تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : Hadisai arba'in (40) kan halayyar musulunci da ladduba أربعون حديثا تتعلق بالأخلاق الإسلامية والآداب


طاهر جبريل دكو
_9 _September _2016هـ الموافق 9-09-2016م, 07:01 PM
2016/09/07

HADISAI ARBA'IN (40) KAN HALAYYAR MUSULUNCI DA LADDUBA أربعون حديثا تتعلق بالأخلاق الإسلامية والآداب (http://abubakarhamza.blogspot.com.ng/2016/09/hadisai-arbain-40-kan-halayyar.html)






















HADISAI ARBA'IN (40)
KAN HALAYYAR MUSULUNCI DA LADDUBA
أربعون حديثا تتعلق بالأخلاق الإسلامية والآداب
















TATTARAWAR DA TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA




بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشرف المرسلين، وعلى آله وصحبه أجمعين، أما بعد:
فهذه طائفة كبيرة من الآثار النبوية التي تتعلق بالأخلاق التي رغب إليها الإسلام، والتي حذر منها، وبالآداب الإسلامية، والله أسأل القبول والإخلاص.


Babu magana, babu tura wani sako, ko alamar jin dadi ko burgewa, KAWAI, hadisi ne guda daya zan turo, a group dinku, mai taken: DAGA TASKAR MA'AIKI (صلى الله عليه وسلم), Duk wanda yake son yayi magana da Admin; wato: Abubakar Hamza Misau akan wannan zaure, to sai ya turo wasika a "pravet", Kuma ba zan kawo hadisi a wannan zauren ba, Sai wanda ya inganta daga Manzon Allah (S.A.W), ta yadda zaka iya dauka Kai-tsaye ka yi aiki da shi, Saboda *KARATUN HADISI DA AIKI DA SHI, SHINE: TSIRA* Kuma za a iya yada su, a sauran zauruka domin, mu samu mu rabauta da yin aiki da hadisin, da ke cewa: *Ku isar daga gare ni, ko da aya ce guda*. Idan kuma hadisan suka taru; suka yi yawa: zamu tattara su a cikin wani littafi. Allah yayi mana albarka, mu da zurriyarmu gabadaya, Amin.
Lura da shawara mai muhimmanci da Na samu, Na fifita Samar da "Broadcast list" maimakon group Dana bude. Don haka, kowa zai ga sakon hadisi, Na kullum da Nayi bayani ta pravet nasa, ba a group ba, Shi kuma group din zan fitar da kowa daga cikinsa, Sannan Na goge shi.. .. .. Afwan, Na gode muku matuka






الحديث الأول:


عن عُمَرَ بْنَ الْخَطَّابِ رضي الله عنه قال: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، يَقُولُ: إِنَّمَا الأَعْمَالُ بِالنِّيَّاتِ، وَإِنَّمَا لكل امْرِئٍ مَا نَوَى، فَمَنْ كَانَتْ هِجْرَتُهُ إِلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ فَهِجْرَتُهُ إِلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ، وَمَنْ كَانَتْ هِجْرَتُه لدُنْيَا يُصِيبُهَا، أَوِ امْرَأَةٍ يَنْكِحُهَا فَهِجْرَتُهُ إِلَى مَا هَاجَرَ إِلَيْهِ.


متفق عليه (خ: ١، م: ١٩٠٧).

HADISI NA FARKO:

An ruwaito daga Umar dan Alkhaddabi (r.a) ya ce: Na ji Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: *Dukkan aiyuka suna tare da niyya, kuma lallai kowane mutum yana samun sakamakon abinda yayi niyya; Wanda hijirarsa ta kasance saboda Allah ne da Manzonsa to sakamakon hijirarsa tana ga Allah da Manzonsa. Wanda kuma hijirarsa ta kasance saboda wata duniya ce da zai same ta, ko kuma wata matar da zai aure ta, to sakamakon hijirarsa yana ga abinda yayi hijira dominsa*.

Bukhariyy [1], da Muslim [1907] suka ruwaito shi.


الحديث الثاني:


عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَال:َ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّم:َ *إِنَّ اللَّهَ لا يَنْظُرُ إِلَى صُوَرِكُمْ وَأَمْوَالِكُمْ، وَلَكِنْ يَنْظُرُ إِلَى قُلُوبِكُمْ وَأَعْمَالِكُمْ*.


رواه مسلم (٢٥٦٤).

HADISI NA BIYU:


An ruwaito daga Abu-hurairah (r.a) ya ce: Manzon Allah (s.a.w) ya ce: *Lallai ne Allah baya yin dubi izuwa ga surar jikinku da dukiyoyinku, Saidai yana yin dubi ne izuwa ga zukatanku, da aiyukanku*.

Muslim [2564] ya ruwaito shi.




Saboda hadisai biyu, da suka gabata, Sai mu tsayu Wajen gyara niyyoyinmu, da zukatanmu, da aiyukanmu, Allah ya taimake mu, Amin.


الحديث الثالث:


عن أَنَس رضي الله عنهٍ‏:‏ قَالَ‏:‏ كَانَ رَسُول اللَّه ِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَحْسَنَ النَّاسِ خُلُقًا.


متفق عليه (خ: ٦٢٠٣، م: ٢٣١٠).

HADISI NA UKU:

An ruwaito daga Anas (r) ya ce: *Manzon Allah ya kasance yafi dukkan Mutane kyan hali*.

Bukhariyy [6203], da Muslim [2310] suka ruwaito shi.


الحديث الرابع:


عن عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرٍو رضي الله عنهما أنه ذكر رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَال: *لمْ يَكُنْ فَاحِشاً وَلَا مُتَفَحِّشًا*. وَقَالَ، قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: *إِنَّ مِنْ خِياركُمْ أَحاسنَكُمْ أخْلُاقًا*.


متفق عليه (خ: ٣٥٥٩ م: ٢٣٢١).

HADISI NA HUDU:

An ruwaito daga Abdullahi bn Amrin -Allah ya kara yarda a gare su- lallai ne shi ya ambaci Manzon Allah (S.A.W) sai ya ce: *Manzon Allah bai kasance mutum mai aikata ko fadin yasassun zantuka ba, kuma bai kasance mai kakalar hakan ba*. Sannan ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: *Lallai ne zababbu a cikinku sune wadannan da suka fi kyan hali*.

Bukhariy [3559], da Muslim [2321] suka ruwaito shi.




الحديث الخامس:


عن أبي هريرة رضي الله عنه، قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: *أَكْمَلُ الْمُؤْمِنِينَ إِيمَانًا أَحْسَنُهُمْ خُلُقًا، وَخِيَارُكُمْ خِيَارُكُمْ لِنِسَائِهِمْ خُلُقًا*


رواه أبو داود: برقم: ٤٦٨٢، والترمذي، رقم: ١١٦٢، وقال: حديث حسن صحيح.

HADISI NA BIYAR:

An ruwaito daga Abu-Hurairah -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: *Muminin da yafi Muminai cikar imani shine wanda ya fi su kyan hali. Zababbun cikinku kuma, sune wadanda suka fi kyan hali ga matansu*.

