تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : HUXUBAR MASALLACIN ANNABI (صلى الله عليه وسلم) JUMA'A, 03/SHAWWAL/1437H Daidai 08/07/2016M


طاهر جبريل دكو
_9 _July _2016هـ الموافق 9-07-2016م, 05:24 PM
2016/07/08
HUdUBAR MASALLACIN ANNABI ta, 3/SHAWWAL/1437H daga SHEHI HUSAINI DAN ABDUL'AZIZ ALU AL-SHEIKH







HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 03/SHAWWAL/1437H
Daidai 08/07/2016M




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI HUSAINI XAN ABDUL'AZIZ ALU AL-SHEIKH







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA

SE KUMA ME, BAYAN SHUXEWAR WATAN AZUMI?
Shehin Malami wato: Husaini xan Abdul'aziz Alu Al-Sheikh –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: SE KUMA ME, BAYAN SHUXEWAR WATAN AZUMI, Wanda kuma ya tattauna a cikinta, akan watan ramadana da tunatarwa kan shuxewar yininsu da dadarensu, da abinda suka qunsa a cikinsu na aiyukanmu; na alkhairinsu da sharrinsu, Sannan ya ambaci lamarin tayar da boma-bomai da ya zama sababin zubar da jinane da kashe rayuka a qasar Harami guda biyu, Yana mai faxakar da iyaye da Maluma da wayayyu da kafafen yaxa labaru cewa su riqa karantar da samari suna faxakar da su kan shari'ar Allah (تعالى).

بسم الله الرحمن الرحيم
Godiya ta tabbata ga Allah akan ni'imominsa da ba a qididdige su. Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke ba shi da abokin tarayya, a lahira da duniya, kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa, annabi zavavve, kuma bawa zavavve. Ya Allah ka yi daxin salati da sallama da albarka a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, ma'abuta gaskiya da bin dokoki da taqawa.
"Ya ku waxanda suka yi imani ku bi dokokin Allah da taqawa, kuma ku faxi magana ta daidai * Zai gyara muku aiyukanku, kuma ya gafarta muku zunubanku, kuma duk wanda ya yi xa'a wa Allah da Manzonsa to haqiqa ya rabauta da rabo mai girma" [Ahzab: 70-71].

'Yan'uwan Musulunci
Ka yi mamakin saurin shuxewar kwanaki, da wucewar watanni! Shi mai hankali wanda aka yi masa dacen taufiqi shine yake riqan kwanaki da watanni a matsayin lokatai na kusantar Allah majivinci –جل وعلا-, Sai ya kiyaye yin biyayya a gare shi, a sirrance da a bayyane.

Kuma lallai abinda ya wajaba akan musulmi a cikin wannan rayuwar shine ya yi qoqarin tabbatar da manufar samar da shi, a tsawon rayuwarsa gabaxayanta; ta hanyar tsayuwa akan tauhidi da bin dokoki , da biyayya wa Allah.
Saboda rayuwa gabaxayanta; Manufarta mafi girma itace, yin aiki da umurnin Allah, da qoqarin tabbatar da yin bauta a gare shi (سبحانه), Allah (تعالى) yana cewa:
"Ka ce: Lallai sallata da yanke-yankena, da rayuwata, da mutuwata ga Allah ne Ubangijin talikai * Bashi da abokin tarayya, kuma da aikata haka aka umurce ni, kuma nine farkon musulmai" [An'aam: 162-163].
Kuma Allah (تعالى) yace: "Kuma, ka bauta wa Ubangijinka har sai mutuwa ta zo maka" [Hijir: 99].
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana ambaton Allah a dukkan lokutansa.

Ya ku taron Musulmai!!
Idan har Musulmi ya tsayu a cikin watan ramadana don ya amfana da lokutansa, ta hanyar gaggawa cikin aikata aiyukan alkhairori, da kuma kusantar Ubangiji da sauran mustahabbai, To wajibi ne akansa yayi godiya wa Allah ([g (جل وعلا) akan haka, Sai kuma yayi iya qoqarinsa a cikin shekaransa gabaxayanta, wajen aikata dangogin xa'a, gwargwadon iko, saboda Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Mafi soyuwan aiyuka a wurin Allah shine wanda aka dawwama akansa, koda ya yi kaxan", Bukhariy da Muslim.

Ka yi hanyoyin samun lada, da kwasan garavasar kyawawan aiyuka, a cikin shari'ar rangwame da sauqi da rahama da falala (shari'ar musulunci), suna da matuqar yawa, kuma nau'i-nau'i ne, a cikin zantuka da aiyuka.

'Yan'uwan Musulunci!!
Sha'anin da yafi girma, Shine musulmi ya tsayu wajen aikata aiyuka na wajibi, da nisantar munana; ababen kyama da shari'a ta yi hani akansu, Allah (تعالى) yana cewa:
"Ka tsayu, kamar yadda aka umurce ka, da waxanda suka tuba a tare da kai, kuma kada ka qetare iyaka" [Hud: 112].
Kuma Manzonmu (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Ka ce: Na yi Imani da Allah, sa'annan ka tsayu", Muslim ya ruwaito shi.

Ya ku bayin Allah!
Ku kiyaye aiyunku kyawawa da kuka aikata, kuma ku nisanci gurvata abinda Allah yayi muku ni'ima da shi, saboda fallasasshen Mutum a madubi na shari'a, kamar yadda nassoshi suka nuna shine: Wanda zai gina aiyuka kyawawa manya-manya, sa'annan sai ya rushe su, ta hanyar sakar wa gavvansa linzami cikin zaluntar halittun Allah, da yin ta'addanci a gare su, cikin magana ko aiki.

