تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : HUdUBAR MASALLACIN ANNABI (صلى الله عليه وسلم) ta Abdulbariy Al-Subaitiy, 10/Shawwal/1437H Daidai da 15/Yuli/2016M


طاهر جبريل دكو
_18 _July _2016هـ الموافق 18-07-2016م, 01:32 PM
HUdUBAR MASALLACIN ANNABI (صلى الله عليه وسلم) ta Abdulbariy Al-Subaitiy, 10/Shawwal/1437H Daidai da 15/Yuli/2016M







HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 10/Shawwal/1437H
Daidai da 15/Yuli/2016M




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHIN MALAMI ABDULBARIY XAN AWWADH AS-SUBAITIY






TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA

I
Shehin Malami wato: Abdulbariy xan Auwadh Al-Subaitiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi huduba
1437H, mai taken: I, Wanda kuma ya tattauna a cikinta,.

بسم الله الرحمن الرحيم
Yabo ya tabbata ga Allah; Yabo ya tabbata ga Allah Wanda ya yi mana baiwa da ni'imar aminci da zaman lafiya, Ina yin yabo a gare shi (سبحانه) kuma ina godiya a gare shi, kuma ina roqonsa wa'aztuwa da xaukar izina, kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya, wanda yake cewa: "Kowani abu a wurinsa yana da ma'auni" [Ra'ad: 8].
Kuma ina shaidawa lallai shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa, yayi kira zuwa ga Allah cikin hikima, da gwanancewa. Allah yayi qarin salati a gare shi da iyalansa matukar dare da yini suna canjin aiki.

Bayan haka:
Ina yin wasiyya a gare ku, da ni kaina da bin dokokin Allah, Allah (تعالى) yana cewa:

Allah (تعالى) yana cewa: "Allah Wanda ya sanya qasa ta zama MATABBATA a gare ku" [Gafir: 64].
Ma'ana: Ya sanya qasa ta zamto wurin da akansa kuke samun aminci da tabbatuwa, kuke rayuwa, kuma kuke sassarafa qasa, domin ku aikata abinda kuka ga dama, kuma kuke tafiya a kan hanyoyi ko vangarorinta.
Sha'anonin rayuwa mabanbanta gabaxayansu sun ratayu ne, da SAMUN AMINCI DA TABBATUWA, Kuma rayuwa ba za ta yiwu ba, matuqar aka rasa samun aminci da wurin nitsuwa da tabbatuwa, saboda aminci abu ne da ake cikiyar samu da nema, kuma buqata ce ta dole, kuma babu wani mutum da baya buqatar aminci da wurin nitsuwa da tabbatuwa.
Ita kuma rayuwa, bata yin daxi wa mutum, kuma mutum baya samun walwala, kuma ba zai samu nashaxin raya qasa ba, face a qarqashin inuwar aminci da nitsuwa, ko samun tabbatuwa, wanda shine mafi tsadan abin nema, kuma mafi daraja daga cikin kyautukan abin bauta (wato: Allah); Allah yana cewa: "Kuma muka ce: Ku sauka gabaxaya daga aljanna (zuwa duniya), kuma, kuna da matabbata a cikin qasa, da jin daxi zuwa wani lokaci" .
Don haka, Abun da ya tattara ni'imar duniya da jin daxinta, ko samun walwala da sa'ada a cikinta ya ratayu ne akan samun sabuban aminci da nitsuwa ko samun tabbatuwa, Wannan ya sanya Manzon Allah (S.A.W) yake cewa: "Wanda ya wayi-gari a cikinku da aminci ga ransa, ko a cikin jama'arsa da iyalansa da dukiyarsa, ya wayi-gari da lafiya a cikin jikinsa, ya wayi-gari a wurinsa akwai abincin yininsa, to kamar an haxa masa duniya ne kwacakam xinta".

Kuma shi mumini an yi masa umurnin ya yawata a doron qasa, don neman inda zai samu tabbatuwa ko aminci da nitsuwa, Allah (تعالى) yana cewa: "Lallai waxannan da Mala'iku suke xaukan rayukansu, suna masu zaluntar kayukansu, Su kan ce: A kan me kuka kasance? Sai su ce: Mun kasance waxanda aka raunata su, a bayan qasa, Sai su ce: Ashe qasar Allah bata kasance mai yalwar faxi ba; da za ku yi qaura ko hijira zuwa gare ta!" [Nisa'i: 97].

