga wanda yake so daga bayinsa; yana kuma kuntatawa ga wanda ya so; ba don Allah ya ba mu sa'a ba da mu ma ya kifar da mu. Abin mamaki, hakika kafurai ba sa rabauta."
83. Wancan gida na lahira muna sanya shi ga wadanda ba sa nufin girman kai da barna a bayan kasa. Kyakkyawan karshe kuma na masu tsoron Allah ne.
84. Duk wanda ya zo da kyakkyawan aiki, to yana da (lada) fiye da shi; wanda kuma ya zo da mummunan aiki, to ba za a saka wa wadanda suka aikata munanan ayyuka ba face daidai da abin da suka kasance suna aikatawa.
85. Hakika wanda ya saukar da Alkur'ani lallai zai mayar da kai zuwa Makka. Ka ce: "Ubangijina shi ya san wanda ya zo da shiriya da kuma wanda yake cikin bata mabayyani."
86. Kuma ba ka kasance kana zaton a saukar maka da littafi ba, sai dai (an yi haka ne) don rahama daga Ubangijinka. To kada ka zamanto mai taimakon kafirai.
87. Kuma lallai kada su hana ka (isar da) ayoyin Allah bayan an riga an saukar maka da su, kuma ka yi kira zuwa ga Ubangijinka, kuma lallai kada ka zamanto daga mushrikai.
88. Kuma kada ka bauta wa wani abin bautar daban tare da Allah sai shi, kowane abu mai hallaka ne sai zatinsa kawai (wato Allah); hukunci (duk) nasa ne, domin kuwa gare shi za a komar da ku.