Ya ku taron Musulmai!
A qarshe-qarshen watan azumi, a lokacin da musulmai suke farin cikin qarisa azumi da salloli ko tsayuwar dare, bayan kuma Allah ya yi wa Musulmai dacen kammala tilawar maganar Allah Mai hikima, Masani: Sai kwatsam musulmai suka tashi da jin labarin aika-aikan kaiwar harin boma-boman da suka zubar da jini suka kuma kashe rayuka suka tsoratar, har guda uku, a qasar harami guda biyu, wanda a cikinsu suka qunshi mafi girman ababen qi, Daga cikin laifuka kuma mafi muninsu, Daga cikin kaba'irai kuma mafi girmansu, daga wata qungiya, wanda ta karkace daga karantarwar wahayin alqur'ani da sunnar Manzo, sannan qungiyar ta gudu daga jama'ar musulmai, kuma ta haifar da ababen da suka jawo varna mai girma a qasashen musulmai, da kuma sharri mai yaxuwa, Wanda babu mai farin ciki da aukuwar haka sai maqiyan addini.
Shin waxannan, ba za su ji tsoron damqar Mai girma Allah ba, Shin ba za su yi taqawar Mabuwayi Mai rinjaye ba. Ina suke lokacin da Ubangijinsu zai tambaye su, kan kashe rayukan mutanen da basu jib a, basu gani ba?! Menene kuma matsayansu dangane da mahaliccinsu, alhalin suna yawo da varna mai faxi, ta hanyar razanar da amintattu, masu bauta, da sallah, ta hanyar kashe marasa laifi, masu azumi, musamman a kusa da masallacin ManzonSa amintacce, a cikin wata mai girma, alhalin sauran mutane su kuma suna cikin salloli, da qanqan da kai ga Ubangijin talikai!
Ku saurara!
Ya ku samari Musulmai!
Ku tsaya, tsayawa ta hankalta, da tunani, kuma ku xauki darasi daga munanan qarshe, wacce aqidun waxanda suka karkace daga jama'ar musulmai, su ke kai su, mutanen da suka halatta jinin masu bauta, masu azumi, da salloli, da i'itikafi (don yin bauta) ga Ubanjinsu, suna masu ruku'i da qanqan-da kai (a gare shi).
Ya wanda aqida da tunani suka sanya shi zamewa daga (turbar) daidai, har ya kauce wa hanya ya bar turbar gaskiya… Ka tuba izuwa ga Ubangijinka gabanin ka sadu da shi, Ka dawo zuwa ga hanyar muminai kamar yadda Ubangijinka ya umrce ka da aikata haka, kuma Manzonsa (صلى الله عليه وسلم) ya umurce ka da aikata haka, Ka komo izuwa ga kewayen jama'ar musulmai, saboda nassoshin shari'a sun tsawatar maka, daga fanxare wa jama'a, kuma sun hane ka, kan raba kai, da nisantar jama'a.
Kuma mafi girman hanyar da Shexanun aljanu ko na mutane suke bi don vata kwakwale, kuma domin fitar da su daga shiriya miqaqqa, ita ce: Nisantar jama'ar (musulmai) masallata, da shiriyar masu bauta, da turbar muminai, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma kada ku bi hanyoyin da shexan ya tsattsara, lallai shi a gare ku, maqiyi ne mabayyani" .
Kuma Alqur'ani da sunna basu nusar da mu ba, sai izuwa ga ababen da zasu gyara halayenmu, Kuma a duk lokacin da muka yi nisa da haka, sai varna mai faxi ta auku.

Ya ku samari musulmai!
Lallai mafi girman takobi ko makamin masu qiyayya da musulunci, kuma maqiya annabi Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) suke bi; domin kekketa alfarmar addini, ko kuma domin su yaqar garurrukan musulmai: Mafi girman makaminsu shi ne Ta hanyar qosar da sabbuban jawo rabuwar kai (a cikin al'ummah), da fitar da samari daga jama'ar musulmai, da hujjojin da zahirinsu rahama ne, baxininsu kuma azaba, wato: hujjar taimakon addini, da yin hidima wa lamuransa. Hakan kuma baya kasancewa daga gare su sai bayan sun nesanta samari daga Maluma na Allah, da jiga-jigan faqihai masu tantancewa, da shugabanni masu neman kawo gyara.
Kuma duk wanda ya karanta tarihi to hakan zai bayyana masa qarara; Saboda (a tarihance) babu abinda ya sha gaban al'ummar Annabi Muhammadu (S.A.W) wajen hidima ga addininta, da yaxa saqon Annabinta, fiye da fitinar (khawarijawa) ta fanxarewa jama'ar musulmai, wanda dukkan ma'abuta musulunci gabaxaya suke tare da ita. Saboda idan akwai irin waxannan fitintinun to ba za a iya hidima wa addini ba, kuma ba zai yiwu a yi masa hidima ba, kuma ba za a iya tsayar da wata rayuwa managarciya ba. Hasali ma fanxarewa jama'ar musulmai bai jawo komai ga musulunci da musulmai ba, sai varna mai girma, ga al'ummar annabi Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) da kuma sharri mai yaxuwa, wanda harshen mai fasaha bai isa ya qididdige irin varnar ba, a wuri irin wannan.

Ya ku Mutanen wannan qasa !
Lallai qasarku ana nufinta da sharri, cikin hidimarta ga harami guda biyu, da kuma cikin abinda Allah yayi mata na ni'imomi masu yawa, sai ku haxakanku akan alkhairi, ku nisanci rabuwa da dukkan nau'ukansa, ku kiyaye tarkon maqiya, da masu jiran ganin sharri, waxanda suke yin fata a gare ku, da al'ummarku, da 'ya'yanku da jikokinku masu zuwa suke muku fatan qarewa da halaka da rugujewa.

Lallai kafafen sadarwa wajibi ne akansu su gyara tafiyarsu, kuma su zama an fiskantar da su don kawo amincin al'ummai, da kiyaye yara da jikoki.
Kuma wajibi ne akan dukkan musulmai su nisanci makami mai illa, wanda raunin da yake yi yana zubar da jini, Shine: Jita-jita masu mugun manufa, da qarerayi da ake watsawa.
Wajibi ne ga ma'abuta garin harami biyu, su zama jinni da tsoka tare da jagororinsu, suna xauka daga malumansu na Allah, waxanda aka yi musu shaida da zurfin ilimi da addini da tsantseni da hikima da sanin jiya-da-yau.
Kuma wajibi ne akan kowa, ya rinjayar da maslahohi na gabaxaya, akan na xaixaiku. Kuma suyi ta faxi-tashi wajen hidima wa qasarsu, da gaskiya da ikhlasi, suna masu neman lada da sakayya (a wurin Allah), saboda su qasar harami ne guda biyu da suke yin hidima wa addini, kuma suke yin hidima wa musulmai gabaxaya, wajibi ne su yi qoqari wajen haka, suna xaukar haka daga faxakarwar addininsu da manufofin shari'arsu.
Wajibi ne akan iyalai su riqa kula da 'ya'yansu samari, suna bibiyar halayensu, suna dubi cikin yanayinsu, kuma su riqa sanya musu ido cikin ababen da suke fiskanta, tare da komawa zuwa ga Allah (جل وعلا) da yin addu'ar cewa ya kiyaye 'ya'yansu daga kowace fitina da jarabawa da aqida vatacciya, saboda addu'a daga iyaye guda biyu sababi ne mai girma na samu gyaruwa.

