طاهر جبريل دكو
_13 _January _2016هـ الموافق 13-01-2016م, 06:00 PM
BismilLah, walhamdu lilLah, Was-Salatu was- Salamu 'ala RasulilLah, wa 'ala alihi wa sahbihi wa man walah. A bayani da ya gabata na yi tambaya a karshe, duk da Allah bai sa an samu wanda ya amsa ba, amma duk da haka yana da kyau na kara yin wata tambayar game da yakin "Badar" duba da cewa shine yakin da ya fi kowane muhimmanci a tarihin musulunci, kuma yana da kyau matuka mu san irin bajintar da muminan farko: Sahabbai (RA) suka yi, don mu kara kaimi wajen kaunatarsu da yi musu addu'a ta gari, kamar yadda Allah Ta'ala ya umarce mu. Mun ambaci cewa mutum 14 ne suka yi shahada a yakin "Badar", ina ma a samu wanda zai ambato mana sunayen biyar kacal daga cikinsu don mu sansu mu rike sunayensu? A yanzu zan yi magana ne game da: SULHUN HUDAIBIYA Hudaibiyya wata alkarya ce kusa da Makka, asali sunan wata rijiya ce a wannan alkaryar wadda take kusa da bishiyar da Ma'aiki (SAW) ya zauna karkashinta lokacin da Sahabbansa (RA) suka yi mubaya'a. Hijira tana shekara ta (6), a watan Zulkida, Ma'aiki (SAW) ya dauki hanya zuwa garin Makka tare da Sahabbansa don su yi Umara. Sun yi salla a Zulhulaifah, daga nan Ma'aiki (SAW) ya yi wa rakuman da zai yi hadaya da su guda 70 rataye, da kuma alamomi. Sannan ya tura Busr bn Sufyan al-Khuza'i (RA) don yin leken asiri ga kuraishawa. Sun ci gaba ta tafiya, har suka isa 'Usfan' [kauye mai misalin nisan mil 36 kafin a shiga Makka] a nan ne Busr (RA) ya zo da labarin cewa, Kuraishawa suna can sun sha alwashin ba zasu bari Ma'aiki (SAW) ya shiga Makka ba. Ma'aiki (SAW) ya shawarci Sahabbansa, sai Abubakar (RA) yace: "Ya Ma'aikin Allah! Yanzu dai ba yaki muka fito yi ba, ziyartar dakin Allah zamu yi, mu ci gaba da tafiya, duk wanda ya hana mu wucewa sai mu murkushe shi". Sai Ma'aiki (SAW) yace: (To, mu ci gaba Allah ya taimaka mana!) A 'Usfan' Ma'aiki (SAW) ya yi wa jama'a 'Sallar tsoro', sannan ya canja hanya, ya bi wadda take da wahalar tafiya, har suka isa 'Hudaibiya', taguwarsa ta durkusa da kanta a wajen... A nan Ma'aiki (SAW) yace: "Na rantse da wanda raina yake hannunsa! Duk wani sharadi da zasu gindaya, matukar akwai girmama hurumin Allah a cikinsa, to zan yarda da shi". [Bukhari: 2731, 2732]. Da yake Mushrikai sun riga isa, sai suka sauka inda ruwa yake, su kuma musulmai suka samu wurin da ruwansa kadan ne; don haka suka yi ta fama da kishi, sai Ma'aiki (SAW) ya ciro daya daga cikin kibiyoyinsa ya umarci Sahabbansa su jefa ta cikin rijiyar wurin, nan da nan sai ruwa ya bubbugo da yawa. Ma'aiki (SAW) ya dauki lokaci don ya fahimtar da Kuraishawa cewa ziyartar dakin Allah suka zo yi kawai; don haka ne ya tura Usman bn Affan (RA) Makka don ya yi musu bayanin hakan. A lokacin da Usman bn Affan (RA) ya shiga Makka, Kuraishawa sun rike shi, ya dade kwarai bai dawo ba, har dai labari ya isarwa Ma'aiki (SAW) cewa an kashe Usman (RA). Sai Ma'aiki (SAW) ya umarci Sahabbansa su yi mubaya'a a kan ba zasu koma ba, sai dai duk su mutu, tun da ga abin da ya faru. To wannan mubaya'ar da suka yi itace ake kira 'BAI'ATUR RIDHWAN'. Gaba dayan Sahabban da suke tare da shi sun yi mubaya'a, in banda wani mutum guda daya mai suna al-Jaddu bn Kais. Farko Ma'aiki (SAW) shi ya fara yin mubaya'a a madadin Usman bn Affan (RA), daga nan sai sauran sahabbai suka biyo baya. Wadanda suka