تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : su wane ne 'yan shi'a kuma menene mafarin akidarsu?


طاهر جبريل دكو
_7 _October _2015هـ الموافق 7-10-2015م, 03:11 PM
بسم الله الرحمن الرحيم
1- : su wane ne 'yan shi'a?
Amsa: malaminsu Muhammad xan Muhammad xan Nu'uman wanda ake wa laqabi da Almufid ya na cewa; su ne mabiya Amirul mu'minina Aliyu –s.s.a- ta fuskar wala'i gare shi da qudurce shugabancinsa bayan Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ba tare da rabewa ba[1] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn1) tare da kore khalifanci ga waxanda su ka gabace shi a maqamin khalifanci, kuma ya sanya shi a qudurce, abin bi daga gare su ba mabiyi ba ga xayansu bisa haqiqa.([2] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn2))[3] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn3)
Tskokaci: lallai lafazin (shi'a) idan aka sake shi a wannan zamanin baya komawa face ga 'yan shi'a ithna ashariyya, saboda 'yan shi'a ithna ashariyya su ne galibin 'yan shi'a yau a Iran, da Iraqi, da Rusia, da Lubnan, da qasashen yankin tekun fasha, da sauran wurare, kuma saboda lallai littafansu na hadisi da riwayoyi sun game mafi yawan ra'ayoyi na qungiyoyin 'yan shi'a waxanda su ka bayyana a zamunnan da su ka gabata.
2- Me ne ne tushen madhabar shi'a?
Amsa: Zance mafi rinjayi na malamai masu tahqiqi shi ne cewa lallai wanda ya dasa (aqidar shi'anci) kuma ya bayyanata shi ne Abdullahi bnu Saba'i bayahude, kai! Wannan shi ne abin da littafan mazahabar shi'a da kansu su ka tabbatar, haqiqa sun nassnata cewa ibnu Saba'i bayahude shi ne farkon wanda ya shahara da da'awar imamancin Aliyu binu Abi Xalib (Allah Ya qara ma sa yarda) wannar ita ce aqidar cewa akwai nassi game da imamar Aliyu Xan Abi Xalib (Allah Ya qara ma sa yarda) kuma wannar ita ce tushen shi'anci. Kamar yadda littafan na 'yan shi'a su ka ce lallai shi ne farkon wanda ya fara bayyana suka ga surakanen Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) sayyidina Abubakar da sayyidina Umar da sayyidina Usman (Allah Y qara mu su yarda) kuma shi ne farkon wanda ya bayyana aqidar raja'a, kuma ya yi da'awar allantakar syyidina Aliyu Xan Abu Xalib (Allah Ya qara ma sa yarda) … har dai zuwa qarshe. Hamshaqin malamin nan nasu Alhasan Alnubakhti: (Saba'iyyawa su ne mabiya Abdullahi Xan Saba'i, kuma ya kasance shi ne ya bayyana suka ga Abubakar da Umar da Usman da sahabbai kuma ya barranta daga gare su, kuma ya ce lallai sayyidina Aliyu (amincin Allah ya tabbata a gare shi) shi ya umurce shi da yin hakan. Sai sayyidina Aliyu ya kama shi ya tambaye shi game da wannan maganar ta shi da ya tabbatar da ita sai ya yi umurni da cewa a kashe shi.[4] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn4) Har zuwa inda ya ce: (jama'a da yawa daga ma'abuta ilimi cikin mabiya Aliyu (Amincin Allah ya tabbata gare shi) sun hakaito cewa: lallai Abdullahi xan Saba'i ya kasance bayahude sannan ya musulunta, kuma ya yi wala'i ga Aliyu (amincin Allah ya tabbata gare shi) kuma ya kasance a lokacin da ya ke kan yahudancinsa ya na faxin irin wannan maganr game da Yusha'u xan Nun bayan rasuwar Annabi Musa (amincin Allah ya tabbata a gare shi)[5] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn5) sannan bayan musuluntar sa kuma sai ya faxi kwatankwacin wannan game da Aliyu (amincin Allah ya tabbata gare shi) bayan rasuwar Annbi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi). Kuma shi ne farkon wanda ya fara yayata wajibcin imamancin Aliyu (amincin Allah ya tabbata gare shi) kuma ya nuna barrantuwarsa daga maqiyansa kuma wanda ya tona asirin waxanda su ka sava ma sa ya ((kuma kafirta su)).[6] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn6) Daga haka ne waxanda su ka sava wa 'yan shi'a su ka ce asalin shi'anci da rafilanci daga yahudanci aka xauko shi)[7] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn7)
Sannan malamin malaman mazhabar shi'a Sa'adul Qummi ya ambaci matsayar Ibnu Saba'i bayahude yayin da labarin mutuwar Aliyu (Allah Ya qara masa yarda) ya riske shi ta yadda ya yi da'awar cewa bai mutu ba, kuma ya ce zai dawo ya kuma wuce gona da iri game da shi.[8] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftn8)
[1] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftnref1) - Abin nufi da wannan shi ne lallai xan shi'a imamiyya shi ne wanda ya qudurce cewa lallai Aliyu – Allah Ya qara ma sa yarda – shi ne khalifa bayan Manzon Allah – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi – kai tsaye ba tare da wani a tsakaninsu ba, wannan ko ya ginu ne akan kore khalifancin sayyidina Abubakar da Umar da Usman, saboda haka sifan shi'anci ba ya gaskata a - ra'ayin wannan malamin nasu Almufid sai – ga wanda ya qudurce khalifancin sayyidina Ali xan Abi Xalib- Allah Ya qara ma sa yarda tun daga komawar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi – har zuwa sa'adda sayyidina Ali ya yi shahada.

