طاهر جبريل دكو
_17 _August _2016هـ الموافق 17-08-2016م, 04:26 PM
HADISAI ARBA'IN KAN HAJJI DA UMRAH DA ZIYARA أربعون حديثا تتعلق بالحج والعمرة والزيارة
HADISAI ARBA'IN KAN HAJJI DA UMRAH DA ZIYARA
أربعون حديثا تتعلق بالحج والعمرة والزيارة
TATTARAWAR DA TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشرف المرسلين، وعلى آله وصحبه أجمعين، أما بعد:
فهذه طائفة كبيرة من الآثار النبوية التي تتعلق بالعمرة والحج وزيارة المدينة، والله أسأل القبول والإخلاص، فقد ورد عن عُمَرَ بْن الْخَطَّابِ رضي الله تعالى عنه قال: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، يَقُولُ: «إِنَّمَا الأَعْمَالُ بِالنِّيَّاتِ، وَإِنَّمَا لكل امْرِئٍ مَا نَوَى، فَمَنْ كَانَتْ هِجْرَتُهُ إِلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ فَهِجْرَتُهُ إِلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ، وَمَنْ كَانَتْ هِجْرَتُه لدُنْيَا يُصِيبُهَا، أَوِ امْرَأَةٍ يَنْكِحُهَا فَهِجْرَتُهُ إِلَى مَا هَاجَرَ إِلَيْهِ». رواه البخاريّ، ومسلم([1]).
An ruwaito daga Umar xan Alkhaxxabi (r.a) yace: Na ji Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "Dukkan aiyuka su kan inganta tare da niyya, kuma lallai kowane mutum yana samun sakamakon abinda yayi niyya; Wanda hijirarsa ta kasance saboda Allah ne da ManzonSa to sakamakon hijirarsa tana ga Allah da Manzonsa. Wanda kuma hijirarsa ta kasance saboda wata duniya ce da zai same ta, ko saboda wata matar da zai aure ta, to sakamakon hijirarsa yana ga abin da yayi hijira dominsa. Bukhariy [lamba: 1], da Muslim [lamba: 1907] suka ruwaito shi.
بيان أنّ حج بيت الله الحرام من الخمس التي بني عليها الإسلام
عَنِ عبد الله بْن عمر رضي الله عنهما، قَالَ: سمعتُ رَسُول اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يقول: «بُنِيَ الْإِسْلَامُ عَلَى خَمْسٍ، شَهَادَةِ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللَّهِ، وَإِقَامِ الصَّلَاةِ، وَإِيتَاءِ الزَّكَاةِ، وَصَوْمِ شَهْرِ رَمَضَانَ، وَحَجَّ الْبَيْتِ». رواه البخاري ومسلم([2]).
HAJJI YANA CIKIN GINSHIQAI BIYAR DA AKA GINA MUSULUNCI AKANSU
An ruwaito daga Abdullahi xan Umar (r.a) yace: Naji Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "An gina musulunci akan abubuwa guda biyar; Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Muhammadu manzon Allah, da tsayar da salla, da bada zakka, da yin hajjin wannan xakin, da azumin watan ramadana".
Bukhariyy [8] da Muslim [16] suka ruwaito shi.
بيان أنّ الحج مِن أسباب دخول الجنة
عَنْ مُعَاذِ بْنِ جَبَلٍ رضي الله عنه قال: قلت يا رسول اللهأَخْبِرْنِي بِعَمَلٍ يُدْخِلُنِي الْجَنَّةَ، وَيُبَاعِدُنِي مِنَ النَّارِ؟ قَالَ: "لَقَدْ سَأَلْتَ عَنْ عَظِيمٍ، وَإِنَّهُ لَيَسِيرٌ عَلَى مَنْ يَسَّرَهُ اللهُ عَلَيْهِ، تَعْبُدُ اللهَ وَلَا تُشْرِكُ بِهِ شَيْئًا، وَتُقِيمُ الصَّلَاةَ، وَتُؤْتِي الزَّكَاةَ، وَتَصُومُ رَمَضَانَ، وَتَحُجُّ الْبَيْتَ". الحديث رواه الترمذي وقال: حديث حسن صحيح.
YIN HAJJI SABABI NE NA SHIGA ALJANNA
An ruwaito daga Mu’azu xan Jabal (R.A) yace: Nace ya Manzon Allah bani labarin wani aiki da zai shigar da ni aljanna, kuma ya nisantar da ni daga shiga wuta, sai ya ce: Haqiqa ka yi tambaya game da abu mai girma, saidai abu ne mai sauqi ga wanda Allah ya sauqaqe shi a gare shi; ka bauta wa Allah ba tare da ka haxa shi da wani ba, kuma ka tsayar da Sallah, kuma ka bada zakka, kuma ka azumci Ramadan, sannan ka ziyarci xakin Allah. Tirmiziy ya ruwaito shi [ 2616] kuma yace: Hadisi ne mai kyau ingantacce.
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ: أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «العُمْرَةُ إِلَى العُمْرَةِ كَفَّارَةٌ لِمَا بَيْنَهُمَا، وَالحَجُّ المَبْرُورُ لَيْسَ لَهُ جَزَاءٌ إِلَّا الجَنَّةُ»([3]).
