المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : Assalamu'alaikum,malam dan Allah wata ce mijin ta yace hujin hanci na burge shi.


طاهر جبريل دكو
_13 _January _2016هـ الموافق 13-01-2016م, 05:53 PM
Tambaya: Assalamu'alaikum,malam dan Allah wata ce mijin ta yace hujin hanci na burge shi. So tana so ta huda sai aka ce mata babu kyau a musulunci. Shin malam ya abun yake? Haramun ne,ko kuwa tana iya hudawa tasa dankunne tayi kwalliya da shi?
Wa alaikum assalam, An tambayi sheikh Ibnu Uthaimin akan wannan mas' alar ta huda Hancı sai yake cewa: Huda Hancı zai iya zama canza halittar Allah, amma idan Garin da matar da ta huda hancin take ana yın ado a hanci, ta yadda hakan ya zama al'ada, to babu laifi ayi hakan. Duba: Majmu'u Fatawaa Ibnu Uthaimin 11/137. Haka nan an tambayi Sheik Abdul Muhsin Al'abbad akan haka a darasinsa da yake gabatarwa a Haram, sai ya ce babu laifi akan haka.
Bisa Abin da ya gabata ya halatta matar BAHAUSHE ta huda hancinta saboda ta sanya abin kwalliya tun da al'adarsu ce, saboda ya tabbata sahaban Annabi s.a.w mata suna huda kunnansu suna sanya 'yan kunnaye Kamar yadda hadisin Bukhari mai lamba: 98 yake nuni zuwa hakan. Allah ne mafi sani.