[2] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftnref2) - Saboda haka a wannan aqidar, sayyidina Aliyu - Allah Ya qara ma sa yarda – a zahiri ne ya ke mabiyi ga khalifofin nan guda uku, amma a voye kam ba shi ya ke bin su ba, su su ke bin sa ba, sai dai a babin taqiyya.

[3] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftnref3) - Awa'ilul maqalat fi madhahibil mukhtarat shafi na 35, babi game da bambancin da ke tsakanin 'yan shi'a cikin abin da aka jingina gare su na shi'anci da mu'utazilawa cikin abin da ta cancanta na sunan mu'utazilanci wallafar malaminsu Almufid wanda ya rasu a shekara ta 413 bayan hijira.

[4] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftnref4) - Firqu sshi'a shafi na 50. (ikhtilafu sshi'atil alawiyya ba'ada qatli amiril mu'minina Aliyin alaihissalam) Assaba'iyya na Alhasan binu Musa Anubakhti daga cikin malamansu a qarni na uku bayan hijira.

[5] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftnref5) - Wato ya na da'awar allantaka gare su su biyun lokacin da ya ke kan yahudancinsa sannan kuma ya yi irinta game da sayyidina Aliyu xan Abu Xalib (Allah Ya qara ma sa yarda) bayan ya yi da'awar musulunci. A duba (littafi mai su na) Al'anwarunnu'maniyya 2\234 (Nurun fi bayanil firaqi wa adyaniha da abin da ke alaqa da shi na muqaddima da abin da aka riskar zuwa gare his) na Ni'imatullahi Abduliahi Alhusaini almusawi aljaza'iri wanda ya rasu shekara ta 1112. Malaminsu mai suna Muhammad Ibnul Hasan Alhurrul amili( wanda ya rasu shekara ta 1104) ya sifanta shi da faxinsa (mai daraja masani muhaqqiqi, mai yawan sani mai girman matsayi) Amalul Amil fi ulama'i jabali amil 2\336 lamba ta 1035.

[6] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftnref6) - wannan maganar da ke cikin baka ta na cikin wata nuskha ta littafin firaqu sshi'a na Nubakhti da Alqummi shafi na 33 tahqiqin dr Abdul mun'im Alhanfi bugun daru rrashid bugu na farko shekara ta 1412.

[7] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftnref7) - Firaqu sshi'a shafi na 50 (ikhtilafu sshi'atu Alawiyya ba'da maqtali amiril mu'umina Aliyi (Alaihi ssalam Assaba'iyya)

[8] (http://www.afaqattaiseer.org/vb/#_ftnref8) - Amaqalat wal firaq shafi na 10 zuwa 21 wallafar Sa'ad binu Abdillahil ash'ari Alqummi wanda ya rasu a shekara ta 301.