طاهر جبريل دكو
_30 _September _2015هـ الموافق 30-09-2015م, 09:40 PM
HAQIQANIN ABIN DA YA FARU GAME DA KISAN HUSANIN –ALLAH YA QARA YARDA A AGARE SHI.
An yi wa Yazidu mubaya'a a matsayin shugaban musulmi a shekara ta sittin bayan hijira, alhali ya na xan shekara talatin da huxu. Husaini bai yi mubay'a ba, haka nan ma Abdullahi xan Zubairu kuma sun kasance su na Madina. An neme su da su yi mubaya'a ga Yazidu sai Abdullahi xan Zubairu ya ce: zan yi nazari cikin daren nan bayan nan zan ba ku labari game da ra'ayi na. Sai su ka ce: ya yi. Cikin dare sai ya fice daga Madina ya tafi Makka ba tare da ya yi mubaya'a ba.
Yayin da aka zo da Husaini aka ce da shi: ka yi mubaya'a sai ya ce: ni ba zan yi mubaya'a a sirrance ba, sai dai ni zan yi mubaya'a ne a gaban jama'a. sai su ka ce: hakan ya yi. Yayin da dare ya yi sai ya fita ya bi bayan Abdullahi xan Zubairu. WASIQUN MUTANEN KUFA ZUWA GA SAYYIDINA HUSAINI
Labari ya isa ga mutanen Iraqi cewa Husaini bai yi mubaya'a ga Yazidu xan Mu'awiya ba, dama kuma su ba su son Yazidu haka nan Mu'awiya, su ba wanda su ke so sai Aliyu da 'ya'yansa – Allah Ya qara yarda a gare su - sai su ka riqa aikawa da wasiqu zuwa ga Husaini xan Aliyu dukkaninsu su na cewa – acikin wasiqun nasu- lallai mu mun yi ma ka mubaya'a kuma mu babu wanda mu ke so sai kai. kuma babu bai'ar Yazidu a wuyoyinmu, mu bai'armu ta ka ce. Wasiqu su ka yawaita ga Husaini har sai da yawansu ya kai sama da wasiqu xari biyar dukkanin su daga mutanen Kufa su na kiran sa da cewa ya taho gare su.
HUSAINI YA AIKA MUSLIMU XAN AQILU
Daga nan ne Husaini xan Aliyu – Allah Ya qara masa yard - ya aika xan baffansa Muslim xan Aqilu xan Abu Xalib domin ya bi sawun al'amuran a can Kufa kuma ya tabbatar da haqiqanin gaskiyarsu. Yayin da Muslim xan Aqilu ya isa Kufa sai aka dinga tambayar sa – game da Husaini har sai da ya tabbatar da cewa lallai mutane ba su son Yazidu, kawai Husaini xa Aliyu su ke so. Sai ya sauka a gidan Hani' xan Urwa mutane na zuwa xaixaikunsu da tawagarsu su na masa mubaya'a a madadin Husaini xan Aliyu –Allah Ya qara musu yarda baki xaya.
A wannan lokacin sahabin Annabi Nu'manu xan Bashir shi ne gwamnan Yazidu a garin Kufa, yayin da labari ya iso gare shi game da cewa lallai fa Muslim xan Aqilu ya na nan a cikin gari mutane su na ta yi masa mubaya'a a madadin Husaini sai ya yi kamar bai ji komai ba kuma bai nuna damuwa ba game da al'amarin, har sai da wasu daga cikin waxanda ke tare da shi su ka fita zuwa wurin Yazidu a kasar Sham su ka labarta masa abin da ke gudana, su ka ce masa lallai mutane na nan su na ta yi wa Muslim xan Aqilu mubaya'a amma Nu'umanu xan Bashir bai xauki abin da muhimmanci ba.
NAXA UBAIDULLAHI BIN ZIYAD A MATSAYI SABON GWAMNAN KUFA.
Yazidu ya yi umarni da tuve Nu'umanu xan Bashir ya kuma aika Ubaidullahi xan Ziyad a matsayin sabon gwamna a Kufa, dama can shi ne gwamnan Basra sai aka haxa masa har da Kufa saboda ya magance wannan al'amarin. Sai Ubaidullahi xan Ziyad ya isa Kufa cikin dare alhali ya naxe fuskarsa a cikin rawani, ya kasance duk lokacin da ya wuce jama'a ya kan yi musu sallama sai su ce: amincin Allah ya tabbata a gare ka ya xan xiyar Manzon Allah, su na zaton cewa Husaini ne ya shigo gari avoye ya na mai vadda sawu cikin dare. Saboda haka sai Ubaidullahi xan Ziyad ya tabbatar da cewa al'amarin ba na wasa ba ne, kuma lallai mutane fa su na nan su na jiran Husaini xan Aliyu ne. daga nan sai ya shiga fadansa na gwamna sa'annan ya tura xaya daga cikin 'yantattun bayinsa mai suna Ma'aqilu don ya bibiyi al'amarin kuma ya gano wanda ke quqqulla shi.
Sai ya tafi ya na mai riya cewa shi wani mutum ne daga garin Himsu, kuma ya zo ne da dinari dubu uku domin taimaka wa Husaini – Allah Ya qara masa yarda – sai ya riqa tambaya har sai da aka nuna masa gidan Hani' xan Urwa, sai ya shiga ya taradda Muslimu xan Aqilu ya yi masa mubaya'a ya kuma ba shi wannan dinari dubu ukun, sa'annan ya dinga kaiwa da komowa na tsawon kwanaki har sai da ya fahimci abin da ke tare da su sa'annan ya koma wurin Ubaidullahi xan Ziyad ya kwashe labarin duk ya ba shi.
FITAN HUSAINI DON TAFIYA GARIN KUFA
Bayan al'amura sun kankama, kuma mutane masu yawa sun yi wa Muslim xan Aqilu mubaya'a sai ya aika wa Husaini ya na mai umurtan shi da ya gabato zuwa Kufa komai ya daidaita.
Sai Husaini ya fito daga Makka ya kama hanyar Kufa a ranan tarwiyya – takwas ga watan zulhijja- dama shi Ubaidullahi ya riga ya san abin da Muslimu xan Aqilu ya aikata sai ya ce ku je ku taho min da Hani'i xan Urwa, sai aka zo da shi, sai ya ce da shi ina Muslimu xan Aqilu? Sai ya ce ban sani ba.
Nan take sai ya kira bawan nan na shi mai suna Ma'aqilu sai ya shiga ya same shi sai ya ce: shin ka san shi? Sai ya ce ee!! Nan take sai gwiwarsa ta yi sanyi ya tabbatar da cewa dama ashe al'amarin makirci ne daga Ubaidullahi xan Ziyad. Sai Ubaidullahi xan Ziyad ya ce masa: ina Muslimu xan Aqilu? Sai ya ce da shi: na rantse da Allah ko da aqarqashin dunduniyata ya ke b azan xaga tab a – wato ba zan faxa ma ka inda ya ke ba- saboda haka sai Ubaidullahi ya dake shi kuma ya sa aka tsare shi.
MUTANEN KUFA SUN TAVAR DA MUSLIMU XAN AQILU
Labari ya isa zuwa ga Muslimu xan Aqilu sai ya fito da runduna ta mayaqa dubu huxu ya yi wa fadar gwamna Ubaidullahi qawanya mutanen Kufa ma duk sun fito tare da shi. A wannan lokacin kuwa manyan gari suna nan a wurin Ubaidullahi xan Ziyad sai ya ce da su; ku watsa mutane daga Muslim xan Aqilu. Ya yi musu alqawurra ya kuma razana su da rundunar Sham, kan ka ce kwabo kawai sai ga shugabanni sun kama watsa mutane daga bin Muslimu xan Aqilu.
