طاهر جبريل دكو
_11 _April _2015هـ الموافق 11-04-2015م, 06:43 PM
RABON GADO (9)
Tambaya:
Wato malam mahaifinmu su ukune awaje mahaifinsu , mahaifin namu da kuma kannensa mata guda biyu, kaga su uku kenan, to shi maihaifinmu sai Allah yayi masa rasuwa shekaru biyar da suka wuce, ya bar mahaifinsa da kannan nan nasa mata guda biyu, to kwanannan kuma wata uku da suka wuce sai Allah ya yiwa shi wannan kaka namu rasuwa kafin yarasu sai yace a bamu wani gida saboda mahaifinmu bai gaje shi ba, muma kuma ba za mu gaje shi ba, to amma kuma wani malami yace min za mu gaji kakannamu saboda mahaifinmu kadai dansa namiji, sannan malam kakan na mu ya bar mata guda daya, malam zuciyata ta kasa nutsuwa ya abin yake, nagode Allah ya karama ilmi da takawa.
Amsa:
To dan'uwa ina rokon Allah ya amsa addu'arka, tabbas kuna da gadonsa, saboda 'ya'yan mamacin da matarsa, ba za su cinye dukkan dukiyar ba, sannan abin da ya ba ku yana raye ba zai hana ku cin gado ba, don haka, za'a raba dukiyar gida 24 a bawa kannen mahaifinku mata gida 16, matarsa kashi uku, ku kuma a baku ragowar.
Allah ne mafi sani
Jamilu Zarewa
23\3\2015