طاهر جبريل دكو
_13 _January _2016هـ الموافق 13-01-2016م, 05:51 PM
ANGO YA MUTU KAFIN AMARYA TA TARE, YAYA BATUN GADO DA TAKABA ? Tambaya: Assalam pls an daura auren wasu yau ba'a dauko amarya ba sai gobe, amma Allah yayi wa angon rasuwa..tambayata anan wai shin za tayi takaba? Kuma tanada gadonshi? Amsa: To dan'uwa idan miji ya mutu bayan an daura aure kafin ya tare da amryarsa, ya wajaba amaryarsa ta yi masa takaba, kuma a bata gadonta cikakke, kamar yadda Annabi S.a.w. ya yi hukunci da hakan ga Barwa'u 'yar Washik lokacin da mijinta ya mutu kafin su tare a hadisi mai lamba ta: 1145, wanda Tirmizi ya rawaito kuma ya inganta shi . Allah ne mafi sani. Dr. Jamilu Yusuf Zarewa 5\1\2016