Ya malaman wannan al'ummar!
Himmatuwa da lamuran wannan al'ummar ya kasance kuna sanya hikima a cikinsa da kaifin hankali, da kyautata duban mai zai kai ya komo, kuma mu kiyayi kowani Magana ko fatawar da samari za su iya fahimtarta ba a gurbinta ba, ko su su xora ta ba a ingantaccen wajen xaukar ta ba. Wannan kuma ba zai yiwu ba, sai idan ana lura da manufofin shari'a, waxanda maluman musulunci suka yi bayaninsu, tare da kyautata karatun fahimtar addini ta hanya miqaqqa, wanda zai xauki samari izuwa ga aiki da hikima da bi sannu-sannu, da tausasawa, da nisantar gaggawa.

Daga qarshe:
Kalmar godiya ce, ga jami'an tsaro a qasarmu, da kuma mutum na farko mai kula da tsaro (shugaba), saboda suna kan tozo na azama, da hasama, da kula da hidima wa musulmai, da kiyaye musu amincinsu, da zaman lafiya, bayan Allah (جل وعلا); da fatan Allah ya saka musu da mafi alkhairin sakamako, kuma Allah ya kiyaye su daga kowani mummuna. Kuma ya karvi wanda yam utu daga cikinsu cikin shahidai, kuma Allah ya warkar da kowani maras lafiya mai rauni.

Ina faxar wannan maganar, kuma ina neman gafarar Allah wa ni da ku da sauran musulmai daga kowani zunubi, sai ku nemi gafararsa, lallai shi mai gafara ne mai rahama.

HUXUBA TA BIYU
Ina godiya wa Ubangijina kuma ina yin yabo a gare shi.

Ya ku Musulmai:
Yana daga falalar Allah (سبحانه) ga al'umma: Abinda ya shar'anta a gare su, na aiyukan biyayya da xa'a; waxannan da za su basu lada mai yawa, Saboda (ai) ya tabbata daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) faxinsa:
"Wanda yayi azumin ramadana, sannan ya biyar da guda shida a watan shawwal, to kamar ya azumci shekara ne".

Kuma baya halatta –a xayan zancen maluma guda biyu da yafi fitowa fili-, ga wanda akwai ramukon azumi na wajibi akansa ya gabatar da azumi na mustahabbi; saboda yin hakan ya saba wa qa'idodin shari'a, da kuma nassoshi ingantattu.

Sai ku kasance –Ya ku bayin Allah- kuna masu xaukar darasi daga watan azumi, wanda zai kai ku izuwa ga falaloli masu girma, da halayya kyawawa. Kuna masu siffantuwa da sifar kyauta a rayuwarku gabaxaya, da kuma kyautatawa da jin qai a asirce da a bayyane.
Kuna rayuwa a matsayin al'ummar annabi Muhammadu wacce take rayuwa a duniya da halayya maxaukaka, da kyawawan ababe masu girma. Kuma yin hakan, yana cikin MANUFOFIN ADDININ UBANGIJINKU na farlanta farillai, da wajabta wajibabbu.

Sannan yana daga cikin aiyuka mafi girma: Yin salati da sallama ga annabi mai karimci,
Ya Allah! Kayi salati da sallama da albarka ga annabinmu kuma shugabanmu, masoyinmu annabi Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa gabaxaya.
Ya Allah! Ka xaukaka musulunci da musulmai, Ya Allah! Ka kiyaye musulmai a kowani wuri, Ya Allah! Ka kiyaye musulmai a kowani wuri, Ya Allah! Ka kiyaye musulmai a kowani wuri, Ya Allah! Ka kiyaye su da kiyayewarka, da kulawarka da kariyarka, Ya Allah! Ka yayebaqin cikinsu, ka kawar da vacin ransu.
Ya Allah! Ka yi maganin maqiya musulunci, Ya Allah! Ka yi maganin maqiya musulmai, Ya Allah! Ka vata tsare-tsarensu da makircinsu, Ya Ma'abucin girma da karramawa, Ya Allah! Ka vata tsare-tsarensu da makircinsu, Ya Mabuwayi Ya Mai hikima.
Ya Allah! Ka gafarta wa muminai maza da muminai mata, da musulmai maza da musulmai mata, rayayyu daga cikinsu da matattu.
Ya Allah! Ka datar da majivincin lamarinmu zuwa ga abinda ka ke so, kuma ka yarda, Ya Ma'abucin girma da karramawa.
Ya Allah! Ka kiyaye qasarmu daga dukkan mummuna da abin qi, da sauran qasashen musulmai, Ya Allah! Ka kiyaye qasarmu daga dukkan mummuna da abin qi, da sauran qasashen musulmai, Ya Ma'abucin girma da karramawa.
Ya Allah! Ka kiyaye jami'an tsaronmu, Ya Allah! Ka kiyaye jami'an tsaronmu, Ya Allah! Ka qarfafe su, ka datar da su, ka tagaza musu, Ya Rayayye Ya tsayayye.
Ya Allah! Ka kiyaye mahajjata da masu umrah, Ya Allah! Ka kiyaye mahajjata da masu umrah, Ya Allah! Ka kiyaye mahajjata da masu umrah, Ya Ma'abucin girma da karramawa. Kuma ka mayar da su zuwa qasashensu cikin lafiya da riba, Ya Rayayye, Ya Tsayayye.
Ya Allah ka bamu mai kyau a duniya, A lahira shima mai kyau, Ka kare mu daga azabar wuta.
Ya Allah! Ka sanya mu cikin waxanda ka karvi azuminsu da sallolinsu, kuma ka gafarta musu zunubansu, Ya Rayayye Ya tsayayye.
Ya Allah! Ka samar wa musulmi wani lamari na shiriya, Ya Allah! Ka samar wa musulmi gabaxaya wani lamari na shiriya, wanda zaka gyara halinsu da shi, Ya rayayye Ya tsayayye.
Qarshen addu'armu shine: ALHAMDU LILLAHI RABBIL ALAMINA.




