تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : Zan cire hakorin makka saboda kaucewa lam'a a alwalata ?


طاهر جبريل دكو
_9 _December _2015هـ الموافق 9-12-2015م, 02:15 PM
ZAN CIRE HAKORIN MAKKA SABODA KAUCEWA LAM'A A ALWALATA ?

Tambaya:
Mlm da gaske ne da ake cewa hakorin Makka lam'a ne ? saboda ruwan alwala ba ya taba ainihin hakorin mutum ?


Amsa:
To malam a zance mafi inganci, bai zama dole ruwan kurkure Baki sai ya game dukkan hakora ba, saboda abin da ake nufi da kurkure baki shi ne zagaya ruwa a baki a fito da shi, don haka hakorin Makka ba zai kawo lam'a ba, amma kuma wasu malaman suna ganin kurkure baki ba zai cika ba sai ruwan ya game, don haka barin sanya hakorin Makka Shi ne ya fi, saboda fita daga sabanin malamai abin so ne.

Ya wajaba ga maza su guji sanya hakorin zinare, saboda Allah ya haramta zinare ga mazan al'umar Annabi Muhd s.a.w. kamar yadda Tirmizi ya rawaito kuma ya inganta a Sunan dinsa a hadisi mai lamba ta: 1720.
Allah ne mafi Sani.
Don neman karin bayani duba Alminhaj sharhin Müslim na Nawawy 3/105.

Dr. Jamilu Zarewa
12/11/2015