تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : ARBA'UNAN NAWAWIYYA Arba'una Hadis الأربعون النويوية


طاهر جبريل دكو
_12 _October _2015هـ الموافق 12-10-2015م, 08:27 PM
ARBA'UNAN NAWAWIYYA Arba'una Hadis (http://abubakarhamza.blogspot.com/2015/10/arbaunan-nawawiyya.html)
















HADISAI ARBA'IN KAN QA'IDODIN MUSULUNCI








NA
IMAM ANNAWAWIY














TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
الحديث الأول:
عن أمير المؤمنين أبي حفص عُمَرَ بْنَ الْخَطَّابِ رضي الله تعالى عنه قال: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، يَقُولُ: «إِنَّمَا الأَعْمَالُ بِالنِّيَّاتِ، وَإِنَّمَا لكل امْرِئٍ مَا نَوَى، فَمَنْ كَانَتْ هِجْرَتُهُ إِلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ فَهِجْرَتُهُ إِلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ، وَمَنْ كَانَتْ هِجْرَتُه لدُنْيَا يُصِيبُهَا، أَوِ امْرَأَةٍ يَنْكِحُهَا فَهِجْرَتُهُ إِلَى مَا هَاجَرَ إِلَيْهِ».
رواه إماما المحدثين: أبو عبد الله محمد ابن إسماعيل بن إبراهيم بن المغيرة بن بردزبه البخاريّ، وأبو الحسين مسلم ابن الحجاج بن مسلم القشيري النيسابوري، في صحيحيهما اللذين هما أصح الكتب المصنفة.
HADISI NA FARKO:
An karvo daga sarkin muminai, Baban Hafs, Umar xan Alkhaxxabi (r.a) yace: Na ji Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "Dukkan aiyuka suna tare da niyya, kuma lallai kowane mutum yana samun sakamakon abinda yayi niyya; Wanda hijirarsa ta kasance saboda Allah ne da Manzonsa to sakamakon hijirarsa tana ga Allah da Manzonsa. Wanda kuma hijirarsa ta kasance saboda wata duniya ce da zai same ta, ko kuma wata matar da zai aure ta, to sakamakon hijirarsa yana ga abinda yayi hijira dominsa.
Shugabannin maluman da suka rubuta littatafan hadisai ne suka ruwaito shi; Wato: Baban Abdullahi Muhammadu xan Isma'ila xan Ibrahima xan Almugiyrah xan Bardizbah, (Albukhariy), Da kuma AbulHusaini Muslimu xan Alhajjaju xan Muslimu, Alqushairiyyu Annaisaburiyyu. A cikin ingantattun littatafansu [Sahihul Bukhariy, lamba: 1, da Sahihu Muslim, lamba: 1907], waxanda kuma sune mafi ingancin littatafan da aka rubuta.


الحديث الثاني:
عن عمر رضي الله تعالى عنه أيضًا قال: بَيْنَمَا نَحْنُ عِنْدَ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ذَاتَ يَوْمٍ، إِذْ طَلَعَ عَلَيْنَا رَجُلٌ شَدِيدُ بَيَاضِ الثِّيَابِ، شَدِيدُ سَوَادِ الشَّعَرِ، لَا يُرَى عَلَيْهِ أَثَرُ السَّفَرِ، وَلَا يَعْرِفُهُ مِنَّا أَحَدٌ، حَتَّى جَلَسَ إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَأَسْنَدَ رُكْبَتَيْهِ إِلَى رُكْبَتَيْهِ، وَوَضَعَ كَفَّيْهِ عَلَى فَخِذَيْهِ، وَقَالَ: يَا مُحَمَّدُ أَخْبِرْنِي عَنِ الْإِسْلَامِ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «الْإِسْلَامُ أَنْ تَشْهَدَ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، وَتُقِيمَ الصَّلَاةَ، وَتُؤْتِيَ الزَّكَاةَ، وَتَصُومَ رَمَضَانَ، وَتَحُجَّ الْبَيْتَ إِنِ اسْتَطَعْتَ إِلَيْهِ سَبِيلًا»، قَالَ: صَدَقْتَ، قَالَ: فَعَجِبْنَا لَهُ يَسْأَلُهُ، وَيُصَدِّقُهُ، قَالَ: فَأَخْبِرْنِي عَنِ الْإِيمَانِ، قَالَ: «أَنْ تُؤْمِنَ بِاللهِ، وَمَلَائِكَتِهِ، وَكُتُبِهِ، وَرُسُلِهِ، وَالْيَوْمِ الْآخِرِ، وَتُؤْمِنَ بِالْقَدَرِ خَيْرِهِ وَشَرِّهِ»، قَالَ: صَدَقْتَ، قَالَ: فَأَخْبِرْنِي عَنِ الْإِحْسَانِ، قَالَ: «أَنْ تَعْبُدَ اللهَ كَأَنَّكَ تَرَاهُ، فَإِنْ لَمْ تَكُنْ تَرَاهُ فَإِنَّهُ يَرَاكَ»، قَالَ: فَأَخْبِرْنِي عَنِ السَّاعَةِ، قَالَ: «مَا الْمَسْئُولُ عَنْهَا بِأَعْلَمَ مِنَ السَّائِلِ» قَالَ: فَأَخْبِرْنِي عَنْ أَمَارَتِهَا، قَالَ: «أَنْ تَلِدَ الْأَمَةُ رَبَّتَهَا، وَأَنْ تَرَى الْحُفَاةَ الْعُرَاةَ الْعَالَةَ رِعَاءَ الشَّاءِ يَتَطَاوَلُونَ فِي الْبُنْيَانِ»، قَالَ: ثُمَّ انْطَلَقَ فَلَبِثْتُ مَلِيًّا، ثُمَّ قَالَ لِي: «يَا عُمَرُ أَتَدْرِي مَنِ السَّائِلُ؟» قُلْتُ: اللهُ وَرَسُولُهُ أَعْلَمُ، قَالَ: «فَإِنَّهُ جِبْرِيلُ أَتَاكُمْ يُعَلِّمُكُمْ دِينَكُمْ». رواه مسلم.