MAS'ALOLI CIKIN AZUMI WADANDA HUKUNCINSU KE IYA BUYA GA DAYAWA DAGA MUTANE


MUHIMMAN MAS'ALOLIN DA HUKUNCINSU KE IYA VUYA DANGANE DA AZUMI

Amsawar Shehin Malami, Abdul'aziz xan Abdullahi Ibnu-baaz, Allah yayi masa rahama, amin

NA XAYA DA NA BIYU:
YIN MAFARKI BAYA KARYA AZUMI,
HAKA KUMA JINKIRTA YIN WANKAN JANABA
Tambaya: Idan mai azumi ya yi mafarki a cikin yinin ramadhana Shin azuminsa yana lalacewa, ko a'a? kuma shin wajibi ne akansa ya yi gaggawan yin wanka? Kuma shin ya halatta a jinkirta wankan janaba dana haila da kuma na biki? ([1])
Amsa: Shi dai mafarki baya lalata azumi; saboda ya kan kasance ne ba da zavin Shi mai yin azumin ba, Amma kuma wajibi ne akansa ya yi wanka matuqar ya ga ruwan maniyyi, da kuma zai yi mafarki bayan sallar asubah, amma sai ya jinkirta wankansa har zuwa lokacin sallar azahar to da babu laifi cikin hakan, haka kuma da zai yi jima'i da matarsa cikin dare amma sai ya jinkirta wankansa zuwa bayan fudowar alfijir to babu qunci akansa cikin hakan, saboda ya tabbata daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) cewa:
«كَانَ يُصْبِحُ جُنُبًا مِنْ جِمَاعٍ ثُمَّ يَغْتَسِل ويَصُومُ».
"Lallai Shi ya kasance yana wayan gari da janaba sakamakon jima'i, sannan sai ya yi wanka ya kuma yi azumi"([2]).
Haka itama mace mai haila da mai jinin biqi (haihuwa), da za su yi tsarki da daddare saidai kuma basu samu su ka yi wanka ba sai bayan ketowan alfijir to basu da wata matsala; kuma azuminsu ingantacce ne. Saidai kuma baya halatta a gare su, haka Shima mai janaba su jinkirta wankan zuwa futowar rana, saboda wajibi ne akansu su yi gaggawar yin wanka gabanin fudowar rana; domin su samu su yi sallah a cikin lokacinta, kuma wajibi ne ga namiji ya yi gaggawan yin wanka don ya riski sallar asuba a cikin jam'i([3]). Kamar yadda wajibi ne ga mai haila da mai jinin biqi su yi gaggawan yin wanka idan suka ga alamun tsarki a cikin dare domin su sallaci sallar magriba da ishah na wannan daren, kamar yadda jama'a daga cikin sahabban Annabi (صلى الله عليه وسلم) su ka yi fatawa da haka, lamarin kuma haka ya ke da za su yi tsarkin a lokacin la'asar dole ne su yi gaggawan wanka domin su samu su sallaci azahar da la'asar gabanin faxuwar rana. Allah ne majibincin dacewa!

NA UKU DA NA HUXU:
AZUMI BAYA LALACEWA DA YIN MAFARKI
HAKA BAYA LALACEWA DA FITAR JINI KO AMAI:
Tambaya: Na kasance mai azumi sai na yi barci a masallaci, dana tashi sai na samu cewa na yi mafarki, Shin mafarkin yana da tasiri ga azumina? Tare da cewa banyi wanka ba sai kawai na yi sallah ba tare da nayi wankan ba.
Wata rana kuma dutse ya rotse min kai sai jini ya kwarara, Shin azumina ya lalace saboda fitan jini?
Dangane da amai kuma shin yana bata azumi ko a'a? Ina fatan a amfanar da ni? ([4])
Amsa: Lallai mafarki baya lalata azumi, kuma baya yi masa tasiri; saboda kasancewarsa yana fita ne ba a cikin zabin mutum ba, Sai dai kuma wajibi ne akansa ya yi wankan janaba idan har maniyyi ya fita daga gare shi, saboda Annabi (صلى الله عليه وسلم) yayin da aka tambaye shi kan haka, sai ya amsa da cewa mai mafarki zai yi wanka ne; idan har ya ga ruwa (maniyyi).
Sallar da ka aikata ta kuma ba tare da ka yi wanka ba wannan jahilci ne daga gare ka, abun kyama, kuma dole ne akanka ka sake sallah bayan ka yi wanka, kana mai tuba zuwa ga Allah (سبحانه وتعالى).
Shi kuma dutsen da ya rotse kanka har ya kwararar da jinni babu komai akan haka.
Shi kuma amai da ya fita maka ba tare da zavinka ba, to ba zai vata maka azuminka ba; saboda faxin Annabi (صلى الله عليه وسلم):
«مَنْ ذَرَعَهُ الْقَيْءُ فَلَا قَضَاءَ عَلَيْهِ، وَمَنِ اسْتَقَاءَ فَعَلَيْهِ الْقَضَاءُ».
Ma'ana: "Wanda amai ya rinjaye shi to babu ramukon azumi akansa, duk kuma wanda ya janyo amai to wajibi ne akansa ya yi ramuko"([5]), Ahmad da ma'abota littafan "sunan" suka rawaito shi da isnadi ingantacce.
$&$