Lamarin neman nitsuwa da tabbatuwa, ko samun aminci sha'aninsa yana da girma, wannan ya sanya Allah (ta'alah) ya sanya shi a matsayin sifa na lada, ko sakamakon 'yan aljanna da ni'imarsu, a inda Allah (تعالى) yake cewa: "Ma'abuta aljanna a wannan yinin sune suke da matabbata ta alkhairi, kuma su suka fi kyan wurin kishingixa" [Furqan: 24].
Kuma Allah (سبحانه) ya ce: "Suna masu dawwama a cikinta, Matabbata ta kyautata, da matsaya" [Furqan: 76 ].

Kuma addinin musulunci ya tanadi narkon azaba mafi tsanani ga yin varna a doron qasa bayan gyaruwanta, da amincinta da tabbatuwanta, Allah (تعالى) yana cewa: "Daga cikin mutane akwai wanda maganarsa a kan rayuwar duniya zata baka mamaki, kuma yace Allah yana shaide da abinda ke cikin zuciyarsa, amma shi mai matsanancin husuma ne * Idan kuma ya juya, sai ya yi tafiya a bayan qasa don ya yi varna a cikinta, ya kuma halaka shuka da 'ya'ya, kuma Allah baya son varna * Kuma idan aka ce masa: ka bi dokokin Allah da taqawa, sai buwayar savo ta xauke shi, to jahannama ta ishe shi, kuma tir da jahannama ta zama wajen shumfuxi" .
To, duk wanda ya yi varna a bayan qasa, ya kuma rushe ma'anonin da suke kawo aminci da tabbatuwa, da da'awa ko riyawar cewa shi gyara yake yi, ko kuma zai kawo gyara, da kuma da'awar cewa: Shi, yana daga ma'abuta gaskiya, to wannan mavarnaci ne, kamar yadda Allah (تعالى) ya ce: "Idan aka ce musu: Kada ku yi varna a doron qasa, Sai su ce: Lallai mu masu kawo gyara ne * Ku saurara! Lallai su, mavarnata ne, saidai basu sani ba" [Baqara: 11-12].

Musulunci da tsari ko manhajinsa da ya zo daga Ubangiji, shine: Mavuvvugar samun aminci da tabbatuwa, kuma shine tushensa; wato: tabbatuwa ko amincin cikin zuci, da tabbatuwa ta samun aminci da zaman lafiya, da tabbatuwa ko aminci a cikin al'umma.
Kuma musulunci yana gusar da sabuban da suke jawo tsanani da wahala ko qunci da takura, Allah (تعالى) yana cewa: "Wanda Allah ya nufi ya shiryar da shi, ya kan yalwata zuciyarsa da son musulunci, Wanda kuma ya nufi ya vatar da shi, ya kan sanya qirjinsa ya zama cikin qunci, kai ka ce, yana hauhawa sama" [An-aam: 125].

Kuma musulunci ya sanya xaukacin abinda Allah ya ajiye a bayan qasa, na dukiyoyi masu girma, da qofofin shigan kuxi masu yawa a qarqashin gudanarwan mutane, domin su samar da aminci da tabbatuwa, Allah (تعالى) yana cewa: "Shine wanda ya sanya muku qasa abar horewa mai sauqi, sai kuyi tafiya cikin vangarorinta, kuma ku ci daga arziqinsa, kuma zuwa gare shi za a tayar da ku" [Mulk: 15].

Kuma dukkan umurni da hani (wato: تكاليف الشريعة), da manufofin shari'a (مقاصد الشريعة), da wajibabbunta na lalura (ضرورات الشريعة), sun zo ne don su tabbatar da ginshiqan kawo tabbaci ga rayuwar mutane, Wannan kuma kasancewar umurni da hani na wannan shari'ar, suna komawa ne izuwa ga kiyaye manufofin shari'ar a cikin halittu. Kuma waxannan manufofin babu makawa sai an samar da su gabanin tsayuwar maslahohin addini dana duniya, ta yadda idan aka rasa su, maslahohin duniya ba za su tsayu ba, Sai ma su gurvace, su lalace, har a rasa rayuwa. A lahira kuma a yi rashin tsira, tare da rasa tabbatacciyar ni'ima, sai kuma su dawo da hasara mabayyaniya.
Manufofin kuma sune: (1) Kiyaye addini, (2) da rayuka, (3) da tsatso, (4) da dukiyoyi, (5) da hankali.

