المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : HUXUBAR MASALLACIN ANNABI (صلى الله عليه وسلم) JUMA'A, 13/ALMUHARRAM/1438H daidai da 14/OKTOBA/ 2016M


طاهر جبريل دكو
_16 _October _2016هـ الموافق 16-10-2016م, 11:26 AM
HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 13/ALMUHARRAM/1438H
daidai da 14/OKTOBA/ 2016M








LIMAMI MAI HUXUBA
DR. SALAH XAN MUHAMMADU ALBUDAIR














TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم


A

HUXUBAR FARKO

Bayan haka:


Ya ku Musulmai!!
Ku yi godiya wa Allah, akan ni'imomi da kyautuka, kuma ku yi yabo a gare shi, akan abin da ya tunkuxe muku, na azabobi da bala'oi.
Kuma ku xauki ibra ko darasi da waxannan da su ke kewaye da ku, saboda KASASHE NAWA NE aka samu rabuwar kan (mutanensu), shugabanci kuma ya wargaje, kwar-jini ko girmama hukunci ya faxi qasa, har ya zama babu shugaba, babu haxin kai, sai ma'abuta wannan qasar suna yaqi da junansu, haxin kansu ya tsattsage, zaman lafiyarsu kuma ya wulaqanta.
Shi kuma lamarin zaman lafiya, idan har ya samu koma-baya, sai rashin aminci ya yi girma, dawo da amincin kuma ya yi wahala. Saboda fitina barci ta ke yi, babu mai tayar da ita (daga barcinta) sai mai dauxa, kuma babu mai jawo ta face mutum mai ha'inci, kuma babu mai sake ta (ga mutane) face mai yawan zalunci.
Fitina lallai ana mata barbara ne da ciki: ta hanyar habaici (ko maganganun da ba na kai-tsaye ba), sai kuma ta haife, ko ta auku: da kalmomin zaburarwa ko kwaxaitarwa.
Kuma wace manufa ce ke fatan samu, Wanda ba shi da wata sana'a, sai kiran mutane su fito zanga-zanga ko fito-na-fito, da muzaharori, da tuntsurar da gwamnatoci, ko fita daga xa'ar ma'abuta mulki da shugabanni ! ?
Bayan kuma, abubuwan da su ka auku (a qasashe daban-daban) sun tabbatar cewa: FICEWA DAGA XA'AR MASU MULKI DA SHUGABANNI SHI NE GINSHIQIN SHARRI DA FITINA DA BALA'I, saboda An ruwaito daga Usaid bn Hudair (رضي الله عنه), ya ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai ne Ku, a bayana, za ku haxu da son kai (na shugabanni), Sai ku yi ta haquri, har ku haxu da ni, akan tafki", Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.
Imam An-Nawawiy ya ce: ((Kalmar "asarah" tana nufin: Kevance kai da abubuwan duniya, da fifita kansu da shi, akanku; Ma'ana: Ku ji maganan shugabanni, kuma ku yi musu biyayya, koda sun keve kansu da kayan duniya, koda kuma ba su isar da haqqoqinku da su ke wurinsu izuwa gare ku ba)).
Shekhul Islami Ibnu-Taimiyya (رحمه الله تعالى) shi kuma ya ce: ((Kaxan ne,, wanda su ke ficewa daga biyayyar shugaba mai iko, face ya kasance abinda aikinsu ke haifarwa na sharri, shi ya fi yawa, akan abinda hakan ke haifarwa na alkhairi)).
Kuma Amru bn Al-aas (R.A) yana faxa; cikin wasiyyar da ya yi wa xansa: ((YA KAI XANA! Samun shugaba adali ya fi alkhairi a kan sauqar ruwa, da samun raquma. Shi kuma zama qarqashin shugaba azzalumi maqetaci, ya fi alkhairi akan fitinar da za ta dawwama)).