An ruwaito daga Abu-hurairah (Allah ya qara yarda a gare shi), Lallai Manzon Allah (s.a.w) ya ce: ((Umrah zuwa wata umarah na kankare zunuban da ke tsakaninsu, hajji kuma kuvutacce ba shi da sakayya sai aljanna)
. Annabi (r) ya sake cewa:
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ: أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَنْ حَجَّ لِلَّهِ فَلَمْ يَرْفُثْ، وَلَمْ يَفْسُقْ، رَجَعَ كَيَوْمِ وَلَدَتْهُ أُمُّهُ»([4]).
An ruwaito daga Abu-hurairah (Allah ya qara yarda a gare shi), Lallai Manzon Allah (s.a.w) ya ce: (Duk wanda ya yi aikin hajji don Allah, bai yi batsa ko jima'i ba, da fasikanci: zai komo kamar ranar da uwarsa ta haife shi).
Abu-hurairah -t-, lallai Annabi (r) ya ce:
412 - (1337
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه، قَالَ: خَطَبَنَا رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: «أَيُّهَا النَّاسُ قَدْ فَرَضَ اللهُ عَلَيْكُمُ الْحَجَّ، فَحُجُّوا»، فَقَالَ رَجُلٌ: أَكُلَّ عَامٍ يَا رَسُولَ اللهِ؟ فَسَكَتَ حَتَّى قَالَهَا ثَلَاثًا، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: " لَوْ قُلْتُ: نَعَمْ لَوَجَبَتْ، وَلَمَا اسْتَطَعْتُمْ "، ثُمَّ قَالَ: «ذَرُونِي مَا تَرَكْتُكُمْ، فَإِنَّمَا هَلَكَ مَنْ كَانَ قَبْلَكُمْ بِكَثْرَةِ سُؤَالِهِمْ وَاخْتِلَافِهِمْ عَلَى أَنْبِيَائِهِمْ، فَإِذَا أَمَرْتُكُمْ بِشَيْءٍ فَأْتُوا مِنْهُ مَا اسْتَطَعْتُمْ، وَإِذَا نَهَيْتُكُمْ عَنْ شَيْءٍ فَدَعُوهُ»
وفي لفظ:
(Ya ku mutane! Lallai Allah ya farlanta muku yin aikin hajji; sai ku yi hajji. Sai wani mutum ya ce: Shin a kowace shekara ne ya ma'aikin Allah? Sai yace: Da nace: E! da hakan ya wajaba, da kuma kun gagara iyawa).
"أنه قَالَ: لَوْ قُلْتُ: نَعَمْ لَوَجَبَتْ، وَلَمَا اسْتَطَعْتُم"([5]).
Ma'ana: (Ya ku mutane! Lallai Allah ya farlanta muku yin aikin hajji; sai ku yi hajji. Sai wani mutum ya ce: Shin a kowace shekara ne ya ma'aikin Allah? Sai yace: Da nace: E! da hakan ya wajaba, da kuma kun gagara iyawa).
faxinsa (r):
"تَعَجَّلُوا إِلَى الْحَجِّ؛ فَإِنَّ أَحَدَكُمْ لا يَدْرِي مَا يَعْرِضُ لَه"([6]).
Ma'ana: (Ku yi gaggawan zuwa hajji; saboda xayanku bai san abinda ka iya bijiro masa ba). Kuma an ruwaito hakan daga Annabi, da kuma sahabbai (hadisi marfu'i da mauqufi), ta hanyoyi da sashinsu ke qarfafa sashi cewa:
"مَنْ اسْتَطَاعَ الْحَجّ فَلَمْ يَحُجَّ؛ فَلْيَمُتْ إنْ شَاءَ يَهُودِيًّا وَإِنْ شَاءَ نَصْرَانِيًّا"([7]).
Ma'ana: (Wanda ya samu damar ya yi hajji, sai kuma bai yi hajjin ba, to ya mutu in ya ga dama a bayahude, ko in ya so ya mutu akan addinin nasara).
1-
Aliyu -t- cewa lallai Manzon Allah (r) yace:
"رُفِعَ الْقَلَمُ عَنْ ثَلاثَةٍ؛ عَنِ النَّائِمِ حَتَّى يَسْتَيْقِظَ، وعَنِ الصَّبيّ حَتَّى يَبْلُغَ، وَعَنِ الْمَجْنُونِ حَتَّى يفيق"([8]).
Ma'ana: (An xage alqalami akan mutane guda uku; maibarci har sai ya tashi, da yaro qarami har sai ya balaga, da kuma mahaukaci har sai ya wartsake).
Balaga:
يجب الحج على المكلف (البالغ العاقل) المستطيع
عَنْ عَلِيٍّ رضي الله عنه، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: "رُفِعَ الْقَلَمُ عَنْ ثَلاثَةٍ: عَنِ النَّائِمِ حَتَّى يَسْتَيْقِظَ، وَعَنِ الْمَجْنُونِ حَتَّى يفيق، وعَنِ الصَّغِيرِ حَتَّى يَبْلُغَ"([9]).