Al'ummomin da suke fatan samun bunqasa da ci-gaba suna farawa ne da kakkafa ginshiqan samun aminci da tabbatuwa, kuma wannan shine farkon abinda Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya fara magana akansa, a lokacin da ya shiga garin Madina, yana mai hijira, saboda ya faxi ma'anonin da za su jawo aminci da tabbatuwa, cikin kalmomin soyayya da salamar aminci, a inda yake cewa: "Ya ku mutane! Ku yaxa sallama, ku ciyar da abinci, ku sada zumunci, ku yi sallah da dare alhalin mutane suna barci, Sai ku shiga aljanna da salamar aminci".
A nan, Musulunci ya kafa tsari ko manhajin da zai jawo aminci da tabbatuwa, wanda ginshiqinsa shine : kyakkaywar mu'amalar da take ginuwa akan 'yan'uwantaka, da watsar da tsanani ko tsanantawa, da qarfafa taimakakkeniya.
Sai garin Madina ya wayi-gari a matsayin babban misali, wajen aminci da salama da haxewar kai, da tabbatuwa.

Mai yin tunani cikin halin al'ummomin da suka rasa aminci da tabbatuwa a cikinsu, idanunsa ba za su kasa ganin yaxuwar tashin hankali da firgici ba, sai mutane su riqa wayan-gari basu da wani aminci akan dukiyoyinsu ko mutuncinsu (wato: iyalansu).

Wanda kuma yafi kowa sanin qimar aminci da tabbatuwa sune: Waxannan da aka jarrabe su da rashin aminci; har suka gudu suka bar qasarsu, ko suka yi nesa da iyalansu, suka kuma xanxani xacin yunwa, ko kuma qasarsu ta faxa cikin duhun zaman kara-zube da rashin tsari, har ake zubar da jinane akan turvayarta, Sai gawawwakin mutane, ko vangarorin jikinsu suke ta zuba, a cikinta, ko yanayin kwace dukiyoyi da wawashe su ya game ko-ina, a cikinta.

Kuma, da haka ne za mu sani cewa: Lallai samun aminci da tabbatuwa, a cikin garurruka da rayuka da dukiya da mutunci (ko iyalai) aljannar Allah ce, da baiwarsa ga muminai tun a nan gidan duniya, kuma shine mafi girman abinda Allah yayi baiwa da shi ga al'ummai da mutane, Allah (تعالى) yana cewa: "Sai su bauta wa Ubangijin wannan xaki * Wanda ya ciyar da su daga yunwa, kuma ya amintar da su daga tsoro" [Quraish: 3-4].
Kuma masu hankali basa shakkar cewa, lallai aminci shine ginshiqin bunqasa, kuma shine kyakkyawan yanayin da zai kai ga gina qasa, ko bunqasa ta, da kawo aikin rayar da qasa.

Yana daga abinda ke rushe aminci, ko ya sanya ginshiqansa rawa, Yaxuwar jita-jita, da bazuwar qare-rayi, da kuma karvarsu ba tare da tunani ko tsanaki ba.
Yin haka kuma yana tayar da fitintinu, kuma yana shuka rarrabuwar kai da savani.
Kamar yadda, munana xaukar ababen da aka samu ta kafar sada zumunta na zamani (facebook,,,); kafar da take da matsayi na gaba-gaba wajen samun himmar mutane: ya haifar da kwan-gaba, kwan-baya wajen tarbiyya, kuma ya sanya shakku kan wasu aqidun, kuma ya rushe dayawa daga tabbatattun halayya, Sai waxannan hanyoyin -da irin wannan fahimtar- suka wayi-gari a matsayin gatarin da ke rurrushe, aminci da zaman lafiya.

Sakaci wajen mu'amala da haram, da qoshi da dukiyar riba, yana kwashe ginshiqan tabbaci ta vangaren dukiya, Allah (تعالى) yana cewa: "Allah yana kwashe albarkar riba, kuma yana bunqasa sadakoki, Kuma Allah baya son dukkan mai kafirci mai yawan savo" [Baqara: 276].

Qetare iyaka da riqon sakainar kashi ga ni'imomi, da qaranta yin godiya, tare da almubazzaranci, ko rowa, su kuma suna jawo rashin nitsuwa ko rashin aminci a cikin al'ummai, Allah (تعالى) yana cewa: "Sau dayawa mun halaka alqaryoyi waxanda suka yi sako-sako da lamarin rayuwarsu, Kuma waxancan sune wuraren zamansu, ba a zauna a cikinsu, a bayansu ba, sai xan kaxan, kuma mun kasance mune masu gajewa" [Qasas: 58].

