تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : WALIYYAN ALLAH! (Muhammad Rabi’u Rijiyar Lemo)


طاهر جبريل دكو
_14 _December _2015هـ الموافق 14-12-2015م, 12:31 PM
WALIYYAN ALLAH! (Muhammad Rabi’u Rijiyar Lemo)
WALIYYAN ALLAH! (Muhammad Rabi’u Rijiyar Lemo) November 28, 2013 Sheikh Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo WALIYYAN ALLAH! Waliyyi shi ne wanda ya yi imani da Allah, yake kuma jin tsoronsa, kamar yadda Allah Madaukakin Sarki ya fada a cikin littafinsa mai girma, Suratu Yunus aya ta 62 – 63. Dukkan musulmi mai tsoron Allah waliyyin Allah ne, gwargwadon imaninsa gwargwadon walittakarsa, mafiya darajar waliyyai Annabawa da Manzannin Allah, sai Sahabban Annabi (S.A.W), Siddikai, shahidai sai Salihan bayi. Babu wani zamani ko lokaci tun farkon zuwan musulunci har zuwa daf da tashin Alkiyama da babu waliyyan Allah a cikinsa. Akwai waliyyan Allah Mata kamar yadda ake samunsu a maza, akwai waliyyan Allah a cikin malamai da masu Mulki, da yan kasuwa, da talakawa da masu kudi. Ahlussunnati Wal Jama’a sun yi imani da samuwar waliyyan Allah, har ma karamominsu, kamar yadda Alkur’ani da Hadisai ingantattau suka tabbatar da hakan. Walittaka bata haduwa da yin shirka da bokanci ko da’awar komai Allah ne, duk wanda dayan wadannan abubuwa na shirka ko bokanci ko da’awar komai Allah ne ya tabbata a kansa to wannan ba waliyyin Allah ba ne, sai dai waliyyin Shaidan. Kuskure ne babba takaita waliyyan Allah akan wasu mutane ko jama’a ko darika, a ce kadai a cikinsu ake samun waliyyai. Haka nan kuskure ne ayyana wasu mutane ko mutum a ce duk wanda baya sonsa ko baya son su, baya son waliyyai, ko yana gaba da waliyyai, ko bai yarda da waliyyai ba. Haka nan kuskure ne babba fitar da sahaban Manzon Allah daga waliyyan Allah, har a rika ganin mai kaunarsu baya son waliyyai, mai zaginsu da aibata su masoyin waliyyai ne, tunda dai ya yarda da wasu mutane da ake kirawa walittaka. Kofar walittaka a bude take, babu wani mutum da zai zama cikamakin waliyyan Allah, duk wanda ya yi da’awar shi ne cikamakin waliyyai a yau ko a zamanin baya, hakika ya yi kuskure, kuma ya fadi abin da ba haka yake ba, cikamakin waliyyai shi ne karshen mumini da zai bar wannan duniya. Allah ya sanya mu cikin waliyyansa na gaskiya, masu kaunar waliyyan gaskiya, Annabwa da Siddikai da Salihan bayi. Ameen.