HAJJI NA WAJABA NE AKAN BALIGI MAI HANKALI, MAI IKO
An ruwaito daga Aliyu (r.a), daga Annabi (s.a.w) lallai shi ya ce: "An xauke alqalami akan mutane guda uku; Ga mai barci har sai ya tashi, da kuma mahaukaci har sai ya wartsake, da qaramin yaro har sai ya balaga).
"أنّ امْرَأَةً رَفَعَتْ صَبِيًّا، فَقَالَتْ: يَا رَسُولَ اللهِ! أَلِهَذَا حَجٌّ؟ قَالَ: نَعَمْ، وَلَكِ أَجْر"([10]).
Ma'ana: (Lallai wata mata ta xaga wani yaro, sai tace: Ya ma'aikin Allah! Shin akwai hajji akan wannan? Sai yace: E, ke kuma kina da lada).
faxinsa (r):
"أَيُّمَا صَبِيٍّ حَجَّ ثُمَّ أَدْرَكَ فَعَلَيْهِ حَجَّة أُخْرَى، وَأَيُّمَا عَبْدٌ حَجَّ ثُمَّ عتِقَ فَعَلَيْهِ حَجَّة أُخْرَى"([11]).
Ma'ana: (Duk wani yaron da ya yi hajji, sannan ya balaga, to wajibi ne akansa ya yi wani hajjin na daban, Duk kuma bawan da ya yi hajji sa'annan aka 'yanta shi, to wajibi ne akansa ya yi wani hajjin na daban).
"وَأَيُّمَا عَبْدٌ حَجَّ ثُمَّ عتِقَ فَعَلَيْهِ حَجَّة أُخْرَى".
Ma'ana: (Kuma duk bawan da ya yi hajji sa'annan aka 'yanta shi, to wajibi ne akansa ya yi wani hajjin na daban).
faxinsa (r):
"لا يَحِلُّ لامْرَأَةٍ تُؤْمِنُ بِاللهِ وَالْيَوْمِ الآخِرِ، أَنْ تُسَافِرَ سَفَرًا يَكُونُ ثَلاثَةَ أَيَّامٍ فَصَاعِدًا، إِلا وَمَعَهَا أَبُوهَا، أَوِ
ابْنُهَا، أَوْ زَوْجُهَا، أَوْ أَخُوهَا، أَوْ ذُو مَحْرَمٍ مِنْهَا"([12]).
Ma'ana: (Baya halatta ga wata mace; da ta yi imani da Allah da kuma ranar qarshe; ta yi tafiya ta kwanaki uku, ko fiye, face a tare da ita akwai ubanta, ko xanta, ko mijinta, ko dan'uwanta, ko kuma wani muharraminta).
yace:
"إِنَّ امْرَأَتِي خَرَجَت حَاجَةً، وإِنِّي اكْتُتِبْتُ فِي غَزْوَةِ كَذَا: (انْطَلِقْ فَحُجَّ مَعَها)"([13]).
Ma'ana: (Lallai matata ta fita i zuwa ga hajji, lallai ni kuma an rubuta ni don zuwa yaki wuri kaza: Ka tafi kayi hajji tare da ita).
A'ishah - رضي الله عنها- a lokacin da ta tambaye shi, shin akwai "jihadi" akan mata? Sai yace:
"نَعَمْ، عَلَيْهِنَّ جِهَادٌ لا قِتَالَ فِيهِ: الْحَجُّ وَالْعُمْرَة"([14]).
Ma'ana: (E, akwai jihadi akansu wanda babu zubar da jini a cikinsa; aikin hajji da umrah), da kuma saboda faxinsa (r) ga Abu-razin -t- yayin da ya tambaye shi cewa babansa ba zai iya yin hajji da umrah ba, da kuma tafiya, Sai yace:
"حُجَّ عَنْ أَبِيكَ واعْتَمِرْ"([15]).
Ma'ana: (Ka yi hajji ga babanka, ka yi masa umrah).
Abdullahi xan Abbas -t-, yace:
"وَقَّتَ رَسُولُ اللَّه r لأَهْلِ المَدِينَةِ ذَا الحُلَيْفَةِ، وَلأَهْلِ الشَّأْمِ الجُحْفَةَ، وَلأَهْلِ نَجْدٍ قَرْنَ المَنَازِلِ، وَلأَهْلِ اليَمَنِ يَلَمْلَمَ، هُنَّ لَهُنَّ، وَلِمَنْ أَتَى عَلَيْهِنَّ مِنْ غَيْرِ أهلهِنَّ؛ مِمَّنْ أَرَادَ الحَجَّ وَالعُمْرَةَ، وَمَنْ كَانَ دُونَ ذَلِكَ، فَمِنْ حَيْثُ أَنْشَأَ، حَتَّى أَهْلُ مَكَّةَ مِنْ مَكَّةَ"([16]).
