طاهر جبريل دكو
_9 _December _2015هـ الموافق 9-12-2015م, 02:11 PM
ZAN IYA YIWA MATATA KOME, BAYAN TA FARA JINI NA UKU ?
Tambaya:
Malam idan mace tana iddah Har tana Kan jini na uku. miji zai iya maida ta?
Amsa :
To Dan'uwa Allah yana cewa a suratul Bakara aya ta : 228, "Kuma matan da aka şaki, za su jira (kur'i) uku kafin su gama idda", saidai Malamai sun yi sabani game da ma'anar (kur'i) a ayar . A wajan malaman Malikiyya kur'i a ayar yana nufin tsarki, don haka duk matar da aka saka in dai ta shiga jini na uku to miji ba shi da damar yi mata kome, saboda za'a sake ta ne a tsarki sai ta yi jini sai tsarki, sai jini sai tsarki, daga ta shiga jini na uku za ta zama ta kammala iddarta.
Malaman Hanafiyya sun fassara (Kur'i) a waccar ayar da jini, don haka mutukar mace ba ta kammala jini na uku ba, to miji zai iya mata kome, Tun da za ta fara idda ne da jini, don haka ba zata kammala ba sai a karshen jini na uku.
Wasu Malaman suna inganta Mazahabar Hanafiyya saboda Annabi s.a.w ya kira haila da sunan Kur' i a hadisin Imamu Ahmad mai lamba ta: 25681>
Don neman karin bayani duba : Tafsirin Ibnu-Kathir 1/607. Allah ne mafi Sani.
Dr.Jamilu Zarewa
8/11/2015