NA BIYAR:
FITAR MAZIYYI DA SHA'AWA BAYA KARYA AZUMI
Tambaya: Idan mutum ya yi sumba alhalin yana azumi, ko kuma ya kalli wassu finafinai na tsiraici sai maziyyi ya fita masa, Shin akwai ramukon azumi akansa? Idan kuma hakan ya kasance a cikin kwanaki ne mabanbanta shin ramukon dole su zama a jejjere, ko za a iya yinsu a rarrabe?
Allah ya muku sakayya da mafi alherin sakamako saboda hidima ga musulunci ! ([6])
Amsa: Fitan maziyyi baya lalata azumi a maganar da ta fi inganci daga cikin maganganun maluma guda biyu, lamarin haka ya ke sawa'un ya fita ne saboda sunbantar mata, ko kuma ta hanyar kallon finafinai, ko kuma makamantan haka daga abubuwan da su ke tada sha'awa.
Saidai kuma baya halatta ga musulmi ya kalli finanai tsiraici da batsa, ko kuma sauraron abinda Allah ya haramta na sauraron waqoqi, ko kayan kaxe-kaxe.
Fitar maniyyi kuma da sha'awa to shi yana lalata azumi; sawa'un hakan ya auku ne sakamakon runguma ko sumbanta ko maimaita kallo, ko makamancin haka daga cikin sabbuban da su ke tada sha'awa; kamar wasan fitar da maniyyi (istimna'i), da makamancinsa.
Yayin da mafarki ko yin tunani su kuma azumi ba ya vaci da su, koda kuwa maniyyi ya fita da sababinsu.
Kuma ba dole ba ne jerantawa wajen ramukon ramadhana, hasalima ya halatta a rarrabe hakan, saboda gamewan faxin Allah ta'alah:
ﭽ ﭵ ﭶ ﭷ ﭸ ﭹ ﭺ ﭻ ﭼ ﭽ ﭾ ﭿ ﭼ البقرة: ١٨٤
Ma'ana: "Duk wanda ya kasance daga cikinku maras lafiya ko akan tafiya to sai ya qididdigi wassu yinin na daban", .

NA SHIDA:
HUKUNCIN MUTUMIN DA RUWA YA SHIGA CIKINSA BA TARE DA ZAVINSA BA
Tambaya: Mutum ne yake azumi sai ya yi wanka da shawa (fanfo), to saboda qarfin tunkuxowar ruwan sai ya shige masa cikinsa ba tare da zavinsa ba, Shin akwai ramukon azumi akansa? ([7])
Amsa: Babu ramukon azumi akansa; saboda bai yi gangancin aikata hakan ba, sai hukuncin ya zama kamar na mutumin da aka tilasta masa, ko mutumin da ya yi mantuwa.

NA BAKWAI:
HUKUNCIN HAXIYE MIYAU GA MAI AZUMI:
Tambaya: Menene hukuncin hadiye yawu ga mai azumi? ([8])
Amsa: Yawu baya cutar da azumi, don haka idan mutum ya haxiye shi ba komai, kamar yadda in ya tofar da shi ba komai. Amma kaki da yake fitowa daga qirji ko daga hanci, wanda larabawa ke kira (nukhamah), ko kuma (nukha'ah) wanda shi kuma shi ne kaki mai kauri da yake fitowa daga qirji ko kuma daga kai, irin waxannan wajibi ne ga mutum namiji ko mace, su tofar ko fitar da shi, tare da rashin haxiye shi. Yayin da shi kuma yawu na al'ada babu matsala akansa, kuma baya cutar da mai azumi; namiji ne ko mace.


NA TAKWAS:
HUKUNCIN [B]AMFANI DA NA'URAR FESA ISKA A CIKIN BAKI (INHALER) DON MATSANANCIN BUQATA HAKA, A WAJEN MAI AZUMI:
Tambaya: Menene hukuncin amfani da na'urar maganin da ake fesa iska a cikin baki (inhaler), ga mai azumi a cikin yini (wato: da rana), ga mai ciwon quncin qirji da wahalar yin numfashi (Asma)? ([9])
Amsa: Hukuncinsa shine halacci; idan har lalura ta buqatar da mutum zuwa ga hakan, saboda faxin Allah mabuwayi da xaukaka a cikin "suratul an'aam":
ﭽ ﭚ ﭛ ﭜ ﭝ ﭞ ﭟ ﭠ ﭡ ﭢ ﭣ ﭼ الأنعام: ١١٩
Ma'ana: "Kuma ya muku dalla-dallan abubuwan da ya haramta su akanku, saidai wanda lalura ta buqatar da ku zuwa gare shi", [An'aam: 119]. Kuma saboda kasancewarsa baya kama da ci da sha, sai ya yi kama da jinin mutum da ake xauka don aunawa ko bincike, ko kamar allurar da ba a sanya abinci a cikinta ba.
NA TARA:
HUKUNCIN [B]CI KO SHA DA MANTUWA GA MAI AZUMI:
Tambaya: Menene hukuncin wanda ya ci ko ya sha da mantuwa a cikin yinin ramadhana? ([10])
Amsa: Babu wata matsala akansa kuma azuminsa ingantacce ne, saboda faxin Allah (سبحانه وتعالى) a qarshen suratul baqarah:
ﭽ ﯥ ﯦ ﯧ ﯨ ﯩ ﯪ ﯫﯬ ﭼ البقرة: ٢٨٦
Ma'ana: "Ya Ubangijinmu kada ka kama mu idan muka yi mantuwa ko muka yi kuskure", . Kuma ya inganta daga Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) cewa Allah ta'alah ya ce:
«قَدْ فَعَلْتُ».
Ma'ana: "Lallai na amsa"([11]). Da kuma saboda abunda ya tabbata daga Abu-hurairah (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) lallai ya ce:
«مَنْ نَسِيَ وَهُوَ صَائِمٌ، فَأَكَلَ أَوْ شَرِبَ، فَلْيُتِمَّ صَوْمَهُ، فَإِنَّمَا أَطْعَمَهُ اللهُ وَسَقَاهُ».
Ma'ana: "Duk wanda ya manta alhalin yana azumi sai ya ci ko ya sha, to ya cika azuminsa; saboda Allah ne ya ciyar da shi, ya kuma shayar da shi"([12]), Bukhariy da Muslim su ka rawaito shi.

NA GOMA:
HUKUNCIN ALLURAR JIJIYA DA TA DAMTSE KO GAVVAI
GA MAI AZUMI
Tambaya: Menene hukuncin amfani da allurar da ake yinta a jijiya, da wacce ake yi damtse ko a gabbai ga mai azumi, menene kuma banbacinsu? ([13])
Amsa: Ingantaccen magana shi ne: Gabaxayansu biyun (ta jijiya da ta damtse) basa vata azumi, wanda kawai take vata azumi itace allurar da ake sanya mata abinci. Haka kuma xaukan jini don bincike, shima azumi baya karyewa da shi, saboda akwai banbanci tsakaninsu da yin qaho. Amma shi kuma qaho da wanda ya yi shi da wanda aka yi masa dukkansu azuminsu ya karye, a maganar maluma da ta fi inganci, wannan kuma saboda faxinsa (صلى الله عليه وسلم):
«أَفْطَرَ الحَاجِمُ وَالمَحْجُومُ».
Ma'ana: "Da mai qaho da wanda aka yi masa qahon azuminsu ya lalace"([14]).