halarci wannan mubaya'ar, sune Allah ya yi wa kirari da yabo, ya saukar da Suratul Fat'h, wadda daga cikinta ne Allah yake cewa: ( ﻟﻘﺪ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻦ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﺇﺫ ﻳﺒﺎﻳﻌﻮﻧﻚ ﺗﺤﺖ ﺍﻟﺸﺠﺮﺓ، ﻓﻌﻠﻢ ﻣﺎ ﻓﻲ ﻗﻠﻮﺑﻬﻢ ﻓﺄﻧﺰﻝ ﺍﻟﺴﻜﻴﻨﺔ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﻭﺃﺛﺎﺑﻬﻢ ﻓﺘﺤﺎً ﻗﺮﻳﺒﺎً ). ﺍﻟﻔﺘﺢ : 18 (Hakika Allah ya yarda da muminai yayin da suke yin mubaya'a da kai a karkashin bishiya, sai Allah ya san abin da yake cikin zukatansu sannan Ya saukar musu nutsuwa, Ya kuma sakanta musu da mabayyanin budi na kurkusa [wato cin nasara]). [Fat'h: 18]. Wannan ayar tana nuni karara bisa yardar Ubangiji wadda cikin gaggawa ta lullube gaba dayan sahabbai wadanda suka halarci wannan mubaya'a. Wato Allah ya yarda da su nan take a lokacin da suke yi wa Ma'aiki mubaya'a, ba bayan an kare ta ba. An karbo daga Jabir bn Abdillahi (RA) yace: "A ranar Hudaibiya Ma'aiki SAW yace damu: (Kune mafi alherin wadanda suke bayan kasa) yawanmu kuwa ya kai mutum dubu da dari hudu". [Bukhari: 4154. Muslim: 1856]. A wani hadisin Ma'aiki (SAW) yace: (Babu daya da zai shiga wuta daga cikin jama'ar da suka yi mubaya'a a karkashin bishiya). [Ibn Hibban: 4802, Abu Dawud: 4655]. Usman bn Affan (RA) ya dawo, Sa'annan maganar sulhu ta fara. Mai neman cikakken bayani game da yadda yarjejeniyar ta gudana, zai iya komawa [al-Bidayah wan-Nihayah: 4/164]. Abu mai mahimmanci a maganar hudaibiya wanda yake nuni zuwa girman falalar wadanda suka halarci wannan sulhun shine fadin Allah Ta'ala da yace: "Lallai, hakika Allah ya yarda ga muminai a lokacin da suke yi maka mubaya'a karkashin bishiya…" Allah bai taba yarda da mutum ba, sannan daga baya ya zo ya yi fushi da shi. Wannan ya nuna cewa babu wani abu da ya faru ga wadannan Sahabbai da ya goge yardar da Allah Madaukaki ya yi da su. Kololuwar ni'imar da Allah zai yi wa bawansa, itace ta yarda gare shi, domin ta fi kowane abu girma da daraja. DAGA CIKIN DARUSAN DA ZAMU KOYA: Ma'aiki (SAW) yana mu'amalantar Sahabbansa ne cikin amincewa da cikakkiyar yarda, shi ya sanya ya tura Busr (RA) don leken asiri, ya tura Usman (RA) don tattaunawa da Kuraishawa, ba don cikakkiyar yarda da amincewa ba, ba yadda za'a yi ya tura su, sannan kuam ya yarda da maganganunsu bayan sun dawo. Ma'aiki (SAW) yana shawarta kuma ya dauki shawarar Sahabbansa (RA), kamar yadda Abubakar (RA) ya bada shawara aka karba. Mu'jizar Ma'aiki (SAW) ta bayyana a wannan kissar, lokacin da mutane suka shiga tsanani na rashin ruwa. Ma'aiki (SAW) ya nuna cewa musulmai tamkar jiki guda ne, a kan mutum daya su duka suka dau alwashin bayar da rayukansu, yayin da labarin cewa an kashe Usman (RA) ya zo musu. Wannan kuma ya nuna yadda Ma'aiki (SAW) yake damuwa da lamarinsu. Mahimmancin wannan Sulhun, da mubaya'ar da aka yi wa Ma'aiki (SAW) ya sanya Allah ya saukar da suratul Fat'h, wadda ta yi busharar cewa abin da ya faru nasara ce ga musulmi, ko da kuwa a fili zasu iya ganin kamar koma baya ne. Shi ya sanya ya zamo sharar fage zuwa ga bude garin Makka (Fat'h Makka). Yardar Allah Ta'ala, masanin abin da yake zuciyoyi, ga Sahabban Ma'aiki (SAW), ya nuna girman matsayi da daukakar wadannan jama'a. Babu wani mai kulli da gilli da kyashi da zai fadi abu akasin haka, har kuma a saurare shi... Walhamdu lilLahi Rabbil Alamin