المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : Nasiha a cikin mutane, tozartawa ne ! ! !


طاهر جبريل دكو
_9 _December _2015هـ الموافق 9-12-2015م, 02:17 PM
NASIHA A CIKIN MUTANE, TOZARTAWA NE ! ! !

Tambaya:
Aslm alkm. Dan Allah meye hukuncin wanda idn yaga anyi kuskure yake toxarta mutum a cikin jama'a? Shugaba ne na mkrnt yake jan jam'i rana daya dalibi yaja da aka idar da sallah sai aka parayiwa dalibin toxarta a gaban dalibai maxa da mata kan cewa bai kamata ba, ni ina ganin da an kirashi gepe an masa pada da karin haske ko a hadasu iya maxa ayi musu xaipi. Meye hukuncin haka?

Amsa:
Wa alaikum assalam, Yiwa mutum Nasiha a cikin mutane bai dace ba, kuma hanya ce da za ta hana shi amsar nasihar, in ba wanda aka yiwa nasihar yana da tsananin iklasi ba, Annabi s.a.w. yana cewa: "Wanda ya suturta musulmi Allah zai suturta shi", kamar yadda muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 2074.

Allah ne mafi sani
Jamilu Zarewa
20/11/2015