طاهر جبريل دكو
_2 _October _2016هـ الموافق 2-10-2016م, 02:09 PM
بســــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــم الله الرحـــــــــــــــــــــــمن الرحــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــيم
يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تُقَدِّمُوا بَيْنَ يَدَيِ اللَّهِ وَرَسُولِهِ وَاتَّقُوا اللَّهَ إِنَّ اللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٌ (1)
Ya ku wadan da su ka yi imani, ka da ku sha gaban Allah da ManzonSa. Ku ji tsoron Allah, lallai Allah Mai ji ne Masani.
يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَرْفَعُوا أَصْوَاتَكُمْ فَوْقَ صَوْتِ النَّبِيِّ وَلَا تَجْهَرُوا لَهُ بِالْقَوْلِ كَجَهْرِ بَعْضِكُمْ لِبَعْضٍ أَنْ تَحْبَطَ أَعْمَالُكُمْ وَأَنْتُمْ لَا تَشْعُرُونَ (2)
Ya ku wadan da su ka yi imani, ka da ku daukaka muryoyinku sama da muryar Annabi kuma ka da ku bayyana Magana gare shi saboda ka da ayyukanku su rushe ba tare da kun sani ba.
إِنَّ الَّذِينَ يَغُضُّونَ أَصْوَاتَهُمْ عِنْدَ رَسُولِ اللَّهِ أُولَئِكَ الَّذِينَ امْتَحَنَ اللَّهُ قُلُوبَهُمْ لِلتَّقْوَى لَهُمْ مَغْفِرَةٌ وَأَجْرٌ عَظِيمٌ (3)
Lallai wadanda su ke runtse muryoyinsu a gurin Manzon Allah, wadannan su ne wadan da Allah Ya yalwata zukatansu da tsoron Allah. Su na da wata gafara da sakamako mai girma.
إِنَّ الَّذِينَ يُنَادُونَكَ مِنْ وَرَاءِ الْحُجُرَاتِ أَكْثَرُهُمْ لَا يَعْقِلُونَ (4)
Lallai wadanda su ke kwala ma ka kira daga bayan dakuna ma fi yawancin su ba su hankalta.
وَلَوْ أَنَّهُمْ صَبَرُوا حَتَّى تَخْرُجَ إِلَيْهِمْ لَكَانَ خَيْرًا لَهُمْ وَاللَّهُ غَفُورٌ رَحِيمٌ (5)
Kuma da za su yi hakuri har sai ka fito zuwa gare su lallai da ya fi alheri a gare su, Allah Mai gafara ne Mai jin kai.
يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِنْ جَاءَكُمْ فَاسِقٌ بِنَبَإٍ فَتَبَيَّنُوا أَنْ تُصِيبُوا قَوْمًا بِجَهَالَةٍ فَتُصْبِحُوا عَلَى مَا فَعَلْتُمْ نَادِمِينَ (6)
Ya ku wadan da su ka yi imani, idan wani fasiki ya zo mu ku da wani labari ku bi diddigi don tabbatarwa saboda ka da ku auka wa wasu bisa jahilci sai ku wayi gari ku na ma su nadama game da abin da ku ka aikata.
وَاعْلَمُوا أَنَّ فِيكُمْ رَسُولَ اللَّهِ لَوْ يُطِيعُكُمْ فِي كَثِيرٍ مِنَ الْأَمْرِ لَعَنِتُّمْ وَلَكِنَّ اللَّهَ حَبَّبَ إِلَيْكُمُ الْإِيمَانَ وَزَيَّنَهُ فِي قُلُوبِكُمْ وَكَرَّهَ إِلَيْكُمُ الْكُفْرَ وَالْفُسُوقَ وَالْعِصْيَانَ أُولَئِكَ هُمُ الرَّاشِدُونَ (7)
Kuma ku sani cewa lallai cikinku akwai Manzon Allah, da zai biye mu ku cikin yawancin al'amura da sai ku wahala, sai dai Allah Ya soyar da imani gare ku kuma Ya sanya – mu ku- kyamar kafirci da fasiqanci da sabo, wadancan su ne shiryayyu.
