تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : Ma'anonin sunayen allah madauakin sarki


طاهر جبريل دكو
_29 _April _2015هـ الموافق 29-04-2015م, 05:06 PM
الــلــه
Allah.
Wannan shi ne tushe na dukkanin sunayen Allah, wanda dukkanin sunayen Allah su ke komawa gare shi kuma su ke dangantuwa gare shi, ya kunshi ma'anoninsu baki daya a dunkule. Ma'anar "Allahu" shi ne: abin bauta, wanda Ya cancanci a bauta maSa Shi kadai saboda kamalarSa ta kowace fiska. Kuma lallai wannan suna shi ne sunan da ya zo a cikin Alkur'ani da adadi mafi yawa, domin Allah Ya ambaci kanSa da wannan suna a cikin Alkur'ani a sama da wurare 2200, kuma wannan suna shi ne sunan da mafi yawan zikirori su ka rataya da shi, kamar su hamdala, tasbihi, hailala, isti'aza, haukala, hasbala, basmala da dai sauransu, saboda falalolin da su ka tattara ga wannan suna har wasu malamai na cewa shi ne sunan Allah mafi girma wanda ba a rokonSa wani abu da shi face Ya biya bukatar mai rokon (wato; ismul-lahil a'azam). Kuma sunan da ke dangantuwa da shi a cikin sunayen bayi shi ne mafi kyawun sunaye wato; Abdullahi.

طاهر جبريل دكو
_29 _April _2015هـ الموافق 29-04-2015م, 05:11 PM
الإلـــه
Al'ilahu
wanda ya ke nufin abin bauta bisa cancanta, daya ne daga cikin sunayen Allah Madaukakin sarki, wanda ya ke kunshe da ma'anar kadaita Allah da dukkan nau'ukan bauta (wato; uluhiyya), wannan suna tushensa daya ne da ((Allahu)) kuma sun yi tarayya a cikin dunkulalliyar ma'ana, duk da cewa kowannensu ya na dauke da wata ma'ana ta musamman in har za a fadada bayani.

طاهر جبريل دكو
_29 _April _2015هـ الموافق 29-04-2015م, 05:25 PM
الــرحـــــمــن
((Ar-Rahmanu)) Mai Rahama
ya na nufin mai gamammiyar rahama. Wannan sunan ya maimaitu a cikin Alkur'ani kusan sau 57, kuma ya na nuni zuwa ga abubuwa kamar haka;



Sifantuwar Allah Madaukakin sarki da sifar rahama.
Rahamar Allah ta game dukkan komai, mutum, aljani da dabba, musulmi da kafiri mai rai da maras rai.
Yalwar wannan rahamar da nau'antuwar ta, watau ta kunshi nau'uka dabam daban kamar; halittar bayi, azurta su da dukkanin bukatunsu na ci da sha da sutura da lafiya da kwanciyar hankali, haka nan ma da rarrabe musu tsakanin gaskiya da bata.
Wadatuwar bayi daga bukatuwa zuwa ga wanin Allah, saboda Shi ne kadai Ya sifantu da sifa ta rahama gamammiya yalwatacciya kuma Ya ke da ikon sadar da ita ga wanda Ya nufa.
Wannan suna ya na daga cikin sunayen Allah wadanda da Annabi -tsira da aminci su tabbata a gare shi- ya kira su da (Ismu Allahil a'azam) wadanda idan aka roki Allah da su Ya ke amsawa. Saboda haka bawa ya rika tawassuli zuwa ga Allah da wannan suna idan zai yi addu'a, misali ya ce: ((Ya Rahmanu irhamni)) ma'ana ya Mai rahama, Ka rahamshe ni.

Ya wajaba bawa ya rika tausaya wa bayin Allah domin shi ma Allah Ya gama shi da rahamarSa, saboda masu jinkan wasu Allah ma Ya na jin kan su.