طاهر جبريل دكو
_25 _September _2016هـ الموافق 25-09-2016م, 02:59 PM
Huduba
Hudubar Juma'a daga Masallacin Annabi (SAW), 15/zulhijjah/1437h
Mai huduba/ Shehin Malami Dr. Abdulbariy Al-Subsitiy
Bayan haka:
Ragowar aiyukan hajji sun kusanci karewa, Tawagogin Mahajjata su kuma sun fara daddaure kayayyakindu don komawa garurruka ko kasashensu, bayan gama hajji a wannan lokaci mai tarin nasara,wanda ya cika da tarin hidimomi da suka kammala, da kuma nasarori masu girma, da kuma aiyuka wanda dukkan bangarori na hukuma (wato: ma'aikatu) suka yi aiki tukuru akansu, tare da bunkasa tunani-tunanin zamanin, don ganin sun yi hidima ga masu ziyara da mahajjata; Don haka; Allah ya yi sakayyar alkhairi ga shugabannin wannan kasa, wadanda suka kashe dukiya a yalwace, kuma suka zuba ido a lokacin gudanar da aiyukan ... kuma (Allah) ya yi albarka ga mazaje masu gaskiya da su ka aikata aikin daukaka, da kyautata tsare-tsaren hajji, sai suka mayar da sharewar da take ta haushi kurame, wadanda su ke munana surar nagartattun abubuwa, su ke kuma kirkiro labarun abubuwan karya, Shi hasken rana idan ya fito, hannu baya boye shi.
Hakika Allah ya yi mana ni'imar lokutan da'a, wadanda alherorinsu suke bibiyar juna, kuma a cikinsu rahamomin Ubangiji (سبحانه) suke lullube mu, da kuma gafara,,,
Daga cikin wadanda aka yi musu gamda-katar ko dace -Allah ya ya sanya mu daga cikinsu mu da ku- akwai wanda ya koma kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi (shi ne wanda ya yi hajj mabruur),
Daga cikinsu kuma akwai mutumin da Allah ya gafarta masa zunuban shekaru biyu...(shine mutumin da yayi azumin yinin arfa kenan)
Wancan ita ce martaba madaukakiya wanda mutanen da aka yi musu dace su ka kai izuwa gare ta, kuma sabuwar farar fefa mai tsarki wacce mutanen da suka zage damtse su ka same ta, ta kan tattara tunanin mai hankali, ta sanya shi yin aiki don kiyaye wannan daukaka, da kokarin wanzuwa akan wannan matsayi na daukaka, wanda da shi ne zai samu daukakar gafara, da tatacciyar rahama.
Aiyukan masu takawa a kowani lokaci shine tunkude munanan aiyuka da kyawawa, Allah (تعالى) yana cewa:
Lallai kyawawa suna tafiyar da munana.
kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
Kuma ka bi bayan mummuna da aikata kyakkyawa. Tirmiziy da Hakim su ka ruwaito shi.
Kokarin tsarkaka na yau da kullum, daga daudodin rayuwa, da dawwamammen tsarkake takardar aiki basa karewa, da karewar lokutan ibadu na musamman, kuma lamarinsu baya takaituwa da wani wuri kebantacce (kamar Makka da arfa, da Madina), ko da wani lokaci sananne (kamar: kwanaki goman zulhijja); wannan kuma kasancewar shu'umcin yin zunubai ya kan gadar da hana bawa aikata wani alkhairi, kuma ya haifar masa da tabewa, kuma lallai dabaibayin zunubai yana hana bawa tafiya zuwa ga biyayyar Allah, ko ya hana bawa gaggawa izuwa ga hidimar Ubangijinsa, kuma lallai nauyin zunubai su kan sanya mutum jin nauyin aikata alkhairori, da ko su hana shi jin nashadi lokacin biyayya, Kuma don haka ne, Musulmi ya ke neman aiyukan da suke kankare zunubai, suke kuma daga darajoji, domin ya tsarkake ransa, yana cikiyar samun tsarkaka da daukaka.
YANA DAGA CIKIN MANYAN SABUBAN SAMUN GAFARA Tauhidin Allah da kadaita shi cikin bauta; saboda duk wanda ya tabbatar da kalmar tauhidi a cikin zuciyarsa, to sai ta fitar masa so, da girmama, ko ganin kwarjinin duk abinda ba Allah ba, daga nan kuma sai zunubansa da kura-kurensa su kokkone, gabadayansu, koda sun kai kamar kunfan teku, kai wani lokacin suna ma iya juya zunuban zuwa ga aiyuka kyawawa.
Kuma ana kankare zunubai: Da yin guzurin bin dokokin Allah ko takawa, wanda shine mafi alherin guzuri, Allah ta'alah yana cewa:
Duk wanda ya yi takawar Allah yana kankare masa munanan aiyukansa, kuma sai ya girmama masa lada.
Kuma Allah (تعالى) yana cewa:
Ya ku wadanda su ka imani idan har kun bi dokokin Allah da takawa zai sanya muku ma'auni, kuma zai kankare munanan aiyukanku kanana, kuma ya gafarta muku, lallai ne Allah ma'abucin falala ne mai girma.