Ma'ana: (Manzon Allah –r- ya sanya "ZULHULAIFAH" ga mutanen Madina a matsayin wurin xaura niyya, mutanen Shaam kuma ya sanya musu "AL-JUHFAH", ga mutanen Najdu kuma "KARNUL MANAZIL", mutanen Yamen kuma ya sanya musu "YALAMLAM". Waxannan miqaatan na waxannan mutanen ne, da kuma duk wanda ya zo musu ba daga cikin ahlin wajen ba; na waxanda suka nufi yin hajji da umrah. Wanda kuma yake gaba (ta ciki) da waxannan miqatai to zai yi niyya ne daga wurin da ya fari hakan, Su kuma mutanen Makka daga garin Makka).
"إِنَّمَا الأَعْمَالُ بِالنِّيَّات"([17]).
Ma'ana: (Lallai dukkan aiyuka su kan inganta ne tare da niyya).
"الْحَجُّ عَرَفَةُ"([18]).
Ma'ana: (Aikin hajji shine tsayuwar arafah).
A'ishah - رضي الله عنها- ta ce:
"مَا أَتَمَّ اللَّهُ حَجَّ امْرِئٍ، وَلاَ عُمْرَتَهُ لَمْ يَطُفْ بَيْنَ الصَّفَا وَالمَرْوَة" ([19]).
Ma'ana: (Allah baya cika hajjin mutum ko umrarsa matuqar bai yi xawafi tsakanin safah da marwah ba), da kuma saboda faxinsa (r):
"اسْعَوْا، فَإِنَّ اللَّهَ كَتَبَ عَلَيْكُمُ السَّعْي"([20]).
Ma'ana: (Ku yi sa'ayi saboda Allah ta'alah ya wajabta muku yin sa'ayi).
"خُذُوا عَنِّي مَنَاسِكَكُم".
Ma'ana: (Ku kwaikwayi aikin hajjinku daga gare ni).
Abdullahi xan Abbas -t-:
"أُمِرَ النَّاسُ أَنْ يَكُونَ آخِرُ عَهْدِهِمْ بِالْبَيْتِ، إِلا أَنَّهُ خُفِّفَ عَنِ الْمَرْأَةِ الْحَائِضِ"([21]).
Ma'ana: (An umurci mutane da cewa aikinsu na qarshe ya zama xawafin xakin Allah ne, Sai dai kuma an yi rangwame ga macen da take haila).
Abdullahi xan Abbas -t- cewa:
"مَنْ نَسِيَ مِنْ نُسُكِهِ شَيْئًا أَوْ تَرَكَهُ فَلْيُرِقْ دَمًا" ([22]).
Ma'ana: (Duk mutumin da ya manta wani abu daga cikin aikinsa, ko kuma ya barshi to sai ya zubar da jini).
"إِنَّ اللَّهَ وَضَعَ عَن أُمَّتِي الْخَطَأَ، وَالنِّسْيَانَ، وَمَا اسْتُكْرِهُوا عَلَيْهِ"([23]).
Ma'ana: (Lallai Allah ta'alah ya yi rangwame wa al'ummata kan kuskure da mantuwa, da kuma abinda aka tilasta su akansa).
Ka'ab xan Ujrah -t- a lokacin da kwarkwatan kansa suka cutar da shi:
"احْلِقْ رَأْسَكَ، وَصُمْ ثَلاَثَةَ أَيَّامٍ، أَوْ أَطْعِمْ سِتَّةَ مَسَاكِينَ، أَوْ انْسُكْ بِشَاةٍ"([24]).
Ma'ana: (Ka aske kanka; sai ka yi azumin yini uku, ko ka ciyar da miskinai guda shida, ko kuma ka kusanci Ubangijinka da yanka akuya).
Abdullahi xan Abbas -t- cewa:
"مَنْ نَسِيَ مِنْ نُسُكِهِ شَيْئًا أَوْ تَرَكَهُ فَلْيُرِقْ دَمًا"([25]).

(لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ، وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، لا إِلَهَ إِلا اللهُ وَحْدَهُ، أَنْجَزَ وَعْدَهُ، وَنَصَرَ عَبْدَهُ، وَهَزَمَ الأَحْزَابَ وَحْدَهُ).
LA ILAHA ILLAL LAHU WAHDAHU LA SHARIKA LAHUW, LAHUL MULKU, WA LAHUL HAMDU, WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN QADIIR. LA ILAHA ILLAL LAHU WAHDAH, ANJAZA WA'ADAH, WA NASARA ABDAH, WA HAZAMAL AHZABA WAHDAH.
"لا إِلَهَ إِلا اللَّهُ وَحْدَهُ لا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ، وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ".
LA ILAHA ILLAL LAHU WAHDAHU LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU, WA LAHUL HAMDU, WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN QADIIR.
BABI NA BIYAR: WURAREN DA AKA SHAR'ANTA ZIYARTARSU A GARIN MADINAH:
"لاَ تُشَدُّ الرِّحَالُ إِلا إِلَى ثَلاَثَةِ مَسَاجِدَ: المَسْجِدِ الحَرَامِ، وَمَسْجِدِ الرَّسُولِ r، وَمَسْجِدِ الأَقْصَى"([26]).
Ma'ana: (Ba a xaura sirdi -a kimtsa tafiya da nufin lada- Sai in zuwa ga masallatai ne guda uku:
1) Masallaci mai alfarma -da ke garin Makkah-.
2) Da masallacin wannan Manzo -r-.