HADISI NA BIYU:
An ruwaito daga Umar (r.a) yace: Wata rana muna wurin Manzon Allah (s.a.w), Sai wani mutum ya vullo mana, mai tsananin farin tufafi, mai tsananin baqin gashi, babu wata alamar tafiya a tattare da shi, har ya zauna kusa da Annabi (s.a.w); Sai ya jingina guiwoyinsa zuwa guiwoyinsa, ya kuma xora tafukansa akan cinyoyinsa, yace: Ya Muhammadu, bani labari akanMusulunci? Yace: Ka shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma annabi Muhammadu manzon Allah ne, kuma ka tsayar da salla, kuma ka bada zakka, kuma ka yi azumin watan ramadana, kuma ka yi hajjin xaki; idan ka samu hanyar zuwa gare shi. Sai yace: ka yi gaskiya, Sai muka yi mamakinsa; yana tambayarsa kuma yana gaskata shi.
Sai yace: ka bani labari akan imani? Yace: Ka yi Imani da Allah, da Mala'ikunsa, da littatafansa, da Manzanninsa, kuma ka yi Imani da qaddara na alkhairinsa dana sharrinsa.
Yace: To ka bani labari akan "ihsani"? Sai yace: Shine ka bauta wa Allah kamar kana ganinsa, idan kai baka ganinsa to shi yana ganinka.
Yace: To ka bani labari akan qiyamah? Sai yace: Wanda ake tambayarsa akanta bai fi wanda yayi tambayar sanin lokacinta ba. Sai yace: To ka bani labara kan alamominta? Sai yace: Baiwa ta haifi uwar gijiyarta, kuma zaku ga marasa takalma, tsiraru, masu kiyon dabbobi suna yin gini masu tsayi.
Yace: Sannan sai ya tafi, sai na zauna na wani lokaci, Sa'annan sai yace: Ya kai Umar shin ka san wanene mai yin wannan tambayar? Sai yace: Allah ne da manzonsa suka sani. Yace: Lallai shi mala'ika Jibrilu ne, y azo muku, domin ya karantar da ku addininku". Muslim yaruwaito shi [lamba: 8]


الحديث الثالث:
عَنِ أبي عبد الرحمن عبد الله بْنِ عُمَرَ بن الخطاب رضي الله عنهما، قَالَ: سمعتُ رَسُول اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يقول: «بُنِيَ الْإِسْلَامُ عَلَى خَمْسٍ، شَهَادَةِ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللَّهِ، وَإِقَامِ الصَّلَاةِ، وَإِيتَاءِ الزَّكَاةِ، وَصَوْمِ شَهْرِ رَمَضَانَ، وَحَجَّ الْبَيْتِ». رواه البخاري ومسلم.
HADISI NA UKU:
An ruwaito daga Abu-abdirrahman, Abdullahi xan Umar xan Alkhaxxabi (r.a) yace: Naji Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "An gina musulunci akan abubuwa guda biyar; Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Muhammadu manzon Allah, da tsayar da salla, dabada zakka, da yin hajjin wannan xakin, da azumin watan ramadana".
Bukhariy [8] da Muslim [16] suka ruwaito shi.


عن أبي عبد الرحمن عَبْدِ اللهِ بن مسعود رضي الله عنه، قَالَ: حَدَّثَنَا رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ -وَهُوَ الصَّادِقُ الْمَصْدُوقُ-: " إِنَّ أَحَدَكُمْ يُجْمَعُ خَلْقُهُ فِي بَطْنِ أُمِّهِ أَرْبَعِينَ يَوْمًا نُطْفَةً، ثُمَّ يَكُونُ فِي ذَلِكَ عَلَقَةً مِثْلَ ذَلِكَ، ثُمَّ يَكُونُ فِي ذَلِكَ مُضْغَةً مِثْلَ ذَلِكَ، ثُمَّ يُرْسَلُ الْمَلَكُ فَيَنْفُخُ فِيهِ الرُّوحَ، وَيُؤْمَرُ بِأَرْبَعِ كَلِمَاتٍ: بِكَتْبِ رِزْقِهِ، وَأَجَلِهِ، وَعَمَلِهِ، وَشَقِيٌّ أَوْ سَعِيدٌ، فَوَالَّذِي لَا إِلَهَ غَيْرُهُ إِنَّ أَحَدَكُمْ لَيَعْمَلُ بِعَمَلِ أَهْلِ الْجَنَّةِ حَتَّى مَا يَكُونُ بَيْنَهُ وَبَيْنَهَا إِلَّا ذِرَاعٌ، فَيَسْبِقُ عَلَيْهِ الْكِتَابُ، فَيَعْمَلُ بِعَمَلِ أَهْلِ النَّارِ، فَيَدْخُلُهَا، وَإِنَّ أَحَدَكُمْ لَيَعْمَلُ بِعَمَلِ أَهْلِ النَّارِ، حَتَّى مَا يَكُونُ بَيْنَهُ وَبَيْنَهَا إِلَّا ذِرَاعٌ، فَيَسْبِقُ عَلَيْهِ الْكِتَابُ، فَيَعْمَلُ بِعَمَلِ أَهْلِ الْجَنَّةِ، فَيَدْخُلُهَا "