Abu-Dawud [4682], da Tirmiziy [1162] suka ruwaito shi. Tirmiziy ya ce: *Hadisi ne mai kyau ingantacce*


الحديث السادس:


عن أبي هريرة رضي الله عنه، قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: *الْإِيمَانُ بِضْعٌ وَسَبْعُونَ -أَوْ بِضْعٌ وَسِتُّونَ- شُعْبَةً، فَأَفْضَلُهَا قَوْلُ: لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، وَأَدْنَاهَا إِمَاطَةُ الْأَذَى عَنْ الطَّرِيقِ، وَالْحَيَاءُ شُعْبَةٌ مِنْ الْإِيمَانِ* .


متفق عليه (خ: ٩ م: ٣٥).


HADISI NA SHIDA:

An ruwaito daga Abu-Hurairah -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: *Imani ressa ne guda saba'in da doriya, ko kuma ya ce: sittin da doriya, Mafi girma daga cikinsu shine: Fadin LA ILAHA ILLAL LAHU. Wanda kuma yafi kankanta shine: Gusar da ABU MAI CUTARWA daga hanya. Itama KUNYA reshe ne daga ressan imani*.

Bukhariy [9], da Muslim [35] suka ruwaito shi.


الحديث السابع:


عن عمران بن حصين رضي الله عنه قال: قال رَسُول اللَّهِ صَلَّى الله عليه وسلم: *الحياء لا يأتي إلا بخير*.
متفق عليه (خ: 6117م: 37).
وفي رواية لمسلم: *الحياء خير كله*.
HADISI NA BAKWAI:

An ruwaito daga Imrana bn Husaini -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Manzon Allah -Sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: *Kunya ba ta zuwa face da alkhairi*.

Bukhariy [6117], da Muslim [37] suka ruwaito shi.

A wata riwaya ta Muslim *Kunya dukkanta alheri ne*.


الحديث الثامن*:
عن أَبِي ذرٍّ؛ جُنْدَبِ بنِ جُنَادَةَ رضي اللَّه عنه قال: قال لي النبيُّ صلى اللَّه عليه وآله وسلم : «لاَ تَحقِرنَّ مِن المعْرُوفِ شَيْئاً ولَوْ أنْ تلْقَى أخَاكَ بِوجهٍ طلقٍ».
رواه مسلم (2626).

*HADISI NA TAKWAS*
An ruwaito daga Abu-Zarrin; wato: Jundub bn Junada -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Manzon Allah -Sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce mini: *Kada ka raina kyakkyawan abu, koda kuwa ka hadu da 'dan'uwanka ne da fiska sakakkiya*.
Muslim [2626] ya ruwaito shi.


الحديث التاسع*:
عَنْ أَبِي ذَرٍّ رَضِيَ اللَّهُ تَعَالَى عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «تَبَسُّمُكَ فِي وَجْهِ أَخِيكَ لَكَ صَدَقَةٌ».
رواه التِّرْمِذِيُّ: ( 1956).

*HADISI NA TARA*
An ruwaito daga Abu-Zarrin; -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Manzon Allah -Sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: *Murmushinka ga fiskar 'dan'uwanka, a gare ka: sadaka ne*.
Tirmiziy [1956] ya ruwaito shi, da Ibnu-Hibbana [474, da 529], Tirmiziy ya ce: Hadisi ne mai kyau (hasan) .


*الحديث العاشر*
عن ابن عبَّاس رضي الله عنهما قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم للأشجِّ -أشجِّ عبد القيس-: «إِنَّ فِيكَ خَصْلَتَيْنِ يُحِبُّهُمَا اللهُ: الْحِلْمُ، وَالأَنَاةُ»، رواه مسلم.

*HADISI NA GOMA*
An ruwaito daga Abdullahi bn Abbas; -Allah ya kara yarda a gare su- ya ce: Manzon Allah -Sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce wa Ashajju; wato: Ashajju na kabilar Abdulkais *Lallai ne a tattare da kai akwai sifofi guda biyu; da Allah ya ke sonsu; Su ne: Hakuri da nitsuwa*.
Muslim [17] ya ruwaito shi.


الحديث الحادي عشر*
عن عائشة رضي الله عنها، أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: *إِنَّ اللَّه رَفِيقٌ َ يُحِبُّ الرِّفْقَ فِي الأَمْرِ كُلِّهِ*، رواه البخاري [6927].


وأخرجه مسلم [2593] بلفظ:
*إِنَّ اللَّهَ رَفِيقٌ يُحِبُّ الرِّفْقَ، وَيُعْطِي عَلَى الرِّفْقِ مَا لا يُعْطِي عَلَى الْعُنْفِ، وَمَا لا يُعْطِي عَلَى مَا سِوَاهُ*.

*HADISI NA GOMA SHA DAYA*
An ruwaito daga A'isha -Allah ya kara yarda a gare ta- Lallai Manzon Allah -Sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: *Lallai ne Allah mai tausasawa ne; yana son tausasawa a cikin dukkan al'amura*.
Bukhariy [6927] ya ruwaito shi.

Kuma Muslim ya fitar da hadisin [2593] da lafazin:
*Lallai Allah mai tausasawa ne; yana son tausasawa, Kuma Allah yana bayarwa a kan tausasawa* -na yabo da sakamako mai girma, a duniya da lahira- *irin abinda baya bayarwa a kan tsanantawa, da kuma irin abinda baya bayarwa a kan wasu sifofin* -kyawawa; wadanda ba shi ba-.


الحديث الثاني عشر*
عن عَائِشَةَ رضي الله عنها، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: *إِنَّ الرِّفْقَ لا يَكُونُ فِي شَيْءٍ إِلا زَانَهُ، وَلا يُنْزَعُ مِنْ شَيْءٍ إِلا شَانَهُ* أخرجه مسلم [برقم: 2594].

*HADISI NA GOMA SHA BIYU*
An ruwaito daga A'isha -Allah ya kara yarda a gare ta- Lallai Manzon Allah -Sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: *Lallai tausasawa baya kasancewa cikin wani abu, face ya kawata shi. Kuma ba a cire tausasawa daga wani abu, face ya munata shi* (ya bar shi da aibi).
Muslim [2594] ya ruwaito shi.


الحديث الثالث عشر*
عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِك رضي الله عنهٍ،
عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: *يَسِّرُوا وَلاَ تُعَسِّرُوا، وَبَشِّرُوا وَلاَ تُنَفِّرُوا*، متفق عليه [خ: برقم: 69، م: برقم: 2593].

*HADISI NA GOMA SHA UKU*
An ruwaito daga Anas -Allah ya kara yarda a gare shi- daga Manzon Allah -Sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: *Ku saukaka; kada ku tsananta, kuma ku yi bushara; kada ku yi abinda zai kori mutane*.
Bukhariy [69] da Muslim [1734] su ka ruwaito shi.