NA SHA XAYA, DA SHA BIYU:
HUKUNCIN YIN AMFANI DA MAKILIN, DA MAXIGI
Tambaya: Menene hukuncin amfani da makilin xin goge haqora, da kuma maxigin kunne (magani), dana hanci, dana ido, ga mai azumi? Kuma idan mai azumi ya ji xanxanonsu a cikin maqogoronsa me zai aikata? ([15])
Amsa: Tsaftace haqora da makilin baya karya azumin mai azumi, saboda hukuncinsa kamar yin aswaki ne, Saidai kuma wajibi ne akansa ya kiyaye silalewan wani abu zuwa cikinsa, Amma inda wani abu zai rinjaye shi ya shiga cikin cikinsa ba tare da nufi ba to babu ramuko akansa.
Haka maganin xigawa a ido da kunne azumi baya karyewa in an xiga su a zancen da yafi inganci daga zantukan maluma guda biyu, Saidai kuma in har ya ji xanxanon abubuwan da ya xiga a maqogoronsa to ya rama wannan azumin yafi tsentseni a gare shi, tare da cewa yin hakan ba wajibi ba ne akansa, saboda kasancewar ido da hanci ba kafofi ne na shigar da abinci da abin sha ba.
Amma maganin da ake xigawa ta hanci to shi kam baya halatta; saboda kasancewar hanci mashiga ne na abinci, don haka ne Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ke cewa:
«وَبَالِغْ فِي الِاسْتِنْشَاقِ إِلَّا أَنْ تَكُونَ صَائِمًا».
Ma'ana: "Kuma ka kai maqura wajen shaqar ruwa a hanci saidai in ka kasance mai azumi"([16]). Kuma wajibi ne ga mutumin da ya aikata hakan ya rama azumi, saboda wannan hadisin da wadanda suke da ma'ana irin tasa, matuqar ya ji xanxanon abun da ya xiga a cikin maqogoron nasa, Allah shi ne majivincin dacewa.

NA SHA UKU:
HUKUNCIN [B]SHAQAR TURARE (NA FESAWA DANA KONAWA)
Tambaya: Shin ya halatta ga mai azumi ya shanshana qamshin turaren fesawa ko na gaushi da ake qonawa? ([17])
Amsa: Mai azumi ba zai shaqi turaren wuta (Uud) ba, amma sauran turare waxanda ba na qonawa ba, to babu laifi akansu, Amma turaren uud kam ba zai shanshane shi ba; saboda wassu maluma suna ganin cewa wannan turaren yana karya azumi idan mai yinsa ya shake shi; saboda ya kan tafi zuwa ga kwakwalwa, kuma tafiyat tasa ta kan zama da qarfi, Amma da zai shaqe shi ba tare da nufi ba to ba zai karya masa azuminsa ba.

Tambaya: Shin a cikin yinin ramadhana ya halatta ya yi amfani da tirare, misali: turaren uud na mai da ake shafawa, da koloniya, da kuma turaren gaushi da ake qonawa? ([18])
Amsa: E, ya halatta, da sharaxin kada ya shaqi turaren gaushi da ake qonawa.

NA SHA HUXU:
HUKUNCIN AMFANI DA TOZALI, DA KAYAN KWALLIYA A CIKIN YININ RAMADHANA
Tambaya: Menene hukuncin amfani da tozali ko wassu kayan kwalliya ga mata a cikin yinin ramadhana, kuma shin yana vata azumi ko a'a? ([19])
Amsa: Tozali baya karya azumin 'ya mace, ko na namiji, a mafi ingancin zance guda biyu na maluma, a kowani irin hali. Saidai kuma ayi amfani da shi da daddare shi ya fi dangane da mai azumi mace ko namiji. Haka kuma abubuwan da mata ke ado da su na sabulu ko mayuka, ko makamancin haka na dangin abubuwan da su ke alaqa da fata kawai, misalin su qunshi (lalle), da kayan barbaxe-barbaxe da makamantan haka, dukkan waxannan babu laifi ga mai azumi mace, ko namiji su yi amfani da shi, tare da cewa baya halatta a yi amfani da kayan shafe-shafe matuqar zai cutar da fiska (kamar canza mata kala), Allah shine majivincin dacewa!

NA SHA BIYAR:
YI DA MUTUM (GIBA) DA ANNAMIMANCI DA ZAGI SAVO NE DA SUKE YIN MIKI GA AZUMI, TARE DA TAUYE LADANSA
Tambaya: Shin cin naman mutane yana daga abubuwan da suke vata azumin mutane? ([20])
Amsa: Yi da mutum (wato: giba) baya cikin abubuwan da su ke vata azumi, Shi ne kuma: ambaton mutum da abinda ya ke qi, saboda faxinsa mabuwayi da xaukaka:
ﭽ ﭟ ﭠ ﭡ ﭢ ﭼ الحجرات: ١٢
Ma'ana: "Kada sashinku ya yi gibar sashi", [Hujuraat: 12].
Haka kuma annamimanci da zagi da qarya dukkansu basa cikin abubuwan da su ke vata azumi, Saidai manya-manyan savo ne da ya zama wajibi a kiyaye su, mai azumi da wanda ba mai azumi ba su nisance su, kuma lallai suna kawo givi ga azumi, su kuma rage masa ladansa; saboda faxin Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم):
«مَنْ لَمْ يَدَعْ قَوْلَ الزُّورِ، وَالْعَمَلَ بِهِ، وَالْجَهْلَ، فَلَيْسَ لِلَّهِ حَاجَةٌ أَنْ يَدَعَ طَعَامَهُ وَشَرَابَهُ».
Ma'ana: "Duk wanda bai bar zancen qarya da aiki da ita, da wauta ba, Allah bashi da buqatar ya bar abincinsa da abin shansa" ([21]). Bukhariy ya rawaito shi a sahihinsa.
Da kuma saboda faxinsa:
«الصِّيَامُ جُنَّةٌ، فَإِذَا كَانَ يَوْمُ صَوْمِ أَحَدِكُمْ، فَلَا يَرْفُثْ، وَلَا يَصخَبْ، فَإِنْ سَابَّهُ أَحَدٌ أَوْ قَاتَلَهُ، فَلْيَقُلْ: إِنِّي صَائِمٌ».
Ma'ana: "Azumi garkuwa ne, idan ranar azumin xayanku ya zo to kada ya yi batsa balle jima'i, kada kuma ya yi shewa, idan wani ya zage shi ko ya nemi faxa da shi to ya ce: Ni mai azumi ne" ([22]). Bukhariy da Muslim su ka rawaito shi.
Hadisai kan wannan mas'ala suna da yawa.

