المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : القواعد الأربع تأليف شيخ الإسلام محمد بن عبد الوهاب qa'idoji guda huxu


طاهر جبريل دكو
_10 _October _2015هـ الموافق 10-10-2015م, 05:24 PM
القواعد الأربع تأليف شيخ الإسلام محمد بن عبد الوهاب

QA'IDOJI GUDA HUXU





WALLAFAR MALAMIN MUSULUNCI




MUHAMMADU XAN ABDULWAHHAB ALLAH YA YI MA SA RAHAMA








TARJAMAR



XAHIRU JIBRIL DUKKU
1436\ 12\ 27 AH





بسم الله الرحمن الرحيم
Ina roqon Allah mai karimci, Ubangijin Al'arshi mai girma Ya jivince ka a duniya da lahira, kuma Ya sanya ka mai albarka a duk inda ka ke. Kuma Ya sanya ka daga cikin waxanda idan aka ba shi sai ya yi godiya, idan aka jarrabe shi sai ya yi haquri, idan ya yi zunubi kuma sai ya nemi gafara, domin waxannan su ne tushen samun rabo.
Ka sani – Allah Ya shiryar da kai zuwa ga yi masa xa'a- cewa lallai hanifiyya Addinin Annabi Ibrahim shi ne; ka bauta wa Allah Shi kaxai ka na mai tsarkake addini gare Shi kamar yadda Allah Ya ce:
{وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالأِنْسَ إِلاَّ لِيَعْبُدُونِ}
Ma'ana: "kuma ba Mu halicci aljanu da mutane ba sai dai don su bauta miNi"
Idan ka gane cewa Allah Ya halicce ka ne domin bautar Sa, sai kuma ka gane cewa bauta ba kiran ta bauta har sai ta kasance tare da tauhidi, kamar yadda salla ba'a kiran ta salla sai ta kasance an yi ta da tsarki. Saboda haka idan shirka ta shiga cikin bauta vatata ta ke yi tamkar hadasi idan ya shiga cikin alwala.
To! Idan ka fahimci cewa: lallai shrka idan ta cakuxu da ibada ta kan vata ta, kuma ta rusa aiki, kuma ma'abucin ta ya kasance cikin waxanda za su dawwama a cikin wuta, sai ka gane cewa abu mafi muhimmanci akan ka shi ne sanin hakan, da fatan Allah ya kuvutar da kai daga wannan sarqaqiyar wacce ita ce shirka ga Allah wacce Allah Ya ce game da ita:
{إِنَّ اللَّهَ لا يَغْفِرُ أَنْ يُشْرَكَ بِهِ وَيَغْفِرُ مَا دُونَ ذَلِكَ لِمَنْ يَشَاءُ}
Ma'ana: " Lallai Allah ba Ya gafartawa idan aka (mutu) ana maSa shirka, kuma Ya na gafarta abin da bai kai hakan bag a wanda Ya so".
Wannan kuma zai faru ne ta hanyar fahimtar wasu qa'idoji guda huxu Allah Ya ambace su a cikin littafinsa;
Qaida ta xaya: Ka sani cewa lallai kafiran da Manzon Allah – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi – ya yaqa sun tabbatar da cewa Allah – maxauaki - Shi ne mahalicci mai gudanarwa, amma hakan bai shigar da su musulunci ba. dalili akan hakan shi ne faxinSa maxaukaki:
{قُلْ مَنْ يَرْزُقُكُمْ مِنَ السَّمَاءِ وَالْأَرْضِ أَمَّنْ يَمْلِكُ السَّمْعَ وَالْأَبْصَارَ وَمَنْ يُخْرِجُ الْحَيَّ مِنَ الْمَيِّتِ وَيُخْرِجُ الْمَيِّتَ مِنَ الْحَيِّ وَمَنْ يُدَبِّرُ الْأَمْرَ فَسَيَقُولُونَ اللَّهُ فَقُلْ أَفَلا تَتَّقُونَ}
Ma'ana: " Ka ce: wa ya ke azurta ku daga sama da qasa ko kuma wa ya ke mallakan ji da gani kuma wa ya ke fitar da rayayye daga matacce kuma ya fitar da matacce daga rayayye, kuma wa ya ke gudanar da al'amura? Da sannu za su ce Allah ne, sai ka ce: shin ba za ku ji tsoron Allah ba?.