الحديث الرابع عشر*
عَنْ عَائِشَةَ رضي الله عنها، قَالَتْ: *مَا ضَرَبَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ شَيْئًا قَطُّ بِيَدِهِ، وَلا امْرَأَةً، وَلا خَادِمًا، إِلا أَنْ يُجَاهِدَ فِي سَبِيلِ اللَّهِ، وَمَا نِيلَ مِنْهُ شَيْءٌ قَطُّ فَيَنْتَقِمَ مِنْ صَاحِبِهِ، إِلا أَنْ يُنْتَهَكَ شَيْءٌ مِنْ مَحَارِمِ اللَّهِ، فَيَنْتَقِمَ لِلَّهِ عز وجل*. رواه مسلم [ رقم: 2328].

HADISI NA GOMA SHA HUDU
An ruwaito daga A'isha -Allah ya kara yarda a gare ta- ta ce: *Kwata-kwata Manzon Allah -Sallal lahu alaihi wa sallama- bai taba dukan wani abu da hannunsa ba; kuma be taba dukan wata Mata ko wani hadimi ba, Saidai idan zai yi jihadi fiySabilil lahi. Kuma ba a taba cutar da shi -cikin zance ko aiki- da wani abu ba, Sai ya dauki fansa daga wanda ya cutar da shi, Saidai idan an keta wani abu na alfarmar Allah; Sai ya daukar wa Allah Mabuwayi da daukauka fansa*.
Muslim [2328] ya ruwaito shi.


الحديث الخامس عشر*
عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله عنه، قَالَ: *كُنْتُ أَمْشِي مَعَ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَعَلَيْهِ رِدَاءٌ نَجْرَانِيٌّ غَلِيظُ الْحَاشِيَةِ، فَأَدْرَكَهُ أَعْرَابِيٌّ، فَجَبَذَهُ بِرِدَائِهِ جَبْذَةً شَدِيدَةً نَظَرْتُ إِلَى صَفْحَةِ عُنُقِ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، وَقَدْ أَثَّرَتْ بِهَا حَاشِيَةُ الرِّدَاءِ مِنْ شِدَّةِ جَبْذَتِهِ، ثُمَّ قَالَ: يَا مُحَمَّدُ مُرْ لِي مِنْ مَالِ اللَّهِ الَّذِي عِنْدَكَ، فَالْتَفَتَ إِلَيْهِ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَضَحِكَ، ثُمَّ أَمَرَ لَهُ بِعَطَاءٍ*.
متفق عليه
[خ: رقم: 5809، م: 1057].

*HADISI NA GOMA SHA BIYAR*
An ruwaito daga Anas -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: *Na kasance ina tafiya tare da Manzon Allah* -sallal lahu alaihi wa sallama- *alhalin a jikinsa akwai mayafi dan garin Najran, mai kaushin gefe, Sai wani Bakauye ya riske shi, sannan ya fizge shi da mayafinsa fizga mai tsanani*. Anas ya ce: Da na yi dubi zuwa jikin wuyan Manzon Allah -Sallal lahu alaihi wa sallama- sai ga mayafin ya bar wata alama; saboda tsananin fizgar da aka yi masa, Sa'annan sai bakauyen ya ce: *Ya Muhammadu! Bani daga dukiyar Allah da take wurinka!* *Sai Manzon Allah ya juya izuwa gare shi, sai ya yi dariya, sa'annan ya yi umurnin a bashi kyauta*.
Bukhariy [5809] da Muslim [1057] su ka ruwaito shi.


الحديث السادس عشر*
عن سُلَيْمَانَ بْنِ صُرَدٍ رضي الله عنه، قَالَ: اسْتَبَّ رَجُلانِ عِنْدَ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّم ٌفجعل َأَحَدُهُمَا تحمر عيناه وتنتفخ أوداجه، فَقَالَ رسول اللهُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: *إِنِّي لأَعْرف كَلِمَةً لَوْ قَالَهَا لَذَهَبَ عَنْهُ الذي يَجِدُ؛ أَعُوذُ بِاللَّهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ* متفق عليه
[خ: 6115رقم: ، م: 2610].

*HADISI NA GOMA SHA SHIDA*
An ruwaito daga Sulaiman bn Surad -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: *Wasu mazaje biyu sun yi zage-zage a wurin Annabi* -sallal lahu alaihi wa sallama- Sai 'Daya daga cikinsu idanunsa biyu suka yi ja, jijiyoyin wuyansa kuma su ka kukkunburo, Sai Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: *Lallai ne na san wata kalmar da ya fade ta, to da abinda ya ke ji, ya tafi; ita ce: A'UZU BILLAHI MINA AL-SHAIDANI AL-RAJIM*.
Bukhariy [6115] da Muslim [2610] su ka ruwaito shi.


الحديث السابع عشر*
عَنْ أَبي هُرَيْرَةَ رَضِيَ الله عنه، أَنَّ رسُولَ الله صلى الله عليه وسلم قَالَ: *لَيسَ الشَّديدُ بِالصُّرَعَةِ،إِنَّمَا الشَّديدُ الَّذِي يَمْلِكُ نَفْسَهُ عِنْدَ الْغَضَبِ*. متفق عليه
[خ: رقم: 6114 ، م: 2609].

*HADISI NA GOMA SHA BAKWAI*
An ruwaito daga Abu-Hurairah -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Lallai Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: *Ba wai mai karfi shine jarumi ba (Wanda ke yawaita kayar da Mutane), Lallai mai karfi shine wanda ke mallakar ransa a lokacin fushi*.
Bukhariy [6114] da Muslim [2609] su ka ruwaito shi.


الحديث الثامن عشر*
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه، أَنَّ رَجُلاً قَالَ لِلنَّبِيِّ صلى الله عليه وسلم: أَوْصِنِى، قَالَ: *لاَ تَغْضَبْ*، فَرَدَّدَ مِرَارًا، قَالَ: *لاَ تَغْضَب*ْ.
رواه البخاري[ 6116].

*HADISI NA GOMA SHA TAKWAS*
An ruwaito daga Abu-Hurairah -Allah ya kara yarda a gare shi, Lallai wani mutum ya ce wa Annabi -sallal lahu alaihi wa sallama- Ka min wasiyya, Sai ya ce: *Kada ka yi fushi* Sai ya maimaita tambayar dayawa, Sai ya ce: *Kada ka yi fushi*.
Bukhariy [6116] ya ruwaito shi.


الحديث التاسع عشر*
عَنْ عَيَّاضِ بْنِ حِمَارٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: قَال رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: *إِنَّ اللَّهَ أَوْحَى إِلَيَّ أَنْ تَوَاضَعُوا؛ حَتَّى َلا يفخر أَحَدٌ عَلَى أَحَدٍ، وَلا يبغي أَحَدٌ عَلَى أَحَد*"،
أَخْرَجَهُ مُسْلِمٌ [ 2865].

*HADISI NA GOMA SHA TARA*
An ruwaito daga Iyadh bn Himar -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: *Lallai ne Allah ya yi wahayi zuwa gare ni; cewa: Ku kaskantar da kai; har ya kasance wani mutum ba ya yin alfahari ga wani, kuma wani ba ya yin ta'addanci ko zaluntar wani*.
Muslim [2865] ya ruwaito shi.


