المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : Muhimmancin huxubar juma'a a musulunci


طاهر جبريل دكو
_22 _August _2015هـ الموافق 22-08-2015م, 09:36 PM
MUHIMMANCIN HUXUBAR JUMA'A A MUSULUNCI
(أهمية خطبة الجمعة في الإسلام)

NA
ASH-SHAIKH ABDULMUHSIN AL-BBAD

TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA



بسم الله الرحمن الرحيم
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Allah ya yi qarin salati da sallama da albarka ga ManzonSa annabinmu Muhammadu xan Abdullahi da iyalanSa, da sahabbanSa, da duk wanda yabi shi.
Bayan haka;
Lallai sha'anin huxubar juma'a a musulunci yana da girma, kuma tana da muhimmancin gaske, fa'idarta kuma tana da girma, amfaninta kuma abu ne mai gamewa, Kuma muhimmancin nata yana bayyana ta waxannan fiskokin;
Na xaya: Lallai yana daga cikin sharruxan sallar juma'a huxubobi guda biyu su rigaye ta, Saboda yin huxuba a ranar juma'a wajibi ne, zuwa da ita kuma gabanin sallah abu ne na dole.
Na biyu: Lallai yinin juma'a yinin idi ne na sati, ita kuma huxubar; huxubar idin sati ne da take maimaituwa a duk bayan kwanaki guda bakwai (sati), Kuma yana daga cikin dalilan haka; Faxin Annabi (صلى الله عليه وسلم):
«قَدِ اجْتَمَعَ فِي يَوْمِكُمْ هَذَا عِيدَانِ، فَمَنْ شَاءَ أَجْزَأَهُ مِنَ الْجُمُعَةِ، وَإِنَّا مُجَمِّعُونَ».
Ma'ana: "Lallai idi guda biyu sun haxu a cikin yininku wannan, Duk wanda ya so, to idi ya isar masa ba sai ya je sallar juma'a ba, Amma mu za mu yi juma'a", [Abu-Dawud ya rawaito shi, lamba: 1073, da isnadi hasan, daga Abu-Hurairah].
Kuma ya zo a cikin [SahihulBukhariy, lamba: 5572] daga Abiy-Ubaid ('yantaccen bawan Ibnu-Azhar) yace:
(شَهِدْتُ العِيدَ مَعَ عُثْمَانَ بْنِ عَفَّانَ، فَكَانَ ذَلِكَ يَوْمَ الجُمُعَةِ، فَصَلَّى قَبْلَ الخُطْبَةِ، ثُمَّ خَطَبَ فَقَالَ: «يَا أَيُّهَا النَّاسُ، إِنَّ هَذَا يَوْمٌ قَدِ اجْتَمَعَ لَكُمْ فِيهِ عِيدَانِ، فَمَنْ أَحَبَّ أَنْ يَنْتَظِرَ الجُمُعَةَ مِنْ أَهْلِ العَوَالِي فَلْيَنْتَظِرْ، وَمَنْ أَحَبَّ أَنْ يَرْجِعَ فَقَدْ أَذِنْتُ لَهُ».
Ma'ana: "Na halarci sallar idi tare da khalifah Usman, hakan kuma ya kasance a ranar juma'a, Sai yayi sallar idin gabanin yayi huxuba, sa'annan ya yi huxuba, yace: Ya ku mutane! Lallai wannan yini ne da idi guda biyu suka haxu muku a cikinsa, Duk wanda ya so, ya jira sallar juma'a daga cikin mutanen unguwar awali to ya jira, Wanda kuma ya so ya koma to nayi masa izini".
Ya zo a cikin [Sunan Ibnu-Majah, lamab: 1098, da isnadi hasan ligairihi] daga Abdullahi xan Abbas, daga Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
«إِنَّ هَذَا يَوْمُ عِيدٍ، جَعَلَهُ اللَّهُ لِلْمُسْلِمِينَ، فَمَنْ جَاءَ إِلَى الْجُمُعَةِ فَلْيَغْتَسِلْ، وَإِنْ كَانَ طِيبٌ فَلْيَمَسَّ مِنْهُ، وَعَلَيْكُمْ بِالسِّوَاكِ».
Ma'ana: "Lallai wannan ranar idi ne da Allah ya sanya shi, Duk wanda zai zo zuwa ga juma'a to ya yi wanka, idan kuma akwai turare to ya shafa wani abu daga cikinsa, kuam ina horonku da yi aswaki".
Na uku: Lallai halartar masallaci don yin sallar juma'a da sauraron huxubobi guda biyu gabanin haka wajibi ne, saboda faxin Allah (mabuwayi da xaukaka):
{يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا نُودِيَ لِلصَّلاَةِ مِنْ يَوْمِ الجُمُعَةِ، فَاسْعَوْا إِلَى ذِكْرِ اللَّهِ وَذَرُوا البَيْعَ، ذَلِكُمْ خَيْرٌ لَكُمْ إِنْ كُنْتُمْ تَعْلَمُونَ} [الجمعة: 9].
Ma'ana: "Ya ku waxanda suka yi imani idan aka yi kiran sallah a ranar juma'a, to sai ku taho zuwa ga ambaton Allah, kuma ku bar kasuwanci, Yin haka shi yafi alkhairi a gare ku in kun kasance kun sani", [Jumu'a; 9].
Ita wannan itace huxubar wani abinda tafiya zuwa gare shi yake wajibi, savanin wassu huxubobin waxanda ba na jumma'a ba, waxanda halartarsu ba wajibi ba ne, haka kuma sauraronsu ba dole ba ne.
