المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : tarjamar ma'anar suratul waqi'ah zuwa harcen hausaترجمة سورة الواقعة إلى لغة الهوسا


طاهر جبريل دكو
_15 _February _2017هـ الموافق 15-02-2017م, 09:07 PM
SURAR WAKI'A
A Makka aka saukar da ita
(Ayoyinta 96)
(Muna fara wa da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai).
1. Idan mai afkuwa ta afku (watau alkiyama).
2. Babu wata kai nunfashi mai karya tawa game da afkuwarta.
3. Mai kaskantarwa (kuma) mai daukakawa.
4. Idan aka girgiza kasa girgizawa.
5. Aka kuma dandake duwatsu dandakewa.
6. Sannan suka zama kamar kura abar shekewa.
7. Kuka kuma kasance dangogi guda uku.
8. To, ma'abota dama, ba a sanar da kai ma'abota dama ba?
9. Da kuma ma'abota hagu, ba a sanar da kai ma'abota hagu ba.
10. Da kuma masu rigegeniya (wajen alhairi).
11. Wadancan su ne makusanta.
12. A cikin aljannar ni'ima.
13. Suna da yawa cikin (mutanen ) farko.
14. Kuma kadan ne daga (mutanen) karshe.
15. A kan gadaje masu ado.
16. Suna kishingide a kansu suna kallon (juna).
17. 'Yan yara masu dawwamammun (shekaru) suna kai kawo a kansu.
18. Da kofuna da sintala masu murikai da kuma kofi na giya mai gudana.
19. Ba sa jin ciwon kai, da ita kuma ba sa buguwa.
20. Da kuma 'ya'yan itatuwa daga abin da suke so su zaba.
21. Da kuma naman tsunt-………masu tsanani farin idaniya, bakin
22. Da kuma (matar) Hurul'aini masu tsananin farin idaniya, bakin idaniyar da farinta masu dara daran idanu.
23. Kamar misalin tataccen lu'ulu'u abin boyewa.
24. Sakamako ne na abin da suka kasance suna aikata wa.
25. Ba kuma sa jin wani zancen banza ba kuma (sa jin) na barna.
26. Sai dai ai ta cewa aminci-aminci (suna watsa sallama a tsakaninsu).
27. Ma'abota dama, su wane ne ma'abota dama?
28. A cikin magarya marar kaya.
29. Da kuma ayaba masu 'ya'ya dori-dori dab-da-dab.
30. Da inuwa abar ja (watau marar karewa).
31. Da kuma ruwa mai kwararowa.
32. Da 'ya'yan itaciya masu yawa.
33. Ba mai yankewa ba kuma ba abr hanawa ba.
34. Da shimfudu masu tudu.
35. Mu Muka kage su kagowa.
36. Sannan Muka sanya su budurwowi.
37. Masu tsananin soyayya ga mazajensu kuma tsareku.
38. Don ma'abota dama.
39. Suna da yawa daga mutanen farko.
40. Kuma suna da yawa daga mutanen karshe.
41. Ma'abota hauni kuma su wane ne ma'abota hauni.
42. (Suna cikin iska mai zafi mai tsanani da kuma tafasasshen ruwa.
43. Da kuma inuwa ta tirnikakken bakin hayaki.
44. Ba mai sanyi ba kuma ba kyan gani ba ya kare (zafi).
45. Hakika su, sun kasance mani'imta kafin wannan (a duniya ba sa sha'awar bin Allah).
46. Sun kuma kasance suna zarewa a kan zunubi Mai girma.
47. Sun kuma kasance suna cewa shin yanzu idan mun mutu mun zama kuma kasa da kasusuwa yanzu lallai za a tashe mu?
48. Shin ko kuwa iyayenmu na farko"
49. Ka ce: "Hakika na farko da na karshe.
50 Lallai za a tattara su zuwa ranar lokaci sananne.
51. Sannan kuma hakika ya ku wadannan batattun makaryata ne.
52. Lallai masu ci ne daga bishiyar zakkumi.
53. Sannan masu cika ciki ne da ita.
54. Sannan kuma masu shan tafasasshe ne a kansa.
55. Sannan masu shan ne shan rakuma masu tsananin kishir ruwa.
56. Wannan shi ne garar bakinsu ranar sakamako.
57. Mu ne Muka halicce ku saboda me ba kwa gaskata wa.
58. Shi ba kwa ganin abin da kuke (fitarwa) na maniyi.
59. Shin yanzu ku ne kuke halittarsa ko kuwa Mu ne masu halittar?
60. Mu Muka kaddara mutuwa, a tsakaninku, mu ba masu gajiyawa ba.
61. A bisa Mu canja misalinku, Mu kuma fare ku cikin abin da ba ku sani ba.
62. Hakika kuma ku kun san farkon halittarku, don me ba kwa wa'azantuwa.
63. Shin Yanzu ba kwa ganin abin da kuke noma wa.
64. Shin ku ne kuke tsuro da shi ko Mu ne Masu tsurowar.
65. Idan da Mun so lallai da Mun sanya shi busasshe marar (amfani), sai ku wayi gari kuna mamaki.
65. Hakika lalle (kuna cewa) Mu masu hallakarwa ne.
67. (Wani lokacin kuna cewa), ba haka ba ne Mu dai masu haramta wa ne.
68. Shin Yanzu ba kwa ganin ruwan da kuke sha ba.
69. Shin yanzu ku ne kuka sauko shi daga hadarin ko kuwa Mu ne Masu sakkowa (da shi).
70. Idan da mun so sai mu sanya shi mai zartsi, don me ba kwa godewa ne?
71. Shin yanzu ba kwa ganin wutar da kuke kunna wa.
72. Shin yanzu ku ne kuka fari bishiyarta ko kuwa Mu ne Muka fara.
73. Mu ne Muka sanya ta izina da kuma amfani ga matafiya (a bayan kasa).
74. Saboda haka sai ka yi tasbihi da sunan Ubangijinka Mai girma.
75. Sannan kuma ba sai na yi rantsuwa da masaukin taurari.
76. Hakika kuma ita rantsuwa ce babba idan da kun sani.
77. Hakika lallai shi Alkur'ani ne mai girma.
78. A cikin littafi abin boyewa (da karewa).
79. Ba mai taba shi sai masu tsarki.
80.Saukakke daga Ubangijin talikai.
81. Shin yanzu da wannan zance kuke lakolako. (da wulakantawa)
82. Kuke kuma sanya arzikinku hakika ku kuna karyata (shi).
83. Saboda me idan (rai) ta zo makogwaro.
84. Ku kuma a wannan lokacin kuna kallo.
85. Mu kuma Mu Muka fi kusa da shi fiye da ku, sai dai kuma ba kwa gani.
86. Saboda me idan da kun kasance ba ababen yi wa hisabi ba ne.
87. Ku dawo da ita mana idan kun kasance masu gaskiya.
88. Amma kuma idan ya kasance daga makusanta.
89. To suna cikin hutawa kuma arziki kyakkyawa, da kuma aljannar ni'ima.
90. Amma kuma idan ya kasance daga ma'abota dama.
91. To aminci a gareka daga ma'abota dama.
92. Amma kuma idan ya sance daga makaryata batattu.
93. To garar baki ta ruwan zafi.
94. A kuma shiga Jahannama ana konuwa.
Hakika wannan lallai shi ne gaskiyar sakankancewa.
96. Saboda haka sai ka yi tasbihi da sunan Ubangijinka Mai girma.