FITINTINU suna gajiyar da masu kaifin kwakwala, suna kuma kunyata jahilai, Kuma idan yaqi ya kunnu, mutane kuma su ka kama faxace-faxace, sai hankula su zame; su yi kure, duga-dugai kuma su goce, Tunani ko hankula su kuma, su shiga ximuwa, Sai dai wanda ilimi da haquri su ka qawata shi, sannan ya ji tsoron aukawa cikin zunubi da zalunci.


KUMA HIKIMAR HARSHE, DA TA TAKOBI na kasancewa ne cikin: Tsanaki, wanda ke tunkuxe wauta, da ilimin da ke kore jahilci, da hankali wanda ke kawar da mutum daga aukawa cikin fitina.
Hankulanku –Ya ku mutanena- kada ku nisance su
Kuma kada ku, yanke zumuncinku, da juya baya wa juna


Ya ku Musulmai !!
Idan sautuka su ka cakuxa, Husumomi kuma su ka tsananta, kiraye-kiraye kuma su ka bayyana, Muzaharori da fito-na-fito su ka tsayu, to lallai farkon wanda ke ribatar hakan, har ya haye tsakiyarta ya bayyana, Su ne: Maqiyan musulmai, waxanda siyasarsu ta kafu a kan xaukar haqqoqin musulmai ba a bakin komai ba, da halatta cin dukiyarsu da varna, da halaka garurrukansu, da rurrusa tattalin arziqinsu, da kuma mamaye dukiyoyinsu, da yaxa zaman kara-zube a cikin qasashensu, suna masu riqan abubuwan da su ka auku a matsayin hanyar bi, don tabbatar da buqatunsu munana.


Shi kuma ADALCI ba za su zana iyakokinsa, da hukunce-hukuncensa, da tsare-tsarensa ba: Qasashe 'yan mamaya azzalumai, waxanda su ka faxa cikin rami mai zurfi, kuma qarfi ya ruxe su.


Haqiqanin rahama da adalci a cikin zukatan masu rahama, ba zai yi daidai da riya hakan ba; wanda (a kullum) masu kisa waxanda su ka kakkafa kayukansu, a matsayin masu yin wasici ga qasashen duniya, wai kuma masu kare haqqoqi, da kiyaye aminci da zaman lafiya.
Kuma ta yaya zai kiyaye zaman lafiya wanda ya shuka zanga-zangar fito-na-fito, ya kuma qarfafi juyin juya-hali da tuntsurar da gwamnatoci, ya kuma kunna yaquka, da faxace-faxace, ya taimaki maha'inta, A shekarun da kuma, su ka yaqi masarautun da su ka kasance sun kai maqura wajen qarfi da wadaci da zaman lafiya?!


Haqiqa al'ummomin wannan zamani, da majalisar amincinsu sun xau alqawura, kan kakkafa zaman lafiya, da tabbatar da aminci, sai dai kuma kamar sun yi alqawari ne kan rurrushe zaman lafiya, ko kamar sun qulla cewa za su share shi (daga doron qasa)!
Rattaba hannu don kawo zaman lafiya, bai zama komai ba, face zane a saman takardu, da tawadar qarya akan fefofi, daga bishiyoyin cin amana da yaudara;


Sau nawa, aka rattaba hannun, don kawo zaman lafiya, Wanda iskar siyasa sai ta yi wasa da ita, ta arewa da kudu


Idan har za ku rubuta wani alqawari na kawo zaman lafiya, To ku sanya hawayen iyayen da aka kashe musu 'ya'ya; cakuxe da tawadar


Ko ku yi zanen tsarin, da jinanen waxanda aka kashe da zalunci,
Kuma ku tuna wata rana mai tsananin firgici da su ka samu kansu a cikinta


Sai ku qirqiro adalci ga dukkan mutane,
Ba wurin kiyon da zai zama yabanya ga masu qarfi kawai ba


Ya ku masu riya kiyaye zaman lafiya ! !
Haqiqa lamarin samun aminci da zaman lafiya ya wulaqanta, qarqashin kwaxayin qasashe, sai zaman lafiya a qarqashin siyasosinku ya zama buri ne da aka rasa, kuma qarya ce abar qi.