Na huxu: Lallai halin musulmi a lokacin sauraron huxubar juma'a kamar halinsa ne, a lokacin yin sallah; ba zai riqa magana ko yin magana da wani ko yin wani aiki da zai shagaltar da shi ga barin ji ko sauraron huxubar ba, Yana cikin dalilan haka; Faxinsa (صلى الله عليه وسلم):
"إِذَا قُلْتَ لِصَاحِبِكَ يَوْمَ الجُمُعَةِ: أَنْصِتْ، وَالإِمَامُ يَخْطُبُ، فَقَدْ لَغَوْتَ".
Ma'ana: "Idan kace wa abokinka a ranar juma'a: Ka yi shiru, alhalin limami yana yin huxuba, to lallai ka yi wargi", [Bukhariy ya ruwaito shi, lamba: 934, da Muslim , lamba: 1965]. Da kuma faxinsa (صلى الله عليه وسلم):
«مَنْ تَوَضَّأَ فَأَحْسَنَ الْوُضُوءَ، ثُمَّ أَتَى الْجُمُعَةَ، فَاسْتَمَعَ وَأَنْصَتَ، غُفِرَ لَهُ مَا بَيْنَهُ وَبَيْنَ الْجُمُعَةِ، وَزِيَادَةُ ثَلَاثَةِ أَيَّامٍ، وَمَنْ مَسَّ الْحَصَى فَقَدْ لَغَا».
Ma'ana: "Duk wanda ya yi alwala sai ya kyautata alwalar, sa'annan ya zo juma'a sai ya saurara ya kuma yi tsiru, an gafarta masa abinda ke tsakaninsa da tsakanin juma'a, da qarin kwanaki guda uku. Duk wanda kuma ya tava tsakuwa to lallai ya yi wargi", [Muslim ya rawaito shi, lamba: 1988].
Amma muhimmancin huxuba dangane da limami mai yinta to ya kasance ne saboda halartarta wajibi ne, haka kuma sauraronta, da kuma saboda aikata hakan yana neman mai huxubar ya bada cikakkiyar himmatuwa, da kula na musamman da huxubarsa, sai hakan ya sanya shi ya yi iya qoqarinsa wajen tanadar huxubar, irin tanadar da zai tava ko-ina na maudu'in huxubar, ba kuma tare da ya tsawaita ba, daxin daxawa kuma ana son mai yin huxuba ya rinqa jin cewa huxuba tana da gamammen amfani, da kuma lada ko sakayya mai girma, wannan kuma saboda faxinsa (صلى الله عليه وسلم):
"مَنْ دَعَا إِلَى هُدًى كَانَ لَهُ مِنَ الْأَجْرِ مِثْلُ أُجُورِ مَنْ تَبِعَهُ، لَا يُنْقِصُ ذَلِكَ مِنْ أُجُورِهِمْ شَيْئًا، وَمَنْ دَعَا إِلَى ضَلَالَةٍ، كَانَ عَلَيْهِ مِنَ الْإِثْمِ مِثْلُ آثَامِ مَنْ تَبِعَهُ، لَا يُنْقِصُ ذَلِكَ مِنْ آثَامِهِمْ شَيْئًا".
Ma'ana: "Duk wanda ya yi kira zuwa ga wata shiriya to lallai yana da lada kwatankwancin ladan waxanda suka bi shi, kuma hakan ba zai tauye komai daga ladansu ba. Kuma duk wanda ya yi kira zuwa ga wata vata to yana da zunubi akansa kwatankwacin zunuban waxanda suka bi shi; kuma hakan ba zai tauye komai daga zunubansu ba", [Muslim ya rawaito shi, lamba: 6804, daga Abu-Hurairah (رضي الله عنه)].
Kuma ya dace huxubar ta zama a rubuce, wannan kuma saboda rubuta ta zai tattara duk abinda yake waste na wannan maudu'in, kuma shi zai haifar da samun nitsuwa wajen cewa huxubar ta samu sifa ta gamewa, tare da kuvuta daga kubcewan wassu daga cikin ma'anoni masu muhimmanci, ko dalilan da a lokacin huxubar za su qi zuwa a kwakwalwarsa; idan har limamin ya yi huxubar daga kansa; ba daga abinda ya rubuta ba.
Kuma yana da muhimmanci sosai, mai yin huxuba ya kula wajen koro dalilai, daga littafin Allah (alqur'ani), da hadisai, da maganganun magabata, tare da komawansa (limami) izuwa ga littatafan da suka haxa ko tattara, maganganun salaf (magabata) da suke magana akan maudu'ai da yawa, musamman littatafan baya-baya, waxanda suke fitar da waxannan maganganun daga littatafa masu girma, kamar littafin siyaru a'alamu annubala'i na Az-zahabiy, da littafin Tarikhu bagdaad na Alkhaxib Albagdadiy, da wassunsu.
Kuma ita huxubar juma'a tana daidai da darasin sati; wanda halartarsa wajibi ne akan kowani musulmi, kuma musulmi ya kan fahimci addininsa a cikinta; sai ya san aqidarsa, da kuma hukunce-hukncen shari'a mabanbanta. Karantar da mutane hakan kuma shine shiriyar Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) , da kuma aikin sahabbansa, a bayansa (Allah ya qara yarda a gare su).
Kuma yana daga cikin karantarwar Annabi (صلى الله عليه وسلم) ga mutane, da ta sahabbansa, al'amuran addininsu mabanbanta a cikin huxubobin juma'a, Misalan da suke tafe:
(1) Hadisin Abdullahi xan Umar (رضي الله عنهما)

????????
????????
Zan karisa, da izinin Allah
????????
????????