NA SHA SHIDA:
HUKUNCIN GANIN MATA GA MAI AZUMI, DA GAISAWA DA WAXANDA BA MUHARRAMANSA BA
Tambaya: Idan mutum ya yi dubi da-gangan ga mace ajnabiyyarsa (wacce ba haramcin aure a tsakaninsu), saboda kyanta, ko tufarta ko jikinta, -alhalin yana azumi- Shin azuminsa ya lalace ko kuma hakan makruhi ne; Allah zai iya karvar azuminsa, Sai kuma ya yi sakayya a gare shi akan kallonsa? Ku mana fatawa akan haka, da fatan Allah ya baku lada? ([23])
Amsa: Haramun ne akansa ya kalli mata, idan kuma da sha'awa ne haramcin ya fi tsanani, saboda faxin Allah (سبحانه وتعالى):
ﭽ ﭾ ﭿ ﮀ ﮁ ﮂ ﮃ ﮄﮅ ﭼ النور: ٣٠
Ma'ana: "Ka ce da muminai su rintse daga ganinsu, kuma su kiyaye farjojinsu", [Nuur: 30].
Kuma saboda kasancewar sake ido yana daga cikin hanyoyin aukuwar alfasha, don haka wajibi ne rintse ido tare da kiyaye dukkan sabbuban aukuwar fitina, Saidai kuma azuminsa ba zai lalace ba matuqar maniyyi bai fita ba, Amma wanda ya yi maniyyi to shi azuminsa ya vaci, kuma dole ya yi ramuko. Allah shine mai datarwa!

Tambaya: Menene hukuncin mutumin da ya yi musabaha da matar da bata halatta a gare shi ba, ko ya yi magana da ita a cikin yinin ramadhana alhalin yana azumi, itama tana azumi, Shin hakan yana vata azumi, ko kuma rage masa lada? Fatan za a faxakar da mu, kuma shin akwai kaffara ne akansa? ([24])
Amsa: Musabaha da matar da akwai aure tsakaninku (ajnabiyya) baya halatta, wannan kuma saboda Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
«إِنِّي لَا أُصَافِحُ النِّسَاءَ».
Ma'ana: "Lallai ni bana musabaha da mata"([25]). Kuma A'ishah (رضي الله عنه) ta ce:
«وَاللهِ مَا مَسَّتْ يَدُ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَدَ امْرَأَةٍ قَطُّ، ما كان يُبَايِعُهُنَّ إلا بِالْكَلَامِ».
Ma'ana: "Ina rantsuwa da Allah! Hannun Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) bai tava tava hannun wata mace ba, saboda bai kasance yana yi musu mubaya'a ba sai da magana"([26]).
Wannan kuma tana nufin: Matar da akwai halaccin aure a tsakaninsu, waxanda ba muharramai suke a gare shi ba. Amma ita kuma wacce ta haramta ga mutum kamar yar'uwarsa, ko babarsa to babu laifi ya yi musabaha da su.
Amma dangane da yin magana da matar da akwai halaccin aure a tsakani: Idan har magana ce ta halal wacce babu tuhuma ko kokonto akanta; kamar ace ya tambaye ta kan 'ya'yanta, ko kan mahaifinta, ko kan wata buqata daga cikin buqatun makwabta ko dangi to wannan babu komai, amma in kuma maganar ta kasance zance ne da ya ta'allaqa da varna ko zina, ko sanya lokutan zina, ko mai tada sha'awa, ko neman ta buxe wani vangare na jikinta dukkan waxannan basa halatta.
Yayin da idan zancen ya zama tare da cikakken sitira da hijabi, babu kuma kokonto a cikinsa da tuhuma, ba kuma akan sha'awa ba ne, to babu laifi akansu cikin irin wannan maganar, saboda kasancewar Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya yi magana da mata, kuma mata sun yi magana da shi, don haka babu qunci akan haka.
Azumin kuma ya inganta; musabaha bata lalata shi, haka kuma zance yake, matuqar maniyyi bai fita ta sanadiyyarsa ba, In kuma maniyyi ya fita to wajibi ne akansa ya yi wanka, kuma azumin ya lalace, dole akansa ya biya shi –in har azumin na wajibi ne.
Kuma wajibi ne akan musulmi ya kiyayi abubuwan da Allah ya haramta masa, kada kuma ya yi musabaha da matar da bata halatta ba a gare shi, kada kuma ya yi magana da ita da sha'awa, ko ya kalli kyanta, saboda Allah yana cewa:
ﭽ ﭾ ﭿ ﮀ ﮁ ﮂ ﮃ ﮄﮅ ﮆ ﮇ ﮈﮉ ﮊ ﮋ ﮌ ﮍ ﮎ ﭼ النور: ٣٠
Ma'ana: "Ka ce da muminai su rintse wani abu na ganinsu, kuma su kiyaye farjojinsu, yin haka shine yafi tsarki a gare su, lallai Allah mai bada labari dangane da abinda suke aikatawa", [Nuur: 30]. Don haka; Kiyaye abubuwan da suke sabbaba sharri wajibi ne akan mumini a duk inda ya ke. Muna roqon Allah ya kare mu tare da sauran musulmai daga dukkan mummuna. Yabon Allah da sallamarsa su qara tabbata ga Annabinmu Muhammadu da iyalansa da sahabbansa gabaxaya.
$&$

Allah ne masani, Wannan shine abinda na tato mana daga littatafan Shehin Malami, Abdul'aziz xan Abdullahi Ibnu-baaz. Allah yayi masa rahama.