Ba'a gushe ba wannar matar ta zo ta ja xanta, wannan mutumin ya zo ya ja xan uwansa, wannan jagoran ya zo ya gargaxi jama'arsa har sai da duk mutane su ka waste masa bawanda ya saura tare da shi face mutane talatin cikin dubu huxu! Kai rana bat a faxi ba ma face babu wanda ya saura tare da Muslimu xan Aqilu, duk mutane sun tafi sun bar shi shi kaxai ya na yawo a hanyoyin Kufa bai ko san inda zai je ba.
Sai ya qawanqwasa qofar wata mata 'yar qasar Kinda sai ya ce da ita ina butar ruwan sha.
Sai ta yi mamakin sa sa'annan ta ce masa: kai kuma wanene? Sai ya ce ni ne Muslimu xan Aqilu ya kuma kwashe labarinsa duk ya bata na yaudarar da mutane su ka yi masa, da kuma cewa ga Husaini na nan tafe domin ya riga ya aika masa cewa ya taho.
Sai ta shigar da shi gidan maqwabta ta kawo masa ruwa da abinci sai dai xanta ya kai wa Ubaidullahi xan Ziyad gulman inda Muslimu xan Aqilu ya ke.
Sai ya aika masa mutum saba'in su ka je su ka kewaye shi, sai ya yaqe su, amma aqarshe ya sallama musu yayin da su ka masa alqawarin cewa zasu amintar da shi.
Sai aka xauke shi zuwa fadar gwamna inda Ubaidullahi xan Ziyad ya ke, yayin da ya shiga sai Ubaidullahi ya tambaye shi game da sababin waxannan yaqe-yaqen na sa, sai ya ce bai'a ce a wuyoyinmu ga Husaini xan Aliyu. Sai ya ce a she ba bai'ar yazidu ba ce a wuyarka?
Sai ya ce masa lallai ni zan kashe ka. Sai ya ce masa; bar in yi wasiyya. Sai ya ce: an bar ka yi wasiyyar. Sai ya waiwaya sai ya ga Umar xan Sa'ad xan Abi waqqas, sai ya ce da shi: kai ka fi kusanci da ni a dangantaka, taho in yi ma wasiyya. Sai ya ja shi zuwa gefe a cikin gida sa'annan ya yi masa wasiyya da cewa ya tura xan aike zuwa ga Husaini ya ce da shi ya koma. Sai Umar xan Sa'ad ya aika wani mutum zuwa wurin Husaini domin ya ba shi labarin yadda al'amarin ya kaya, ya kuma sanar da shi cewa lallai fa mutanen Kufa sun ha'ince shi. Muslim ya faxi wannan mashahurin zancen na sa:
Ya na mai cewa: ka koma da iyalanka, ka da ka ruxu da mutanen Kufa, domin haqiqa mutanen Kufa sun yi ma ka qarya kuma ni ma su yi min qarya, shi ko maqaryci dama ba shi da ra'ayin kansa.
Daga nan sai aka kashe Muslimu xan Aqilu a ranar Arfa alhali Husaini ya riga ya fito daga Makka a ranat tarwiyya gabanin kashe Muslimu xan Aqilu da yini xaya.
QOQARIN SAHABBAI NA GANIN SUN HANA HUSAINI FITA ZUWA KUFA.
Haqiqa da yawa daga cikin sahabbai sun yi qoqarin hana Husaini xa Aliyu fita zuwa Kufa. Sune:
Abdullahi xan Umar, Abdullahi xan Abbas, Abdullahi xan Amru xan Aass, Abu Sa'idin Alkhudri da Abdullahi xan Zubairu, da xan uwansa Muhammad ibnul Hanafiyya, duk waxannan yayin da su ka samu labarin cewa Husaini ya na shirin fita zuwa Kufa sun hana shi, ga maganganunsu nan:
Abdullahi xan Abbas ya ce wa Husaini yayin da ya ke shirin fita zuwa Kufa: ba don ka da mutane su aibanta ni su aibanta ka ba, da na qanqame kanka da hannayena ban bar ka ka tafi ba. (duba Albidaya wannihaya na ibnu Kathir 8\ 161)
Abdullahi xan Umar: Imamu Assha'abi ya ce; Xan Umar ya kasance a garin Makka sai labari ya iske shi cewa Husaini ya kama hanyar Iraqi, sai ya riske shi a hanya bayan ya yi tafiyar dare uku sa'annan ya ce masa: ina ka nufa?
Sai ya ce da shi Iraqi, kuma ya fitar masa da wasiqun da mutanen Iraqi su ka turo masa su na sanar da shi cewa su na tare da shi, ya ce waxannan duk wasiqunsu ne da bai'arsu. Sai Xan Umar ya ce masa ka da ka je wurinsu, sai Husaini ya nace sai ya tafi.
Sai Xan Umar ya ce masa: lallai ni zan ba ka wani hadisi, haqiqa Jibrilu ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya ba shi zavi tsakanin duniya da lahira, sai ya zavi lahira, bai zavi duniya ba. kai kuma wata tsoka ce daga jikinsa, na rantse da Allah babu wanda zai same ta daga cikinku har abada. Kuma Allah bai kautar da ita daga barin ku ba face saboda abin da shi ne mafi alheri gare ku. Sai ya qi ya koma. Sai Xan Umar ya rungume shi ya na ta rusa kuka. Sa'annan ya ce: ina ba wa Allah ajiyan ka, kai mutum ne da ke fuskantar barazanar kisa. (duba Albidaya wannihaya 8\ 162)
Abdullahi xan Zubairu ya ce wa Husaini: ina za ka? Yanzu za ka tafi zuwa ga mutanen da su ka kashe babanka su ka soki yayanka? Kul ka je wurin su. Sai Husaini ya nace cewa lallai sai ya tafi. (duba Albidaya wannihaya 8\ 163)
Abu Sa'idin Alkhudri –Allah Ya qara masa yarda – ya ce: ya kai baban Abdullahi (ya na nufin Husaini) lallai mai nasiha ce gare ka kuma mai tausaya mu ku, haqiqa labari ya riske ni cewa jama'arku daga Kufa sun rubuto mu ku wasiqu su na gayyatar ku zuwa gare su, to ka ka tafi wurin su, domin ni na ji babanka a Kufa ya na cewa: haqiqa sun ishe ni kuma na tsane su, suma sun qosa da ni kuma sun tsane ni. Ba za su tava cika alqawari ba. duk wanda ya ribata da su ya ribaci tavavviyar kibiya. Na rantse da Allah ba su da niyyar arziqi kuma ba su da himma akan komai kuma ba su iya haquri da takwabi. (duba Albidaya wannihaya 8\ 163)
Daga cikin waxanda su ka ba Husaini shawarar rashin fita zuwa Kufa koma bayan sahabbai akwai Alfarazdaq mawaqin nan, domin bayan fitar Husaini ya haxu da Alfarazdaq sai ya ce masa: daga ina?! Sai ya ce: daga Iraqi, sai ya ce masa: ya mutanen Iraqi? Sai ya ce: zukatansu na tare da kai amma takubbansu na tare da banu umayya. Sai ya dai nace akan sai ya fita, kuma ya ce Allah abin neman taimako. (duba Albidaya wannihaya 8\ 168)
HUSAINI YA ISO QADISIYYA
Saqon Muslimu xan Aqilu ya iso ga Husaini ta hanyar xan saqon da Umar xan Sa'ad ya turo, sai Husaini ya yi niyyar komawa, sai ya shawarci 'ya'yan Muslimu xan Aqilu sai su ka ce: sam! Wallahi ba za mu koma ba har sai mun xau fansar babanmu. Sai ya xauru akan ra'ayinsu.
Bayan Ubaidullahi xan Ziyad ya tabbatar da fitowar Husaini sai ya umarci Alhurru xan Yazidu At-tamimi da cewa ya ja gaba da runduna ta mutum dubu xaya domin su haxu da Husaini a hanya, sai ya haxu da Husaini a kusa da Qadisiyya.
