طاهر جبريل دكو
_13 _January _2016هـ الموافق 13-01-2016م, 05:49 PM
NA YI WANKAN JANABA, SAI MANIYYI YA SAKE ZUBO MINI ? Tambaya: Assalamu Alaikum tambayata itace idan mata ta sadu da mijinta tayi wanka immidietly bayan ta gama tana zaune sai taji sperm ya zubo mata shin zata kara yin wani wanka ko kuma wanda tayi ya isa ? Amsa: Wa alaikum assalam, To idan sabuwar Sha'awa ce ta zo mata, ta zubar da maniyyi, ya wajaba ta sake wanka, amma idan saboda saduwar da suka yi ne a baya : za ta wanke wurin ne, ta sake alwala, amma babu bukatar sake wanka, wanda ta yi na farko ya isa. Duba Bidayatu Almujtahid 1\48 da Insaf 1\232.. Allah ne mafi sani Dr. Jamilu Zarewa 2\1\2016