فَضْلًا مِنَ اللَّهِ وَنِعْمَةً وَاللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ (8)
Falala ce daga Allah da ni'ima. Allah Masani ne Mai hikima.
وَإِنْ طَائِفَتَانِ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ اقْتَتَلُوا فَأَصْلِحُوا بَيْنَهُمَا فَإِنْ بَغَتْ إِحْدَاهُمَا عَلَى الْأُخْرَى فَقَاتِلُوا الَّتِي تَبْغِي حَتَّى تَفِيءَ إِلَى أَمْرِ اللَّهِ فَإِنْ فَاءَتْ فَأَصْلِحُوا بَيْنَهُمَا بِالْعَدْلِ وَأَقْسِطُوا إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ الْمُقْسِطِينَ (9)
Idan wasu jama'a guda biyu su ka yaki juna, to ku sasanta tsakanin su. Idan daya ta yi zalunci akan 'yar uwarta sai ku yaki wacce ta yi zaluncin har sai ta koma kan umurnin Allah. Idan ta koma to ku sasanta tsakanin su bisa adalci, kuma ku yi adalci. Lallai Allah Ya na son ma su adalci.
إِنَّمَا الْمُؤْمِنُونَ إِخْوَةٌ فَأَصْلِحُوا بَيْنَ أَخَوَيْكُمْ وَاتَّقُوا اللَّهَ لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ (10)
Abin sani kawai, muminai 'yan uwan juna ne saboda haka ku sulhunta tsakanin 'yan uwanku biyu. Kuma ku ji tsoron Allah ko ayi mu ku rahama.
يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا يَسْخَرْ قَوْمٌ مِنْ قَوْمٍ عَسَى أَنْ يَكُونُوا خَيْرًا مِنْهُمْ وَلَا نِسَاءٌ مِنْ نِسَاءٍ عَسَى أَنْ يَكُنَّ خَيْرًا مِنْهُنَّ وَلَا تَلْمِزُوا أَنْفُسَكُمْ وَلَا تَنَابَزُوا بِالْأَلْقَابِ بِئْسَ الِاسْمُ الْفُسُوقُ بَعْدَ الْإِيمَانِ وَمَنْ لَمْ يَتُبْ فَأُولَئِكَ هُمُ الظَّالِمُونَ (11)
Ya ku wadan da su ka yi imani, ka da wasu su yi isgilanci ga wasu. Ya na yiwuwa su kasance ma fiya alheri sama da su. haka nan ma ka da wasu mata su yi isgilanci ga wasu matan saboda ta na iya yiwuwa su fi su alheri. Ka da ku yi zunden kawukanku kuma ka da ku rika jifan juna da lakubba. Tir da suna! Fasikanci bayan imani. Kuma duk wanda bai tuba ba to wadan nan su ne azzalumai.
يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اجْتَنِبُوا كَثِيرًا مِنَ الظَّنِّ إِنَّ بَعْضَ الظَّنِّ إِثْمٌ وَلَا تَجَسَّسُوا وَلَا يَغْتَبْ بَعْضُكُمْ بَعْضًا أَيُحِبُّ أَحَدُكُمْ أَنْ يَأْكُلَ لَحْمَ أَخِيهِ مَيْتًا فَكَرِهْتُمُوهُ وَاتَّقُوا اللَّهَ إِنَّ اللَّهَ تَوَّابٌ رَحِيمٌ (12)
Ya ku wadan da su ka yi imani, ku nisanci da yawa daga zato, lallai wani sashe na zato zunubi ne, ka da ku rika kwakkwafi, kuma ka da sashinku ya ci naman sashe. Yanzu dayan ku zai so ne a ce ya ci naman dan uwansa ya na matacce? Kun kyamaci hakan. Ku ji tsoron Allah. Lallai Allah Shi ne Mai yawan karban tuba Ma jin kai.