3) da kuma masallaci mai nisa -da ke Qudus-).
"صَلاَةٌ فِي مَسْجِدِي هذَا خَيْرٌ مِنْ أَلْفِ صَلاَةٍ فِيمَا سِوَاهُ، إِلاَّ الْمَشْجِدَ الْحَرَام"([27]).
Ma'ana: (Sallah a masallacina wannan yafi alkhairi fiye da sallah dubu a waninsa; sai dai masallaci mai alfarma).
ya ce:
(بسم الله، والصلاة والسلام على رسول الله، اللهُمَّ افْتَحْ لِي أَبْوَابَ رَحْمَتِك).
"BISMILLAH, WAS SALATU WAS SALAMU ALA RASULIL LAH, ALLAHUMMA IFTAH LIY ABWABA RAHMATIK".
"مَا بَيْنَ بَيْتِي وَمِنْبَرِي رَوْضَةٌ مِنْ رِيَاضِ الجَنَّة"([28]).
Ma'ana: (Tsakanin gidana da minbarina dausayi ne daga dausayin aljanna).
faxinsa (r):
"مَا مِنْ أَحَدٍ يُسَلِّمُ عَلَيَّ إِلا رَدَّ اللَّهُ عَلَيَّ رُوحِي حَتَّى أَرُدَّ عَلَيْهِ السَّلام"([29]).
Ma'ana: (Babu wani mutum guda da zai yi min sallama face Allah ya dawo min da raina don na amsa masa sallama).
(السلام عليك يا رسول الله، السلام عليك يا أبا بكرٍ، السلام عليك يا أبتاه).
Ma'ana: (aminci ya qara tabbata akanka ya ma'aikin Allah, aminci ya tabbata akanka ya Aba-bakrin, aminci ya tabbata akanka ya babana!)
kamar hadisin:
(مَنْ حَجَّ ولم يَزُرْني فقد جَفانِي).
Ma'ana: (Duk wanda ya yi aikin hajji, bai ziyarce ni ba; To ya gajarta wajen bani haqqina –ma'ana: yayi mini jafa'i-). Da hadisin:
(مَنْ زارَ قبري وَجَبَتْ له شفاعَتِي).
Ma'ana: (Wanda ya ziyarci kabarina cetona ya tabbata masa).
faxinsa (r):
"مَنْ تَطَهَّرَ فِي بَيْتِهِ ثُمَّ أَتَى مَسْجِدَ قُبَاءَ، فَصَلَّى فِيهِ صَلاةً، كَانَ لَهُ كَأَجْرِ عُمْرَةٍ"([30]).
Ma'ana: (Duk wanda ya tsarkaka –yayi alwala- a gidansa sa'annan ya zo masallacin Quba'a; kana ya sallaci wata sallah a cikinsa to yana da kamar ladan umrah".
"زُورُوا الْقُبُورَ؛ فَإِنَّهَا تُذَكِّرُ الموت"([31]).
Ma'ana: (Ku ziyarci qaburbura; domin ziyartarsu yana tuna mutuwa).
"السَّلامُ عَلَيْكُمْ أَهْلَ الدِّيَارِ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُسْلِمِينَ، وَإِنَّا، إِنْ شَاءَ اللهُ لَلاحِقُونَ، أَسْأَلُ اللهَ لَنَا وَلَكُمُ الْعَافِيَةَ"([32]).
Ma'ana: (Amincin Allah ya tabbata a gare ku ya ku ma'abota waxannan gidajen; muminai da musulmai, kuma lallai muma –insha Allahu- muna nan tafe, Ina roqon Allah lafiya ga mu da ku).
Waxannan sune wuraren da aka shar'anta ziyartarsu a garin Madinah.
Amma sauran wurare da wassu daga gama-garin mutane ke zaton cewa ziyartarsu shari'a ce, kamar wurin da taguwar Annabi (r) ta duqa, da masallacin juma'a, da rijiyar da zoben Annabi (r) ya faxa a cikinta, da kuma rijiyar da Usmanu ya saya wa musulmai (bi'iru usman), da masallatai guda bakawai (al-masajidus saba'ah), da masallacin alqibla guda biyu (qiblatain), Duk waxannan ziyartarsu ba shi da wani dalili, kuma bai tabbata daga Annabi (r) cewa ya ziyarci waxannan wuraren ba, ko ya yi amurni da a ziyarce su ba, haka kuma magabata na kwarai suma bamu samu cewa su kan ziyarci waxannan wuraren ba. Kuma babu wani masallaci a garin Madina da ke da wata falala ta musamman in banda masallacin Annabi (r) da kuma masallacin Quba'a. Annabi kuma (r) ya ce:
"مَنْ عَمِلَ عَمَلا لَيْسَ عَلَيْهِ أَمْرُنَا فَهُوَ رَد"([33]).
Ma'ana: (Duk wanda ya aikata wani aikin da babu umurninmu akansa to an mayar masa).
Don haka; ya dace ga musulmi idan har ya ziyarci garin Madina ya taqaita wajen ziyartar wuraren da aka shar'anta ziyartarsu, ya kuma nisanci wuraren da ba a shar'anta ziyartarsu ba.