HADISI NA HUXU:
An ruwaito daga Abiy-abdurrahman, Abdullahi xan Mas'ud (r.a), yace: Manzon Allah (s.a.w) ya bamu labari, kumashine mai gaskiyaabun gaskatawa, cewa: "Lai xayanku ana tara halittarsa a cikin mahaifiyarsa kwanaki arba'in yana maniyyi, Sa'annan sai ya kasance jinni gwargwadon haka, sa'annan sai ya kasance tsoka gwargwadon haka, Sa'annan sai a turo Mala'ika zuwa gare shi; sai ya busa masa rai, sai a umurce shi da kalmomi guda huxu; rubuta arziqinsa, da ajalinsa, da aikinsa, kuma shaqiyyi ne ko mai rabo, Na rantse da wanda babu wani abin bautawa idan bas hi ba; Lallai xayanku zai yi ta yin aiki irin na 'yan aljanna, har sai ya zama babu wani abu a tsakaninsa da tsakaninta sai zira'i, sai littafi ya rigaye shi; sai kuma yayi aiki irin na 'yan wuta; sai ya shige ta. Kuma lallai xayanku zai yi ta yin aiki irin na 'yan wuta, har sai ya zama babu wani abu a tsakaninsa da tsakaninta sai zira'i, sai littafi ya rigaye shi; sai kuma yayi aiki irin na 'yan aljanna; sai ya shige ta".
Bukhariy [3208] da Muslim [2643] suka ruwaito shi.


HADISI NA BIYAR:
An karbo daga Ummul Mu’uminina Ummu Abdullahi Aishatu (R.A) tace manzon Allah (SAW) “yace wanda ya kirkiro wani abu cikin lamarinmu wannan abin da baya cikinsa to a mayar masa da kayansa.” Bukhari ( 2695) Muslim (1718) Aruwayar Muslim Wanda duk ya aikata wani aiki daba umarninmu a kai an mayar masa da shi.




HADISI NA SHIDA:
An karbo daga abu Abdullahi Nu’umanu dan Bashir, (R.A) y ace “Na ji Manzon Allah (S.A.W) yana cewa, “Lallai halal a bayyane take, kuma lallai haramun a bayyane take, amma a tsakaninsu akwai al’amura masu rikitarwa, da yawa daga cikin mutane ba su san sub a. Duk wanda ya nisanci abubuwa masu rikitarwa, hakika ya nemi kubutar da addininsa da mutuncinsa. Wanda ya auka cikin abubuwa masu rikitarwa, to ta auka cikin haram. Kamar makiyayi ne da yake kiwo a gefen shinge, ya kusanta ya shiga (Ya yi kiwo) a cikinsa. Ku saurara! Kowane sarki yana da iyaka. Ku saurara! Iyakar Ubangiji it ace abubuwan day a haramta. Ku saurara! Lallai a cikin jiki akwai wata tsoka, idan ta gyaru, dukkan jiki ya gyaru, idan ta lalace, dukkan jiki ya lalace. Ku saurara! (Wannan tsokar daya) it ace zuciya.” Bukhari (#59) da Muslim.




HADISI NA BAKWAI:
An karbo daga Abu Rukayya (shine) tamimdan Ausid Dari (R.A) yace, Annabi (S.A.W) yace Addini nasiha ne ! sai muka ce, ga wa ? Sai yace, “ ( Nasiha ne ) ga Allah, da littaffansa da Manzonsa, da shugabannin musulmin da dukkan mutane, Muslim ne rawaito (55).




HADISI NA TAKWAS:
An karbo daga Abdullahidan Umar R.A yace, “ lallai Annabi (S.A.W) yace, “An umarce ni in yaki mutane, har sai sun shaida babu abin bautawa da gaskiya sai allah (sun yarda Annabi )Muhammad manzon Allah ne su tsayar da Sallah, kuma su bayar da zakka idan sun aika haka, sun kare jininsu da dukiyoyinsu daga gare ni, sai hakkin musulunci, hisabinsu yana wajen Allah madaukakin sarki (Bukhari (25) da Muslim (22) suka rawaito shi.




HADISI NA TARA:
An karbo daga Abu Hurair Abdur-rahman dan Sakhirin (R, A) yace, naji manzon Allah (S.A.W) yana cewa duk abin dana hane ku (da bari) to ku nisance shi abin da na umarce ku ku zo dashi (wannan abin ) gwargwadon iko abin daya hallakar da wadanada suke kafi ku yawan tambayoyinsu da sabawarsu ga Annabawansu (Bukhari 7288) da Muslim 1337).




HADISI NA GOMA:
An karbo daga Abu hurairata (R.A) yace, manzon Allah (S.A.W) yace, lallai Allah tsarkakke ne kuma baya karbar abu, sai tsarkakke, Allah ya umarci muminai da irin abin daya umarci manzanni da shi yace, yaku manzanni ku ci daga dadddan abubuwan kuma yi aiki nagari kuma (Allah) yafada lokacin da yake umartar muminai yaku wadanda suka yi imani ku ci daga dadadan abububawan da muka azurta ku da shi sannan Annabi (S.A.W) ya ambaci wani mutum da yake tsawaita tafiya gashin kansa yayi gizo yayi kura yana mika hannayensa zuwa sama yana cewa ya rabbi ya rabbi amma kuma abincinsa haramun ne, abin shansa haramun ne, tufafinsa haramun ne an ciyar dashi haram tayaya za amsa masa (Addu’arsa) Muslim (1015).




