تسجيل الدخول

مشاهدة النسخة كاملة : Darusan da za'a amfana da su a cin zaben janar buhari


طاهر جبريل دكو
_11 _April _2015هـ الموافق 11-04-2015م, 06:40 PM
Jamilu Zarewa (https://www.facebook.com/n/?profile.php&id=100000342768425&aref=104910997&medium=email&mid=b84efd3G5af3a177562bG640d095G96Gf43a&bcode=1.1427833017.AblO35RPMEqpB-50&n_m=dukku111%40yahoo.com)
DARUSAN DA ZA'A AMFANA DA SU A CIN ZABEN JANAR BUHARI

Tabbas akwai muhimman darusa da za mu amfana da su, game da lashe zaben da Muhd Buhari ya yi, a 2015, ga wasu daga ciki :
1. Mulki Allah yake bada shi, in ban da haka da bai ci zabe ba, saboda kwace mulki a hannun mai shi da kamar wuya.

2. Gaskiya da rikon amana suna da mutukar muhimmanci a rayuwa, Janar Buhari bai mallaki abin da zai iya tsayawa KANSILA ba, amma saboda gaskiyarsa mutane sun tsabe shi kyauta a matsayin shugaban kasa.

3. Komai yana da ajalin da Allah ya sanya masa, ya tsaya takara har sau uku a baya bai samu nasara ba, amma sai yanzu a karo na hudu.

4. Zalunci ba ya dorewa, na dade ina jin cewa Goodluck ba zai ci wannan zaben ba, saboda a sunnar Allah azzalumi ba ya karko.
5. Muhimmancin komawa ga Allah, tabbas talakawa sum jima suna rokon Allah ya kawo musu canji, ga shi kuma yi amsa musu.

6. Siyasar Nigeria ta fara canzawa, a kasa a tsare, a raka, a jira, a fada din, da talakawa suka yi yana nuna yadda mutane suka san 'yancinsu.

7. Duk shugaban da yake bin maslahar kansa bai damu da ta talakawa ba, to zai iya rasa kujerarsa a lokacin da bai zata ba.

JAMILU ZAREWA 31/8/2015