يَاأَيُّهَا النَّاسُ إِنَّا خَلَقْنَاكُمْ مِنْ ذَكَرٍ وَأُنْثَى وَجَعَلْنَاكُمْ شُعُوبًا وَقَبَائِلَ لِتَعَارَفُوا إِنَّ أَكْرَمَكُمْ عِنْدَ اللَّهِ أَتْقَاكُمْ إِنَّ اللَّهَ عَلِيمٌ خَبِيرٌ (13)
Ya ku mutane! Lallai Mu Mun halitta ku daga na miji da mace kuma mun sanya ku bangarori da kabilu saboda ku san juna. Lallai ma fi karimcin cikin ku a wurin Allah Shi ne ma fi tsoron Allah. Lallai Allah Mai ilimi ne –game da ku – kuma Ma sani- game da abin da ku ke kai .
قَالَتِ الْأَعْرَابُ آمَنَّا قُلْ لَمْ تُؤْمِنُوا وَلَكِنْ قُولُوا أَسْلَمْنَا وَلَمَّا يَدْخُلِ الْإِيمَانُ فِي قُلُوبِكُمْ وَإِنْ تُطِيعُوا اللَّهَ وَرَسُولَهُ لَا يَلِتْكُمْ مِنْ أَعْمَالِكُمْ شَيْئًا إِنَّ اللَّهَ غَفُورٌ رَحِيمٌ (14)
Mutanen kawye su ka ce mun yi imani. Ka ce ba ku yi imani ba tukunna sai dai ku ce mun mika wuya. Imani bai shiga zuciyarku ba tukunna. Idan ku ka yi wa Allah da ManzonSa da'a ba zai tawye mu ku komai ba daga ayyukanku. Lallai Allah Mai yawan gafara ne Mai jin kai.
إِنَّمَا الْمُؤْمِنُونَ الَّذِينَ آمَنُوا بِاللَّهِ وَرَسُولِهِ ثُمَّ لَمْ يَرْتَابُوا وَجَاهَدُوا بِأَمْوَالِهِمْ وَأَنْفُسِهِمْ فِي سَبِيلِ اللَّهِ أُولَئِكَ هُمُ الصَّادِقُونَ (15)
Abin sani kawai muminai su ne wadanda su ka yi imani da Allah da ManzonSa sa'annan ba su yi kokwanto ba kuma su ka yi jihadi don daukaka Kalmar Allah da dukiyoyinsu da rayukansu. Wadannan su ne ma su gaskiya.
قُلْ أَتُعَلِّمُونَ اللَّهَ بِدِينِكُمْ وَاللَّهُ يَعْلَمُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ وَاللَّهُ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ (16)
Ka ce: za ku sananr da Allah ne game da addininku, alhali Allah Ya na sanin abin da ke cikin sammai da kasa. Allah masani ne ga dukkan komai.
يَمُنُّونَ عَلَيْكَ أَنْ أَسْلَمُوا قُلْ لَا تَمُنُّوا عَلَيَّ إِسْلَامَكُمْ بَلِ اللَّهُ يَمُنُّ عَلَيْكُمْ أَنْ هَدَاكُمْ لِلْإِيمَانِ إِنْ كُنْتُمْ صَادِقِينَ (17)
Su na yi ma ka gori ne wai don sun Musulunta. Ka ce: ka da ku yi min gorin musuluncinku. A a! Allah ne zai goranta mu ku saboda Ya shiryar da ku zuwa ga imani in har kun kasance ma su gaskiya.
إِنَّ اللَّهَ يَعْلَمُ غَيْبَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَاللَّهُ بَصِيرٌ بِمَا تَعْمَلُونَ (18)
Lallai Allah Ya na sanin abin da ya faku a cikin sammai da kasa. Kuma Allah Mai gani ne ga abin da ku ke aikatawa.