المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : muhimman fatawowi daga malam Jamilu zarewa hukuncin jinin da ya ke zuwa wa mace a yayyanke


طاهر جبريل دكو
_30 _March _2015هـ الموافق 30-03-2015م, 12:58 AM
2:11am Feb 28
JINI YANA ZUWA MIN A YAYYANKE ! !

Tambaya :
Assalamu Alaiykumو Malam matata ta haihu sati biyu kenan, to Malam yanzu takan wuni Jini bai zoba sai da Daddare in ta kwanta sai Jinin yazo. To shin Malam za ta iya yin wanka/tsarki da safe tayi sallolin Azahar zuwa Isha'i ? Kokuma yaya zatayi? Nagode Allah Yaqara illimi mai albarka.

Amsa:
To dan'uwa a zance mafi inganci duk yinin da ta ga jini to yana daukar hukuncin jinin biki ne , haka ma tsarki yana daukar hukunce-hukuncen tsarki, ta yadda za ta yi wanka duk yinin da ba ta ga jini ba, Saidai idan yana yayyankewa kusa-kusa, to tana iya jinkirta wankan, sai ta hada sallolin da ba ta ga jini ba a lokutansu, saboda yin wanka a kowanne lokaci akwai wahala a ciki, kuma Allah yana cewa : "Bai sanya muku kunci a cikin addini ba" Suratu Hajj 78.

Allah ne mafi sani .

Don neman Karin bayani duba Almugni na Ibnu Khudaamah 1\214.

Jamilu Zarewa
22\2\2015