Sai ku rage sautin fantamawar da ku ke juyi a cikinsa, domin kada ku tayar da mafarkin mayunwata, da waxanda aka kora, ko aka qauratar daga garurrukansu !


Ku sake rage sautin wargin da ku ke wasa a cikinsa, domin ka da ku yanke mafarke-mafarken yaran da su ke ci-gaba da barci a qarqashin rusassun xakuna da gidaje da asibitoci ! !


Kuma ku voye hotunan nuna tsananin farin ciki da nashaxi da murmushi a lokutan ganawanku, domin kada ku karya zukatan waxanda aka yi masu raunuka, da waxanda su ke cikin baqin ciki ! ! !


Shi kuma fiskantar gungun 'yan Sunnah, a hukumominsu, da jagororinsu, da manya-manyansu, da malumansu, da qarfinsu, da tattalin arziqinsu, da kuma aikin qaqaba takunkumi, a garurrukan Sunnah, da qalubalantar masallatai da majami'oi, da makarantun Ahlus Sunnah, ana qirga shi a matsayin ta'addacin da aka tsattsara, akan musulmai gabaxaya, kuma laifuka ne na yaqi, kuma keta alfarmar haqqoqin 'yan adam musulmi ne a garurrukansu da qasarsu.


Ya ku Musulmai !!
Kuma haqiqa ta fita daga al'ummar musulmai a zamanin da, da na yanzu, wata qungiya, da ta karkata izuwa ga munanan aqidu, wanda ta sava wa ginshiqan addini da su, kuma ta ci karo da aqidar musulmai da su, ta kuma qudurci aqidar kafirta sahabbai, da riya cewa sun yi ridda, kuma qungiyar ta ginu akan cewa, an jirkita alqur'ani mai karimci, da aqidar cewa, a tauye (alqur'ani) ya ke, kuma su ka halatta zubar da jinin ahlus sunnah waljama'a, duk da yawan mazhabobinsu da banbancin makarantunsu.
Kuma lallai abubuwan da su ka auku a tarihi, da waxanda su ke gudana (a yau) suna nuna cewa:
Lallai su 'yan shi'a su ne makamin maqiya; da su ke sukan kwankwason al'umma da su, kuma su ne abin hawan maqiya, da su ke hawa domin rurrushe qasashen Musulmai.
Kuma lallai garwashin wuta, da durorrukan qiyayya da su ke ta sauqa ga iyalanmu a garin Shaam da Halab.
Da siyasar yunwatarwa, da tsoratarwa, da rushe-rushe, wanda sojojin sa kai na Husi su ke aiki da shi a birnin San'a'a (ta qasar Yaman).
Da kuma munanan laifukan da taron qabilu su ke aikata su a qasar Iraqi da Siriya.
Da jinkirin da manyan qasashe ke yi wajen bin matakai na aiki cikin gaggawa domin tsamar da waxannan al'ummomin = babban dalili ne da ke nuna yadda ake ha'intar waxannan mutanen. Kuma shi ne babban sababin da ya tunkuxa jagororinmu da mutanenmu, wajen xaukar matakai na aiki, cikin gaggawa, domin kare garurrukansu, daga munanan tsare-tsare da ake fiskantar da su gare su, ba tare da an togance wani ba, daga cikinsu.
Lallai ne, waxancan aqidu fanxararru, ba komai ba ne face wasa ne na siyasa a asalinsu da tushensu, Wanda sautinsu ya fita daga tsirkiyar xaukar fansan jinin Husaini (رضي الله عنه) da kuma da'awar nuna soyayya ga iyalan Manzo (S.A.W), Sai aka yi wasa da hankulan dayawa daga gama-garin mutane (marasa ilimi), aka kuma boye shi bayan tufafin addini da aka jirkita, su ka kuma tura jelansu izuwa garin San'a'a, da Shaam, da kuma masu da'awan shi'anci izuwa ga kowani gari, domin su isar da manufofin shi'a munana, wanda ga asasinsu, su ka ginu akan yaqar littafin Allah (alqur'ani) da sunnar Manzo, da jama'ar musulmai, da qasar musulunci, da larabawa.
Sai ya tabbata a bayan haka, cewa lallai wajibin da ya fi wajaba, da kuma abinda ya fi muhimman lamura muhimmanci, shi ne: Tsayuwan jagororin musulmai da hukumominsu, wajen kare jama'arsu, daga waxancan aqidun munana, da wasa ta siyasa wulaqantacciya, da kuma fito-na-fito na masu bautar gumaka majusawa.
Kuma maqiyan musulunci na nesa, basu gushe ba suna quqqula ittifaqoqi a asirce, tare da xagutocin wannan mazhaba (na shi'a) mummuna, suna kukkuna fitintinu a garurrukanmu na musulunci, kuma suna iza wutar yaqe-yaqe da faxace-faxace.
Sai dai kuma, ba za ta savu ba; saboda dukiyoyinmu da duk abinda mu ka mallaka, da rayukanmu, fansa ne domin gamawa da waxancan jelan, da kuma mafarke-mafarkensu masu najasa, kuma fansa ne domin kiyaye haxin kanmu, da qarfinmu, da daularmu.