Wallahu a'alam ! ! !





([1]) An watsa wannan maqaalar a littafin AD-DA'AWAH (1/120), fitarwar: Mu'assatud da'awas sahafiyyah, da kuma FATAWA ISLAMIYYAH, tattarawar: Sheikh Muhammadul musnid, (2/132), da kuma MAJMU'U FATAWA WA MAQAALAAT MUTANAWWI'AH, (15/277-278).
([2]) Bukhariy da Muslim suka rawaito shi daga hadisin A'ishah (رضي الله عنها), (Sahihul Bukhariy, lamba: 1930, da Muslim: lamba: 1109).
([3]) Har zuwa wannan gavar mun ciro shi ne daga littatafai guda biyu da suka gabata, Daga nan har zuwa qarshen tambayar shi kuma ya zo a cikin MAJMU'U FATAWA WA MAQAALAAT MUTANAWWI'AH, (15/278).
([4]) An watsa wannan maqaalar a littafin AD-DA'AWAH (1/121), da MAJMU'U FATAWA WA MAQAALAAT MUTANAWWI'AH, (15/275).
([5]) Wannan ya zo daga hadisin Abu-hurairah (رضي الله عنه), Wanda Imam Ahmad ya rawaito shi (2/498), da Abu-dawud (lamba: 2382), da Tirmiziy, (lamba: 720), yace hadisi ne mai kyau (hasan), da Ibnu-maajah, (lamba: 1676).
([6]) FATAWA ISLAMIYYAH, tattarawar: Sheikh Muhammadu almusnid, (2/134), da MAJMU'U FATAWA WA MAQAALAAT MUTANAWWI'AH, (15/ 267).
([7]) MAJMU'U FATAWA WA MAQAALAAT MUTANAWWI'AH, (15/279).
([8]) FATAWA ISLAMIYYAH, tattarawar: Sheikh Muhammadu almusnid, (2/125), da MAJMU'U FATAWA WA MAQAALAAT MUTANAWWI'AH, (15/ 313).
([9]) Wannan yana cikin littafin: TUHFATUL IKHWAN BI AJWIBATIN MUHIMMATIN TATA'ALLAQU BI ARKAANIL ISLAAM, Tattarawar Sheikh Muhammad As-shayi', (tambaya ta 24, a vangaren azumi), yana kuma cikin MAJMU'U FATAWA WA MAQAALAAT MUTANAWWI'AH, (15/ 265).
([10]) Wannan yana cikin littafin: TUHFATUL IKHWAN, (tambaya ta 16), yana kuma cikin MAJMU'U FATAWA WA MAQAALAAT MUTANAWWI'AH, (15/ 291-292).
([11]) Muslim ya rawaito shi daga hadisin Abdullahi xan Abbas (رضي الله عنهما), (lamba: 1206).
([12]) Bukhariy da Muslim suka rawaito shi daga hadisin A'ishah (رضي الله عنه), (Sahihul Bukhariy, lamba: 1933, da kuma 6669, Sai Imam Muslim: lamba: 1155).
([13]) TUHFATUL IKHWAAN BI AJWIBATIN MUHIMMATIN TATA'ALLAQU BI ARKANIL ISLAAM, (13), da MAJMU'U FATAWA WA MAQAALAAT MUTANAWWI'AH, (15/ 258).
([14]) An rawaito wannan lafazin daga adadi da yawa na sahabban Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) Daga cikinsu akwai: Sauban (رضي الله عنه) Imam Ahmad ya rawaito hadisinsa (5/276), kuma an rawaito cewa Imam Ahmad ya ce: Hadisin Sauban shine mafi ingancin abinda aka ruwaito a wannan babin. Kamar yadda Imam Ahmad ya sake rawaito shi daga hadisin: Rafi'i xan Khadij (رضي الله عنه) (3/465), da Abu-dawud (lamba: 2367-2371), da Tirmiziy (lamba: 774) ya kuma inganta shi, da Alhakim a cikin "Almustadrak", (lamba: 1561), ya inganta shi, kuma Imam Zahabiy yayi masa muwafaqah (1/591).
([15]) TUHFATUL IKHWAAN, (tambaya ta 14 akan azumi), da MAJMU'U FATAWA WA MAQAALAAT MUTANAWWI'AH, (15/ 260-261).
([16]) Abu-dawud ya rawaito shi (lamba: 142), da Tiamiziy (lamba: 788), yace: hadisi ne mai kyau ingantacce (hasan sahih), da Nasa'iy (lamba: 87), da Ibnu-maajah (lamba: 407).
([17]) MAJMU'U FATAWA WA MAQAALAAT MUTANAWWI'AH, (15/266-267).
([18]) An ambace shi a cikin littafin FATAWA ISLAMIYYAH, (2/128), da MAJMU'U FATAWA WA MAQAALAAT MUTANAWWI'AH, (15/ 267).
([19]) An yada shi a cikin littafin DA'AWAH (2/170), da MAJMU'U FATAWA WA MAQAALAAT MUTANAWWI'AH, (15/ 259-260).
([20]) MAJMU'U FATAWA WA MAQAALAAT MUTANAWWI'AH, (15/ 320).
([21]) Bukhariy ya rawaito shi daga hadisin Abu-hurairah (رضي الله عنه), (lamba: 1903).
([22]) Bukhariy da Muslim su ka rawaito shi (Bukhariy, lamba: 1904, da Muslim, lamba: 1151), lafazin na Muslim ne.
([23]) MAJMU'U FATAWA WA MAQAALAAT MUTANAWWI'AH, (15/ 268-271).
([24]) MAJMU'U FATAWA WA MAQAALAAT MUTANAWWI'AH, (15/ 269).
([25]) Imam Ahmad ya rawaito shi, daga hadisin Umaimah bint Ruqaiqah, (6/357), da Nasa'iy (lamba: 4181), da Ibnu-maajah (lamba: 2874), kuma Albaniy ya inganta shi a cikin littafin "As-sahihah", (lamba: 529).
([26]) Bukhariy ya rawaito shi, (lamba: 4891), da Muslim (lamba: 1866).