Qa'ida ta biyu: lallai su su na cewa: Ai mu ba mu kiraye su mu ka nuface su ba face don neman kusanci da ceto. Dalili akan kusanci faxinSa maxaukaki:
{وَالَّذِينَ اتَّخَذُوا مِنْ دُونِهِ أَوْلِيَاءَ مَا نَعْبُدُهُمْ إِلاَّ لِيُقَرِّبُونَا إِلَى اللَّهِ زُلْفَى إِنَّ اللَّهَ يَحْكُمُ بَيْنَهُمْ فِي مَا هُمْ فِيهِ يَخْتَلِفُونَ إِنَّ اللَّهَ لا يَهْدِي مَنْ هُوَ كَاذِبٌ كَفَّارٌ}
Ma'ana: " waxanda su ka riqi majivinta koma bayansa (su na cewa) mu ba mu bauta mu su face don su kusantar da mu zuwa ga Allah kusanci. Lallai Allah zai yi hukunci a tsakanin su game da abin da su ke savani a cikin sa. Lallai Allah ba Ya shiryar da wanda ya ke maqaryaci mai yawan kafirci". Dalilin ceto kuma shi ne faxinSa maxaukaki:
{وَيَعْبُدُونَ مِنْ دُونِ اللَّهِ مَا لا يَضُرُّهُمْ وَلا يَنْفَعُهُمْ وَيَقُولُونَ هَؤُلاءِ شُفَعَاؤُنَا عِنْدَ اللَّهِ}
Ma'ana: "Kuma su na bautawa wannin Allah abin da ba ya iya cutar da su kuma ba ya iya amfanar da su, kuma su na cewa: waxannan su ne masu ceton mu a gaban Allah".
Ceto kala biyu ne; ceto korarre da ceto tabbatacce. Shi ceto korarre shi ne wanda aka nema daga wanin Allah cikin abin da ba bu mai ikon aiwatar da su sai Allah. Dalili shi ne faxinSa maxaukaki:
{يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا أَنْفِقُوا مِمَّا رَزَقْنَاكُمْ مِنْقَبْلِ أَنْ يَأْتِيَ يَوْمٌ لا بَيْعٌ فِيهِ وَلا خُلَّةٌ وَلا شَفَاعَةٌ وَالْكَافِرُونَ هُمُ الظَّالِمُونَ}
Ma'ana: " Ya ku waxanda su ka yi imani, ku ciyar daga abin da Mu ka azurta ku kafin wani yini ya zo wanda babu saye da sayarwa a cikinsa kuma babu abokantaka kuma babu ceto. Kuma kafirai su na azzalumai".
Shi kuma ceto tabbatacce shi ne wanda ake naman sa daga Allah, shi mai yin ceton ana karrama shi ne da ceton, shi kuma wanda za a ceta shi ne wanda Allah Ya yarda da maganarsa sa aikinsa bayan an –Allah Ya ba da izinin cetonsa. Kamar yadda Allah maxaukaki Ya ce:
{مَنْ ذَا الَّذِي يَشْفَعُ عِنْدَهُ إِلاَّ بِإِذْنِهِ}
Ma'ana: "Wanene wannan da ya isa ya yi ceto a wurinSa idan ba da izininSa ba?"
Qa'ida ta uku: lallai Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi – ya yi galaba ne akan wasu mutane da su ka sha bamban a cikin abubuwan bautarsu, daga cikin su akwai masu bautar mala'iku, daga cikin su kuma akwai masu bautar annabawa da salihai, daga cikin su kuma akwai masu bautar itatuwa da duwatsu, daga cikin su kuma akwai masu bautar rana da wata. Kuma Manzon Allah ya yaqe su gaba xayansu bai rarrabe tsakanin su ba. dalili game da hakan shi ne faxinSa maxaukaki:
{وَقَاتِلُوهُمْ حَتَّى لا تَكُونَ فِتْنَةٌ وَيَكُونَ الدِّينُ كُلُّهُ لِلَّهِ}
Ma'ana: "Kuma ku yaqe su har sar fitina ta gushe kuma addini ya zama na Allah". Dalili game da bautar rana kuma shi ne faxinSa maxaukaki:
{وَمِنْ آيَاتِهِ اللَّيْلُ وَالنَّهَارُ وَالشَّمْسُ وَالْقَمَرُ لا تَسْجُدُوا لِلشَّمْسِ وَلا لِلْقَمَرِ وَاسْجُدُوا لِلَّهِ الَّذِي خَلَقَهُنَّ إِنْ كُنْتُمْ إِيَّاهُ تَعْبُدُونَ}
Ma'ana: " daga cikin ayoyinSa akwai dare da yini da rana da wata. Ka da ku yi sujjada ga rana haka nan ma wata, ku yi sujjada ga Allah wanda ya halicce su in har kun kasance Shi kaxai ku ke bautawa". Dalili akan mala'iku kuma shi ne faxinSa maxaukaki:
