طاهر جبريل دكو
_21 _December _2016هـ الموافق 21-12-2016م, 06:50 PM
GARKUWA GOMA DAGA SHARRIN SHEDANU
Aljannu su wasu halittu ne daga halittun Allah maxaukakin sarki, Allah Ya halicci su ne domin bauta gare shi kamar mutane Allah Ya ce:
{وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْإِنْسَ إِلَّا لِيَعْبُدُونِ } [الذاريات: 56]
Ma'ana: Kuma ban halicci aljanu da mutane ba sai don su bauta mi ni. Saboda haka su na tarayya da mutane cikin wasu sifofi haka nan kuma sun sha bamban da su cikin wasu sifofin:
Abubuwan da su ke tarayya da 'ya'yan Adamu a cikinsu
Sun dace da 'yan Adam cikin kasncewar su su ma an halicci su ne domin bauta kamar yadda aka halicci mutane domin hakan.
Haka nan kamar mutane su ma su na dangantuwa zuwa ga addinani mabambanta da saboda haka cikin su akwai muminai akwai kafirai a cikin musulman su ma akwai na gari akwai na banza.
Su ma su na dangantuwa zuwa ga qasashe da garuruwa.
Abubuwan da su ka sava da su ka sha bamban da bil Adama a cikin su
Asalin halittar su daga harcen wuta ne.
Su na da qudura da ta zarce ta bil Adama, kamar saurin qaura daga wani wuri zuwa wani, suna da qudura na ban mamaki wurin aiwatar da ayyuka ma su girma da wahala a cikin xan qanqanin lokaci.
Suna da qudura na rkixa daga wata sifa zuwa wata sifa kamar surar xan Adam ko dabba.
Sun kasu zuwa sinfi Uku: wasu masu fikafikai ne masu iyo a sararin samaniya.
Wasu masu rikixa zuwa surorin macizai da karnuka.
Wasu kuma kullum cikin tafiye-tafiye su ke. su tashi daga wannan garin zuwa wancan.
Baya yiwuwa – galibi- ga bil Adam ya gan su a kan asalin halittar sua ta haqiqa.
Su aljannu ba a tava ba wa wani daga cikin su annabta.
Daga cikin abincinsu akwai kasusuwa da bil Adama su ka ci su ka yar, idan su ka ambaci sunan Allah akan shi sai Allah Ya tufatar da shi da nama su ci. Haka nan dabbobinsu suma su na samun abincinsu daga kashin dabbobin bil Adama.
Sun fi yawan rayuwa a kufayi da ramuka da wuraren savon Allah da hayaniya kamar wuraren kixe-kixe da kasuwanni saboda abubuwan da ke wuraren na ha'inci da cuta da rantse-rantsen karya.
Garkuwowi Goma daga sharrin shexanu.
Garkuwa ta Xaya: neman tsarin daga sharrin shexan jefaffe kamar yadda Allah Ya ce:
{وَإِمَّا يَنْزَغَنَّكَ مِنَ الشَّيْطَانِ نَزْغٌ فَاسْتَعِذْ بِاللَّهِ إِنَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ } [الأعراف: 200]
Ma'ana: kuma idan wani waswasi na shexan ya bijiro maka, to ka nemi tsarin Allah. Lallai Shi –Allah- Shi ne mai ji masani. (Suratul A'raf 200)
Ya zo a cikin sahihul Bukhari daga hadisin Adiyyu xan Thabit daga Sulaimanu xan Surad ya na cewa: na kasance ina zaune tare da Annabi (صلى الله عليه وسلم) alhali wasu mazaje biyu sun zage zage har fuskar xayan su ta yi jazur jijiyoyin wuyanshi sun kumburo, sai Annabi (صلى الله عليه وسلم) y ace wallahi ni na san wata kalma da zai fax eta da abin da ya ke ji ya gushe daga gare shi. Da zai ce: أعوذ بالله من الشيطان الرجيم)))) da abin day a ke ji ya tafi daga barin shi" Bukhari da Muslim ne su ka ruwaito shi.
Garkuwa ta Biyu: karanta surorin nan biyu –suratul falaq da suratunnas- ya na da tasiri mai ban mamaki wurin tunkuxe sharrin shexan shi ya sa Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: mai neman tsari bai nemi tsari da kamar su ba. Kamar yadda ya ce: lallai wanda ya karanta su yayin day a wayi gari da yayin day a yammaita tare da suratul ikhlas –wato qulhuwallahu ahad- sun wadatar da shi daga komai.
Garkuwa ta Uku: karanta ayatul kursiyyu. Kamar yadda zo a cikin sahihul Bukhari daga hadisin Muhammad ibnu Sirin daga Abu huraira Allah Ya kara yarda a gare shi.
Garkuwa na: karanta suratul baqara. Ya zo a cikin sahihul Bukhari daga hadisin Abu huraira cewa Manzon Allah ya ce : kada ku mai da gidajen ku su zama kamar maqabartu, kuma duk gidan da ake karanta suratul Baqara a cikinsa shexani ya na guje ma sa.