HADISI NA GOMA SHA XAYA:
An karbo daga Abu Muhammad (Shine) hassan Dan Abu dalib, Jikan Annabi (S.A.W) abin kaunarsa yace, na haddato daga bakin Annabi (S.A.W) yace, ka kyale duk abin da ke sa ka maka kokwanto zuw abin dab a ya maka kokwanto. Tirmizi (2520) da Nasa’I (5711) suka rawaito shi, Tirmizi yace, hadisi ne mai kyau, ingantacce.




HADISI NA GOMA SHA BIYU:
An karbo daga Abu Hurairata yace, Manzon Allah (S.A.W) yace, yana daga kyawun musulunci mutum barin abinda baya da mahimmanci, a gare shi tirmizi da Ibnu Majah ( 2318) ( 3976).


HADISI NA GOMA SHA UKU:
An karbo daga Abu Hamza, anas Dan malika (R.A) yaron gidan Annabi (S.A.W) yace manzon allah yace,dayanku bay a zama mai cikakken imani har sai yaso dan uwansa abin da yake sowa kansa Bukhari (13) da muslim (45) suka rawaito.


HADISI NA GOMA SHA HUXU:
An karbo daga Abdullahi dan mas’ud (R.A) yace, manzon Allah (S.A.W) yace, jinin mutum musulmi baya halatta sai daya daga cikin laifuka guda uku: magidanci mai zina da ran da ta kasha raid a wanda ya bar addininsa ya rabu da jama’a Bukhari ( 6878) da Muslim (1676).


HADISI NA GOMA SHA BIYAR:
An karbo daga Abu Hurairata( R,A) yace, lallai Annabi (S.A.W) yace wanda ya kasance yayi imani da Allah da kuma ranar karshe, ya fadi alheri ko yai shiru wanda ya kasance yayi imani da Allah da ranar karshe to ya girmama makocinsa wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar karshe to ya girmama bakonsa Bukhari da Muslim ( 6918), (48) suka rawaito.




HADISI NA GOMA SHA SHIDA:
An karbo daga Abu hurairata R.A yace, wani mutum yazo, yace da Annabi kayi min wasiyya sai yace da shi kada kai fushi, sai yayi ta maimaita bukatarsa, sai (Annabi) yace, kada kai fushi Bukhari (6116) ya rawaito.




HADISI NA GOMA SHA BAKWAI:
An karbo daga Abu ‘ya’ala shaddadu bin Ausi R.A daga Annabi s.a.w yace Allah ta’ala ya wajabta kyautatawa ga kowanne irin abu (da mutum zai yi a duniya) idan kuka yi nufin kisa ku kyautatawa kinsan, Idan kun yi nufin yanka (dabba ku kyautatawa yankan, kowanne dayanku (dan zai yi yankan) ya wasa wukarsa ya hutar da abin yankansa. Muslim 1955 ya rawaito shi.


HADISI NA GOMA SHA TAKWAS:
An karbo daga Abu Zarri, shine Jundubu Bin Junada, da Abu Abdurrahman shi ne mu’azu dan Jabal R.A, yace manzon Allah s.a.w yace, kaji tsoran Allah, a duk inda kake, kabi mummunan aikin da kayi da kyakykyawan aiki,) ya shafe mummunan ka dabi’anci mutane da kyakykywar dabi’a Tirmizi 1987 ya rawaito yace: hadisi ne hasanun a wani bugun yace, hasanun sahihun.




HADISI NA GOMA SHA TARA:
An karbo daga Abdullahi dan Abas(RA) y ace nakasance abayan manzon allah (SAW) wata rana sai yace da ni, “ya kai yaro! Zan sanar da kai wasu jumloli: Ka kiyaye dokar Allah, sai kai ma ya kiya ye ka; ka kiytaye dokar Allah za ka same shi ya na yana yi maka jagoranci; idan zaka roka to ka roki Allah; idan zaka nemi temako ka nemi temakon Allah. Ka sani cewa da al’umma zasu taru kan su amfane ka da wani abu, ba zasu iya amfanar dakai komaiba , sai da abin da Allah yarubuta maka (cewa naka ne). Idan da al’umma zasu taru kan sucuce ka da wani abu, bas u isa su cuce ka ba, said a abin da Allah ya riga ya rubuta maka. An riga ancire alkalami, takardun sun bushe.” Tirmizi (#2516) ya rawaito, yace hadisine mai kyau ingantacce.
A wata riwayar wadda bat a tirmizi ba, “Ka kiyaye dokar Allah, zaka samu Ubangiji agaban ka (ya na majagoranci), ka nemi sanin Allah alokacin da ka ke cikin yalwa, zai san da kai alokacin da kake cikin tsanani. Ka sani duk abin day a kus kurema ka, dama can ba ayi shi don ya kuskure maka ba. Ka sani cewa cin nasara yana tare da hakuri, yayewar musiba tana tare da bakin ciki,kuma lallai atare da tsanani akwai sauki.”.


HADISI NA ASHIRIN:
An karbo daga Abu Mas’ud Ukbatu dan Amaru Al’ansari Albadariy R.A yace Manzon Allah s.a.w yace, yana daga cikin abin da mutane suka riska daga zancen Annabtar farko idan har ka zamto ba ka jin kunya to ka aikata duk abinda kakeso Bukhari 3483.