Sai Alhurru ya ce da shi: zuwa ina ya xan 'yar Manzon Allah? Sai ya ce; zuwa Iraqi.
Sai ya ce: lallai ni ina umurtanka da komawa ka da Allah Ya jarrabe ni da kai, koma ta inda ka fito, ko kuma ka tafi Sham can wurin Yazidu ka da ka tafi zuwa Kufa.
Sai Husaini ya qi hakan sannan ya ci gaba da tafiya ta vangaren Iraqi, shi ma Alhurru xan yazidu ya dinga qoqarin shan kanshi ya na hana shi, sai Husaini ya ce masa, kauce ka ba ni wuri xan wabi!
Sai Alhurru xan Yazidu ya ce: na rantse da Allah da wani ne ya faxi wannan daga cikin larabawa ba kai ba da na xau mataki akan sa da uwarsa. Sai dai me zan iya cewa! Bayan mahaifiyarka ita ce shugaban matan duniya?!
ISOWAR HUSAINI KARBALA KISAN HUSAINI –ALLAH YA YA QARA MASA YARDA
Husaini ya tsaya a wani wuri da ake cewa da shi ((Karbala)) sai ya tambaya; me ne wannan? Sai su ka ce masa: Karbala, sai ya ce: karbu wa bala'un. Ma'ana baqin ciki da jarrabawa.
Yayin da rundunar Umar xan Sa'ad- wacce adadinta ya kai dubu huxu – ta iso, sai ya yi magana da Husaini cewa ya taho tare da shi su tafi Iraqi wurin Ubaidullahi xan Ziyad, sai ya qi.
Amma yayin da ya ga lallai al'amarin da gaske su ke yin sa sai ce wa Umar xan Sa'ad: zan ba ka zavin xayan abubuwa uku, ka zavi wanda ka so daga cikin su.
Sai ya ce: menene su? Sai ya ce; ka bar ni in koma, ko in tafi wata kafa daga cikin kafafen musulmai, ko in tafi wurin Yazidu har sai na aza hanuna akan hanunsa na yi masa mubaya'a a Sham.
Sai Umar xan Sa'ad ya ce: eh! Na yarda kai ka aika zuwa wurin Yazidu ni kuma in aika zuwa wurin Ubaidullahi xan Ziyad sai mu jiya mu gani shin ya ya al'amarin zai kasance? Sai shi Husaini bai aika wurin Yazidu ba, shi kuma Umar xan Sa'ad sai ya aika zuwa ga Ubaidullahi xan Yazidu. Yayin da xan saqon ya isa wurin Ubaidullahi xan Ziyad ya ba shi labarin abin da ke faruwa na cewa Husaini ya na cewa: ina ba ku zavi tsakanin waxannan abubuwan guda uku, sai Ubaidullahi xan Ziyad ya amince Husaini ya zavi duk wanda ya so daga cikin su.
Awannan lokacin tare da Ubaidullahi xan Ziyad akwai wani mutum da ake cewa Shamru ibnu Dhijaushan ya kasance ya na daga na hanun daman Ubaidullahi xan Ziyad, sai ya ce: wallahi ba zai yiwu ba, har sai ya xoru akan hukuncinka. Sai Ubaidullahi ya ruxu da maganrsa ya kuma ce haka ne, har sai ya xoru akan hukuncina.
Sai Ubaidullahi xan Ziyad ya aika Shamru xan Dhijaushan kuma ya ce masa: ka tafi har ya yarda da hukuncina, idan Umar xan Sa'ad ya yarda da hakan shi ken an, idan kuma bah aka ba, to kai ne shugaban rundunar amaimakon shi.
Dama Ubaidullahi ya shirya wa Umar xan Sa'ad runduna ta mutum dubu haxu da zai tafi da su zuwa garin Rayyu, sai ya ce masa ka fara magance matsalar Husaini sannan sai ka wuce Rayyu, dama ya yi masa alqawain jagorancin garin na Rayyu.
Sai Shamru xan Zijaushan ya fita ya kama hanya har ya isa wurin Husaini ya na mai tabbatar masa da cewa babu makawa sai ya xoru akan hukunci Ubaidullahi xan Ziyad shi ko Husaini sai ya qi yarda da hakan kuma ya ce: sam! na rantse da Allah ba zan hau kan hukuncin Ubaidullahi xan Ziyad ba.
HUSAINI YA NA TUNATAR DA RUNDUNAR KUFA ALLAH
Adadin waxanda su ke tare da Husaini mahaya ne su saba'in, rundunar Kufa kuma su dubu biyar ne. yayin da vangarorin guda biyu su ka ja daga sai Husaini ya ce da rundunar Ubaidullahi xan Ziyad: ku yi wa kanku qiyqqmullaili ku yi tunani da kyaw, yanzu zai yi mu ku kyau a ce kun yaqi iri na? alhali ni ne xan 'yar Annabinku? kuma babu wani wanda ya ke xan 'yar annabi a doron qasa yau koma baya na? kuma Manzon Allah –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya faxa game da ni da xan uwana: "waxannan biyun shugabanni ne na samarin gidan aljanna"
Sai Husaini ya ci gaba da kwaxaitar da su akan barin umurnin Ubaidullahi xan Ziyad ya na kiran su zuwa ga shi cikin eundunarshi. Sai mutum talatin su ka dawo vangarenshi cikin su har da Alhurru binu Yazid At-tamimi, wanda da shi ne jagoran 'yan gaba na rundunar Ubaidullahi xan Ziyad. Sai aka ce Alhurru binu yazid: ka zo nan tare da mu kana jagorantar 'yan gaba daga rundunarmu amma yanzu za ka koma wurin Husaini?!
Sai ya ka da baki ya ce: kaicon ku! Wallahi ni ina ba wa kai na zavi ne tsakanin Aljanna da Wuta, na rantse da Allah b azan zavi wanin Aljanna ba ko da za a gutst-gutsu da ni kuma a qone ni.
Bayan nan sai Husaini ya yi sallar azahar da la'asar a ranar alhamis, shi ya yi wa rundunonin guda biyu duka limanci, rundunar Ubaidullahi xan Ziyad da waxanda su ke tare da shi, saboda da ya ce mu su: ku da limaminku muma da limaminmu. Sai su ka ce: A'a! za mu yi sallah a bayanka. Sai su ka yi sallar azahar da la'asar a bayan Husaini. Yayin da magariba ta qarato sai su ka hau dawakansu su ka nufo Husaini, shi ko Husaini ya na nan sakaye da kansakalinsa yayin da ya gansu bayan ya xan runtsa kaxan sai ya ce: menene haka kuma? Sai mutanensa su ka ce: sun dai gabato kam. Sai ya ce: ku je ku magantu da su ku ce mu su: me ku ke so ne?
Sai mahaya ashirin su ka tafi cikin su har da Al'abbas xan Aliyu xan Abu Xalib xan Uwan Husaini, sai su ka yi magana da su su ka tambaye su abin da su ke so. Sai su ka ce: ko dai ya yarda da hukuncin Ubaidullahi xan Ziyad ko kuma ya yi yaqi.
Sai su ka ce: bari mu ba wa Abu Abdillahi labari, sai su ka dawo wurin Husaini –Allah Ya qara masa yarda - su ka ba shi labari. Sai ya ce: ku ce mu su: su xan saurara ma na wannan daren, gobe za mu ba su labari, sai na yi wa Ubangijina salla, domin ni na kan so in yi wa Ubangijina salla mai yawan albarka maxaukaki.
Saboda haka sai ya kwana a wannnan daren nasa ya na yi wa Ubangijinsa salla ya na neman gafara ya na ta addu'a shi da waxanda ke tare da shi Allah Ya qara ma su yarda baki xayan su.
