المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : Muhimman fatawowi daga malam jamilu zarewa; da wanne zan fara sallar jam'i ko halartan matata da ta ke cikin halin nakuda


طاهر جبريل دكو
_11 _April _2015هـ الموافق 11-04-2015م, 06:51 PM
MATATA TANA NAKUDA, GA SHI KUMA AN TADA SALLAR JAM'I !

Tambaya:
Wani ne a office ana kiran shi a waya, matarshi na matsanancin hali na naquda, ana buqatarsa, ikon Allah kuma gashi an tada iqama za'a yi sallah sai wasu suka ce ya tafi wurin mara lfy. wasu kuma suka ce ya tsaya ya gama sallar, me ya kamata ya yi ?

Amsa :
To dan'uwa abin da yake daidai anan Shi ne : ya tafi wajan matarsa, saboda idan hakkin Allah da na bayi suka ci karo, akan gabatar da na bayi, saboda shi Allah mawadaci ne.
Sannan za ta iya hallaka idan ka bar ta ba ka je ba, sallar jam'i kuma akwai sabani akan wajabjinta, ga shi kuma za ka iya gamawa ka dawo kafin lokacinta ya fita, yana daga cikin ka'idojin sharia, duk abin da ake bukatarsa yanzu-yanzu akan gabatar da shi akan wanda za'a iya jinkirtawa, ko da bai kai shi daraja ba.

Allah ne mafi sani

Jamilu Zarewa
22\3\2015