Lallai ne fitintinun da suke kewaye da mu, sun nuna mana, kuma mun koya daga gare su, cewa: Kiyaye aminci da tabbatuwa, wani lamari ne da ba za a iya wadatuwa ga barinsa ba. Kuma yin aiki don tabbatar da ginshiqan aminci, da kakkafa vangarorinsa, da yin duka da qarfe ga hannun mai rushe-rushe da mavarnaci wajibi ne na shari'a, kuma abun nema ne ga qasashe.

Kuma kiyaye samun aminci da tabbatuwa yana tabbata ta hanyar samar da Imani, da kuma yin riqo da alqur'ani da Sunnah, da samar da haxin kai, da guje wa sabuban da suke jawo rabuwar kai da savani, Allah (تعالى) yana cewa: "Duk wanda ya sava wa Manzo bayan shiriya ta bayyana masa, kuma ya ke bin turbar da ba ta muminai ba, za mu jivinta masa abinda ya jivinta, kuma mu shigar da shi jahannama, kuma ta yi muni ga makoma" [Nisa'i: 115].

Aminci yana tabbatuwa kuma yana dawwama: Ta hanyar yaxa ilimin da ke haskaka duhu, ya kuma yaye baqin ciki, ya kawo bunqasa, sannan ya riqa bada kariya daga aqidu da shubuhohi, ko aukawa cikin qari ko sakaci (ga addini). Kuma shi ilimi shine ginshiqin samun rabo ga xaixaikun mutane, da kuma wadaci ga al'ummomi, Allah (تعالى) yana cewa: "Ka ce: Shin waxanda suke da sani, za su yi daidai da waxanda basu da sani" [Zumar: 9].

Kuma aminci yana dawwama: Da ambaton falalar Allah (تعالى), da yin godiya a gare shi, Allah (تعالى) yana cewa: "A lokacin da Ubangijinka ya bada shela cewa: Idan kuka yi godiya, to zan yi qari a gare ku, Idan kuma kuka butulce to lallai azabata mai tsanani ce" [Ibrahim: 7].

Allah yayi mini albarka ni da ku, cikin alqur'ani mai karamci, ya kuma amfanar da mu da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima, Ina faxar maganata wannan, ina kuma neman gafarar Allah, wa NI da KU, da kuma sauran musulmai, ku nemi gafararSa, lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
[B]…

[B]HUXUBA TA BIYU
Yabo na Allah ne wanda ya yi halitta kuma ya daidaita, "Wanda ya qaddara, kuma ya shiryar" [A'alah: 3], Ina yin yabo a gare shi, kuma ina gode masa, akan ni'imarSa da ba a iya qididdige ta, kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yake bashi da abokin tarayya, Maxaukaki Wanda yafi xaukaka,
Kuma ina shaidawa lallai shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa, Wanda ya yi kira zuwa ga kowani alkhairi da shiriya,
Allah ya yi qarin salati akansa da iyalansa da sahabbansa, da waxanda suka bi shiriya.

Aminci yana tabbatuwa kuma yana dawwama: Ta hanyar kulawar al'umma da yin Umurni da kyakkyawa, da hani kan aikata mummuna, tare da bunqasa lamarin aiyukan alkhairi, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma a samu wata al'umma daga cikinku, suna yin kira zuwa ga alkhairi, suna yin umurni da kyakkawa, kuma suna hani ga mummuna, kuma waxannan sune masu samun rabo" [Ali-Imraan: 104].
Sai ya tabbatar da alkhairi, ga al'ummar wanda shine, ginshiqin samun aminci, ta hanyar samar da taimakakkeniya da alaqa, da danqon zumunta da soyayya. Kuma lallai yin aiyuka na alkhairi ko na taimakakkeniya, ginshiqi ne na bunqasar al'umma, da samun wadaci, da aminci, a lokacin da rayuwa zata tabbatu ga marayu da miskinai da matar da ta rabu da mijinta, da marasa lafiya. Kuma aiyukan kyauta, su kan sanya ganuwa ga faxar banbancin matsayi (da ke aukuwa tsakanin masu kuxi da marasa, shi), kuma ganuwa ga hassada, Sai su fiskantar da kowa (talaka da mai kuxi) izuwa ga yin aiki, da tunanin cigaba, da gina al'umma, ko qasa, Allah (تعالى) yana cewa: "Wanda ya yi aiki na kwarai, namiji ne ko mace, alhalin yana mumini, lallai za mu rayar da shi, rayuwa daddaxa, kuma za mu sakanta musu ladansu da mafi kyan abinda suka kasance suke aikatawa" [Nahl: 97].