BABI NA SHIDA: MAGANA KAN LAYYAH:
Anas -t-:
"أنَّ النَّبِيّ r ضَحَّى بِكَبْشَيْنِ أَمْلَحَيْنِ أَقْـرَنَيْنِ، ذَبَـحَـهُمَا بِـيَدِهِ، وَسَـمَّى وَكَـبَّـرَ، وَوَضَعَ رِجْلَهُ
عَلَى صِفَاحِهِمَا"([34]).
Ma'ana: (Lallai Annabi –r- ya yi layyah da raguna guda biyu masu roxin fari da baqi, madaidaita qaho guda biyu, ya yanka su da hannayensa, yana mai anbaton sunnan Allah, da yin kabbara, ya kuma xora qafarsa a gefen wuyansu).
Abu-ayyub -t- cewa:
"كَانَ الرَّجُلُ فِي عَهْدِ رسول الله r يُضَحِّي بِالشَّاةِ عَنْهُ، وَعَنْ أَهْلِ بَيْتِهِ، فَيَأْكُلُونَ وَيُطْعِمُون"([35]).
Ma'ana: (Mutum ya kasance a zamanin manzon Allah –r- ya kan yi layyah da akuya -ko tinkiya-, wa kansa, da kuma iyalan gidansa, sai su ci, su kuma ciyar).
"نَحَرْنَا مَعَ رَسُولِ اللهِ r عَامَ الْحُدَيْبِيَةِ الْبَدَنَةَ عَنْ سَبْعَةٍ، وَالْبَقَرَةَ عَنْ سَبْعَة"([36]).
Ma'ana: (Mun yi layyah tare da manzon Allah –r- a shekarar sulhun hudaibiyyah, mutane bakwai ga raqumi xaya, itama saniya xaya mutane bakwai).
"لا تَذْبَحُوا إِلا مُسِنَّةً إِلا أَنْ يُعْسِرَ عَلَيْكُمْ، فَتَذْبَحُوا جَذَعَةً مِنَ الضَّأْن"([37]).
Ma'ana: (Kada ku yi yankar layyah sai dabbar da ake mata laqabi da "musinnah", sai dai in kun rasa wannan, sai ku yanka "jaza'ah" daga cikin tumaki).
"Musinnah" daga cikin raquma itace: wanda ta cika shekaru biyar. Daga cikin "shanu" kuma itace: wanda ta cika shekaru biyu. Daga cikin "awaki" kuma: wacce ta cika shekara xaya. Kuma ana kiranta "Saniyyah".
"أَصَابَنِي جَذَعٌ، قَالَ: ضَحِّ بِه"([38]).
Ma'ana: (Ni na samu "jaza'ah –tinkiya 'yar wata shida" ne, Sai Annabi –r- yace: To sai ka yi layyah da ita).
Uqbah xan Aamir -t-:
"ضَحَّيْنَا مَعَ رَسُولِ اللَّهِ r بِجَذَعٍ مِنَ الضَّأْنِ"([39]).
Ma'ana: (Mun yi layyah tare da manzon Allah –r- da "jaza'ah daga cikin tumaki –wato: 'yar watanni shida-).
1-
2-
3-
Annabi (r) ya ce:
"أَرْبَعٌ لا تُجْزِئُ فِي الأَضَاحِيِّ: الْعَوْرَاءُ الْبَيِّنُ عَوَرُهَا، وَالْمَرِيضَةُ، الْبَيِّنُ مَرَضُهَا، وَالْعَرْجَاءُ الْبَيِّنُ عَرَجُهَا، وَالْعَجْفَاء الَّتِي لا تُنْقِي"([40]).
Ma'ana: (Dabbobi guda huxu basa isarwa a "layyah": Dabba mai harari-garke wacce matsalan idonta ya bayyana, da maras lafiyan da cutarta ta bayyana, da gurguwar da gurguntakanta ya bayyana, da kuma ramammiyar da bata da kitse).
Al-bara'u xan Aazib -t-, yace: Manzon Allah (r) ya ce:
"مَنْ صَلَّى صَلاَتَنَا، وَنَسَكَ نُسْكَنَا فَقَدْ أَصَابَ النُّسُكَ، وَمَنْ ذَبَح قَبْلَ أَنْ يُصَلِّيَ فَلْيُعِدْ مَكَانَهَا أُخْرَى"([41]).
Ma'ana: (Duk wanda ya yi sallah irin tamu, ya kuma yi yanka irin namu to lallai ya dace da yankan layyah akan tafarki, Amma mutumin da ya yi yanka kuma gabanin ya yi sallar idi to sai ya sake yanka wata a madadinta).
Jubair xan Muxim -t- daga Annabi (r) yace:
"كُلُّ أَيَّامِ التَّشْرِيقِ ذَبْح"([42]).
Ma'ana: (Dukkanin ranakun "tashriq" lokacin yanka ne).