الحديث العشرون
عنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه، عَنْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهم عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: *مَا نَقَصَتْ صَدَقَةٌ مِنْ مَالٍ، وَمَا زَادَ اللَّهُ عَبْدًا بِعَفْوٍ إِلا عِزًّا، وَمَا تَوَاضَعَ أَحَدٌ لِلَّهِ إِلا رَفَعَه اللهُ*
أَخْرَجَهُ مُسْلِمٌ [ 2588].

*HADISI NA ASHIRIN*
An ruwaito daga Abu-Hurairah -Allah ya kara yarda a gare shi-, Daga Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: *Babu wata sadaka da ta ke tauye dukiya, Kuma idan bawa ya yi afuwa, Allah baya masa kari, face izza* (da daukaka), *Kuma wani ba zai yi tawali'u, don Allah ba* (wato:kaskantar-da-kai), *face Allah ya daukaka shi*.
Muslim [2588] ya ruwaito shi.


الحديث الحادي والعشرون*
عَنِ الأَسْوَدِ بن يزيد، قَالَ: سَأَلْتُ عَائِشَةَ رضي الله عنها: مَا كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَصْنَعُ فِي بَيْتِهِ؟ قَالَتْ: *كَانَ يَكُونُ فِي مِهْنَةِ أَهْلِهِ* -تَعْنِي خِدْمَةَ أَهْلِهِ- *فَإِذَا حَضَرَتِ الصَّلاَةُ خَرَجَ إِلَى الصَّلاَةِ* .
أَخْرَجَهُ البخاري [676] .

*HADISI NA ASHIRIN DA DAYA*
An ruwaito daga Aswad bn Yazid, ya ce: Na tambayi A'isha -Allah ya kara yarda a gare ta-; cewa: Yaya Annabi -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ke kasancewa a cikin gidansa? Sai ta ce: *Ya kan kasance cikin aiki wa iyalansa* -Tana nufin: *Cikin yin hidima ga iyalansa*- *Idan kuma salla ta halarto, Sai ya fita izuwa ga sallah*.
Bukhariy [676] ya ruwaito shi.


الحديث الثاني والعشرون*
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه: *كُلُّ سُلاَمَى مِنَ النَّاسِ عَلَيْهِ صَدَقَةٌ كُلَّ يَوْمٍ تَطْلُعُ فِيهِ الشَّمْسُ، يَعْدِلُ بَيْنَ الاِثْنَيْنِ صَدَقَةٌ، وَيُعِينُ الرَّجُلَ عَلَى دَابَّتِهِ فَيَحْمِلُ عَلَيْهَا أَوْ يَرْفَعُ عَلَيْهَا مَتَاعَهُ صَدَقَةٌ، وَالكَلِمَةُ الطَّيِّبَةُ صَدَقَةٌ، وَكُلُّ خُطْوَةٍ يَخْطُوهَا إِلَى الصَّلاَةِ صَدَقَةٌ، وَيُمِيطُ الأَذَى عَنِ الطَّرِيقِ صَدَقَة* متفق عليه
[خ: رقم: 2989 م: 1009].

*HADISI NA ASHIRIN DA BIYU*
An ruwaito daga Abu-Hurairah -Allah ya kara yarda a gare shi ya ce: Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: *Kowace gaba a jikin mutane akwai sadaka a kanta, a kowani yinin da rana ta fudo a cikinsa, Ya yi sulhu ko adalci tsakanin mutane biyu sadaka ne, Ya taimaki mutum a kan dabbarsa; sai ya dora a kanta, ko ya sauke masa kayansa daga kanta sadaka ne, Fadar kalma daddada sadaka ne, Kuma dukkan taku da zai taka izuwa ga sallah sadaka ne, Kuma ya gusar da abu mai cutarwa daga kan hanya sadaka ne*.
Bukhariy [2989] da Muslim [1009] su ka ruwaito shi.

Akwai gabbai da suka kai 360 a jikin dan'adam, kuma akwai sadaka akan kowane daya daga cikinsu; idan ya wayi-gari, Saidai kuma yin sallar walaha ta kan isar ga hakan. Kamar yadda hadisi ya tabbatar wadannan bayanan. *Godiya ta tabbata ga Allah*.


الحديث الثالث والعشرون
عن أُمَّ كُلْثُومٍ بِنْتِ عُقْبَةَ رضي الله عنها، أَنَّهَا سَمِعَتْ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: *لَيْسَ الْكَذَّابُ الَّذِي يُصْلِحُ بَيْنَ النَّاس فَيَنْمِي خَيْرًا ِ وَيَقُولُ خَيْرًا*
أَخْرَجَهُ البخاري [2692] ومسلم [2605] .

*HADISI NA ASHIRIN DA UKU*
An ruwaito daga UmmuKulthum 'yar Ukbatu -Allah ya kara yarda a gare ta-; lallai ita, ta ji Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- yana cewa: (Ko, ya yi karya) *Ba Mai karya ba ne; Wanda ke sulhunta tsakanin mutane; sai ya nufi alkhairi, ko ya fadi alheri*.
Bukhariy [2692] da Muslim [2605] su ka ruwaito shi.

Hadisin na nuna muhimmancin yin sulhi tsakanin bangarori guda biyu na musulmai; (kamar miji da mata), koda hakan zai hukunta ya yi karya. matukar babu wata hanyar idan ba ita ba.


الحديث الرابع والعشرون*
عن أَبِي مُوسَى الأشعري رضي الله عنه، قَالَ: كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذَا جَاءَهُ السَّائِلُ أَوْ طلبت إليهُ ْحَاجَةِ قَالَ: *اشْفَعُوا تُؤْجَرُوا، وَيَقْضِي اللَّهُ عَلَى لِسَانِ نَبِيِّهِ مَا شَاءَ*،
أَخْرَجَهُ البخاري [1432] ومسلم [2627] .

*HADISI NA ASHIRIN DA HUDU*
An ruwaito daga Abu-Musa Al-ash'ariy -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya kasance idan mai rokon wani abu ya zo masa, ko aka nemi wata bukata daga wurinsa, ya kan ce: *Ku yi ceto* -ta hanyar bayanin muhimmancin biyan wannan bukatar- *za ku samu lada. Allah* Mabuwayi da daukaka *shi kuma, zai hukunta abinda ya nufa a harshen AnnabinSa -S.A.W-* -na biyan wannan bukatar, ko akasin haka-.
Bukhariy [1432] da Muslim [2627] su ka ruwaito shi.


الحديث الخامس والعشرون*
عَن ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما، في قصة بَرِيرَةَ وزَوجها ... قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّم:َ *لَوْ رَاجَعْتِيه...*ِ قَالَتْ: يَا رَسُولَ اللَّهِ أَتَأْمُرُنِي؟ قَال:َ *إِنَّمَا أَنَا أشفع* قَالَت:ْ لا حَاجَةَ لِي فيه.
أَخْرَجَهُ البخاري [1432].