HADISI NA ASHIRIN DA XAYA:
An karbo daga Abu amrin ko abi Amrata, sufyan dab Abdullahi R.A yace n ace ya Manzon Allah s.a.w fada min wata maganas a cikin addinin musuluncis wadda b azan sake tambayar waninka ba game da ita sai yace, kace na yi imani da Allah sannan kuma ka daidaitu Muslim ya rawaito.




HADISI NA ASHIRIN DA BIYU:
An karbo daga abu Abdullahi Jabir dan Abdullahi Al’ansari (R.A) yace wani mutum ya tambayi Annabi s.a.w yace dashi ba ni labari idan sallaci salloli na wajibi, na azumci watan Ramadan, ha halatta halal, na kuma haramta haram. Ban kara komai a kan haka ba, shin kuwa zan shiga Aljanna, sai Annabi s.a.w yace eh.! Zaka shiga aljanna. Muslim. 15.)




HADISI NA ASHIRIN DA UKU:
An karbo daga Abu Malik haris bin Asim Al-ash’ari yace manzo Allah s.a.w yace Tsarki rabin imani ne, fadin subhanallahi tana cika mizani fadin subhanallahi da Alhamdulillah suna cika ko kowacce daya daga cikinsu) tan a cika abin da ke tsakanin sama da kasa sallah haske ce, sadaka hujja ce hakuri kuma haske ne, alkur’ani hujjane gare ka, ko a kanka dukkan mutane suna jijjifi da safe, daga cikinsu akwai mai zuwa sayar da kansa, ko dai ya ‘yantar da kansa ko kuma ya halakar kansa, Muslim ya rawaitoshi (#223).


HADISI NA ASHIRIN DA HUXU:
An karbo daga Abu zarri Al’gifari R.A daga Annabi s.a.w cikin abin da Annabi ke rawaitowa daga wurin Ubangijinsa lallai Allah madaukakin Sarki yace, yak u bayina na haramta wa kaina zalunci kuma na sanya zalunci ya zamas abin haramtawa a tsakanin ku yaku bayina dukkaniku batattu ne, sai fa wanda na shiryar da shi ku nemi shiryarwata ni kuma in shiryar da ku yak u bayina dukkaniku mayunwata ne sai wanda na ciyar dashi, don haka ku nemi shiryarwata ni kuma in shiryar da ku don haka ku nemi ciyarwata, ni kun azan ciyar daku yaku bayina, kowanenku tsirara yake ba tufafi sai wanda na suturta ku nemi suturata, zan suturtar da ku, yaku bayi zan suturtar daku ku. Ya bayina ! kuna yin laifi dare da rana ni kuma I nagafarta zunubai gaba dayansu ku nemi gafarata ni kuma zan yi muku gafara din nan yaku bayina ba ku isa ku cutar dani ba ballantana kuce zaku cutar dani baku isa ku amfanar dani ba, ballantana kuce zaku amfanar dani yaku bayani da ace na farkonku da na karshenku da mutanenku da aljannunku ku kasance a bias ga zuciyar wani mutum daya cikinsu mafi jin tsoran Allah hakan ba zai kafa komai a cikin mulkina ba, yaku bayina da ace na farkon ku da na karshen ku da mutanen ku da aljannuku ku kasance a bias zuciyar daya mafi fajirci hakan ba zai rage komai dangane da mulkina ba, yaku bayina da ace na farkon kuda na karshen ku da mutanen ku da aljanunku su tsaya a bigire daya, ni kuma kowanne ya roke ni kuma kowanne daya daga cikinku in bashi abin day a roka hakan ba zai rage komai daga cikin abin kee wurina ba sai fa gwargwadon abin da allura ta rage idan an tsoma ta cikin rowan teku yak u bayina kadai ayyukan ku nake kididdige wasu agare ku sannan in na cika muku ladanku. Wadanda ya samus alheri, ya gode wa Allah. Wanda ya sami wanin haka, kar ka ya zargi kowa sai kansa.
Muslim ne ya rawaito shi.


HADISI NA ASHIRIN DA BIYAR:
An karbo daga Abu zarril gifari R.A cikin sahabban Annabi s.a.w da cikin sahabban Annabi s.a.w yace dashi, ya manzon Allah s.a.w ma’abota dukiya sun tafi da lada suna yin sallahr farillah kamar yadda mukeyi suna yin azumin farillah kamar yadda mukeyi kuma suna sadaka da sauran dukiyarsu sai Annabi yace shin Allah bai riga ya baku abin da zaku yi sadaka ba ku abin da zaku yi sadaka dashi shine dukkan wani tasbihi sadaka ne dukkan wata hailala sadaka ce dukkan umarni da kyakykyawan aikin sadaka ne hana mummunan aiki sadaka ne, a gabar kowanne daga cikin akwai sadaka sai sahababai suka ya manzon Allah yanzu mutum zai biya bukatarsa kuma ya zama yana da lada sai Annabi s.a.w yace ku bani labari da ace ya sanya gabar tasa acikin haram shin ya da zunubi ? to haka nan in ya sanya a halal anan zai zama ya na da lada.


HADISI NA ASHIRIN DA SHIDA:
An karbo daga Abu hurairata R.A yace, dukkan gabbai na mutane akwai sadaka a ciki kowanne yini da rana ke hudowa cikinsa da zaka sasanta tsakanin mutane biyu dake rigima da juna sadaka ne, ka taimaki mutum game da dabbarsa, ka dora shi a akai sadaka ne ko kayansa ka dora masa akan dabbarsa sadaka ne, kalma daddada sadaka ce, dukkan taku da zaka yi tattaki zuwa sallah, sadaka ne, dauke wni abu mai cutarwa daga kan hanya sadaka ne, Bukhari (#2989) da Muslim(#1009) suka rawaito shi.