A
Al-bara'u xan Aazib -t-, lallai Annabi (r) yace:
"أَوَّل مَا نَبْدَأُ بِهِ يَوْمنَا هَذَا نُصَلِّي، ثُمَّ نَرْجِعُ فَنَنْحَرُ، فَمَنْ فَعَلَ ذَلِكَ فَقَدْ أَصَابَ سُنَّتَنَا، وَمَنْ ذَبَحَ قَبْلَ ذَلِك فَإِنَّمَا هُوَ لَحْمٌ قَدَّمَهُ لأَهْلِهِ؛ لَيْسَ مِنَ النُّسُكِ فِي شَيْءٍ"([43]).
Ma'ana: (Abun da zamu fara yininmu wannan da shi, shine mu yi sallar idi, sa'annan sai mu dawo don mu soke abun layyarmu. Duk wanda ya aikata haka to ya dace da sunnarmu, Duk kuma mutumin da ya yanka abun layyansa gabanin haka to ya sani cewa: nama ne ya gabatar da shi ga iyalansa, ba layyah ba).
Abdullahi xan Abbas -t- yana siffanta layyar Annabi (r), ya ce:
"ويُطْعِمُ أَهْلَ بَيْتِهِ الثُّلُثَ، وَيُطْعِمُ فُقَرَاءَ جِيرَانِهِ الثُّلُثَ، وَيَـتَصَدَّقُ عَلَى السُّؤَّالِ بِالثُّلُثِ"([44]).
Ma'ana: (Zai ciyar da iyalan gidansa xaya-bisa-uku 1/3, ya ciyar da faqirai makwabtansa xaya-bisa-uku 1/3, kuma ya yi sadaka wa masu roqo da xaya-bisa-uku 1/3).
Buraidah -t-, Lallai Annabi (r) yace:
"كُنْت نَهَيْتُكُمْ عَنْ ادخار لُحُومِ الأَضْاحَى بَعْدَ ثَلاَثٍ فَكُلُوا، فَأَمْـسِكُوا مَا بَـدَا لَكُم"([45]).
Ma'ana: (Na kasance na hana ku ijiye naman layyah fiye da kwanaki uku, to ku ijiye na tsawon yadda ya yi muku).
Ummu-salamah –رضي الله عنها-, daga Annabi (r)
"إِذَا دَخَلَ الْعَشْرُ وَعِنْدَهُ أُضْحِيَّةٌ يُرِيدُ أَنْ يُضَحِّيَ فَلا يَأْخُذَنَّ شَعْرًا، وَلا يَقْلِمَنَّ ظُفُرًا"([46]).
Ma'ana: (Idan kwanaki goma suka shiga, a wajen xayanku ya zama akwai abun layyah da zai yi layya da shi to kada ya cire wani gashi, ko ya yanke wani farce).
"فَلا يَمَسَّ مِنْ شَعَرِهِ وَبَشَرِهِ شَيْئًا"([47]).
Ma'ana: (kada ya tava wani abu daga gashinsa da fatarsa).
([1]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 1), da Muslim (lamba: 1907).
([2]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 8), da Muslim (lamba: 16).
([3]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 1773 ) da Muslim (lamba: 1349).
([4]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 1521, da 1820).
([5]) Muslim ya ruwaito shi (lamba: 1349).
([6]) Ahmad ya ruwaito shi (1/314), Albaniy yace hadisi ne hasan (Duba Irwa'ul galil, 990).
([7]) Duba littafin: Nailu al'audaar (4/337).
([8]) Abu-dawud ne ya ruwaito shi (lamba: 4401), da Ibnu-majah (lamba: 2041), Albaniy ya inganta shi a cikin (Irwa'ul galil, lamba: 297).
([9]) Abu-dawud ya ruwaito shi (lamba: 4401), da An-nasa'iy (6/ 156), kuma Albaniy ya inganta shi a cikin (Irwa'ul galil, lamba: 297).
([10]) Muslim ya ruwaito shi (lamba: 1336).
([11]) Ash-shafi'iy ya ruwaito shi a cikin littafinsa "Musnad" (lamba: 743), da Albaihaqiy (5/179), kuma As-sheikh Albaniy ya inganta shi a cikin (Irwa'ul ggalil, lamba: 986).
([12]) Muslim ya ruwaito shi (lamba: 1340).
([13]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 1862), da Muslim (lamba: 1341).
([14]) Ahmad ya ruwaito shi (6/165), da Ibnu-majah (lamba: 2901), Albaniy ya inganta shi a cikin littafin (Sahih sunan Ibni-majah, lamba: 2362).
([15]) Abu-dawud ya ruwaito shi (lamba: 1810), da An-nasa'iy (5/111), da Ibnu-majah (lamba: 2904, 2905), da Ahmad (1/244), kuma Albaniy ya inganta shi (Sahihun nasa'iy, lamba: 2473).
([16]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 1524), da Muslim (lamba: 1181).
A wani lafazin kuma:
"وَمُهَلُّ أَهْلِ الْعِرَاقِ مِنْ ذَاتِ عِرْقٍ".
Ma'ana: (Wurin da mutane Iraaq zasu xaga sautinsu da niyya shine: ZAATU-IRQIN).
([17]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 1), da Muslim (lamba: 1907).
([18]) At-tirmiziy ya ruwaito shi (lamba: 889), da Abu-dawud (lamba: 1949), da An-nasa'iy (5/256), da Alhakim a cikin littafin almustadrak (2/278), ya kuma inganta shi, Albaniy kuma ya inganta shi (Sahih An-nasa'iy, lamba: 2822).