*HADISI NA ASHIRIN DA BIYAR*
An ruwaito daga Abdullahi bn Abbas -Allah ya kara yarda a gare su- a kissar Barirah da Mijinta... Annabi -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: *Da kin koma karkashinsa?* Ta ce: Ya Ma'aikin Allah, Shin umurni ka ke ba ni? Sai ya ce: *A,a, Ni kawai mai neman ceto ne*, Sai ta ce: To, Bani da bukatarsa.
Bukhariy [5283] ya ruwaito shi.


الحديث السادس والعشرون
عن عبد الله بن عمر رضي الله عنهما، أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: *الْمُسْلِمُ أَخُو الْمُسْلِمِ لا يَظْلِمُهُ وَلا يسلُمُهُ، ومَنْ كَانَ فِي حَاجَةِ أَخِيهِ كَانَ اللَّهُ فِي حَاجَتِهِ، وَمَنْ فَرَّجَ عَنْ مُسْلِمٍ كُرْبَةً فَرَّجَ اللَّهُ عَنْهُ كُرْبَةً مِنْ كُربات يَوْمِ الْقِيَامَةِ، وَمَنْ سَتَرَ مُسْلِمًا سَتَرَهُ الله يوم القيامة*
أَخْرَجَهُ البخاري [2442] ومسلم [2580] .

*HADISI NA ASHIRIN DA SHIDA*
An ruwaito daga Abdullahi bn Umar -Allah ya kara yarda a gare su, lallai Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: *Musulmi dan'uwan musulmi ne; baya zaluntarsa, baya tabar da shi, Wanda ya kasance cikin bukatar dan'uwansa, Allah zai kasance cikin bukatarsa, Duk kuma wanda ya yaye wa musulmi wani bakin ciki, to Allah zai yaye masa wani bakin ciki daga tarin bakin cikin yinin kiyama, Wanda kuma ya rufa asiri wa Musulmi, Allah zai rufa masa asiri a ranar kiyama*.
Bukhariy [2442] da Muslim [2580] su ka ruwaito shi.


الحديث السابع والعشرون*
عَنْ أَنَس بْن مَالِكٍ رضي الله عنه قَالَ: إن كَانَ النبي صلى الله عليه وسلم ليُخَالِطُنَا، حَتّى يَقُولُ لأَخٍ لِي صغير: *يَا أَبَا عُمَيْرٍ، مَا فَعَلَ النُّغَيْرُ؟*ُ.
أَخْرَجَهُ البخاري [6129] ومسلم [2150] .

*HADISI NA ASHIRIN DA BAKWAI*
An ruwaito daga Anas bn Malik -Allah ya kara yarda a gare shi, Ya ce: lallai ne Annabi -sallal lahu alaihi wa sallama- ya kan yi mu'amala; yana hulda da mu, har ya ce; wa dan'uwana karamin yaro: *Ya Abu-Umair, Shin tsuntsun kanari, mutuwa ya yi?*
Bukhariy [6129] da Muslim [2150] su ka ruwaito shi.

Annabi (S.A.W) ya kan fadi abinda ya gabata ne ga wani karamin tsuntsu; da Abu-Umair ke wasa da shi, sai ya mutu-. Wannan kuma na nuna kyakkyawiyar mu'amalar Manzon Allah (S.A.W) da sakewarsa, ko yadda ya ke damuwa da damuwar mutane, koda kuwa yara ne kanana.
Haka hadisin na nuna halaccin yin wasa da tsuntsu, ko sanya shi cikin keji, da halaccin yin alkunya ga wanda bai samu haifuwa ba, ko halaccin yin alkunya ga yaro karami (kamar ace: Abu-umair).


الحديث الثامن والعشرون*
عن عبد الله بن عمر رضي الله عنهما، قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: *الْمُؤْمِنُ الَّذِي يُخَالِطُ النَّاسَ وَيَصْبِرُ عَلَى أَذَاهُمْ أَعْظَمُ أَجْرًا، مِنْ الْمُؤْمِنِ الَّذِي لا يُخَالِطُ النَّاسَ وَلا يَصْبِرُ عَلَى أَذَاهُمْ*
أخرحه البخاري في الأدب المفرد [393] وابن ماجه [4032]، وحسن إسناده ابن حجر في بلوغ المرام [1446].

*HADISI NA ASHIRIN DA TAKWAS*
An ruwaito daga Abdullahi bn Umar -Allah ya kara yarda a gare su- ya ce: Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: *Muminin da ke cikin mutane, ya ke kuma yin hakuri kan cutarwarsu ya fi girman lada akan muminin da baya cikin mutane, kuma baya hakuri akan cutarwarsu*.

Littafin/ *Adabul mufrad* na Bukhariy [393] da Ibnu-Majah cikin *sunan* [4032]. Ibnu-Hajar a cikin littafin *bulugul maram* [1446] ya ce: Isnadinsa *hasan* ne.


الحديث التاسع والعشرون*
عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله عنه، قَالَ: أَسَرَّ إِلَيَّ نَبِيُّ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ سِرًّا، فَمَا أَخْبَرْتُ بِهِ أَحَدًا بَعْدُ، وَلَقَدْ سَأَلَتْنِي عَنْهُ أُمُّ سُلَيْمٍ فَمَا أَخْبَرْتُهَا به.
أَخْرَجَهُ البخاري [6289] ومسلم [2482].


وفي رواية لمسلم أنه قَالَتْ أم سليم رضي الله عنها: لا تُحَدِّثَنَّ بِسِرِّ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَحَدًا.


قَالَ أَنَسٌ: وَاللهِ لَوْ حَدَّثْتُ بِهِ أَحَدًا لَحَدَّثْتُكَ يَا ثَابِت.

HADISI NA ASHIRIN DA TARA
An ruwaito daga Anas bn Malik -Allah ya kara yarda a gare shi, Ya ce: Annabin Allah -sallal lahu alaihi wa sallama *ya gaya min wani sirri, amma ban taba bada labarinsa ga wani Mutum ba, Kuma hakika Ummu-Sulaimin* (wato: mahaifiyarsà) *ta tanbaye ni akan wannan labarin; sai ban bata labari akansa ba*.
Bukhariy [6129] da Muslim [2150] su ka ruwaito shi.

A wata riwaya ta *Muslim* Ummu-Sulaimin ta ce: *Ka da ka bada labarin sirrin Manzon Allah* -sallal lahu alaihi wa sallama- *ga wani*.

Anas ya ce: *Na rantse da Allah! Da zan bada labarin wannan sirrin ga wani Mutum, to da na baka labari akansa ya kai Sabitu!* (Daya daga cikin manyan Daliban Anas).


الحديث الثلاثون*
عن أَبي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ رضي الله عنه قال: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: *إِنَّ مِنْ أَشَرِّ النَّاسِ عِنْدَ اللَّهِ مَنْزِلَةً يَوْمَ الْقِيَامَةِ الرَّجُلَ يُفْضِي إِلَى امْرَأَتِهِ،وَتُفْضِي إِلَيْه،ِ ثُمَّ يَنْشُرُ سِرَّهَا*.
أخرجه مسلم [1437].