Ya ku Musulmai !!
Yaye musibu a tsakanin sahun musulmai alamominsa sun fara bayyana, >>>>>>>>>>>> ………. >>>>>>>>>>>>


yagewa da fuji, da rarrabuwar kai a ra'ayoyi, da son zuciya, da qungiyoyi, da jama'oi, kuma kowace qungiya daga cikinsu tana da wani niyya da manufa, kuma kowace jama'a tana da mashaya (da take xaukar addininta), kuma kowace qungiya tana qanqanta sha'anin wata, kuma tana aikin tsoratarwa daga gare ta. Babu kuma abinda mu ke iya ji sai sautin mai tsoratarwa, mai kashedi, kuma babu abinda mu ke iya gani sai alamar mai tsanantawa mai kaushin rai; Kowa takobinsa yana cinye kubensa; saboda kaifinsa, kuma yana tsananta wa xan'uwansa musulmi; saboda tsananinsa.
Kuma wanda ya kunna wutar savani, ya ke iza ta, ba zai iya tattara abinda ya rarraba na lamarin wannan al'ummar ba, ko haxa kalmarta.
Haka kuma wanda ya ke kore mutane daga addini, da tsanantawa, ko kaushin rai.
Haka mai alfasha wanda ke ta'addaci ga mutane, da zaginsu.
Ko kuma maqiyin da ya ke shiga tsakanin zukatan da su ke guje wa juna, da sahu masu qara nisantar juna.
Haka mutumin da ke yin shisshigi wa ilimi, ya ke kukkutsawa cikin babin fatawa ba tare da ilimi, ko bin abu da tsanaki ba.
Haka wanda ya karkata da bin bidi'a da tatsuniyoyi ko qare-rayi.
Shi kuma savani, a fura'a da mas'alolin fiqihu ba sa hukunta gaba, ko rarrabar kalma da haxin kai, kuma savanin ba ya hukunta bidi'antarwa, ko fasiqantarwa, ko kafirta wanda ya sava wa (irin fahimtarka).
Kuma abinda ke wajaba a haqqin musulmi, shi ne, ya kirdadi ko ya riqa neman gaskiya, sannan ya xauki abin da dalili daga Alqur'ani da Sunnah su ka yi nuni akansa, koda kuwa ya sava wa mazhabarsa, da shehinsa ko malaminsa.
Kuma baya halatta ya riqi savani a cikin waxannan mas'alolin a matsayin wata hanya, ta yin jayayya, da faxa, da qaurace wa juna, da rabuwar kai.
Saboda magabatan kwarai (رضي الله عنهم) sun yi savani a mas'aloli masu yawan gaske, sai dai sashinsu bai kasance yana inkari wa sashi a mas'aloli da za a iya ijtihadi a cikinsu ba, kuma zukatansu sun kasance suna iya xaukar hakan; Imam As-Shafi'I yana cewa: ((Shin, ba zai yiwu mu kasance 'yan'uwan juna ba, koda kuwa ba mu yi ittifaqi a mas'ala ba ! !)).
Kuma dukkan zance, ko aikin da ya sava wa Sunnah ko ijma'i, to wajibi ne a yi inkarinsa. Kuma kowani zance a cikin mas'alar da babu Sunnah ko ijma'i a kanta, kuma ijtihadi na iya samun gurbi a cikinta, to ba a yin inkari ga wanda ya yi aiki, da ita, mujtahidi ne malami, ko kuma muqallidi (mabiyi).