YAQIN XIFF A SHEKARA TA 61 BAYAN HIJIRA.
A safiyar ranar juma'a yaqi ya varke tsakanin vangarorin biyu, yayin da Husaini ya qi amincewa ya sallama kanshi ga Ubaidullahi xan Ziyad a matsayin kamammen yaqi, ga shi vangarorin biyu ba daidai su ke ba a adadi da tanadi, yayin da mutanen Husaini su ka tabbatar da cewa ba za su iya da wannan rundunar ba, sai burinsu guda xaya ya zama kawai na su mutu a gaban Husaini xan Aliyu –Allah Ya qara mu su yarda- sai su ka wayi gari su na ta mutuwa a gaban Husaini xaya bayan xaya har sai da su ka qare gaba xaya babu wanda ya saura sai Husaini xan Aliyu–Allah Ya qara mu su yarda da xansa Aliyu xan Husaini wanda dama ya kasance mara lafiya.
Sai Husaini ya rage shi kaxai tsawon lokaci a cikin yini duk wanda ya kusanto shi sai ya koma don ya na tsoron ka da a jarrabe shi da kashe jikan Manzon Allah.
Haka nan dai al'amarin ya ci gaba da gudana har sai da Shamru bin Zijaushan ya iso, sai ya yi kuwwa a cikin mutane ya ce kaiconku! 'ya'yan wabi, ku yi masa qawanya ku kashe shi! Sai su ka taho su ka yi wa Husaini xan Aliyu qawanya. Sai ya dinga kutsawa tsakanin su da kansakali har sai da ya kashe wanda ya kashe daga cikin su tamkar wani zaki. Kash! Sai dai sarkin yawa ya fi sarkin qarfi.
Sai - matsiyacin nan – Shamru ya sake kuwwa ya ne mai cewa: me ku ke jira da shi? Ku nufe shi! Sai su ka nufi Husaini – Allah Ya qara masa yarda – su ka kashe shi. Wanda ya kashe Husaini daga cikin su kai tsaye shi ne Sinanu ibnu Anas An- nakha'i, kuma ya cire kansa – Allah Ya qara masa yarda- a wani qaulin kuma aka ce wanda ya kashe shi shi ne Shamru- Allah wadansu.
Bayan an kashe Husaini – Allah Ya qara masa yarda – sai aka xauki kansa aka kai wa Ubaidullahi a Kufa, sai ya riqa sa wata sanda da ke hanunsa a cikin bakinsa ya na tsokalawa ya na cewa: amma fa ba dai kyawun wushiya ba kam. Sai Anas xan Malik ya tashi ya ce: wallahi sai na munana ma ka! Haqiqa na ga Manzon Allah –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi – ya na sumbantan gurbin sandan nan na ka a bakinsa. (Duba Almu'ujamul kabir na Xabarani hadisi mai lamba ta 5107)
Ibrahim An-nkha'i ya ce: "Da na kasance cikin waxanda su ka kashe Husaini sannan aka shigar da ni aljanna sai na ji kunyar wucewa ta inda Annabi – tsira da amincin Allah – ya ke ya kalli fuskata. Duba Almu'ujamul kabir hadisi mai lamba ta 2829 kuma isnadinsa ingantacce ne)
WAXANDA AKA KASHE SU TARE DA HUSAINI DAGA IYALAN GIDANSA.
Daga cikin 'ya'yan sayyidina Aliyu xan Abu Xalib an kashe: shi kan shi Husaini, da Ja'afar, da Abbas, da Abubakar, da Muhammad da Usmanu.
Daga cikin 'ya'yan sayyidina Husaini kuma an kashe: Abdullahi, da Aliyu babba. Ban da Aliyu Zainul Abidina.
Daga cikin 'ya'yan sayyidina Alhasan kuma an kashe: Abdullahi da Qasimu da Abubakar.
Daga cikin 'ya'yan Aqilu kuma an kashe: Ja'afar da Abdullahi da Abdurrahman da Abdullahi xan Muslim xan Aqilu, da Muslimu xan Aqilu wanda dama an riga an kashe shi a Kufa.
Daga cikin 'ya'yan Abdullahi xan Ja'afar kuma an kashe: Aunu da Muhammad. (Duba littafin tarihi na Khalifah ibnu Khayyax shafi na 234)
An kashe mutum goma sha takwas dukkaninsu daga ahlu baitin Manzon Allah – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi – a cikin wannan yaqin.
HASASHE GAME DA KISAN HUSAINI – ALLAH YA QARA MASA YARDA.
Daga Ummu Salama – Allah Ya qara ma ta yarda – ta ce: "mala'ika Jibrilu ya ksance a wurin Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- alhali Husaini na tare da ni sai ya yi kuka, sai na sake shi ya shiga wurin Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- sai ya kusanci Annabi– tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- sai Jibrilu ya ce: ka na qaunar shi? Sai Annabi ya ce: eh! Sai Jibrilu ya ce: al'ummarka za ta kashe shi. Ina ka so ma sai in nuna ma ka turvayar kasar da za a kashe shi a kanta. Sai ya nuna masa ita sai ga ta ana ce da ita Karbala" (Duba fada'ilus-sahaba hadisi mai lamba ta 1391) hadisi ne shahararre sai dai mai rauni ne ta dukkanin hanyoyinsa daga Ummu Salama.
Har wa yau ya zo daga Ummu Salama – Allah Ya qara mata yarda – ta ce: na ji aljanu su na yi wa Husaini kuka yayin da aka kashe shi. (Duba fada'ilu As-sahaba hadisi mai lamba ta 1373 kuma isnadinshi mai kyau ne)
Amma abin da ake ruwaitowa na cewa sama ta riqa ruwan jinni, ko dukkanin katangu an shafe su da jinni, ko babu wani dutsen da za a xaga face an tarar qarqashi sa jinni ne, ko ba a yanka wani raqumi ba face dukkaninsa ya zama jinni. Duk wannan qarairayi ne da soki burutsu, ba su da wani sanadi ingantacce zuwa ga Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi – ko kuma wani daga cikin waxanda su ke raye lokacin faruwan abin. Duk kawai zuqi tamalle ne ake shararawa domin tayar da hankula, ko kuma riwayoyi masu tsinkakkun isanadai daga waxanda ba su yi zamani ba da faruwan al'amarin. (Duba Albidaya wannihaya abubuwan da su ka faru a shekara ta 61 bayan hijira)
Daga Abdullahi xan Abbas – Allah Ya qara mu su yarda – ya ce: na ga Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi – a cikin mafarki gashinsa amummurxa duk ya yi qura da tsakar rana, ya na riqe da wata kwalba cikin ta akwai jinni da ya ke bi ya na tsittsinta, sai na ce da shi: ya ma'aikin Allah menene wannan? Sai ya ce: " jinin Husaini ne da abokansa ban gushe ba ina ta bibiyansu tsawon yinin.
Ammar maruwaicin hadisin ya ce: da mu ka kiyaye ranan sai mu ka tarar cewa ranan aka kashe shi. (Duba fada'ilu As-sahaba hadisi mai lamba ta 1380 kuma isnadinsa ingantacce ne)
Kuma annabi ya na cewa: "Duk wanda ya ganni a cikin bacci to haqiqa ni ya gani" Bukhari da Muslim ne su ka ruwaito shi. Kuma Abdullahi xan Abbas ya na cikin waxanda su ka fi kowa sanin Annabi– tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
AZABAR DUNIYA KAFIN NA LAHIRA
Wanda ya yi umarni da kashe Husaini shi ne Ubaidullahi xan Ziyad sai dai fa shi ma ba tare da wani jimawa ba aka kashe shi, wanda ya kashe shi shi ne Mukhtar Ibnu Abi Ubaidi, ya kashe shi ne don xaukar fansar jinin Husaini tare da cewa shi dai Mukhtar xin nan ya daga cikin waxanda su ka tavar da wakilin Husaini Muslim xan Aqilu su na ji su na gani aka kashe shi ba su tavuka komai ba.