Garkuwa ta Huxu: karanta ayoyi biyu na qarshen suratul Baqara. Ya tabbata a cikin sahihul Bukhari da Muslim daga hadisin Abu Musa Allah Ya qara masa yarda ya ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: wanda ya karanta ayoyi biyu na qarshen suratul Baqara a cikin dare, sun wadatar das hi. Haka nan ya zo a cikin Jami'u-ttirmizi daga hadisin Nu'uman ibnu Bashir Allah Ya qara musu yarda daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: Lallai Allah Ya yi wani rubutu gabanin Ya halicci halittu da shekara dubu biyu daga Ya saukar da ayoyi biyu da Ya kamala suratul Baqara da su. Ba za a karanta su ba tsawon darere uku a cikin gida kuma shexan ya kusanci gidan.
Garkuwa ta Biyar: Ayoyi biyu na farkon suratul Ghafir tare da ayatul kursi. Ya zo a cikin Jami'u-ttirmzi daga hadisin Abu huraira Allah Ya qara masa yarda ya ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: wanda ya karanta {حم} المؤمن (wato suratul ghafir) zuwa faxin Allah {إِلَيْهِ الْمَصِيرُ} tare da ayatul kursiyu yayin da ya wayi gari za a kare shi har ya yammaita wanda kuma ya karanta ta yayin da ya yammaita za a kare shi har ya wayi gari. Hadisi ne mai rauni amma ya na da waxanda ke qarfafan shi game da karanta ayatul kursiyyu.
Garkuwa ta Bakwai: faxin LA'ILAHA ILLA LLAHU WAHDAHU LA SHARIKA LAHU LAHUL MULKU WALAHUL HAMDU WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN QADIR kullum qafa xari. Ya zo a cikin Bukhari da Muslim daga hadisin Abu huraira Allah Ya qara masa yarda ya ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: duk wanda ya ce: LA'ILAHA ILLA LLAHU WAHDAHU LA SHARIKA LAHU LAHUL MULKU WALAHUL HAMDU WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN QADIR sau xari a yini tamkar ya 'yanta bayi ne guda goma, kuma za a rubuta masa lada xari kana kuma a kankare masa zunubbai xari kuma za su kasance garkuwa gare shi daga shexan a wannan yinin na shi har ya yammaita, kuma babu wanda zai zo da abinda ya fi na shi sai wanda ya yi fiye da hakan.
Garkuwa ta Takwas: yawan ambaton Allah, kuma wannan shi ne ma fi amfani daga cikin garkuwowi daga shaexan ya zo a cikin jami'u-ttirmizi daga hadisin Alharithul Ash'ari Allah Ya qara masa yarda daga Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: Allah Ya umarci (Annabi) Yahya xan Zakariyya da wasu kalmomi guda biyar akan ya yi aiki da su kuma ya umarci bani isra'ila da su yi aiki da su… daga cikin abubuwan da ya umarce su da shi ya ce: kuma Ya na umurtan ku da ku ambaci Allah domin misalin hakan shi ne misalin wani mutum da abokan gaba su ka tasa shi a gaba a guje har ya isa zuwa ga wata ganuwa sai ya kare kansa daga sharrinsu, to kamar haka ne bawa ba ya tsare kansa daga shaixani sai da ambaton Allah….
Garkuwa ta Tara: Alwala da salla, wannan ma ya na daga cikin mafi girman abubuwand da ake kare kai da su daga sharrin shaixan musamman ma yayin da fushi ya tsananta ko sha'awa, domin ita wuta ce da ta ke tafarfasa a zuciyar xan Adam kamar yadda ya zo a cikin jami'u-ttirmizi daga hadisin Abu Sa'idin Alkhudri Allah Ya qara masa yarda daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: ku saurara! Lallai fushi wani garwashi ne na wuta a cikin zuciyar xan Adam, ba ku yi dubi ba ne zuwa ga jan idanunshi da kumburar jijiyoyin wuyarshi? Duk wanda ya ji wani abu game da hakan ya mannu da qasa. A wani hadisin kuma ana cewa: Lallai shexan an halicci shi ne daga garwashin wuta, shi kuma wuta da ruwa ake kasha shi saboda haka bawa bas hi da wani abu na kashe wutar vacin rai da sha'awa kamar alwala da salla, domin shi fushi wata ne alwala kuma ya na kasha wutar, salla kuma idan ta guda cikin khushu'I da fuskantar Allah da zuciya sai ya tafiyar da tasirin sa. Wannan al'amari ne da yau da gobe ya tabbatar da cewa gaskiya ne wanda baya bukatar neman dalili.
Garkuwa ta Goma: kame wa daga abin da ya zarce buqata na abin da ya shafi kallo da Magana da abinci da yawan cuxanya da mutane, domin lallai shexan kawai ya kan samu nasara ne akan xan Adam ya iya cutar da shi ta waxannan qofofin guda huxu.