المساعد الشخصي الرقمي

مشاهدة النسخة كاملة : muhimman fatawowi daga malam Jamilu zarewa daga ina sahu ya ke farawa?


طاهر جبريل دكو
_30 _March _2015هـ الموافق 30-03-2015م, 12:56 AM
DAGA INA SAHU YAKE FARAWA ?

Tambaya :
Assalamu alaikum mal ya gida ya kuma aiki, mal don Allah innada tambaya mal sahun sallah kan ta dama za'a fara ne ko ta hagu.?

Amsa :
To dan'uwa sahun da yake bin liman zai fara ne daga bayan liman ma'ana a sanya liman a tsakiya, saboda fadin Annabi s.a.w. "Masu hankali daga cikinku, su bi bayana" kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 116. sannan da fadin Anas RA lokacin da yake bada labarin ziyarar da Annabi s.a.w. ya kai gidansu : " Sai muka tsaya ni da marayan a bayansa" kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta :694, daga nan kuma sai a cigaba da cika shi ta bangaren dama.
Haka nan ake so sahu na biyu shi ma ya kasance, ya fara daga tsakiya ya tafi zuwa dama, saboda fadin Bara'u dan Azib RA "Mun kasance idan muka yi sahu a bayan Annabi s.a.w. mu kan so mu kasance a damansa, ya fuskanto mu da fuskarsa " Muslim a hadisi mai lamba ta : 709.

Allah ne mafi sani

Jamilu Zarewa
21\2\2015