Saboda haka su mutanen Kufa sai su ka zamo su na son su yi wa kan su hukunci saboda abin da su ka yi tun farko na qin taika wa Muslimu xan Aqilu har aka kashe shi ba wanda ya motsa daga cikinsu. Na biyu kuma shi ne lokacin da Husaini ya fito babu wanda ya taimake shi daga cikin su sai dai Alhurru Ibnu Yazid At-tamimi da waxanda su ke tare da shi. Amma mutanen Kufa kam sun tavar da shi ne, suma Allah Ya tavar da su.
Shi ya sa ka ke ganin su su na dukan qirazansu su na aikata abin da su ke aikatawa na hargowa don su kankare laifin da iyayensu su ka yi na kashe Husaini kamar yadda su ke riyawa. Shi ya sa rundunar Mukhtar wacce ta xauki fansa ga Husaini ta kira kanta da suna (rundunar tubabbu) saboda tabbatar wa kansu da abin da su ka yi na qasa a gwiwa wurin kare Husaini. Wannan shi ne farkon bayyanar shi'anci a matsayin mazhaba ta siyasa. Amma bayyanr shi'anci a matsayin mazhaba ta aqida da fiqihu kam ya zo ne daga baya qwarai bayan gushewar daular bani umayya da jimawa.
Daga Umaratu xan Umair ya ce: lokacin da aka zo da kan Ubaidullahi xan Ziyad da abokansa sai aka tara su a cikin masallaci a haraba, ya ce: sai na isa wurin su sai na ji su su na cewa: ta iso! ta iso! Sai ga shi nana she wata macijiya ce ta zo ta na ta kutsawa tsakankanin kawuka har sai da ta shiga qofar hancin Ubaidullahi xan Ziyad sai ta tsaya a ciki na wani lokaci, sannan sai ta fito ta yi tafiyar ta har aka daina ganin ta, sannan su ka sake cewa: ta iso! ta iso! Sai ta qara shiga hancinsa, haka nan ta maimaita har sau biyu ko sau uku. (Duba sunanu At-trimidhiy kuma Imamu At-tirmidhi ya ce hadisi na mai kyau ingantacce.
Wannan xaukar fansa ce ramukon gayya daga Allah maxaukakin sarki akan wannan mutumin da ya yi ruwa ya yi tsaki cikin kisan Husaini xan Aliyu –Allah maxaukakin sarki Ya qara masa yarda.
Daga Abu Raja Al'uxaridi ya ce: ka da ku zagi Aliyu, haka nan ma wani daga wannan gidan domin wani maqwabcinmu daga wata qabila daga qabilun larabawa da ake kira Balhajim ya ce: shin ba ku yi dubi ba ne zuwa ga wannan fasiqin, ya na nufin Husaini xan Aliyu. Sai Allah Ya jefa masa hakiya a cikin idanunsa Ya kuma makantar da shi. (Duba Almu'ujamul kabir hadisi mai lamba ta 2830 kuma isanadinsa ingantacce ne)
WAXANDA KE DA ALHAKKIN KISAN JIKAN MANZON ALLAH
Kafin mu kai ga ambaton waxanda ke da alhakkin kisan Sayyidina Husaini –Allah Ya qara masa yarda- bari mu xan waiwaya baya kaxan mu tuno yadda Aliyu da Husaini su ka qare da 'yan shi'ansu.
Daga Aliyu –Allah Ya qara masa yarda – ya na kokawa game da masu jingina kansu da shi wato 'yan shi'a mutanen Kufa: ya na cewa: haqiqa al'ummu sun wayi gari su na tsoron zaluncin shugabanninsu, ni kuma na wayi gari ina tsoron zaluncin talakawana. Na umarce ku da fita jihadi amma kun qi fita, na jiyar da ku maganganu amma kun yi kunnen uwar shegu, na kira ku afili da voye amma kun qi ku amsa, na yi mu ku nasiha amma kun qi ku karvi nasihata, mutane ga su nan a halarce amma kamar ba su nan?! Bayi ne amma sun zama tamkar iyayen giji?! Ina karanta mu ku hukunci ku na guje masa?! Ina mu ku wa'azi da gargaxi mai shiga jiki amma sai ku watsewa daga barinsa?!
Ina kwaxaitar da ku akan yaqan 'yan tawaye amma kafin in kai qarshen magana ta kun waste kowa ya kama gabansa?! Sai ku komo majalissunku ku na ha'intar juna game da wa'azuzzukanku?! Ina daidaita ku da safiya amma kafin maraice kun koma karkatattu kamar bayan maciji?! Mai daidaitawa ya gajiya, wanda ake daidaitawa ya wahalar! Ya ku waxanda su ke halarce da gangan jikinsu amma hankulansu ba su nan! Waxanda soye- soyen zukatansu ya sassava! Waxanda aka jarrabi shugabanninsu da su! Abokinku ya na bin Allah amma ku ku na sava masa. Wallahi na yi burin da ace Mu'awiya ya min canjin ku da mabiyanshi kamar yadda ake canjin zinari da azurfa, ya kwashi mutane goma daga wurina ya ba ni mutum xaya daga cikin su.
Ya ku mutanen Kufa! Na sheda abu uku da wasu guda biyu daga gare ku; kurame ne masu ji, bebaye ne masu magana, makafi ne masu gani. Su ba 'ya'ya na gaskiya ba yayin karo da abokan gaba, haka kuma ba 'yan uwa yardaddu ba a lokacin jarrabawa! Talauci ya lazimce ku ya ku masu kama da rakuman da makiyayinsu ya yi nesa da su, duk lokacin da aka tattara su ta wani gefen sai su sake watsewa tawani vangaren. (Nahajul balagha)
Al'amarin na mutanen Kufa bai tsaya anan ba kawai ba, a'a! sai da su ka tuhume shi da qarya. Sharifu Ar-rida ya ruwaito daga Amirul muminin Aliyu xan Abu Xalib – Allah Ya qara masa yarda – lallai ya ce: "bayan haka: y ku mutanen Iraqi, abin sani kawai ku dai tamkar wata mace ce mai ciki bayan ta samu cikin ya cika kwanakinsa nononta ya cicciko, sai tsayayyenta ya mutu, zawarcinta ya tsawaita kuma wani bare na nesa ya zo ya gaje ta. Wallahi ban taho wurinku don ina so ba, sai dai kawai na taho wurinku ne ana kora ni. Labari ya riske ni kuna cewa Aliyu ya na qarya, Allah Ya tsine mu ku! Wa zan yi wa qarya? (Nahjul balagha)
Alhasan xan Aliyu Allah Ya qara masa yarda Ya ce: ina ganin fa wallahi Mu'awiya ya fi min alheri sama da waxannan, su na riya cewa wai su 'yan shi'a ta ce, amma sun nemi su kashe ni, kuma su ka yi min qwacen kayana, su ka qwace min dukiyata, na rantse da Allah idan Mu'awiya ya xaukan min alqawarin abin da zan kare jinnina da shi in kuma aminta da shi a cikin iyalaina shi ya fi min alheri madadin su kashe ni, iyalaina su walaqanta. Kuma da zan yi yaqi da Mu'awiya da sun cukumi wuya ta sun danqa nig are shi cikin ruwan sanyi.
Har wa yau dai ya sake cewa ga 'yan shi'anshi: ya ku mutanen Iraqi! Rayuwa ta ta qyamace ku saboda abu uku; kisan da ku ka yi wa mahaifina, suka ta da ku ka yi, da qwace dukiyata da ku ka yi. (Duba littafi mai suna Laqad shayya'ani Alhusain wallafar Idris Alhusaini Almaghribi shafi na 283)
YAWDARAR NUTANEN KUFA DA KASANCEWAR SU NE MA KASA HUSAINI.
