طاهر جبريل دكو
_10 _October _2015هـ الموافق 10-10-2015م, 05:29 PM
نواقض الإسلام لشيخ الإسلام محمد بن عبد الوهاب
ABUBUWA MASU WARWARE MUSULUNCI
NA MALAMIN MUSULUNCI
MUHAMMADU XAN ABDULWAHHAB AT-TAMIMI
WANDA AKA HAIFA A SHEKARA TA 1115 YA KUMA RASU A SHEKARA TA 1206 BAYAN HIJIRA.
TARJAMAR
XAHIRU JIBRIL DUKKU.
1436-12- 25 AH
بسم الله الرحمن الرحيم
Ka sani cewa yana daga cikin mafiya girman (abubuwa) masu warware musulunci (abubuwa) goma:
Na xaya: Yin shirka acikin bautan Allah (maxaukaki); dalili akan haka kuwa shine faxin Allah (maxaukaki):
"إِنَّ اللَّهَ لَا يَغْفِرُ أَنْ يُشْرَكَ بِهِ وَيَغْفِرُ مَا دُونَ ذَلِكَ لِمَنْ يَشَاءُ"
Ma'ana: Lallai Allah baYa gafartawa idan akayi masa shirka (wato aka mutu ana shirka ba'a tubaba) kuma Ya na gafarta abinda bai kai shirkaba ga wanda Yaso" Suratun-nisa'i aya ta 48.
Daga cikin haka akwai yin yanka domin wanin Allah kamar wanda ke yin yanka domin aljani ko kabari.
Na biyu: Wanda ya sanya 'yan kamun qafa tsakaninsa da Allah ya na kiran su ya na roqon su ceto kuma ya na dogaro gare su ya kafirta da ijma'in malamai.
Na uka:Wanda bai kafirta mushirikai ba ko ya yi shakka game da kafircinsu ko ya inganta mazhabarsu ya kafirta da ijma'in malamai.
Na hudu: Wanda ya qudurce cewa wanin shiriyar Manzon Allah ta fi shiriyarsa kamala, ko kuma shiriyar waninsa ta fi shiriyarsa kyau- kamar masu fifita hukuncin xagutai akan hukuncinsa- to shi kafiri ne.
Na biyar: Wanda ya qyamaci wani abu daga cikin abin da Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya zo da shi -ko da kuwa ya yi aiki da shi- ya kafirta.
Na shida: Wanda ya yi isgilanci ga Addinin Allah ko sakamakonSa ko uqubarSa ya kafira, dalili akan haka shi ne faxinSa maxaukaki:
{قُلْ أَبِاللَّهِ وَآيَاتِهِ وَرَسُولِهِ كُنْتُمْ تَسْتَهْزِئُونَ - لَا تَعْتَذِرُوا قَدْ كَفَرْتُمْ بَعْدَ إِيمَانِكُمْ} [التوبة: 65 - 66]
Ma;ana: "Ka ce (mu su): da Allah da ayoyinSa da manzonSa ku ka kasance ku na isgilanci? (65) ka da ku bada wani hanzari! Haqiqa kun kafirta bayan imaninku(66)
Na bakwai: Sihiri, daga cikinsa akwai wanda ake yi don nesantarwa akwai wanda ake yi don qwallafa rai akan abu. Dalili akan haka shi ne faxinSa maxaukaki:
{وَمَا يُعَلِّمَانِ مِنْ أَحَدٍ حَتَّى يَقُولَا إِنَّمَا نَحْنُ فِتْنَةٌ فَلَا تَكْفُرْ} [البقرة: 102]
Ma'ana: "kuma (su biyun) ba su karantar da wani face sun ce: abin sani kawai mu fa fitina ne ka da ku kafirta" Suratul Baqara aya ta 102.
Na takwas: Qarfafan mushirikai da taimakonsu akan musulmai. Dalili akan haka faxinSamaxaukaki:
{وَمَنْ يَتَوَلَّهُمْ مِنْكُمْ فَإِنَّهُ مِنْهُمْ إِنَّ اللَّهَ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ} [المائدة: 51] (4)
Ma'ana: "Kuma wanda ya jivince su daga cikinku, to lallai ya na tare da su. Lallai Allah ba Ya shiryar da mutane azzalumai" Suratul Ma'ida aya ta 51.
Na tara: Wanda ya qudurce cewa: akwai wani daga cikin mutane wanda biyayya ga Annabi –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi – ba dole ba ne a gare shi kuma ya halatta gare shi ya fice daga shri'arsa kamar yadda ya halatta ga Khadiru ya fita daga shri'ar Annabi Musa –amincin Allah ya tabbata a gare shi – to shi kafiri ne.
Na goma: Kawar da kai da ko in kula ga addinin Allah, ba ya koyon shi, kuma ba ya aiki da shi. Dalili akan haka shi ne faxinSa maxaukaki:
{وَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنْ ذُكِّرَ بِآيَاتِ رَبِّهِ ثُمَّ أَعْرَضَ عَنْهَا إِنَّا مِنَ الْمُجْرِمِينَ مُنْتَقِمُونَ} [السجدة: 22]
Ma'ana: "Waye mafi zalunci sama da wanda aka tunatar da shi game da ayoyin Ubangijinsa sa'annan ya kawar da kai yi ko in kula da su? Lallai Mu masu xaukar fansa ne akan masu laifi. Suratu As-sajada aya ta 22.
Kuma babu bambanci cikin duk waxannan abubuwa masu warware musuluncin tsakanin mai yi da gangan ko mai yi da gaske ko matsauraci sai dai wanda aka tilasta.
Kuma dukkanin su su na da haxari mai girma, kuma su na yawa faruwa, saboda haka ya kamata musulmi ya yi hattara game da su kuma ya tsaurace wa kansa faruwan su.
Muna roqon Allah tsari daga abubuwan da ke wajabta fushinSa, da raxaxin uqubqrSa.
Allah Ya yi daxin tsira da aminci ga Annabinmu Muhammadu da Alayensa da sahabbansa.