Kuma baya halatta a bada fatawa da abinda ya ke sava wa nassin Qur'ani ko Sunnah, kuma zancen mujtahidi a irin wannan ya kan zama yasasshe, kuma haramun ne a yi taqlidi da mujtahid idan ya yi fatawa da abinda ya sava wa nassoshi na shari'a, kuma haramun ne ayi masa taqlidi; saboda cikin yin taqlidi ga mujtahidi a irin wannan akwai gabatar da maganarsa, akan maganar mai shari'a (Allah da ManzonSa), kuma yin hakan haramun ne, saboda babu ijtihadi a wurin da akwai nassi.
Kuma baya cikin hankali da hikima a ruro wutar husumomi a tsakanin mazhabobin Sunnah, alhalin maqiyan Sunnah suna yagan jikin wannan al'ummar da haqoransu, tare da qarfafawa na kai-tsaye da na bayan fage daga qasashe azzalumai.
Bayan kuma ya zo a cikin littafin Allah mabuwayi: "Kuma kadaku yi jayayya, sai ku raunata, sai qarfinku ya tafi" [Anfal: ].
Saboda yin jayayya na haifar da rauni da shanyewar vangare, da samun rinjaye daga maqiyi.
Kuma Manzon shiriya (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Musulmai jininsu yana daidaita, kuma wanda ya fi qaranta a cikinsu yana iya qulla alkawarinsu, kuma su hanu xaya ne ga wanda ba su ba".
Kuma manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wanda ya yi sallah irin tamu, ya kuma fiskanci alqiblarmu, ya ci abin yankarmu, to wannan shi ne musulmi, wannan, da alqawarin Allah da alqawarin Manzonsa su ke a kansa".


Amma ita kuma AQIDA To lallai haqiqa sahabbai sun yi ittifaqi akanta, kuma babu wani savani da ya auku a tsakaninsu a cikinta, ko jayayya.
Kuma dukkansu sun haxu wajen tabbatar da abinda littafin Allah ya zo da shi, da sunnar Manzo, ba tare da tawili ko kore wani abu ba, kuma ba tare da misaltawa ko kawo canji ba, kuma ba tare da qirqira ko yin bidi'a ba.
Kuma sahabbai (رضوان الله عليهم) sun kasance suna tsawatarwa kan yin bauta da bidi'oi da kuma qirqirarrun lamuran da Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) bai shar'anta su ba.


KUMA YANA DAGA CIKIN BIDI'OI QIRQIRARRU: Wanda wajibi ne a tsawatar akansu: Bidi'ar xawafin qaburbura, da yin yanka don kabari, da yin bakance wa qabari, da neman agajin ma'abutan qabari, da kuma bidi'ar wuce iyaka cikin waliyyai da salihai, ta hanyar ruku'i da qanqan-da-kai, da yin sujjada a gare su, da neman albarka cikin yawunsu da jikinsu.
Kuma qiyasin tabarruki da jikinsu, da lamarin yin tabarruki da mai sonmu abin so; annabi Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) a lokacin yana raye, wannan qiyasin varna ne, ta kowace fiska; saboda, da wani hankalin ne kuma, ko wani dalilin, za a yi qiyasin wani malami ko waliyyi, duk yadda ibadarsa ta kai, a yi qiyasinsa da shugaban mutane; Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) ? !