Haqiqa Muhammadu xan Aliyu xan Abu Xalib wanda aka fi sani da Ibnul Hanafiyya ya yi wa xan uwansa Husaini nasiha ya na mai cewa: ya xan uwa na, lallai mutanen Kufa ka san yaudararsu ga mahaifinka, da xan uwanka. Haqiqa ina gudun ka da kai ma su yi ma ka yadda su ka yi wa waxanda su ka gabace ka. (Duba Alluhufu na ibnu Xawus shafi na 39, da Ashura na Ihsa'i shafi na 115, da Almajalisul fakhira na Abdul Husain shafi na 75, …)
Mawaqin nan Alfarzdaq ya ce wa Husaini yayin da ya tambaye shi game da 'yan shi'ansa waxanda ya ke shirin tafiya gare su: zukatansu na tare da kai amma takubbansu na kanka, al'amari dai daga sama ya ke sauka, kuma Allah Ya na aikata abin da Ya so.
Sai sayyidina Husaini ya ce: ka yi gaskiya, al'amari kam na Allah ne, kuma kullum cikin sha'ani Ya ke, idan qaddara ta sauko da abin da mu ke so mu ke yarda da shi to sai mu yi godiya ga Allah akan ni'imominSa, kuma gare Shi ake neman taimako don godiya gare Shi. Idan kuma qaddara ta kange mu daga isa ga buqata, to wanda dai gaskiya ta kasance ita ce manufar shi kuma sirrinsa tsoron Allah ai bai yi hasara ba.
Haka nan ma lokacin da Husaini ya yi magana da su ya yi nuni zuwa ga aikinsu da ya gabata da irin abin da su ka yi wa mahaifinsa da xan uwansa: ya ce: idan ku ka qi kuma ku ka warware alqawarinku ku ka tuve bai'ata daga wuyoyinku, lallai ina rantsuwa wannan ba abin mamaki ba ne game da ku, haqiqa kun aikata hakan ga babana da xan uwana da xan baffana Muslimu xan Aqilu, ruxaxxe shi ne wanda ya ruxu da ku. (Duba ma'alimul madarasataini 3\71-72, da ma'alil basxin 1\275, bahrul ulum 194, nafsul mahmum 172, khairul as hab 39 da nazmuzzahra' shafi na 170)
Aliyu xan Husaini wanda aka fi sani da Zainul Abidin: ya ce wa 'yan shi'ansa waxanda su ka tavar da mahaifinsa su ka kuma kashe shi: ya na mai munana mu su: Ya ku mutane! Ina haxa ku da Allah kun san cewa kun rubuta wasiqu zuwa ga mahaifina ku ka yaudare shi? Kuma ku ka yi mishi alqawari mai qarfi ku ka yi ma sa mubaya'a amma kuma ku ka yaqe shi ku ka tavar da shi? Kun halaka saboda abin da ku ka gabatar ga kawukanku, da mummunan ra'ayinku, da wani idon za ku kalli Manzon Allah ya yin da zai ce da ku: kun kashe zurriyyata, kun keta alfarmata saboda haka ku ba ku daga al'ummata. Sai muryoyin mata ya xaukaka ta ko wane kusurwa saboda kuka sashin su na ce wa sashi: kun halaka ba ku sani ba.
Sai ya ce: Allah Ya jiqan wanda ya karvi nasihata, ya kiyaye wasiyyata game da Allah da ManzonSa da iyalan gidan Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi – haqiqa abin koyi na qwarai ya tabbata gare mu daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Gabaki xayan su sai su ka ce: dukkaninmu mu na ji kuma mu na biyayya, kuma za mu kiyaye ragamarka ba za mu qi ka ba, kuma ba za mu qaurace ma ka ba, umarninka mu ke jira – Allah Ya yi ma ka rahama – domin lallai mu masu yaqan mai yaqan ka ne, masu amincin da wanda ka ba wa aminci, za mu damqi Yazidu kuma za mu barranta daga wanda ya zalunce ka ya zalunce mu.
Nan take sai ya ce: fau- fau- fau! Mayaudara makirai! An kange ku tsakanin ku da soye soyen ranku, ku na nufin za ku taho gare ni ne kamar yadda ku ka je ga iyayena? Qarya ku ke! Ina rantsuwa da Allah. Raunin da ku ka yi ma na bai ko warke ba tukunna. Jijiyan nan aka kashe mahaifina ya na tare da iyalan gidansa,…. Axxabarasi ya ambaci wannan khuxubar a cikin Al'ihtijaju da ibnu Xawus a cikin malhuf shafi na 92 da Al'amin a cikin lawa'ijul ashjan shafi na 158, da Abbasul Qummi a cikin muntahal amal juzu'i na farko shafi na 572, da Husaini Kurani a cikin Fi rahabi karbala shafi na 183, da Abdurrazzaq Almuqrim a cikin littafinsa mai suna maqtalul Husain shafi na 317, da Murtada iyad a cikin Maqtalul Husain shafi na 87, Abbasul Qummi ya sake maimaita ta a cikin nafsul mahmum shafi na 360 da Rida Alqazwini a cikin littafi mai suna Tazallumuzzahra shafi na 262.
Haka nan ma yayin da Zainul abiding ya wuce mutanen Kufa su na ta ihu da koke- koke sai ya yi mu su tsawa ya na mai cewa: kuna kuka kuna ihu saboda mu? To wa ya kashe mu? (Duba: Almalhuf shafi na 86 da Nafsul mahmum shafi na 357 da Maqtalul Husain shafi na Murtada Iyad shafi na 83 bugu na huxu 1996 da Tazallumuzzahra shafi na257).
Duba huxubar Ummul Kulthum yar sayyidina Aliyu –Allah Ya qara mu su yarda – a cikin littattafai kamar haka; Almalhuf shafi na 91, da Nafsul mahmum shafi na 363, da Maqtalul Husain na Almuqrim shafi na 316, da Lawa'ijul ashjan shafi na 157, da Maqtalul Husain na Murtada Iyad shafi na 86, da Tazallumuzzahra na Rida Alqazwini shafi na 261).
Zainab yar sayyidina Aliyu –Allah Ya qara mu su yarda- ta ce wa 'yan Kufa alhali ta na yi wa taron jama'ar da su ka tare da ihu da koke - koke magana: har za ku yi kuka kuna haushi? Eh! Wallahi kam ku yi kuka mai yawa ku yi dariya kaxan, haqiqa kun tafi da aibi da abin kunya, kuma ba za ku tava iya wanke kanku ba har abada, ya za a yi ku iya wankuwa daga kisan xan cikamakin annabawa. (Duba littafi mai suna Alhusain fi nahdatihi shafi na 295 da abin de biye.
A wata riwayar sai ta ce: ku rufe baki! ya ku mutanen Kufa! Mazajenku su kashe mu, sannan matanku su zo su na ma na kuka? Mai hukunci tsakaninmu da ku Shi ne Allah ranar raba gardama. Abbasul Qummi ya naqlce shi a cikin Nafsul mahmum shafi na 365, kuma Shekh Rida Alqazwini ya ambace shi a cikin Tazallumuzzahra shafi na 264.