*HADISI NA TALATIN*
An ruwaito daga Abu-Sa'id Alkhudriy -Allah ya kara yarda a gare shi, Ya ce: Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama ya ce: *Lallai ne, yana daga mutanen da su ka fi sharrin matsayi a wurin Allah, ranar kiyama; Mutumin da ke saduwa da matarsa, ita ma ta sadu da shi, sa'annan ya yada sirrinta* (ko ita, ta tona asirinsa)*.
Muslim [1437] ya ruwaito shi.



الحديث الحادي والثلاثون
عَنْ أَبي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قال:ُ سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم يَقُولُ: كُلُّ أَمَّتِى مُعَافًى إِلاَّ الْمُجَاهِرِينَ، وَإِنَّ مِنَ الْمَجَاهرة: أَنْ يَعْمَلَ الرَّجُلُ بِاللَّيْلِ عَمَلاً، ثُمَّ يُصْبِحَ وَقَدْ سَتَرَهُ اللَّهُ، فَيَقُول:َ يَا فُلاَنُ عَمِلْتُ الْبَارِحَةَ كَذَا وَكَذَا، وَقَدْ بَاتَ يَسْتُرُهُ رَبُّهُ وَيُصْبِحُ يَكْشِفُ سِتْرَ اللهِ عَنْهُ.
أخرجه البخاري [6069]، ومسلم [2990].

HADISI NA TALATIN DA DAYA
An ruwaito daga Abu hurairah -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Na ji Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- yana cewa: *Dukkan al'ummata za a musu afuwa, in banda masu bayyanar da laifi, Kuma yana daga cikin bayyanar da laifi: Mutum ya aikata wani aiki cikin dare, sai ya wayi gari* alhalin Allah ya rufa masa asiri* *yana cewa: ya wane: ai jiya* da dare *na aikata kaza da kaza; shi ya kwana Ubangijinsa yana rufa masa asiri, sai ga shi ya wayi gari yana yaye sitirar da Allah ya yi masa*.
Bukhariy [6069] da Muslim [2990] su ka ruwaito.


الحديث الثاني والثلاثون
عَنْ أَبِي هُرَيْرَة رضي الله عنهَ، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: لا يَسْتَرُ عَبْدٌ عَبْدًا فِي الدُّنْيَا إِلا سَتَرَهُ الله يوم القيامةُ.
أخرجه مسلم [2590].

HADISI NA TALATIN DA BIYU
An ruwaito daga Abu hurairah -Allah ya kara yarda a gare shi-, daga Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: Bawa ba zai rufa asirin wani bawa ba, a duniya, face Allah ya rufa asirinsa ranar kiyama.
Muslim [2590] ya ruwaito.


الحديث الثالث والثلاثون
عَنْ أَبِي مَسْعُودٍ الأَنْصَارِيِّ رضي الله عنه قَالَ: قال رسول الله صَلَّى اللَّهُُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: *مَنْ دَلَّ عَلَى خَيْرٍ فَلَهُ مِثْلُ أَجْرِ فَاعِلِهُ*.
أخرجه مسلم [1893].

HADISI NA TALATIN DA UKU
An ruwaito daga Abu Mas'ud Al-ansariy -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: *Wanda ya yi nuni zuwa ga wani alheri, to yana da kwatankwacin ladan wanda ya aikata shi*.
Muslim [1893] ya ruwaito.


الحديث الرابع والثلاثون*
عن أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: *مَنْ دَعَا إِلَى هُدًى كَانَ لَهُ مِنْ الأَجْرِ مِثْلُ أُجُورِ مَنْ تَبِعَهُ، لا يَنْقُصُ ذَلِكَ مِنْ أُجُورِهِمْ شَيْئًا، وَمَنْ دَعَا إِلَى ضَلالَةٍ كَانَ عَلَيْهِ مِنْ الإِثْمِ مِثْلُ آثَامِ مَنْ تَبِعَهُ لا يَنْقُصُ ذَلِكَ مِنْ أوزارهم شَيْئًا*
أخرجه مسلم [2674].

*HADISI NA TALATIN DA HUDU*
An ruwaito daga Abu hurairah -Allah ya kara yarda a gare shi- lallai Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: *Wanda ya yi kira zuwa ga wata shiriya, yana da lada kwatankwacin ladan wadanda su ka bi shi; ba tare da hakan ya tauye wani abu daga ladansu ba. Wanda kuma ya yi kira -da'awa- zuwa ga wata bata, yana da zunubi kwatankwacin zunuban wadanda su ka bi shi, ba tare da hakan ya tauye komai daga zunubansu ba*.
Muslim [2674] ya ruwaito.


الحديث الخامس والثلاثون*
عَنْ أَبِي مُوسَى الأشْعَرِيِّ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم: *الْمُؤْمِنُ لِلْمُؤْمِنِ كَالْبُنْيَانِ يَشُدُّ بَعْضُهُ بَعْضًا وشبك بين أصابعه* متفق عليه؛
[خ: 6026]، [م: 2585].

*HADISI NA TALATIN DA BIYAR*
An ruwaito daga Abu Musa Al-ash'ariy -Allah ya kara yarda a gare shi- daga Annabi -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: *Mumini ga mumini kamar gini ne; sashensa yana karfafa sashe*.
Bukhariy [6026] da Muslim [2585] su ka ruwaito.


الحديث السادس والثلاثون*
عَنْ أَبِي مُوسَى الأشْعَرِيِّ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم: *إن الخازنَ المسلمَ الأمينَ، الذي يُنْفِذُ* -وربما قال: *يُعطي*- *ما أُمرَ به، فيعطيه كاملاً مُوَفَّراً، طيبةً به نفسُهُ، فيدفعُه إلى الذي أُمر له به؛ أحدُ المتصدقين* متفق عليه؛ [خ: 2319]، [م: 1023].

*HADISI NA TALATIN DA SHIDA*
An ruwaito daga Abu Musa Al-ash'ariy -Allah ya kara yarda a gare shi- daga Annabi -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: *Lallai mai ajiyar dukiya ko taskance ta, musulmi amintacce mai amana, wanda ke zartar* -Ko, ya ce: *wanda ke bayar da- abin da aka yi masa umarni da shi; ya bayar da abin a kammale, a cike, ransa tana jin dadin hakan, ya kuma tunkuda dukiyar izuwa ga wanda aka ce ya ba shi ita, Shi ma dayan mutane masu sadaka ne guda biyu*.
Bukhariy [2319] da Muslim [1023] su ka ruwaito.


الحديث السابع والثلاثون
عَنْ تَمِيمٍ الدَّاريِّ رضي الله عنه أَنَّ النَّبِي صلى الله عليه وسلم قَالَ: *الدِّينُ النَّصِيحَةُ* قُلْنَا: لِمَن؟ْ قَال:َ *لِلَّهِ، وَلِكِتَابِهِ، وَلِرَسُولِه،ِ وَلأَئِمَّةِ الْمُسْلِمِينَ، وَعَامَّتِهِمْ*
أخرجه مسلم [55].

