طاهر جبريل دكو
_13 _January _2016هـ الموافق 13-01-2016م, 05:58 PM
Magaji F Ishaq Zarewa BAWAN DUKIYA. Son kudi ba shi ne abin zargi ba, domin kuwa wannan sifa ce da 'yan adam suka yi tarayya akanta. Abin zargi shi ne mutum ya zama bawan kudi. Wasu mutanen sukan zama bayin dukiyarsu ba tare da sun sani ba! saboda sakarwa shedan ragamar bangaren soyayyarsu da dukiya da suka yi, hakan sai ya sanya iblis ya ringa rura wutar soyayyarsu da dukiyar har ya wuce misali, daga bisani sai ya hana su aikin alheri da ita, ya kawata musu rowa yana mai tsoratar da su talauci in suna aikin alheri da ita. yana daga cikin alamun bautawa dukiya: * Yiwa kai rowa ko kauro ga iyali. * Rashin tausiyi wurin ciniki. * wahalar da kai wurin nema araha. * Rashin kayutatawa Iyaye, 'yan uwa, abokai da makobta na kusa da na nesa. * Raki ya yin da aka sami asara (Allah Ya kiya ye, ba fata ake yi ba). * gazawa wurin taimakawa marasa galihu, ko aikin addini. * sakaci da rashin kula da ibada ya yin da ake cikin shu'unin dukiya. ds. MANZON ALLAH SALLALAHU ALAIHI WASALLAM YA CE: " BAWAN DUKIYA YA TABE........." Bukhari da Muslim ne suka rawaito ALLAH KA BAMU DUKIYA MAI ANFANI MAI ALBARKA.