Jawad muhaddithi ya na cewa game da mutanen Kufa: kuma haqiqa waxannan sabubban sun sanya Imam Aliyu ya sha wahala daga gare su, Imamu Alhasan kuma ya fuskanci yaudara, kuma aka kashe Muslim xan Aqilu a tsakanin su bisa zalunci, kuma aka kashe Husaini cikin qishi a Karbala kusa da Kufa a hanun sojojin Kufa. (Duba Mausu'atu Ashura shafi na 59)
Husaini Korani ya ce: mutanen Kufa al'amarinsu bai tsaya ga watsewa su bar Imamu Husaini ba, a'a! sun qaura daga nan sakamakon caccanzawar matakansu zuwa mataki na uku wanda shi ne kawai sai su ka fara gaggawar fita zuwa Karbala da yaqan Imamu Husaini –Amincin Allah ya tabbata a gare shi – a Karbala sai su ka riqa rige-rigen dawwana wata matsayar da ta ke yardarm da shexa kuma ta ke fusata Mai rahama. (Duba Fi rihabi Karbala 60-61)
Husaini Korani ya kuma cewa: kuma sai mu ka samu wata matsaya ta daban da ta ke nuna munafurcin 'yan Kufa, sai ka ga irin Abdullahi Ibnu Hauzata At-tamimi ya tsaya a gaban Imamu Husaini ya xaga murya ya na mai cewa: Husaini na cikin ku? Kuma wannan ya na cikin mutanen Kufa wanda a jiya – jiya ya na cikin shi'an Aliyu – Amincin Allah ya tabbata a gare shi – kuma abu ne mai yiwuwa ya kasance cikin waxanda su ka rubuta wa Husaini, sannan sai ga shi nan ya na cewa: ya Husaini: ina ma ka albishir da shiga wuta. (Duba Fi rihabi Karbala shafi na 61)
Murtada Muxahhari ya ce: babu kokwanto kan cewa Kufa 'yan shi'an Ali ne kuma cewa waxanda su ka kashe Imamu Husaini su ne 'yan shi'ansa. (Duba Almalhamtul husainiyya 1\129)
Har wa yau da ya ce: kuma mu gabanin yanzu mun tabbatar da cewa wannan qissar muhimmiya ce ta wannan fuskar kuma mu ka ce: kisan Hsaini ya kasance ne a hanun musulmi, kai ba ma haka kawai ba! a hanun 'yan shi'a bayan shekaru hamsin kawai da rasuwar Annabi, wanna abu ne mai rikitarwa qwarai da gaske kuma ya yi kama da almara mai ban mamaki mai jan hankali qwarai gaske. (Duba Almalhamtul husainiyya 3\93)
Wanda ya yi umarni da kashe Husaini kuma ya yi farin ciki da shi shi ne Ubaidullahi xan Ziyad. Wanda kuma ya kashe Husaini shi ne Shamru Ibnu Zijaushan da Sinanu ibnu Anas An-nkha'i. waxannan ukun dukkaninsu sun kasance cikin 'yan shi'an Aliyu kuma cikin rundunarsa a siffin.
Kazim Al'ihsa'i An-najafi ya ce: Lallai rundunar da ta fita don yaqan Imamu Alhusaini –amincin Allah ya tabbata gare shi – su dubu xadi uku ne, dukkanin su mutanen Kufa. Babu ko xaya daga cikinsu da ya zo daga Sham ko Hijaz ko Hindiya ko Fakistan ko Sudan ko Masar ko Afirka, a'a dukkanin su 'yan Kufa ne da su ka haxu daga qabilu mabambanta. (Duba littafin Ashura shafi na 89).
Husain Bin Ahmad Albaraqi An-najafi: Qazwinin ya ce: "ya na daga cikin abin da aka zargi mutanen Kufa da shi; shi ne sun soki Alhasan xan Aliyu – amincin Allah ya tabbata gare su – kuma sun kashe Husaini bayan sun gayyace shi" Duba Tarikhul Kufa sahfi na 113.
Muhsin Amin ya ce: " sa'annan mutum dubu ashirin daga mutanen Kufa su ka yi wa Husaini mubaya'a, su ka yaudare shi, kuma su ka masa tawaye alhali bai'arsa na rataye a wuyoyinsu, kuma su ka kashe shi" Duba A'ayanus-shi'a 1\126.
Wai wanene kai tsaye ya kashe Husaini? Mashahurin magana a cikin littattafan tarihi shi ne cewa wanda ya kashe Husaini kai tsaye shi ne Sinanu binu Anas An-nakha'i da Shamru binu Zijaushan. Wanda ya xauki nauyin shiraya kisan da umarni da shi kuma shi ne Ubaidullahi xan Ziyad. Da Ubaidullahi xin nan da Shamru kuwa dukkanin su sun kasance a cikin 'yan shi'ar Aliyu kamar yadda Axxusi ya ambata a cikin littafinsa na tarihin mazaje ya qirga Ubaidullahi daga cikin mutanen Aliyu. Duba rijalux-dusi shafi na 120. Shamru binu Zijaushan kuma An-namazi As-shahrudi ya ce game da Shamru: "kuma ya kasance a yaqin siffin ya na cikin rundunar Amirul mu'mina" Duba Mustadrakat ilmi rijalil hadith tarjama ta 6899.
WANI IRIN MATAKI MUSULMI ZAI XAUKA A IRIN WANNAN YANAYIN?
Babu shakka, babu tantama cewa kisan sayyidina Husaini – Allah Ya qara masa yarda ya na daga cikin manyan musibu da ya sami musulmai, domin babu wani xan 'yar annabi a bayan qasa sai shi, kuma an kashe shi ne bisa zalunci –Allah Ya qara masa yarda da shi da iyalan gidansa – kuma kisan shi idan aka yi la'akari da musulmai da su ke doron qasa musiba ce, amma shi idan aka yi la'akari da shi shahada ce da xaukaka da qarin kusanci zuwa ga Allah, ta yadda Allah Ya zave shi domin lahira da aljannan ni'ima a madadin wannan Duniyar nan qazantacciya.
Mu burinmu shi ne ace ma bai fita zuwa Kufa ba, shi ya sa manya-manyan sahabbai su ka yi ta qoqarin hana shi tafiya Kufan, domin da wannan fitan ne azzaluman nan su ka samu dammar xaukan nauyin da ya fi qarfin wuyoyinsu, su ka she shi ya yi shahada abin zalunta. Saboda haka fasadi ya faru mai girma sakamakon wannan kisan da aka yi masa wanda ba'a tsammanin faruwar hakan idan da bai fita ba, sai dai da ya ke dukkanin al'amuran na Allah – maxaukakin sarki ne – duk abin da Allah maxaukakin sarki Ya qaddara to sai ya kasance ko da mutane ba su so ba.
Amma kuma ya kamata mu san cewa kisan Husaini bai fi kisan da aka yi wa annabawa ba. Haqiqa an kashe Annabi Yahaya – amincin Allah Ya tabbata a gare shi- kuma an gabatar da kansa a matsayin sadaki ga karuwa. Haka nan ma an kashe Annabi Zakariyya – amincin Allah Ya tabbata a gare shi- kamar haka nana aka kashe Umar da Usman da Aliyu – Allah Ya qara mu su yarda- waxannan kuma duk sun fi Husaini falala – Allah Ya qara musa yarda. Saboda haka ba ya halitta ga mutum don ya tuna kisan Husaini ya kama marin fuskarsa da yaga tufafinsa da makamancin haka, duk waxannan ayyukan hanannu ne, domin Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – ya ce: " wanda ya mari fuskarsa ya yaga wuyan rigarsa ba ya daga cikin mu" Duba sahihul Bukhari hadisi na 1294.
Kuma annabi –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi – ya ce: " Ni na barranta daga mai ihu da mai aske gashinta da mai yaga tufafinta (wato don faruwar wata musiba) " Duba sahihul Bukhari hadisi na 1296.
Kuma annabi –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi – ya ce: " Lallai mai kukan mutuwa ta na ihu, idan bat a tuba ba, to lallai za a sanya ma ta riga na qaranbau" Duba sahihu Muslim hadisi na 934.
Saboda haka wajibin musulmi idan irr-iren waxannan musibun su ka faru shi ne ya faxi abin da Allah maxaukaki ya yi umarni da shi a faxin Sa:
Ma'ana: "waxan da idan wata musiba ta same su sai su ce: daga Allah mu ke kuma gare Shi za mu koma" Suratul Baqara aya ta 156.