*HADISI NA TALATIN DA BAKWAI*
An ruwaito daga Tamim Ad-dariy -Allah ya kara yarda a gare shi- lallai Annabi -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: *Addini nasiha ne* Sai mu ka ce: Ga wa? Sai ya ce: *Ga Allah, da kuma littafinSa, da ManzonSa, da kuma shugabannin musulmai, da sauran musulmai*.
Muslim [55] ya ruwaito.


الحديث الثامن والثلاثون*
عن جرير بن عبد الله البجلي رضي الله عنه قال: *بَايَعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَلَى إِقَامِ الصَّلاةِ، وَإِيتَاءِ الزَّكَاةِ، وَالنُّصْحِ لِكُلِّ مُسْلِمٍ*،متفق عليه؛
[خ: 57]، [م: 56].

*HADISI NA TALATIN DA TAKWAS*
An ruwaito daga Jarir bn Abdullah Albajaliy -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: *Na yi mubaya'a ga Manzon Allah* -sallal lahu alaihi wa sallama- *a kan tsayar da sallah, da bada zakkah, da yin nasiha ga kowani musulmi*.
Bukhariy [57] da Muslim [56] su ka ruwaito.


الحديث التاسع والثلاثون*
عَنْ عبد الله بنِ مَسْعودِ رضيَ الله ُ عنهُ قال: قالَ رسول اللهِ صلى اللهُ عليْهِ وسلَم: *لا حَسَدَ إلاَّ في اثنَتَيْن؛ِ رَجُلٌ آتَاه اللهُ مَالاً فسَلَّطَهُ عَلى هَلَكتِهِ في الحق، ورجل آتَاهُ اللهُ الحِكْمَةَ فَهُوَ يَقضِي بِها*
*وَيُعَلِمُّها*
متفق عليه؛ [خ: 1409م: 816].

*HADISI NA TALATIN DA TARA*
An ruwaito daga Abdullahi bn Mas'ud -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: *Babu hassada sai cikin abubuwa biyu; Mutumin da Allah ya bashi dukiya, sai ya dora shi akan batar da ita cikin abubuwan gaskiya, da Mutumin da Allah ya ba shi hikima (ko ilimi); sai ya ke hukunci da hikimar, ya ke kuma karantar da ita*.
Bukhariy [1409] da Muslim [816] su ka ruwaito.


الحديث الأربعون*
عن عَدِيِّ بْنِ حَاتِمٍ رصي الله عنه، قَالَ: ذَكَرَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ النَّارَ فَأَعْرَضَ وَأَشَاحَ، ثُمَّ قَالَ: *اتَّقُوا النَّارَ*، ثُمَّ أَعْرَضَ وَأَشَاحَ حَتَّى ظَنَنَّا أَنَّهُ كَأَنَّمَا يَنْظُرُ إِلَيْهَا، ثُمَّ قَالَ: *اتَّقُوا النَّارَ وَلَوْ بِشِقِّ تَمْرَةٍ، فَمَنْ لَمْ يَجِدْ فَبِكَلِمَةٍ طيبة* متفق عليه؛
[خ: 6540م: 1016].

*HADISI NA ARBA'IN*
An ruwaito daga Adiyyu bn Hatim -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ambaci wuta, Sai ya kawar da kai, tsoron kada ta taba shi, sa'annan ya ce: *Ku nemi kariya daga wuta* sa'annan sai ya kawar da kai, tsoron kada ta taba shi, har sai da mu ka yi zaton kai ka ce, yana yin dubi ne zuwa gare ta, sa'annan ya ce: *Ku nemi kariya daga wuta ko da da barin dabino ne, Wanda kuma bai samu ba, to, ko da da kalma ce daddada* .
Bukhariy [6540] da Muslim [1016] su ka ruwaito.




الحديث الحادي والأربعون*
عن أبي هريرة رضي الله عنه أن رَسُول اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عليه وسلم - قال: *قال الله: أَنْفِق يا ابن آدم أُنْفِق عليك* متفق عليه؛
[خ: 5352 م: 993].

*HADISI NA ARBA'IN DA DAYA*
An ruwaito daga Abuhurairah -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: lallai Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: *Allah ya ce: Ka ciyar* -Ya kai dan'adam- *zan ciyar da kai* .
Bukhariy [5352] da Muslim [993] su ka ruwaito shi.


الحديث الثاني والأربعون*


عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّم،َ قَالَ: *مَا مِنْ يَوْمٍ يُصْبِحُ الْعِبَادُ فِيهِ إِلا مَلَكَانِ يَنْزِلان؛ِ فَيَقُولُ أَحَدُهُمَا: اللَّهُمَّ أَعْطِ مُنْفِقًا خَلَفًا، وَيَقُولُ الآخَرُ: اللَّهُمَّ أَعْطِ مُمْسِكًا تَلَفًا*
متفق عليه؛ [خ: 1442 م: 1010].

*HADISI NA ARBA'IN DA BIYU*
An ruwaito daga Abuhurairah -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: lallai Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: *Babu wani yinin da bayi za su wayi-gari a cikinsa, face Mala'iku guda biyu suna sauka, Sai dayansu ya ce: Ya Allah! Ka baiwa mai ciyar da dukiya mayewa. Sai dayan kuma ya ce: Ya Allah! Ka baiwa mai rike dukiya* -mai rowa- *lalacewa* -ko asara-.
Bukhariy [1442] da Muslim [1010] su ka ruwaito shi.


الحديث الثالث والأربعون
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: أَتَى رَجُلٌ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، أَصَابَنِي الجَهْدُ، فَأَرْسَلَ إِلَى نِسَائِهِ فَلَمْ يَجِدْ عِنْدَهُنَّ شَيْئًا، فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: أَلاَ رَجُلٌ يُضَيِّفُهُ هَذِهِ اللَّيْلَةَ، يَرْحَمُهُ اللَّهُ؟ فَقَامَ رَجُلٌ مِنَ الأَنْصَارِ فَقَالَ: أَنَا يَا رَسُولَ اللَّهِ، فَذَهَبَ إِلَى أَهْلِهِ، فَقَالَ لامْرَأَتِهِ: ضَيْفُ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لاَ تَدَّخِرِيهِ شَيْئًا، قَالَتْ: وَاللَّهِ مَا عِنْدِي إِلا قُوتُ الصِّبْيَةِ، قَالَ: فَإِذَا أَرَادَ الصِّبْيَةُ العَشَاءَ فَنَوِّمِيهِمْ، وَتَعَالَيْ فَأَطْفِئِي السِّرَاجَ وَنَطْوِي بُطُونَنَا اللَّيْلَةَ، فَفَعَلَتْ. ثُمَّ غَدَا الرَّجُلُ عَلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ:
*لَقَدْ عَجِبَ اللَّهُ عَزَّ وَجَلَّ -أَوْ ضَحِكَ- مِنْ فُلاَنٍ وَفُلاَنَةَ، فَأَنْزَلَ اللَّهُ عَزَّ وَجَلَّ:
{وَيُؤْثِرُونَ عَلَى أَنْفُسِهِمْ وَلَوْ كَانَ بِهِمْ خَصَاصَةٌ} [الحشر: 9].
متفق عليه؛ [خ: 4889 م: 2054].