KUMA YANA DAGA CIKIN WAXANNAN BIDI'OIN: Bidi'ar yin rawa, da tsalle-tsalle, da karkaxa jiki, da kewayawa, da motsawa ta kowani sashe, a lokacin yin zikiri, a cikin masallatai, da waninsu, wanda hakan yana daga bidi'oin da wasu musulmai ke aukawa cikinsu, saboda jahilci, da taqlidanci.
Kuma dukan wannan, na daga abinda ya wajaba ayi inkarinsa, Sai dai, dole ya zama cikin hikima da wa'azi mai kyau, da zancen da maslahohi za su tabbatu da shi, dangogin varna kuma, a tunkuxe su da shi.


Kuma duk wanda ya auka cikin bidi'a ko varna, wajibi ne akansa ya dawo daga rakiyarsu, saboda komowa izuwa ga gaskiya shi ya fi alkhairi akan dawwama cikin varna.
Kuma babu abin da zai tattara kan mutane face littafin alqur'ani da Sunnah, a bisa fahimtar magabatan al'umma.
Kuma zance ba zai dace ba, sai tare da aiki.
Kuma zance da aiki ba za su dace ba, sai da niyyah.
Haka zance da aiki da niyya ba za su dace ba, face sun yi muwafaqa da Sunnah.



Ina faxan abinda kuke sauraro, kuma ina neman gafarar Allah, kuma sai ku nemi gafararSa; lallai shi ya kasance ga Masu komawa gare shi Mai yin gafara.



HUXUBA TA BIYU
Bayana haka:


Ya ku Musulmai!!
Ku kiyaye!
Sannan ku kiyaye!!
Saboda ba duk wanda ya nannaxa rawani akansa ba ne, ko ya yafa abaya a kafaxarsa ba ne, ko kuma ya zama mai kyan tufa, ya cancanci ya fito ya yi fatawa, ko a saurare shi, ko kuma a bi shi.
Sai ku nisanci bibiyan dayawa daga waxanda suka xaga sauti, ko su ka fito, ta hanyoyin sada zuminci na zamani, waxanda wautarsu da muninsu su ka bayyana daga rubuce-rubucensu, da bidiyoyinsu, saboda sau dayawa su kan yaxa sharri da varna, kuma su kan watsa qarya da abin qyama, kuma su kan faxi wauta da abin qi, Sai dai wanda Allah ya yi rahama a gare su, kuma su kaxan ne.


Kuma lallai waxannan hanyoyin sun wayi gari fili ne na sukuwar kowani marashin ilimin da bai mallaki komai ba, waxanda neman shahara ta ke jansu, qoqarin fitowa ko bayyana ya ke burge su, Wanda (sau dayawa) yawan masu bibiyansa ke ruxar da su, har su ke zaton cewa, babu wanda za a masa sakayya da irin sakayyarsu, kuma wai babu wani da zai iya tsayawa a matsayarsu. Kuma –wallahi- Mutum ya zama wanda ya ke sitirce, ta yadda idan bai halarci wuri ba, ba za a nemi shi ba, faqiri, voyayye, wanda ake rufe masa qofofi, shi ya fi alheri a gare shi, a kan ya kasance shahararre da aikin varna, wanda ya sanu da mummuna.


Ya ku 'yan jarida, da masu xago sauti !!
Ku bada kariya ga addininku, da qasarku; masarautar larabawa ta Saudiyya, kuma ku sanya alqaluman rubutunku cikin abinda zai qarfafi zaman lafiyanku, da haxin kanku, kuma ku nisanci duk abinda zai shuka fitina, da rashin tsari, ya kuma yi allura ga qasqantattun mutane ko wawaye.
Kuma ku nemi tabbaci da bin diddigi cikin duk abinda ku ke rubutawa, ko ku ke faxa.




Sai ku yi salati da sallama ga Ahmad Mai shiriya, Mai kuma ceton Mutane gabaxaya; saboda duk Mutumin da yayi masa salati guda xaya, Allah ta'alah zai yi masa guda goma,