KARKASUWAR MUTANE GAME DA KISAN HUSAINI
Mutane sun kasu zuwa gida uku game da kisan Husaini;
Jama'a ta farko: su ne waxanda su ke cewa lallai an kashe Husaini bisa haqqi kuma shi wai tawaye ya yi wa shugaba, ya yi nufin raba kan musulmi. Su ka ce: ai Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi – ya ce:
Ma'ana: "Duk wanda ya zo ya same ku kun haxu akan biyayya ga wani jagora guda xaya kuma ya yi nufin ya raba kanku, to ku kashe shi ko wanene shi" sahihu Muslim.
Su ka ce: Husaini ya yi nufin raba jama'ar musulmi, manzon Allah – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi – kuma cewa ya yi :" ko wanene shi ku kashe shi" saboda haka su ka ce kisan shi ya yi daidai. Wannar ita ce maganar Nasibawa maqiya Husaini da babanshi–Allah Ya qara musu yarda-
Jama'a ta biyu ita ce wacce ta ce: shi ne shugaban da ya wajaba a yi wa xa'a, kuma ya wajaba a sallama ragamar jagoranci ne gare shi. Wannan shi ne ra'ayin 'yan shi'a.
Jama'a ta uku ita ce jama'ar ahlus-sunna wal jama'a: su cewa su ka yi: an kashe Husaini ne bisa zalunci kuma shahada ya yi kamar yadda Annabi –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
« الحسن والحسين سيدا شباب أهل الجنة ».
Ma'ana:"Alhasan da Husaini shugabanni ne guda biyu na samarin gidan aljanna". Kuma shi Husaini ya yi yunqurin ya dawo gida ko kuma ya tafi wurin Yazidu a Sham, sai mutanen Kufa su ka hana shi, su ka ce sai dai ya tafi wurin Ubaidullahi xan Ziyad a matsayin fursunan yaqi.
Shi ya sa shaikhul Isalam ibnu Taimiyya a lokacin da ya ke bayanin matsaya ta ahlus-sunna game da kisan Husaini ya ce:
فلما قتل الحسين بن علي - رضي الله عنهما - يوم عاشوراء قتلته الطائفة الظالمة الباغية، وأكرم الله الحسين بالشهادة، كما أكرم بها من أكرم من أهل بيته. أكرم بها حمزة وجعفر، وأباه عليا، وغيرهم، وكانت شهادته مما رفع الله بها منزلته، وأعلى درجته، فإنه هو وأخوه الحسن سيدا شباب أهل الجنة، والمنازل العالية لا تنال إلا بالبلاء، كما قال النبي - صلى الله عليه وسلم - «لما سئل: أي الناس أشد بلاء فقال: الأنبياء ثم الصالحون ثم الأمثل فالأمثل يبتلى الرجل على حسب دينه، فإن كان في دينه صلابة زيد في بلائه وإن كان في دينه رقة خفف عنه، ولا يزال البلاء بالمؤمن حتى يمشي على الأرض وليس عليه خطيئة» . رواه الترمذي وغيره.
فكان الحسن والحسين قد سبق لهما من الله تعالى ما سبق، من المنزلة العالية، ولم يكن قد حصل لهما من البلاء ما حصل لسلفهما الطيب، فإنهما ولدا في عز الإسلام، وتربيا في عز وكرامة، والمسلمون يعظمونهما ويكرمونهما... إلخ الفتاوى الكبرى لابن تيمية (1/ 196)
Ma'ana: yayin da aka kashe Husaini xan Aliyu xan Abu Xalib a ranar Ashura, waxanda su ka kashe shi jama'a ne azzalumai masu wuce iyaka. Allah Ya xaukaka Husaini da mutuwar shahada kamar yadda Ya xaukaki iyalan gidansu da ita. Ya karrama Hamza da ita, da Ja'afar da mahaifin Husaini wato Aliyu da sauransu. Kuma shahadarshi ta kasance daga cikin abin da Allah Ya qara xaukaka matsayinsa da ita, Ya xaukaka darajarsa, domin da shi da xan uwansa Alhasan su ne shugabannin samarin Aljanna. Manya-manyan maqamai kuwa ba a samun su sai da jarrabawa kamar yadda Annabi –tsara da amincin Allah- ya ce yayin da aka tambaye shi: aka ce: wanene daga cikin mutane ya fiskantar jarrabawa? Sai ya ce: "annabawa, sa'annan salihai sa'annan sai waxanda su ka fi nagarta sa'annan sai na biye da su, akan jarrabi bawa ne gwargwadon imaninshi, idan ya kasance mai qarfi a cikin addininsa sai a qara jarraban sa, idan kuma ya kasance mai sassauci ne shi a cikin addini sai a sassuta masa jarrabawa, mumini ba zai gushe baa na jarrabansa har sai ya wayi gari ya na tafiya a bayan qasa alhali ba shi da komai na zunubi. Tirmidhi da wanin sa ne su ka ruwaito shi.
Saboda haka Alhasan da Husaini matsayi maxaukaki ya riga ya gabata gare su daga Allah….an haife su a cikin izza ta Musulunci kuma sun tarbiyyantu a cikin izza da karama. Kuma musulmai su na qaunar su su na girmama su…. (Alfatawa alkubra na Ibnu Taimiyya 1\196)
WASU BIDI'O'I GUDA BIYU DA AKA QIRQIRA A MUNASABAR KISAN HUSAIN
Shekhul islam Ibnu Taimiyya ya ce: bayan kisan Husaini mutane sun qirqiri wasu bidi'o'i guda biyu;
Ta farko: bidi'ar nuna baqin ciki da koke- koke tare da marin fusaku da ife-ife zama cikin qishi da waqe-waqen nuna baqin ciki da a ranar Ashura da abin da duk waxannan abubuwan ke kaiwa zuwa gare shi na zagin magabata da tsine mu su da xaura laifi aka wanda bai jib a bai gani ba don dai kawai a samu qofar zagin manyan sahabbai magabata a cikin wannan addinin. Sai a riqa karanta labaru na da mafi yawan su qarairayi ne game faxuwar Husaini, kuma manufar masu yin haka ba komai ba ne face buxe qofar fitina da rarrbuwar kan al'umma, in bah aka ba ina fa'idar mai maita irin wannan duk shekara tare da zubar da jinni da kambama abin da ya wuce da ratayuwa da shi da manne wa qabubura.
Bidi'a ta biyu ita ce bidi'ar farin ciki da murna da rarraba alewa da yalwata wa iyali idan ranar da aka kashe Husaini ya zagayo. Kufa ta kasance gari da acikin ta akwai nau'uka biyu duk; masu taimakon ahlul baiti, wanda jagoransu shi ne Malmukhtar bin Abi Ubaid wannan wanda ya yi da'awar annabta maqaryacin. Da wasu mutanen kuma maqiya ahlul baiti ne daga cikin su akwai Hajaj binu Yusuf At-thaqfi, ba'a vata bidi'a da wata bidi'ar, sai dai a yi raddin bidi'a a rusa ta da sunnar Annabi –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi – wacce ta ke dacewa da faxin Allah – maxaukakin sarki - :
[الذين إذا أصابتهم مصيبة قالوا إنا لله وإنا إليه راجعون] {البقر ة: 156}.
Ma'ana: "Waxanda idan wata musiba ta same su, sai su ce: daga Allah mu ke kuma gare Shi za mu koma" Suratul Baqara aya ta 156. Duba Minhajus-sunna 5\554-555.
Alhadu lillahi rabbil alamin. Allah Ya yi daxin tsira ga Annabinmu sallallahu alaihi wasallam da alayensa da sahabbansa da waxanda su ka bi tafarkinsu har zuwa ranar sakamako.
Dahiru Jibril Dukku.