HADISI NA ARBA'IN DA UKU
An ruwaito daga Abuhurairah -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce:
Wani Mutum ya zo wurin Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- sai ya ce:
Ya Manzon Allah! Matsalar yunwa ce ta kama ni,
Sai Manzon Allah ya tura wa matansa; sai bai samu komai a wurinsu ba,
Daga nan sai Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce:
Shin babu wani mutum -Allah ya yi rahama a gare shi- wanda zai karbi bakuncinsa a wannan dare?
Sai wani mutum daga cikin "Ansaar" ya tashi ya ce:
Ni ne, Ya Manzon Allah.
Sai ya tafi zuwa ga iyalansa; ya ce wa matarsa:
Bakon Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ne; kada ki hana shi komai,
Sai ta ce: Wallahi! Babu komai a wurina sai dan abincin yara,
Ya ce: To, idan yaran su ka bukaci abincin dare sai ki lallabe su har su yi barci, sai ki zo, ki kashe fitila, sai mu nade hanjinmu (wato: Mu kwana da yunwa) a wannan dare.
Sai ta aikata haka.
Sai wannan mutumin ya yi sammako zuwa ga Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- sai Annabi ya ce:
*Hakika Allah* Mabuwayi da daukaka *ya yi mamaki*
-ko kuma, ya ce:
*Allah ya yi dariya*- *daga wane da wance*
Sai Allah mabuwayi da daukaka ya saukar da:
*KUMA ANSAR SUNA FIFITA BUKATUN WASU AKAN TA SU KODA A TARE DA SU AKWAI WATA BUKATA KO TALAUCI* [Hashr: 9].

Bukhariy [4889] da Muslim [2054] su ka ruwaito shi.


الحديث الرابع والأربعون*
عن أبي موسى رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قال: قال رسول الله صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّم: *إن الأشعريين إذا أرملوا في الغزو، أو قل طعام عيالهم بالمدينة جمعوا ما كان عندهم في ثوب واحد، ثم اقتسموه بينهم في إناء واحد بالسوية، فهم مني، وأنا منهم*، متفق عليه؛ [خ: 2486 م: 2500].

HADISI NA ARBA'IN DA HUDU
An ruwaito daga AbuMusa Al'ash-ariy -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: Lallai kabilar Ash'ariyyuna idan guzurinsu a wurin yaki ya kare, ko kuma abincin iyalansu a garin Madina ya karanta, Sai su tattara abinda ya rage musu a cikin tufa daya, sa'annan su raba shi a cikin koko daya, a tsakaninsu daidai da daidai. A kan wannan; Su, suna daga gare ni, Nima, ina daga gare su
(Ma'ana: Shiriyarsu da Halinsu, yana kusa da nawa, nima haka).

Bukhariy [2486] da Muslim [2500] su ka ruwaito shi.


الحديث الخامس والأربعون*
عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِي رضي الله عنهِّ، قَالَ: بَيْنَمَا نَحْنُ فِي سَفَرٍ مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذْ جَاءَ رَجُلٌ عَلَى رَاحِلَةٍ لَهُ، قَالَ: فَجَعَلَ يَصْرِفُ بَصَرَهُ يَمِينًا وَشِمَالا، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: *مَنْ كَانَ مَعَهُ فَضْلُ ظَهْرٍ، فَلْيَعُدْ بِهِ عَلَى مَنْ لا ظَهْرَ لَهُ، وَمَنْ كَانَ لَهُ فَضْلٌ مِنْ زَادٍ، فَلْيَعُدْ بِهِ عَلَى مَنْ لا زَادَ لَه*ُ
قَالَ: فَذَكَرَ مِنْ أَصْنَافِ الْمَالِ مَا ذَكَر،َ حَتَّى رَأَيْنَا أَنَّهُ لا حَقَّ لأحَدٍ مِنَّا فِي فَضْلٍ.
أخرجه مسلم [برقم: 1728].

*HADISI NA ARBA'IN DA BIYAR*
An ruwaito daga AbuSa'id Alkhudriy -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Wata rana mun kasance a cikin wata tafiya tare da Annabi -sallal lahu alaihi wa sallama- sai wani mutum a kan abin hawansa ya zo masa. Maruwaicin hadisin ya ce: Sai mutumin ya rika jujjuya fiskarsa dama da hagu (kamar yana neman abinda zai toshe wata bukata), Sai Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: Wanda a wurinsa akwai abin hawa fiye da daya, to ya bada sadakarsa ga wanda bashi da abin hawa. Wanda kuma ya ke da guzuri dayawa to ya bayar da sauran ga wanda bashi da shi. Maruwaicin ya ce: Sai Annabi ya ambaci nau'uka da dama daga nau'in dukiya, har sai da mu ka ga, kamar Wani daga cikinmu bashi da wani hakki cikin abinda ya saura, na daga dukiya.

Muslim [1728] ya ruwaito shi.


الحديث السادس والأربعون*
عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرٍو رضي الله عنهما، أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: *أَرْبَعٌ مَنْ كُنَّ فِيهِ كَانَ مُنَافِقًا خَالِصًا، وَمَنْ كَانَتْ فِيهِ خَصْلَةٌ مِنْهُنَّ كَانَتْ فِيهِ خَصْلَةٌ مِنْ النِّفَاقِ حَتَّى يَدَعَهَا: إِذَا اؤْتُمِنَ خَانَ، وَإِذَا حَدَّثَ كَذَبَ، وَإِذَا عَاهَدَ غَدَرَ، وَإِذَا خَاصَمَ فَجَرَ*،
متفق عليه؛ [خ: 34م: 58].

*HADISI NA ARBA'IN DA SHIDA*
An ruwaito daga Abdullahi bn Amru -Allah ya kara yarda a gare su-, lallai Annabi -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: *Abubuwa hudu, Duk wanda su ka kasance a tare da shi, ya kasance munafiki ne tatacce. Wanda kuma ke dauke da wata sifa daga cikinsu, to, yana tare da sifar munafurci, har sai ya kyale ta; Idan aka bashi amana sai ya yi ha'inci, idan kuma zai yi magana sai ya yi karya, idan kuma ya yi alkawari sai ya ki cikawa, idan kuma ya yi husuma* -fada- *sai ya yi fajirci*,

Bukhariy [34] da Muslim [58] su ka ruwaito shi.


الحديث السابع والأربعون*
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه، عَنْ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: *آيَةُ الْمُنَافِقِ ثَلاثٌ : إِذَا حَدَّثَ كَذَبَ، وَإِذَا وَعَدَ أَخْلَفَ، وَإِذَا اؤْتُمِنَ خَانَ*
متفق عليه؛ [خ: 33 م: 59].


*HADISI NA ARBA'IN DA BAKWAI*
An ruwaito daga AbuHurairah -Allah ya kara yarda a gare shi-, daga Annabi -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: *Alamomin munafiki guda uku ne; Idan zai yi magana sai ya yi karya, idan ya yi alkawari sai ya karya, idan kuma aka bashi amana sai ya yi ha'inci*.

Bukhariy [33] da Muslim [59] su ka ruwaito shi.