Sai ku yi salati, -Ya ku bayin Allah- ga Manzon shiriya, sabodaAllah ya umurce ku da aikata haka, a cikin littafinsa; a inda yake cewa:
"Lallai Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Yaku waxanda suka yi Imani, ku yi salati a gare shi, da sallama na aminci" [Ahzab: 56].

Ya Allah! kayi salati wa Annabi Muhammadu da iyalanSa da sahabbanSa. Ya Allah!Ka yarda da khalifofi gudahuxu shiryayyu; Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu da iyalansa da sahabbansa masu krimci, ka haxa da mu da baiwarka, da rahamarka, Ya mafificin masu rahama.
Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai, Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai, kuma ka qasqantar da kafirci da kafirai, kuma Ya Allah! Ka ruguza maqiyanka; maqiyan addini, Ya Allah! Ka sanya wannan qasar ta zama da aminci, cikin nitsuwa, da sauran qasashen musulmai.
Ya Allah! Ka karvi azuminmu da sallolinmu da ruku'inmu da sujadanmu, Ya Allah! Ka sanya mu daga cikin waxanda ka karvi azuminsu da sallolinsu ya mafi rahamar masu rahama.
Ya Allah! Lallai ne mu muna roqonka aljanna, kuma muna neman tsarinka daga wuta.
Ya Allah! Muna roqonka alkhairi gabaxayansa; na gaggawa daga cikinsa da na nesansa, wanda muka sani daga cikinsa da wanda ba mu sani ba, kuma muna neman tsarinka daga sharri gabaxayansa; na gaggawa daga cikinsa da na nesansa, wanda muka sani daga cikinsa da wanda ba mu sani ba.
Ya Allah! Lallai ne mu muna roqonka mabuxan alkhairi da qarshensu, da abinda ya tattara su, da farkonsu da qarshensu, da zahirinsa da baxininsa, kuma muna roqonka darajoji maxaukaka a cikin aljanna, Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah! Ka kiyaye rundunoninmu masu tottoshe kafofin varna (ribaxi), Ya Allah! Ka kiyaye jami'an tsaronmu, Ya Ubangijin talikai. Ya Allah! Ka kiyaye su a ko-ina suke, Ya Allah! Ka zama mai qarfafarsu, Mai taimakonsu, Mai tagaza musu, Ya Allah! Ka karvi wanda ya mutu daga cikinsu yana mai shahada, Ya Allah! Ka xaukaka darajarsu cikin darajar "illiyuna", Ya Allah! Ka ninnika kyawawansu, kuma ka yi musu rangwame akan munanansu, kuma ka xinke karayar iyalansu da danginsu, Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah! Wanda ya nufe mu, ko ya nufi musulmai da mummuna, to ka shagaltar da shi da kansa, kuma ka sanya rugujewarsa cikin tsarinsa Ya mai amsa addu'a.
Ya Allah! Ka sanya wannan qasar cikin aminci da zama lafiya da wadaci da yalwa, da sauran qasashen musulmai, Ya Ubangijin halittu.
Ya Allah! Ka datar da shugabanmu zuwa ga abinda kake so, kuma yarda, Ya Allah! Ka datar da shi zuwa ga shiriyarka, kuma ka sanya aiyukansa cikin yardarka, kuma ka bashi lafiya, Ya ubangijin talikai.
Ya Allah! Ka datar da jagororin musulmai wajen yin aiki da littafinka da yin hukunci da shari'arka, Ya mafi rahamar masu rahama.
"Ya Ubangijinmu! Mun zalunci kayukanmu idan baka gafarta mana, ka yi mana rahama ba to zamu kasance daga cikin masu hasara" [A'araf: 23].
"Ya Ubangijinmu! Ka bamu mai kyau a duniya, kuma ka bamu mai kyau a lahira, ka kare mu daga azabar wuta" [Baqarah: 201].

"SUBHANA RABBIKA RABBIL IZZATI AMMA YASIFUN, WA SALAMUN ALAL MURSALINA, WALHAMDU LILLAHI RABBIL ALAMINA" [].