HADISI NA ASHIRIN DA BAKWAI:
????????????????????


HADISI NA ASHIRIN DA TAKWAS:
An karbo daga Abu Najih, shi ne irbadu dan sariya R.A y ace Manzon Allah s.a.w yayi mana wa’azi wa’azi mai isarwa zukata suka tsorata, idanu suka zubar da hawaye. Sai muka ce dashi, ya manzon Allah s.a.w kamar wa’azin mai bankwana to kayi mana wasici da jin tsoran Allah s.a.w kamar wa’azin bankwana to kayi mana wasici sai yace, ina muku wasici da jin tsoran Allah da kuma ji dabi, ko da bawa ne ya zama shugaba a gare ku lallai wanda ya rayu a cikinku da sannu zai ga sabani mai yawa, na umarce ku ku rike sunnata, da sunnonin halifofi shiryayyu. Ku rike tad a hakoranku (Fika), ku kiyaya fararrun ala’mura domin kowacce, bidi’a bat ace. Abu dawud 4607 da Timizi yace wannan hadisi ne mai kyau.ingantacce.


HADISI NA ASHIRIN DA TARA:
An karbo daga Mu’azu dan Jabal R.A yace nace ya Manzon Allah bain labarin wani aiki da zai shigar dani aljanna ya kuma nisantar dani sdaga wuta sai yace hakika kayi tambaya game da abin da yake mai girma si dai abu ne mai sauki ga wanda Allah ya saukake shi a gershi ka bauta wa Allah ba tare da ka hada shi da wani ba, kuma ka tsayar da Sallah, kuma ka bada zakka kuma ka azimci Ramadan sanan ka ziyarci dakin Allah sannan sai Annabi yace shin b azan shiryar da kai kofofin alheri ba? Azumi garkuwa ne sadaka kuma tana shafe kurakurai kamar yadda ruwa yake kasha wuta haka sallar mutum a cikin yankn dare. Sannan ya karanta (fadin Allah) gefen jikinsa yana nisantar gurin kwanciyar su har ya kai inda allah yake cewa ‘ya ‘amaluun (sannan sai Annabi s.a.w yace b azan ba ka labarin kan Al’amarin ba, da ginshikansa da kololuwar samansa ? sai nace eh. Sai yace, kan al’amarin shien musulunci ginshikinsa kuwa sallah kololuwar samansa kuwa jihadi sai Annabi s.a.w yace ba zna baka labairn abin da yake mallakar kusan gaba daya ba sai nace bani labari sai ya akam harshensa yace ka rike wannan sai na ce shin yanzu za akama mud a Maganar da muka yi sai Annabi yace da ma mahaifiyarka ta rasa ka akwai abin da yake jefa mutane a wuta kan fuskokinsu (ko yace) kan hancinsu sai sakamakon abin da harshensu ya fada Tirmizi (# 2616) ya ce hadisi ne mai kyau ingantacce.


HADISI NA TALATIN:
An karbo daga Abu Sa’alaba shi ne Jursumu dan Nasihib (R.A). y ace, “Lallai Allah Ta’ala ya farlanta farilla, kar ku tozarta su, ya sanya iyakokin, kar ku ketare su, ya haramta wasu abubuwa, kada ku keta alfarmarsu, ya yi shiru game da wadansu al’amura don jin kan ku, ba don mantuwa ba, kar ku bincike su. Darakuduni littafinsa sunan (j 4/sh 184 da waninsa.).


HADISI NA TALATIN DA XAYA:
An karbo daga Abu Abbas Sahlu dan sa’ad Assa’idi (R.A) y ace “Wani mutum ya zo wajen Annabi (S.A.W) ya ce “Ya Manzon Allah! Nuna min aikin da idsan na aikata shi, Allah zai kaunace ni, mutane ma za su kaunace ni.” Sai (Annabi (S.A.W) ya ce ”Ka yi zuhudu cikin lamarin duniya, sao Allah ya kaunace ka, kuma ka nisanci abin da ke hunnun mutane, sai mutane su kaunace ka” (1) Ibnu Majah ne ya rawaito shi (#4102) da waninsa ta hanyoyi masu kyau.


HADISI NA TALATIN DA BIYU:
An karbo daga Abu Sa’id, Sa’ad dan Malid dan Sinan Al-Khudiry (R.A) y ace Manzon Allah (S.A.W) y ace “Ba cuta babu cutarwa.”(1) Ibnu Majah ne ya rawaito shi, (#2341) da Darakuduni (#228) da waninsu Musnadan. Haka Imamu Malik ya rawaito shi a cikin Muwaddi (J2/sh 746) daga Amru dan Yahya Mursalan, bai ambaci Abu sa’id ba. Amma hadisin yana da hanyoyin da sashinsus yana karfafa sashi.


HADISI NA TALATIN DA UKU:
An karbo daga Abdullahi dan Abbas (R.A) ya ce, Manzon Allah Annabi (S.A.W). ya ce, “Da za’a bai wa mutune dukkan da’awarsu, da wadansu sun yi da’awar dukiyar wadansu da jininsu’ sai dai hujja tana kan mai da’awa, rantsuwa kuma a kan wanda ya yi musu.”(1) Baihaki ne ya rawito shi a cikin litaffinsa sunan (J 10/sh 252). Wani sashi na hadisin yana cikin Bukhari da Muslim.