([19]) Muslim ya ruwaito shi (lamba: 1277).
([20]) Ahmad ya ruwaito shi (6/421), da Ibnu-khuzaimah (lamba: 2664), da Albaihaqiy (5/98), Albaniy ya inganta shi (Atta'aliq alah Sahih Ibnu-khuzaimah, 4/232).
([21]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 1755), da Muslim (lamba: 1328).
([22]) Ad-daraquxniy ya ruwaito shi (2/191, lamba: 2512), da Albaihaqiy (5/152), da wassunsu. Wannan maganar ta tabbata i zuwa ga Abdullahi xan Abbas cewa shine ya faxe ta, ba Annabi (r) ba, kamar yadda Ibnu-abdilbarri ya faxa (Duba: Al'istizkaar, 12/184), da kuma Albaniy a cikin littafin (Irwa'u algalil, 4/299).
([23]) Ibnu-majah ya ruwaito shi (lamba: 2045), da Al-hakim a cikin "almustadrak" (2/198), kuma ya inganta shi, Shi kuma Az-zahabiy ya tabbatar da wannan hukunci, Albaniy a cikin littafin (Sahihu Ibni-majah, lamba: 1677) shima ya inganta shi.
([24]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 1815), da Muslim (lamba: 1201).
([25]) Albaihaqiy ya ruwaito shi (5/152), Kuma wannan maganar ta tabbata cewa Abdullahi xan Abbas ne ya faxe ta, ba Annabi (r) ba, kamar yadda Ibnu-abdilbarri ya faxa (Al'istizkaar, 12/184), da kuma Albaniy (Irwa'ul galil, 4/299).
([26]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 1189), da Muslim (lamba: 1397), daga hadisin Abu-hurairah (رضي الله عنه).
([27]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 1190), da Muslim (lamba: 1394).
([28]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 1196), da Muslim (lamba: 1391).
([29]) Abu-dawud ya ruwaito shi (lamba: 2041), da Ahmad (2/527), daga hadisin Abu-hurairah (رضي الله عنه), kuma Annawawiy yace: Isnadinsa ingantacce ne (Al'azkaar, lamba: 349), da Ibnulqayyim a cikin (Jala'ul afhaam, lamba: 32), Albaniy kuma yace: hadisi ne hasan (Sahihu attargib, lamba: 1666).
([30]) Ahmad ya ruwaito shi (3/487), da ibnu-majah (lamba: 1412), da An-nasa'iy (2/37), da wassunsu, Albaniy ya inganta shi (Sahihut targib, lamba: 1181), Ka duba; Al'ahadisul waridatu fi fada'ilul madinah, (542).
([31]) Muslim ya ruwaito shi (lamba: 976).
([32]) Muslim ya ruwaito shi (lamba: 975).
([33]) Muslim ya ruwaito shi (lamba: 1718).
([34]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 5553), da Muslim (lamba: 1966).
([35]) Ibnu-majah ya ruwaito shi (lamba: 3147), da At-tirmiziy, ya kuma inganta shi (lamba: 1505), Albaniy ya inganta shi (Sahihu Ibni-majah, lamba: 2563).
([36]) Muslim ya ruwaito shi (lamba: 1318).
([37]) Muslim ya ruwaito shi (lamba: 1963).
([38]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba:5557), da Muslim (lamba:1965) -61, lafazin Muslim ne.
([39]) An-nasa'iy ya ruwaito shi (7/219), Alhafiz Ibnu-hajar yace: Isnadinsa yana da qarfi (Fat-hul bariy, 10/15), kuma Albaniy ya inganta shi (Sahihu An-nasa'iy, lamba: 4080).
([40]) Malik a cikin "muwanxa'a" ya ruwaito shi (248), da Ahmad (musnad, 4/289), da At-tirmiziy (lamba: 1497), ya kuma ce: hadisi ne hasan sahih, da Abu-dawud (lamba: 2802), da An-nasa'iy (7/244), da Ibnu-majah (lamba: 3144), kuma Albaniy ya inganta shi (Sahih sunan an-nasa'iy, lamba: 4073).
([41]) Bukhariy ya ruwaito shi (6/ 238), da Muslim (3/ 1553).
([42]) Bukhariy ya ruwaito shi (4/ 82), da Albaihaqiy (9/ 295), da Ibnu-hibban (lamba: 1008), da Ad-daraqudniy (4/284), Alhaisamiy ya ce: Maruwaitan da Ahmad da waninsa suka ruwaito hadisin ta hanyarsu amintattu ne (Majma'uz zawa'id, 3/ 25).
([43]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 5560), da Muslim (lamba: 1961).
([44]) Alhafiz Abu-musa ya ruwaito shi a cikin "alwaza'if" ya kuma ce: hadisi ne hasan (Ka duba: Almugniy, 8/632).
([45]) Muslim ya ruwaito shi (lamba: 1977, 3/1564).
([46]) Muslim ya ruwaito shi (lamba: 1977).
([47]) Muslim ya ruwaito shi (lamba: 1977).