تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : Halin magabatan kwarai a ramadhana (حال السلف في رمضان)


طاهر جبريل دكو
_11 _June _2015هـ الموافق 11-06-2015م, 02:15 PM
HALIN MAGABATAN KWARAI A RAMADHANA (حال السلف في رمضان)
HALIN MAGABATAN KWARAI
A "WATAN AZUMI" (RAMADHANA)
-حال السلف في رمضان-


TANADAR
VANGAREN ILIMI NA "MADARUL WAXAN"


FASSARAR
ABUBAKAR HAMZA


بسم الله الرحمن الرحيم
Xan'uwana musulmi, … da 'yar'uwata musulma….
Amincin Allah da rahamarsa da albarkokinsa su tabbata a gare ku…. Bayan haka:
Ina tura muku wannan wasiqar, wacce aka qunsa mata bege da kuma gaishe-gaishe masu qamshi, zuwa gare ku, daga zuciyar da ta take sonku don Allah, Kuma Allah muke roqon ya haxa mu a gidan karramawarsa, wacce take matattara ga rahmarsa.
A sakamakon shigowan watan azumi Nake gabatar muku da taqaitacciyar kyauta. Ina fatan ba za ku raina ta ba, sannan kuma za ku karve ta da yalwataccen zuciya. Tare da yi mini nasiha. Allah ta'alah ya kiyaye ku ya baku kariya.
TA YAYA ZA MU FISKANCI WATAN AZUMI MAI ALBARKA?
Allah ta'alah yana cewa:
(شَهْرُ رَمَضانَ الَّذِي أُنْزِلَ فِيهِ الْقُرْآنُ هُدىً لِلنَّاسِ وَبَيِّناتٍ مِنَ الْهُدى وَالْفُرْقانِ) [البقرة: 185ٍ]
Ma'ana: "Watan ramadana da aka sauqar da alqur'ani a cikinsa, shiriya ne ga mutane, da kuma bayanan shiriya da kuma rarrabewa tsakanin gaskiya daga qarya" [185].
Xan'uwana mai karamci:
Lallai Allah ta'alah ya kevance watan ramadhana akan sauran watannin (guda goma sha biyu) da wassu kevantattun abubuwa, da tarin falaloli masu yawa, Daga cikinsu:
· Warin da ke fita daga bakin mai azumi daxinsa a wajen Allah fiye da qamshin turare al-miski.
· Mala'iku su kan yi ta neman gafara ga masu azumi har zuwa lokacin da za su yi buxa baki.
· A watan azumi ana sanya shexanu a cikin sarqoqi da mari.
· Ana bubbuxe qofofin aljanna a watan azumi, kuma a rurrufe qofofin wuta.
· A cikin watan ramadhana akwai wani dare –lailatul qadari- wanda yafi watanni dubu alheri, Mutumin da aka haramta masa samun alherin wannan daren lallai an haramta masa dukkan alheri gabaxayansa.
· Ana gafarta wa masu azumi a daren qarshe na watan ramadhana.
· Allah yana da bayin da yake 'yantar da su daga faxawa wuta, Wannan kuma yakan kasance a cikin kowani dare daga cikin dararen ramadhana.
Ya kai xan'uwana mai karamci:
Watan da ya kevanta da waxannan abubuwan na falaloli, Da wani abu ne ya kamata mu fiskance shi?
Shin da shagalta da yin wargi ko kwanan zaune, ko kuma muyi ta yin guna-guni kan shigowansa, tare da bayyanar da jin nauyinsa akanmu? Allah ya tsare mu daga waxannan gabaxaya.
A'a… Lallai bawan Allah; nagari ya kan fiskanci shigan wannan watan ne kawai da yin kyakkyawiyar tuba, da kuma qulla azama ta gaskiya kan morar wannan watan, ta hanyar cike lokatansa da aikata aiyuka nagari. Muna roqon Allah ya taimake mu wajen kyautata masa bauta.
XAN'UWANA MAI KARAMCI, GA WASSU AIYUKA NAGARI WAXANDA SUKE DA GIRMA A CIKIN WATAN AZUMI (RAMADHANA):
1- YIN AZUMI: Saboda Annabi (r) ya ce:
"كُلُّ عَمَلِ ابْنِ آدَمَ لَهُ، الْحَسَنَةُ بِعَشْرِ أَمْثَالِهَا إِلَى سَبْعِ مِائَةِ ضِعْف، يَقُولُ اللَّهُ U: إِلَّا الصّيام،
فَإِنَّهُ لِي، وَأَنَا أَجْزِي بِهِ، تَرَكَ شَهْوَتَهُ وَطَعَامَهُ وَشَرَابَهُ مِنْ أَجْلِي، لِلــــــــــــصَّائِمِ فَرْحَتَانِ: فَــــرْحَةٌ عِنْدَ
فِطْرِهِ، وَفَرْحَةٌ عِنْدَ لِقَاءِ رَبِّهِ، وَلَخُلُوفُ فَمِ الصَّائِمِ أَطْيَبُ عِنْدَ اللَّهِ مِنْ رِيحِ الْمِسْكِ".
Ma'ana: "Dukkan aiyukan xan adam nasa ne, kyakkyawa guda xaya za a ninnika masa zuwa kwatankwacinsa sau bakwai, zuwa ninki xari bakwai. Allah mabuwayi da xaukaka yana cewa: Saidai azumi, lallai shi kam nawa ne, kuma nine zan yi sakayya akansa, ya bar sha'awarsa da abincinsa da abin shansa don Ni. Mai azumi yana da nau'ukan farin ciki guda biyu, waxanda ransa ke faranta da su, farin ciki xaya a lokacin karya azuminsa, da wani farin cikin a lokacin ganawarsa da Ubagijinsa. Kuma warin bakin mai azumi yafi daxi a wajen Allah fiye da qamshin turaren al-miski". [Bukhariy da Muslim suka fitar da hadisin]. Ya kuma ce:
"".
Ma'ana: "Wanda yayi azumin ramadhana yana mai imani da neman lada an gafarta masa abinda ya gabata daga zunubansa". [Bukhariy da Muslim suka fitar da hadisin].
Kuma babu shakka lallai wannan lada mai yawa ba wai yana kasancewa ne ga wanda ya hanu daga ci ko sha kaxai ba ne, saidai Annabi (r) yace:
"".
Ma'ana: "Wanda bai bar zancen qarya, da aiki da shi ba, to Allah bashi da buqatar ya bar cin abincinsa da abin shansa". [Bukhariy ya fitar da hadisin]. Kuma Annabi (r) yana cewa:
"".
Ma'ana: "Azumi garkuwa ne, Idan yinin azumin xayanku ya zo to kada ya yi batsa, kuma kada ya yi fasiqanci, kada ya yi wauta, Idan kuma wani ya zage shi to sai y ace: Ni mutum ne da nake azumi". [Bukhariy da Muslim suka fitar da hadisin].
2- SALLAR DARE: Saboda Annabi (r) ya ce:

Ma'ana: "Wanda ya yi tsayuwar ramadhana –sallar dare- yana mai imani da neman lada an gafarta masa abinda ya gabata daga zunubansa". [Bukhariy da Muslim suka fitar da hadisin].
().
Ma'ana: "Bayin mai rahama sune waxanda suke tafiya a bayan qasa da nitsuwa. Kuma idan masu wauta suka yi musu Magana sai su faxi: aminci. Kuma sune waxanda suke kwana ga Ubangijinsu cikin sujjada da tsayuwa" [Alfurqaan: 63-64]. Kuma lallai yin sallar dare (qiyamu allaili) xabi'a ce da Annabi (r) da sahabbansa suka saba da ta, A'ishah (r) tana cewa:
"".
Ma'ana: "Kada ka bar yin sallar dare, saboda Manzon Allah -r- ya kasance baya barin yinsa, Kuma ya kasance idan ya yi rashin lafiya ko kasala to sai ya yi sallar a zaune". Kuma Umar xan Al-khaxxab (t) ya kasance ya kan yi sallar raka'oin da ya ga dama a cikin dare, har zuwa lokacin da dare zai raba biyu, to sai ya tashi iyalansa don su yi sallah, sa'annan yace musu: Sallah! Sallah!! yana mai karanta musu:

Ma'ana: "Kuma ka umurci iyalanka da yin sallah".


3- YIN SADAKA: Saboda Annabi (r) ya kasance yafi dukkan mutane yin kyauta, kuma kasance yafi yin kyautar tasa ne a cikin watan ramadana,