HADISI NA TALATIN DA HUXU:
An karbo daga Abu Sa’id Al-Khuduriy (R.A) y ace “Na ji Manzon Allah Annabi (S.A.W).” yana cewa “Duk wanda ya ga abin ki, to ya gusar da shi da hannunsa, in ba shi da iko, ya gusar da shi da harshensa, in ba iko, to ya ki abin a zuci, wannan shi ne mafi raunin imani.(1)” Muslim ne ya rawaito shi (#49).


HADISI NA TALATIN DA BIYAR:
An karbo daga Abu Hurairata (R.A) y ace Manzon Allah Annabi (S.A.W). y ace “Kada ku rika yi wa juna hassada, kada ku yi kore kada ku kiyayya da juna, kada ku juya wa juna bayanku, kada sashenku ya yi ciniki a cikin cinikin dan uwansa. Ku kasance bayin Allah ‘yan uwan juna. Muslim dan uwan muslim ne, kada ya zalunce shi, kada ya kuntatar da shi, kada ka yi masa karya, kada ya wulakantar da shi. Tsoron Allah yana nan (har sau uku).!! Yana nuna kirjinsa,” Ya ishi mutum sharri, ya rika tozartar dad an uwansa musulmi. Jinin kowanne musulmi da dukiyarsa da mutuncinsa, haramun ne a kan musulmi.(1) Muslim ne ya rawaito shi (#2564).


HADISI NA TALATIN DA SHIDA:
An karbo daga Abu hurairata (R.A) daga Annabi yace, wanda duk yakutar wa mumini wani bakin ciki daga bakin cikin duniya to Allah zai kautar da masa da wani bakin ciki daga bakin cikin irin bakin kiyama duk wanda ya kawo sauki ga wanda yake cikin tsanani, Allah zai kawo masa sauki a duniya da lahira, wanda ya suturce musulmi to Allah zai yi masa sutura a duniya d alahira lallai Allah yana cikin taimakon bawa matukar bawan ya kasance mai taimakon dan uwansa musulmi wanda duk ya kam wani tafarki yana neman ilmi a wannan tafarkin Allah zai saukaka masa hanyar shiga aljanna babu wasu mutane da zasu taru a cikin wani daki cikin dakunan Allah sun karanta littafin Allah, sun darasinsa a tsakaninsu da juna, face sai nutsuwa ta sauka kansu, rahama ta lullube su, (mala’iku sun kewaye su) sai kuma Allah ya ambace su fadarsa. Wanda duk aikinsa ya yi sanda da shi, to dangatakarsa ba zai ta yi gaggawa ba zatayi gaggawa da shi ba. Muslim ne rawaito shi (2699) da wanan lafazi.


HADISI NA TALATIN DA BAKWAI:
An karbo daga Dan Abbas (R.A) daga manzon Allah (S.A.W) ciki irin abin abin da ya rawaito daga Ubangijisa yace, Allah ya riga ya rubuta ayyukan alheri da munanan ayyuka, wanda duk ya himmatu zai aikata awani kyakkywan aii sai bai samu aikatawa ba, Allah zai rubuta masa kyakkywana aikin guda dyaa cikakke, idan ku,ma ya himmatu zai aikata wani kyakkywan aiki kuma ya aikata shi ,to ubangiji zai rubuta masa lada goma izuwa ninki dari bakwai zuwa ninki dayawa in ya himmatu aikn kuma bai aikata ba, Allah zai rubuta masa mummunan aiki guda daya Bukhari Da muslmi (6491) (131) a cikin sahihan litattafansu.


HADISI NA TALATIN DA TARA:
An karbo daga Abu Hurairata, (R.A) yace, manzon Allah yace Allah ta’ala yace duk wanda yayi gaba da waliyyina to na bashi sanarwa yazo yayi yaki dani. Bawana ba zai kusance ni ba, da wani abu da na fi kauna, sama da abin da na wajabta masa. Bawana ba zai gushe ba yana kusanta ta da nafiloli har sai na zamanto ina kaunarsa, idan na kaunacee shi, sai na kasance jinsa, da yake ji dashi, da ganinsa da yake gani dashi da hannunsa da yake damka dahsi da kafarsa da yake tafiya da ita. Wallahi idan ya rokeni zan bashi abin daya rokla kuma wallahi idan ya nemi tsarina zan tsareshi Bukhari ne rawaito shi (6502).


HADISI NA ARBA'IN
An karbo daga dan Abbas (R.A) yace “ manzon Allah yace Allah ya yafe wa al’ummata abin da tayi dakuskure da mantuwa d aabind aaka tilasta ta. Hadisin ne mai kyau Ibnu majah ne ya rawaito shi (2045) da baihaki a cikin sunan.


HADISI NA ARBA'IN DA XAYA:
An karbo daga Abdullahi dan Umar (R.A) yace, Manzon Allah ya daafa kafadata yace ka kasance a duniya tamkar kai bako ne ko kuma wanda yake kan hanya dan Umar (R.A) yana cewa idan kai kai yamma kar kayi jiran safiya idan kuma wayi gari to kar ka jira yamma, ka riki aiki alheri lokacin rayuwarka saboda lokacin lafiyarka, saboda lokain rashin lafiyarka ka riki aiki alhei lokacin rayuwarka, saboda ka amfana lokacin mutuwarka, Bukhari ne ya rawaitoshi. (6416).


