المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : Mace za ta iya yin limanci ?


طاهر جبريل دكو
_18 _April _2015هـ الموافق 18-04-2015م, 12:54 AM
MACE ZA TA IYA YIN LIMANCI ?


Tambaya :
Malam a kaset din malam Jafar na ji ya halatta mace tai wa mata yan'uwanta limanci toh in ramadan ya zo na kan tara mata na musu, dayake duk anguwan na dan fi su karatu, toh kusan anguwan ba malamin sunna ko daya sai 'yan bidi'a, shi ne suke nema na baso aya ko hadisi akan hakan mlm ataimakamin don Allah ?

Amsa :
To 'yar'uwa ina rokon Allah ya jikan malam Ja'afar, mu kuma ya kyautata namu karshen, ya halatta mace ta yiwa 'yan'uwanta mata limanci, saboda abin da aka rawaito cewa : Nana A'sha da Ummu Salama –Allah ya kara musu yarda- sun yiwa wasu mata limanci, Nawawy yana cewa wannan hadisin Baihaky ya rawaito shi a Sunan din shi, hakan nan Shafi'i a Musnad dinsa da sanadi mai kyau, Almajmu'u (4/187).
Haka nan an rawaito cewa Annabi s.a.w. ya sanyawa Ummu-waraka ladani, sannan ya umarce ta da ta yiwa matan gidansu limanci, kamar yadda Abu-dawud ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 491, kuma Albani ya kyautata shi.
Bisa dalilan da suka gabata za ki iya yiwa matan unguwarku limanci, tun da kin fi su karatu, Annabi s.aw. yana cewa: "Wanda ya fi iya karatun alqur'ani shi ne zai yi limanci" Muslim 1078.
Idan za ki yi musu limanci za ki tsaya ne a tsakiyarsu in suna da yawa, in kuma ita kadaice sai ta tsaya a damarki.
Allah ne mafi sani

Jamilu Zarewa
13\3\2015