{وَلا يَأْمُرَكُمْ أَنْ تَتَّخِذُوا الْمَلائِكَةَ وَالنَّبِيِّينَ أَرْبَاباً}
Ma'ana: "Kuma ba ya umurtan ku da ku riqi mala'iku a matsayin iyayen giji". Dalili game da bautar Annabawa kuma shi ne faxinSa maxaukaki:
{وَإِذْ قَالَ اللَّهُ يَا عِيسَى ابْنَ مَرْيَمَ أَأَنْتَ قُلْتَ لِلنَّاسِ اتَّخِذُونِي وَأُمِّيَ إِلَهَيْنِ مِنْ دُونِ اللَّهِ قَالَ سُبْحَانَكَ مَا يَكُونُ لِي أَنْ أَقُولَ مَا لَيْسَ لِي بِحَقٍّ إِنْ كُنْتُ قُلْتُهُ فَقَدْ عَلِمْتَهُ تَعْلَمُ مَا فِي نَفْسِي وَلا أَعْلَمُ مَا فِي نَفْسِكَ إِنَّكَ أَنْتَ عَلاَّمُ الْغُيُوبِ}
Ma'ana: "Kuma ambata mu su lokacin da Allah Ya ce ya Isa xan Maryam, shin kai ne ka ce da mutane ku riqe ni da ni da mahaifiyata ababen bauta guda biyu koma bayan Allah? Ya ce: tsarki ya tabbata gare Ka! Ba ya halitta gare ni in faxi abin da ba ni da haqqin faxan sa, in ma da na faxa to haqiqa Ka san shi, Ka na sanin abin da ke cikin raina amma ni ba na sanin abin da ke cikin ranKa, lallai Kai, Kai ne masanin gaibu". Dalilin bautar salihai kuma shi ne faxinSa maxaukaki:
{أُولَئِكَ الَّذِينَ يَدْعُونَ يَبْتَغُونَ إِلَى رَبِّهِمُ الْوَسِيلَةَ أَيُّهُمْ أَقْرَبُ وَيَرْجُونَ رَحْمَتَهُ وَيَخَافُونَ عَذَابَهُ}
Ma'ana: " Waxannan su ne waxanda su ke kira su na masu neman tsani zuwa ga UbangijinSu, wa ya fi kusanci cikin su? Su na fatan rahamarSa kuma su na tsoron azabarSa". Dalilin bishiyoyi da duwatsu kuma shi ne faxinSa maxaukaki:
{أَفَرَأَيْتُمُ اللاَّتَ وَالْعُزَّى وَمَنَاةَ الثَّالِثَةَ الأُخْرَى}
Ma'ana: " Shi ba ku ga Lata da Uzza ba? da Manata wasu ukun na daban". Da hadisin Abu Waqidin Al-laithi –Allah Ya qara ma sa yarda – ya ce:
"خرجنا مع النبي صلى الله عليه وسلم إلى حنين ونحن حدثاء عهد بكفر، وللمشركين سدرة يعكفون عندها وينوطون بها أسلحتهم يقال لها ذات أنواط. فمررنا بسدرة فقلنا: يا رسول الله اجعل لنا ذات أنواط، كما لهم ذات أنواط". الحديث.
Ma'ana: "Mun fita tare da Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi – zuwa hunain alhali muna sabbin musulunta, mushirikai suu na da magarya da su ke zaman dirshan a qarqashinta kuma su ke rataye takubbansu akanta ana cewa da ita zatu anwax. Sai mu ka wuce wata magarya sai mu ka ce: ya ma'aikin Allah, muma kasanya ma na ma'abuciyar rataya kamar yadda su ke da ma'abuciyar rataya. Har zuwa qarshen hadsisin.
Qa'ida ta huxu: lallai mushirikan zamaninmu su fi mushirikan farko shirka, saboda 'yan farko su na shirkansu ne a lokaci na walwala da jin daxin rayuwa, kuma su na yin ikhlasi a lokaci tsanani. Amma mushirikan zamaninmu su shirkarsu da'iman ce a lokacin jin daxi da lokacin tsanani. Dalili shi ne faxinSa maxaukaki:
{فَإِذَا رَكِبُوا فِي الْفُلْكِ دَعَوُا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ فَلَمَّا نَجَّاهُمْ إِلَى الْبَرِّ إِذَا هُمْ يُشْرِكُونَ}
Ma'ana: "Idan su ka yi tafiya a cikin jirgin ruwa sai su kirayi Allah su na masu tsarkake addini gare Shi, yayin da ya tseratar da su zuwa kan qasa sai su koma su riqa shirkansu".
Allah ya yi salati da aminci ga Annabi Muhammadu da Alayensa da sahabbansa.