HADISI NA ARBA'IN DA BIYU:
An karbo daga Abu Muhammad Abudullahi dan Amru dan As (R.A) yace manzon Allah yace, dayanku ba ya zama mumini har sai son zuciyarsa yana biyayya ga abin da nazo da shi. Hadisin ne ingatacce, mai kyau mun rawaito shi acikin littafin Hujja da sanadi ingantacce.


HADISI NA ARBA'IN DA UKU:
An karbo daga Anas dan malik (R.A) naji manzon Allah yana cewa, Allah madaukakin sarki yana cewa, ya kai dan Adam! Lallai ba zaka bauta min ba, kuma ka sanya rai game da rahamata face sai na gafarta maka ban damu ba. Ya kai dan Adam da ace zunubanka zasu cika sashen sama gaba daya, sannan ka nemi gafarata sai in gafarta maka yaka dan Adamda ace zaka zo min da cikin kasa gabad aya zunubi ne sannan ka gamu dani, ba tare da ka hani da kowa ba ni, uma zan kawo maka gafara, cikin kasa. Tirmizi ne rawaitoshi *3540) yace hadisi ne mai kyau yace hadisi ne mai kyau ingantacce.


HADISI NA ARBA'IN DA HUXU:
An karbo daga Dan Abbas (R,A) yace manzon Allah yace, ku riskar da kowanne rabon gado sananne ga ma’abotan wannan rabon, abin da ya ragu to a ba namiji wanda ya fiskanci Bukhari (6732) da Muslim 91615) ne suka rawaito shi.


HADISI NA ARBA'IN DA BIYAR:
An karbo daga Aisha (R.A) tace manzon Allah yace shayarwa tana haramta abin da haihuwa take haramtawa. Bukhari da Muslim (2656) (1444) suka rawaito shi.


HADISI NA ARBA'IN DA SHIDA:
An karbo daga Jabir dan Abdullahi (R.a) yace naji manzon Allah a shekarar bude makka a lokacin manzon Allah yana makka yana cewa lallai Allah da manzonsa sun haramta sayar da gida da mushe da alade, da gunki sai akace ya manzon Allah ba mu labari game da kitsen mushe ana shafawa a jikin jirgin ruwa ana shafawa a fata ana kunna fitilu da shi shin ya halatta ko bai halatta ba, ? sai yace a’a wannan haramun ne sannan sai manzon Allah yace Allah yac Allah ya la’anci yahudawa Allah ya haramta musu kitse sai suka kawata shi sannan suka sayar dashh isuka cinye kudinsa Bukhari da Muslim (2236) (1581) suka rawaito shi .


HADISI NA ARBA'IN DA BAKWAI:
An karbo daga dan Abu Burda daga babansa daga Musal Ash’ariy (R.A) yace Annabi ya tura shi kasar Yemen sai ya tambaye shi dangane da wani abin sha da ake yi acan sai yae menene abin? Sai yace “ Albit’u da Almizru “ sai akace da Abu burda menene Albit’u sai yace, wani tsimi ne da ake yi da zuma, almizru kuwa wani tsimi ne da ake yi da alkama. Sai Annabi yace, duk abu ma sa maye haramun ne Bukhari ne rawaito shi. (4343).


HADISI NA ARBA'IN DA TAKWAS:
An karbo daga Mikdamu dan Ma’adi Yakrib (R.A) yace naji Manzn Allah yana cewa dan Adam bai taba cika wani boki ba ko wani koko mafi sharri, sama da cikinsa ba. Ya ishidan Adam wadansu yan lomomi wand zasu tsaida masa gadon bayansa (Yunwa ba zata galabaita shi ba) idan dole sai ya ci abinci da yawa si ya kasa cikinsa kashi uku, kashi daya abinci kashi biyu ruwa kashi dayan ya barwa wa numfashi.
Ahmad 9j4/sh 132) da Tirmizi 92380) da Ibnu majah (3349) Tirmizi yace, Hadisi ne mai kyau.


HADISI NA ARBA'IN DA TARA:
An karbo daga Abdullahi dan Amru (R.A) daga Annabi yace, “abubuwa guda hudu wanda suka kasance tare d ashi ya kasance munafiki wanda siffa ta munafinci na tare dashi har sai ya bar ta idan yayi magana ya zamanto yayi karya. Idn yayi alkwari sai ya zamanto ya saba. Idan anyi rigima dashi, sai ya ketare dokar Allah idan kuma aka kulla alkawari zai yaudareka (Bukhari da Muslim) (34) ( 58) suka rawaito shi.


HADISI NA HAMSIN:
An karbo daga Umar dan Khaddab (R.A) daga Annabi yace da ace kuma dogara ga Allah hakikanin dogaro da shi da Allah ya azurta ku kamar yadda yake azurta tsuntsaye. Suna sammako da yunwa amma suna dawo wa da yamma suna koshe. Imam Ahmad da Tirmizi da nasa’I da Ibnu Majah, da Ibnu Hibban da Imam Ahmad da Tirmizi da nasa’I da Ibnu Majah da Ibnu Hibban da Ahmad (2344) da Nasa’I a cikin sunan Alubra (J8/sh 79) Da hakim (418) Tirmizi yace, hadisin ne ingantacce.




An karbo daga Abdullahi dan Busur, (R.A) yace wani mutum (mazaunin karkara ) yazo wurin Annabi yace ya Manzon Allah shari’oi sun yi mana yawa a bamu wani babi gamamme da zamu rike. “ Sai Annabi yace kada harshenka ya bushe wajen Ambaton Allah Ahmad ne ya rawaito shi (188, 190).